Sashe 21
A Duniyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
hukunci akan abinda bata sani ba.....bata da yaqini amma shi baiga laifinta ba,ya mata uzuri......hasalima ta burgeshi qwarai,dukkan alamu yana nuna tasan darajar dan adam ne,sai ya maida hankalinsa akanta yana duba shiga da fitar numfashinta. *SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI* *_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_* *_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_* *_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_* *_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_* *ZAFAFA BIYAR* *_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_* *Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU* _TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_ _QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_ _K'ALBIM Mamuhghee_ _AJIYA A DUHU Billynabdul_ _DUNIYATA Huguma_ _Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_ *hudu 2k* *uku 1500* *Biyu 1k* *Daya 500* _YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_ *09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA* *IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA* *09033181070* *BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK* *ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171* *ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI* *AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA* 89825722 Nousaiba lawali maradi 1000cf *_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_* *_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_* *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* *Arewabooks@:Huguma* https://www.arewabooks.com/book?id=675041625c3130f457519997 PAGE 22 __________________________ *_ALBISHIR A GAREKU!!_* *_SHIN KUNSAN UMMUMAHNOOR LUXURIES TA TANADAR MUKU INGANTATTUN KAYAN ADO NA FITA KUNYA KUWA?_* *_KAMAR SU_* Atamfofi Laces Shadda Materials Takalma Jakunkuna Mayafai Trolley Sarka da dan kunne Oil perfumes *_karki tsaya sanya har ayi babu ke,maza garzaya ta nan_* Numbers 08034469681 08135142610 Handles Instagram @ummu_mahnoor_luxuries TikTok username @ummu_mahnoor_luxuries Facebook ummu_mahnoor_luxuries *_inganci da kwalliya shine muradinmu_* ____________________________ Batasan me yasa ba,batasan dalilin da ya sanyata takejin bacin rai sosai akan abun ba. Ta dinga fidda numfashi me dumi a hankali daga baki zuwa hancinta. Cikin nutsatsen takun nan nata take nufar inda tabar busari yana jiranta. Takun da yayi matuqar tafiya da hankali da tunaninsa baya ga zubin mamallakin takun. "Wai har yanzu akwai irin mata masu wannan ajin?" Ya furta qasa qasa ba tare da yasan a waje yayi maganar ba,tana ta'allaqa dubansa a kanta,yana jin tana tafiya da gaba daya kuzari tunaninsa dama hankalinsa gaba daya. Tamkar an zungureshi ko kuma anyi masa qaimi,sai ya saka hannu da wani irin hanzari yana bude murfin motar. Sam gaba daya ya manta da dalilin daya kawosu asibitin,ya kuma manta ma da waye yake tare,burinsa guda daya tal! A yanzu,ya samu isa gareta,yakuma samu daman yin magana da ita. Sallamar tashi ta ratsa kunnenta a sanda take dab da isa wajen da Kekenapep din yake. Ta lumshe idanunta a nutse tana riqe masaqalin jakarta da kyau. Dama tasan hakan zata iya faruwa duba,zaiyi wahala a kallon farko da tayi masa ya iya tsallake halaye da kuma dabi'uj data hanga kai tsaye daga gareshi. "Assalamu alaikum.....don Allah....." Ya katse maganar tashi da kan kanshi lokacin da yasha gabanta idanunsu suka gauraya waje daya. Wani kwarjini na musamman,wani yanayi ya tsarga masa irin wanda bai taba jin irinsa ba. Nashi idanun ya janye a hankali yana qoqarin daidaita