Sashe 11
A Duniyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Qarya kike,wallahi tallahi yarana dinma ba riqonsu kikeyi ba,koda basu taba gaya min ba amma na tabbatar ba irin riqon uwa da 'ya'yanta kike musu ba.....irin riqon da mukayi alqawarin zakiyi musu" Qaramar shewa tadan saki tana tafa hannuwanta hadi da qare masa kallo tsaf ido cikin ido "Dama waye yace maka uwar wani zata iya riqon dan wani tamkar nata?,au ashe bakaji abinda bahaushe ya fadi ba kenan,riqon uwar wani da dan wani ai sai Allah" Mamakinta ne ya qarasa kasheshi,ransa yakai qololuwar bacin da har ya mance da yara ma a wajen "Haka kika ce?,to bari kiji na gaya miki......muddin ba zaki riqe wadannan marayun ba saidai kisan inda dare yayi miki" Idanu ta fidda tana kallonsa cikin maqurar mamaki,wato ya fifita matsayin yaran a kanta kenan?,ta yaya zata ma zauna ta karbi wannan fifikon?,ya za'ayi ma tayi sake har yaga warginta haka?,a gaban yaran ya kafa mata irin wanna sharadin?,ai duk yadda taso ga son zama dashi ba zata karba irin wannan mulkin qarfa qarfan ba. Hannayenta ta sake hadawa ta tafa ta kuma riqe qugunta da kyau tana dubansa "Wallahi kaji na rantse bazan riqe su ba,har nakanma na gaji ai bamuyi abinda zanzo nayi kenan cikin gidan nan ba" "Tunda kuwa kikace haka saidai ki qara gaba" Gabanta yadan fadi,amma batajin zata bari ya gano lagonta "Hakan shi yafi sauqi,amma bazanje nayita zama da dakon aurenka ba,ka gayan meye matsayin tafiyar tawa idan na yita?" Ta kuma tambaya tana watsa hannuwa "Na sakeki saki biyu" "Innalillahi wa 'inna ilaihi raji'un" Me baban suna ya furta yana saka hannuwansa dukka biyu ya toshe kunnuwansa,sannan ya koma ya sulale yana zama tsakanin kujerun falon. "Tafi nono fari,sai me?,dadin abun ai ba kai kadai bane namiji" Ta qarasa fada tana ture kujerun dining din ta sauka a gaggauce zuwa dakinta gabanta yana wani irin bugawa da sauri da sauri. Daga su har abban ba wanda ya iya cewa komai,falon ya dauki shuru kawai sai motsinta daga can uwar daki tana hada kaya gami da sakin maganganu wanda basa iya jin ainihin me take fadi. Mintuna goma kacal ta fito janye da akwatunta da qaramin mayafi yafe a kafadarta. Daga inda yake ya daga rinannun idanunsa yana kallonta. Abba ya saketa ne saboda su,me yasa abban zai saketa saboda dalilinsu?. Fitowarta sai tayi masa kama da fitowar mahaifiyarsu sanda take shirin barin gidan mahaifinsu. Me yasa ake tafiya ne ana barinsu?,farinjini ne basu dashi ko kuwa?,ko wani maqalalle kuma boyayyen abune dasu?,me yasa iyaye mata basa tausayinsu saidai maza?. Baisan yaushe ya yanke wannan hukuncin ba,shidai ya tsinci kansa a gaban mama ne,cikin matuqar tashin hankali da karyar da muryar yake fadin "Don Allah mama kiyi haquri,kada ki tafi saboda mu......" "Na rantse da Allah zan zabga maka mari idan baka bani hanya ba,munafukan banza da wofi wadanda babu alkhairi sam a jikinsu sai masifa da balai nau'i nau'i,ai daya sakenin sai ku ya aureku,gaku nan gashi,kara da kiyashi daukan mara sani" Sai ta wuce abinta ta barshi da zafafan maganganun daya gaza mancewa dasu. "Dawo ka zaun me babban suna,waye yace maka ka bata haquri?,waye yace maka zan iya zama da ita bayan bata sonku?,ba zata iya zama daku ba?,ba zata iya haquri daku ba?......in sha Allah na muku alqawarin dawowa da mamanku nan da sati guda kacal" Maganar data Haifar da wani irin farinciki mara misali a zuciyar faruqee musaddiq harma da sadeeq din da baima mamansu musaddiq din farin sani ba. Yayin da me babban suna yake binsu kawai da idanuwa,don