Sashe 39
A Duniyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
sake sauka kan luggage din da har yanxu ta kasa budewa,sai ta koma ta zauna sosai saman dan madaidaicin rug na gaban gadonta,ta jawoshi jikinta ta soma zugewa Tsala tsalan abayas ne suka fara mata sallama. Abayas masu tsananin kyau da tsadar da suka amsa kudinsu na qasashen dubai da oman da Morocco. Kowacce abaya da shoe din daya dace da ita wanda yawanci takalman kamfanin Gucci Hermes kitton da tom Ford ne. Tsala tsala agoguna na kerewa sa'a data tabbatar kudade ne ba qanana ba aka zuba aka siyesu. Sai wasu siraran abun hannu masu shining da sukafi mata kama da na gold,daga gefensu kuma turaruka ne turmus masu mabanbantan qamshi da kuma tsada. Dan aljihun dake jikin luggage din ta zura hannunta,sai ta fiddo kyakkyawan kwalin,ta juyashi kadan a hannunta,tun bata bude ba ta fahimci kwalin waya ne,saita zazzage ledar kwalin ya fado. A nutse tayi unboxing wayar data jima da sanin kudinta. Aqalla kudin wayar ya tasamma miliyan hudu,sabuwar Samsung 3screen da bata gama fita hannun jama'a ba. Ta riqe wayar a hannu tana juyawa tare da duba qaramin takardar dake nuna a qasar da aka qerata da zafi zafinta acan Ya'aqoub ya siyeta. Ajiye wayar tayi a gefe tana bin kayan da idanu,kaya ne masu tsada dukansu,siyayya ta masu aji masu ji da naira. Babu abinda baiyi kyau ba a ciki amma sam ba abinda ya burgeta. Idanunta ta lumshe zuciyarta tana motsawa. Ta tuna mata da yawa,a daidai yanzun 'yammata nawa ne kamarta suke can suna neman yadda xasu tsira da mutuncinsu?,'yammata nawa ne suka rasa darajarsu saboda neman yadda zasu rufawa kansu asiri?,mata nawa ne suka hadu da abubuwa marasa dadi saboda an rasa me taimakonsu?,bayan al'ummarmu cike take da mawadata irinsu Ya'aqoub din,wanda kyautar dubban daruruwa zuwa miliyoyi ba komai bane don su fita da aljifansu?. Zuciyarta ta tabu sosai,ta shiga tuna wasu shekarun baya da suka shude da rayuwarta,shekarun da sukaso girgiza duniyarta,sukaso jefata wani baqin duqununun ramin da inda ta afka babu rana ko wata na fita daga ciki ko tsere masa?. Sautin qarar daya daga cikin wayoyinta ya katse mata tunaninta,ta bude idonta tana wurgawa inda wayar take,ta miqa hannu a kasalance ta jawota. Mk kamar yadda tayi saving number dinshi haka ya nuna mata. "Mika'il" Ta furta sunan muryarta qasa qasa,yayin da zuciyarta ke wassafa abubuwa da dama a kanshi. Ci gaba tayi da kallon wayar,batayi yunqurin dagawa ba har zuwa sanda wayar take dab da tsinkewa. A kunnenta ta kara wayar,sannan ta maida idanunta ta rufe gami da jan bakinta ta tsuke. "Hi" Ya furta cikin zamudi tamkar ya mance gurin da yake a zaune. Qaramin tsaki taja qasan zuciyarta,ta motsa labbanta a hankali "Assalamu alaikum" Ta fadi a nutse.....sallamar da ta sanyaya masa jiki,ta kuma jefa shakku a cikin zuciyarsa. Itace macen da yakewa kallon bariki ta farko da take matuqar masa kwarjini. Itace ta farko da yake hangen wasu kalan dabi'u da suke jefa shakku da kokwanto cikin zuciyarsa. Baisan kala da adadin matan da yayi mu'amala dasu cikin rayuwarsa ba,amma sai take neman zame masa ta daban. Dan gyaran murya yayi sannan ya amsa mata da "Wa'alaikumussalam.....afuwan.....banyi sallama ba ko?,na matsu da naji muryarki ne.....na kwana da kewa na kuma tashi da ita......ina fatan kin tashi lafiya?" Sai da tasha qamshin nan nata da yake a halittarta sannan ta amsa masa "Lafiya