kansa tare da zallar mamaki yana kuma tambayar kansa "Meye haka?,ita din wace?". Baisan iya adadin kalar matan daya gani ba tun da ya fara zama cikakken namiji zuwa yau. Baisan adadin matan da yayi mu'amala dasu ba daga jinsin yare daban daban,amma yau daya wata mace da baya tunanin ta rufa shekara ashirin da biyar a duniya na neman yi masa kwarjini?. "Lafiya?" Ta jefa masa tambayar tana tsuke fuskarta tare da sake bada tazara tsakaninsu. Qoqarin daidaita nutsuwarsa yayi,sai ya sake mata murmushi hadi da gyara tsaiwarsa sosai a gabanta,yana jin ba wata mace da zata iya kaucewa tarkonsa muddin ya d'ana shi. "Ba lafiya ba......maganar gaskiya kenan.......akwai gagarumin tashin hankali" A mamakance take duba fuskarsa tana yamutse tata tare da qoqarin sakeyi masa sabon karatun da baisan tana yi ba "Amma fa a zuciyata" Ya qarashe maganar yana dafe qirjinsa. Numfashi taja sosai har cikin huhunta sannan ta fesar tana kauda kanta gefe hadi da juya qwayoyin idanunta. Ba shine mutum na farko data taba gamuwa dashi me irin wannan salon ba,don haka tafiyar dashi bazai bata wahala ba. Dukkan wani d'a namiji da zai ratso rayuwarta tayi imanin QADDARARSA ce a nan.......da kuma zallar tsautsayi. Mafi rinjaye daga cikinsu kuma SON RAI da SON ZUKATA. Ba kasafai ta fiya bada kai ta farat daya ba,koda ta tsara amsarka,don tuni ta fahimci duk wani abu da akeson yayi daraja.....kar a bari samuwarsa ta zama ta sauqi. Don haka ta soma tattaki da zummar kubcewa daga gabansa. A gaggauce ya sake tare mata gaba yana dubanta cikin marairaicewa "Ranki ya dade.......na tabbatar girmanki yafi gaban a tsaidaki a hanya....to amma muddin na barki kika wuce din nayi imanin sa'ata ta rayuwa ce ta kubcemin gaba dayanta......ki tallafeni ki sammin minti uku kacal" Ya furta yana nuna yatsunsa guda ukun. Juyowa ta sakeyi a karo na uku tana kallonsa. Ya fiya zaqin baki da yawa,maza irinsa suna da wani hali da dabia da tuni ta gama karatunsa. Tabbas akwai wani abu tattare dashi da wata qila take nema......tana hasashen yiwuwar samun wata qaruwa me girman gaske. Taga irinsa ba daya ba.....ba biyu ba....ba uku ba,har ba zata iya tantance adadi ba. Duk da wannan hasashen amma bata yarda ta nuna masa komai ba. Sai ta sake kau da kanta tana yamutsa fuska "Matsawarka daga hanyata kamar zaifi zame maka alkhairi akan ci gaba da tsaiwar......ina da tarin abubuwa a gabana....." "Bansan ko me ke jiranki ba......amma na tabbatar koda baikai wannan tsaiwar tamu alkhairi ba bazai wuceta ba" Ya fadi a zaqe da fatan samun nasara "Na roqeki kada ki watsan qasa a idanu,ki wofantar da wannan kyakkyawar damar a garemu gaba daya" Ya fadi yana marairaicewa tare da miqa mata wayar hannunsa yana kasheta da idanu gami da karyar da wuya da raunanar da idanun nasa. A nutse ta sauke kallonta akan wayar ta kalla. Tsaleliyar iPhone 16 wadda kana dubanta zakasan bata wani jima da baro dumin kwalin da aka qerata ba. A yangance ta dauke kanta daga kai ta sake maidawa gefanta bayan. Wani numfashi ya fusga da qyar bayan ya gama sauraren jerin lambar wayarta data karanto masa. Sautin muryar nata yana masa wani irin amsa kuwwa a kunnensa. Karon farko daya yadda cewa muryoyin wasu matan kadai suna iya haddasa fitina a zukata da gangar jikkunan maza. Sai yakejin yana sake zurfi ason ya kasance a tare da ita "Sai nakega kaman girma da martabarki ya dara kihau napep.....da zai yiwu da kin sadaukarmin da wannan tsadajjen lokacin na saukeki a gida....." Yana ajewa tana daga masa hannunta,sannan ta fara takawa tana wucewa cikin abun hawan da busari ke jiranta. Har ya bawa napep din wuta suka fice daga harabar asibitin yana tsaye a gurin. Sai daya tabbatar sun qwacewa ganinsa