kunnuwansa da zuciyarsa harma da qwaqwalwarsa sunyi nisa qwarai da abinda ke wakana a falon. Jarin maganganun mutane masu tsananin dafi daya soma girma da jinsu yaketa aunawa. Kullum kwanan duniya wayewar gari zuwa faduwar rana sai yaci karo da wata mummunar kalma da zata zamewa zuciyarsa tabo wadda ta shafesu da mutuncinsu,duk kuma MAAMA itace sila,dama uwa tana iya zama silar bacin suna da rayuwar 'ya'yanta?. Tambayar da amsarta ta kasa samuwa a gareshi kenan,musamman lokacin da MARIYA mahaifiya ga faruqee da musaddiq ta dawo ainihin dakin aurenta da zummar riqe yaranta harma da marayun Allah MUHAMMAD DA ABUBAKAR SADDIQ *************** Faffadan tsakar gida ne ma'abocin yalwa da kuma tarin dakuna da zasu nuna maka yawan adadin mazauna gidan dake cikinsa. Tun daga qofar gida,zauruka guda biyu masu girma har zuwa farfajiyar gidan da wani filin tsakar gida da gidan ya mallaka zakasan cewa asalin ginin gidan anyi gine na masu wadata a wani qarni can baya daya shude. Duk kuwa canzawar siffar ginin zuwa zubin ginin daya dauki shekaru,amma yanayin yadda akayi zuba ginin da kyakkyawan tubali hakan ya hanashi muguwar lalacewa ko muzanta daga suffar kyau zuwa ta tsufa. Dakuna guda hudu manya manya gidan ya mallaka lailaye da siminti da tsakar gidan ya wadatu dashi da fulasta wadda ke nuna yau ta jima da samuwa a jikin ginin gidan. Kafin idanunka yakai ga duqurqusar matakalar bene dake qarshen qofar daki na hudu a jerin dakunan gidan. Rijiya ce da aka dan dagata kuma aka rufeta da murfi na langa langa. Idan ka sake kai dubanka kuma can zuwa sashen hannun hagu na gidan,bayan ka wuce bishiyar mangwaro data samu muhalli na dindin da Tsakiyar gidan,kai tsaye kana iya hangen qofar da tafi kama data makewaye,da kuma qofar babban kitchen na gidan daya hada kowa da kowa. Akwai gurabe daga jikin bangon gidan da zai sanyaka ka fahimci a baya akwai wasu shuke shuke da sukayi zamani daga bangwayen gidan,saidai yanzun babu ko wanne tsiro idan ka cire bishiyar dake a Tsakiyar wadda gushewarta ita din ba abu bane me sauqi. A tsaftace gidan yake ba laifi,wanda kusan gado ne da kuma asali da tsafta daya samo cikin gidan koda kuwa bayan gushewar me gidan da rasuwar mace daya cikin matan aure uku da ma gidan ya mallaka a lokacin rayuwarsa. Safiya ce sosai,kusan qarfe bakwai da rabi na safe agogo ya nuna a daidai lokacin. Kowacce qofa ta gidan a sakaye take,sai wata qofa guda daya qyaure ta ya banbanta da sauran qyamaren gidan kafataninsu. Ba zaka gama fahimtar yadda banbancin yake bai tsaya daga qyauren kawai ba.....aah,har sai ka samu nasarar kutsa kanka cikin ainihin falon dake hade da uwar daki kaman kowanne daki na gidan. Kyawawan labulaye ne da aka yiwa dakin qawanya dasu ruwan toka wadanda sukayi daidai da sofas guda biyu dukkansu 3sitter da aka gewaye falon dasu hakanan suka dace da lallausan daddumar da aka shimfida a tsakaninsu qirar qasar turkiya. Akwai lausasan pillow guda hudu manya dake zube a qasa dukkaninsu kala daya da labule zuwa kujerun. Daga bangon dakin ta fuskar hagu kuwa,bango ne da yasha wallpaper me kyau aka kuma yiwa TV plasma me matsakaicin girma da reciever dinta mazauni na daban. Gaba kadan dasu 'yar madaidaiciyar AC ce ta tsaye wadda ke amfani da hasken rana da aka yiwa kafatanin dakin wayarin dinsa. Wannan ya sanya koda babu wuta ko ina cikin gidan,koda babu wuta ko ina a unguwar wannan dakin baya rabo da ita. Akwai freezer madaidaiciya itama data dace da tsarin dakin,sai manyan frames masu daukan hankali biyu masu