qalau......" "Naji dadi dajin hakan.....yaushe za'a bani damar sake ganinki?" Yayi mata tambayar abinda yafi damunsa kuma cikar burinsa a kanta. "Sai lokacin yayi......idan yayin da kanshi zai kawoka gareni". Sam ba haka yaso ba,sai kuma yake ganin kaman daga gareshi ne,ya kamata ya gyara wasanshi. "Zan iya haqurin jiranki koda na shekara nawa ne......amma inaso kisan akwai zuciyar da tayi matuqar mutuwa a kanki take kuma da buqatar soyayyarki....." "Mika'il......" Aka kira sunanshi daga gefe,muryar ta fusgi hakalinsa,yadan waiwaya kadan ya dube kamilar fuskar nan,daya daga cikin fuskoki biyu dake masa kwarjini cikin kamfanin "Am sorry......zan yanke kiran,ina fatan samun wayarki a bude zuwa anjima,ba kamar yadda nasha wahala jiya ba" Boyayyen tsaki ta saki tana yanke kiran hadi da zame wayar daga kunnenta. Ta wurga fararen idanunta gefe tana sauke qaramar ajiyar zuciya. Wato namiji akan mace tamkar mayen qarfe ne da qarfen kansa?,musamman idan zaki bashi abinda yakeso?,ko kuma yana hasashen samun wata riba ko ganima a kanki?. A nutse ya zuba masa idanunsan nan yana kallonsa lokacin da yake jefa wayarsa a aljihu yakuma iso bakin zagayayyen table din da yake zaune a kai. Muhammad fuad jadda CEO abinda ke rubuce kenan jikin wani dan siririn katako dake zaune sosai saman table din daga gaba gaba. Saidai a maimakon muhammad jaddan,farouq hamza kibiya ne zaune saman kujerar yana duban mika'il da kyau har ya zauna kujerar dake fuskantarsa. "Sassaucina fiye da oganku kamar yana son jawo sakaci da aikinku ko?" Ya jefawa mika'il tambayar yana debe dukkan wani wasa da haba haba da ya saba yi dasu dake saman fuskarsa. Shafar kansa kadan mika'il yayi cikin rusunawa "Sorry sir.....urgent call ne shi yasa....but hakan bazai sake maimaituwa ba" "Mituna nawa nayi ina kallonka ba tare daka sani ba,hankalinka baya jikinka?,ka kuwa san girma da matsayin position da kamfani ta baka mika'il?" Ya sake masa tambayar yana riqe habarsa da yatsarsa guda gami da kafeshi da idanunsa sosai. Yanayin ya tabbatarwa mika'il na gaske ne,a irin wannan lokacin da yake buqatar kusanci na sosai da JADDA DIAMONDCHORE RESOURCES bai kamata ya bari BOSS muhammad ya dawo ya samu wani shaidan banza a kansa ba "Sorry sir.....it will never happen again" Kaman bazai daina kallonsa ba sai kuma ya fesar da iska daga bakinsa,ya tura masa wani folder yana cewa "Ruwanka ka riqe aikinka da kyau,ruwanka kayi wasa dashi.....daga rana ita yau ba zaka sake ganina a company dinku ba,wataqila saidai ziyara......ka kuma fini sanin waye boss dinka" Ya qarashe maganar yana tashi daga saman kujerar. Yadda hankalinta yayi kan zuwa duba aysha yasa gaba daya ta manta da batun wayar da ta bada address din aje a karba. Gaba daya ta manta ma da zaman wayar cikin dakinta. Sai data tabbatar su huda sun dawo daga boko sun wuce islamiyya sannan ta shirya cikin wani dinkin atamfa doguwar riga data bude sosai daga qasa ta zauna mata daga sama cas jikinta,ta kuma lullube kanta da Chantilly veil,takalmi da jakan D&G su suka zama cikamakin adon nata. Kamar ko yaushe tsakar gidan nasu zuwa farfajiyar gidan bata rabo da kai kawon jama'a jifa jifa. Kamar kullum haka ta ratsasu a nutse ta fice ba tare data damu da idanun dake zube a kanta ba. Kamar dai kowanne lokaci,abinda ta baro cikin gidan shine a waje. Yawan idanun jama'a dake kanta ko kadan basu dadata da qasa ba. Tun asali mutum ce me damuwa