sannan ya buga qafarshi yana yarfar da hannunsa,wani shu'umin murmushi yana kubce masa. Ba shakka ita din ME ZAFI ce,ta kuma cancanci dukkan wannan dagawar da kuma jan ajin. Yana da makamai a hannunsa masu tarin yawan da zai iya yaqar zuciyarta yakuma yi nasara ba shakka ko kokwanto. Makami guda daya da dukkan namijin daya mallakeshi yake iya sanya kaza ta kwanta ta yanka masa kanta ta gasa ta kuma kawo kanta da kanta har inda yake don biyan buqatar ranshi. Iya wassafa samuwar nasara kadai a gareshi ya sanya murmushi ya subuce masa. Ya sake buga qafa yana wassafa irin yadda zai tsikari rayuwarsa da tsinke yadda ya kamata "Dole na qarawa kaina kusanci da dukkan qofofin da zasu budemin manya manyan qofofin taskokin da zan miki hidima dasu don mallakar muradina" Ya furta a sarari yana qanqance idanu,muradinsa yana sake ninkuwa,burikansa suna sake fadada. Daidai qofar gidan nasu busari ya ajiiyeta bayan ya fiddo mata dukan kayan daga cikin motar. Cikin farfajiyar gidan ya ajiiyeta mata kayan sannan ya juya yana komawa ciki. Tsaye tayi a farfajiyar gidan da iskar la'asar ke kai kawo. Ba wadatar yara sam,wanda koda ace akwai wadatar nasu tasan cewa ba kowa ne a cikinsu ke aikuwa ba. Kayan sun mata nauyin da ba zata iya dauka ba,tana tsaka da wanna tunanin ta hangi fitowarfitowar nadra,haneefa na biye da ita. *SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI* *_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_* *_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_* *_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_* *_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_* *ZAFAFA BIYAR* *_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_* *Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU* _TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_ _QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_ _K'ALBIM Mamuhghee_ _AJIYA A DUHU Billynabdul_ _DUNIYATA Huguma_ _Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_ *hudu 2k* *uku 1500* *Biyu 1k* *Daya 500* _YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_ *09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA* *IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA* *09033181070* *BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK* *ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171* *ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI* *AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA* 89825722 Nousaiba lawali maradi 1000cf *_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_* *_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_* *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* *Arewabooks@:Huguma* https://www.arewabooks.com/book?id=675041625c3130f457519997 PAGE 23 ___________________________ *_ALBISHIR A GAREKU!!_* *_SHIN KUNSAN UMMUMAHNOOR LUXURIES TA TANADAR MUKU INGANTATTUN KAYAN ADO NA FITA KUNYA KUWA?_* *_KAMAR SU_* Atamfofi Laces Shadda Materials Takalma Jakunkuna Mayafai Trolley Sarka da dan kunne Oil perfumes *_karki tsaya sanya har ayi babu ke,maza garzaya ta nan_* Numbers 08034469681 08135142610 Handles Instagram @ummu_mahnoor_luxuries TikTok username @ummu_mahnoor_luxuries Facebook ummu_mahnoor_luxuries *_inganci da kwalliya shine muradinmu_* __________________________ Nadra,haneefa na biye da ita Dukansu suka watsar da abinda ke hannunsu sannan suka nufota. Fuskokin dauke da madaukakiyar fara'a wadda har tsakiyar zukatansu ta ratsa. Ita daya ce HASKE GIDANSU.....ita daya ce FARINCIKINSU hakanan ita kadai ce BAQINCIKINSU. Rashinta a kusa dasu yakan debe dukkan wata walwala da sakewa tasu,duk da tarin jamaar dake rayuwa a gidan amma duk sanda bata nan