sunayen Allah da ayoyin tsari,biyu kuma masu dauke da zanen nature me kyau. Sassanyan qamshin turaren icce dake zama a daki ya kama labulaye da kujeru da kyau falon yake fiddawa ya zarce kuma har uwar dakin,wanda ya cakuda da qamshin turaren daya zamewa mazauniyar dakin lazim amfani dasu. Labulen bedroom din aka daga,sannan kuma a hankali ta bayyana hannunta riqe da hijabin yarinyar dake tsaye cikin uniform. Matashiya ce wadda duka duka a qiyasce shekarunta ba zasu haura ashirin da biyu ke takowa a kasalance. *_TURQASHI_* *_BIGI SAI BIGI_* *_BABBAN GORO SAI MAGOGIN QARFE_* *_TASTED AND TRUSTED_* *_TASTED AND TRUSTED_* *_TASTED AND TRUSTED_* *_Kina da burin samun ingantaccen TURAREN WUTA me TSANANIN KAMA GURI?_* *_TURAREN WUTAR DA ZAKI SANYAWA DAKI AMMA HATTA DA LABULAYE KAYAN SAWAN DAKE SAQALE A DAKIN SU KAMA DA QAMSHI?_* *_TURAREN WUTAR DA KUJERUNKI ZASU KAMA QAMSHI DARAM?_* *_KI BANKADA LABULAYENKI KIJI SASSANYAN QAMSHI?_* *QAMSHI IYA QAMSHI 24HR* *HUMRA ME TSAYAWA A ZUCIYAR ME GIDA* *NASAN ZAKI TAMBAYI KANKI A INA ZAN SAMU WANNAN?* *INCENSE BY KABO DAUGHTER* *_tayi muku tanadin abubuwa da yawa irinsu_* Khumra Turaren wuta Kulaccam Lablab Oil perfumes Original musk tahara Multipurpose spray *karki kuskura kada kiyi ganganci ayi babu ke,kai tsaye tuntubeta ta wannan number* 08032119803 Ko ki lalubeta ta nan *Instagram handle_incense by kabo daughter* *Facebook_kabo daughter* *Twitter_kabo daughter* __________________________ *SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI* *_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_* *_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_* *_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_* *_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_* *ZAFAFA BIYAR* *_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_* *Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU* _TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_ _QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_ _K'ALBIM Mamuhghee_ _AJIYA A DUHU Billynabdul_ _DUNIYATA Huguma_ _Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_ *hudu 2k* *uku 1500* *Biyu 1k* *Daya 500* _YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_ *09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA* *IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA* *09033181070* *BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK* *ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171* *ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI* *AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA* 89825722 Nousaiba lawali maradi 1000cf *_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_* *_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_* *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* PAGE 13 ___________________________ *_CIKIN DUBU DABAN TAKE_* *_TABBAS AKWAI TURARE AKWAI MUNA TURARE_* *_NA GWADA NA GANI_* *_YA SUBHANALLAHI_* *_QAMSHI NA TASHIN KAN ME GIDA_* *_QAMSHIN DAKE DAGAWA KISHIYA HANKALI_* *_NATACCEN QAMSHI DAKE KAMA GURI DARAM_* *_WANNE GANGANCI NE YA SAKAKI TSAIWA SANYA?_* *_ME KIKE JIRA?_* *WANNAN DIN GUARANTEE NE FA* *TASTED AND TRUSTED 100% PERCENT* *KI SIYA KI GODEMIN HAJIYA* *INCENSE BY KABO DAUGHTER* *_DUNIYAR TURARE ME BADA ASALIN QAMSHI ME KAMA JIKI DA MUHALLI,NUTSATSEN QAMSHI ME SANYAYA ZUCIYA DA DADEWA A WAJE_* *_IDAN KINA DA MATSALA KINA NEMAN TURARE ME KAMA WAJE,KINASON SAKEWA OGA SABON QAMSHIN DAKI DA PARLOR,KE KANKI KINASO KI SHIGA WAJE A DINGA TAMBAYAR WACE TA