da lamarin gabanta. Abubuwa da dama da suke cikin zukatan mutane a kanta bata isa ta gogeshi ba. Abune da tun yana damunta ya zame mata jiki. Suna mata kallon biri ne tana musu kallon ayaba. Anyi walqiya me hasken data haska mata abubuwa masu tarin yawan da suke boye cikin hijabin idanuwan jama'a da wani irin shamaki da tsinkaye da idanuwa basu kaiwa wajen. Wasu mutanen a riga kawai suke mutane.....wasu dattawan a suna ne kawai kuma a baki.......wasu jama'ar da ake tunanin suna gyara ko bada gudunmawar gyaruwar al'umma su din GUBA ne,guba ce wadda bata da magani,guba ce me d'aid'aita komai da wargaza komai. Daidai sanda takai qarshen tunaninta sai ta fidda eye glasses dinta da ba kasafai ta fiya amfani dashi ba ta manne qwayar idanunta. Daya daga cikin abinda ya sanya suke mata mummunan kallo da mafi munin fassara. Eye glasses ne me duhu dake qarawa fuskarta kyau da kuma kwarjini,yake kuma iya hana mutane ganin ainihin qwayar idanunka. A nutse takai bakin titi,saidai yanayin kai kawon abun hawa kadai zai gaya maka akwai qarancin motocin haya "Ki siya mota kawai ki huta sabreen" Ta tuna kalamin qawarta qwaya daya da take da ita duk duniya wato haseena. Karon farko tun wayewar garin ranar ta saki murmushin da batayi niyya ba,abinda ya sanyashi tsaiwa da motarsa cak. Duk da cewa ta daki zuciyarsa tun daga nesa daya hangeta,amma sai gashi farat daya ta sanyashi tsaiwar da baiyi niyya ba. Taga gilmawar farar motar amma saita dauke dukka wani hankalinta zuwa wani sashen,qasan zuciyarta tana fatan bawai ya tsaya bane saboda ita,don a yanzun bata da buqatar qaruwar kowanne namiji cikin rayuwarta. Tana da tarin matsalolin da takeson ta kammala dasu tukunna,mazajen dake cikin rayuwarta kuma a yanzun ta sallami kowa da kalar sallamar data dace dashi kafin ta sake sabon zubi. A hankali motar ta dawo daidai gabanta ta kuma tsaya cak,sannan aka sauke glass din motar,abinda ya bawa sassanyan sanyin ac din dake gauraye a motar damar fitowa waje ya kuma daki fuskarta. Sallamar da yayi mata ta tilastata waiwayowa ta dubeshi. Nutsatse kuma kamili a ido,wankan tarwada wanda ko bai miqe tsaye ba ta tabbatar dogo ne. Zagayayyar Fuskarshi da gemu ya yiwa qawanya,sai idanunsa dake saye a cikin glass. "Bai dace ace zafin rana yana dukan wannan kyakkyawar fuskar ba.....shigo don Allah na rage miki hanya". Jin kai da miskilanci cikin jininta yake,duk daga yanayin kamalar data gani a fuskarta ya mata kwarjini amma saita sake dauke kai ba tare da tace masa kanzil ba. Murmushi ya saki,ya miqa hannu yana bude mata motar "Ki shigo domin Allah". Ya furta yana tsareta da idanu har zuciyarsa yana jin tayi masa. Duk da cewa akwai wani irin kwantaccen kwarjini akan fuskarta wanda bayajin cewa ita kanta tasan tana dashi. Kaman yadda magiyarsa ta dauki hankalinta haka bullowar kawu ta dauki hankalinta. Duk da cewa daga nesa yake amma ta zuba masa idanu da kuma wannan komar tata dake saurin karanto lissafin me lissafi. Cikin qasa da minti daya ta gama karantarsa,zaiyi wuya ace ba ita yaje nema gida ba bai sameta ba ya fito. Batayi shawara ta biyu ba ta juya a hankali ta kama murfin motar ta bude ta shige ta maida ta rufe,daidai sanda motar ke tashi ya iso gurin. "Kaga shegiyar yarinya?,ni zaki gudarwa?,don ubanki ai duk tantirancinki dai idan dare yayi gidan adamu kike dawowa ki kwana ko?,to mu zuba dani dake.......meye amfaninki muddin ba za'a moreki