← Book details Yar Lesbian Ce 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 25

Sashe 9

Yar Lesbian Ce 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yusuf Na ganinsu ya Sauka kasa yana gaidasu, Cikin Nuna kulawa Suke amsa gaisuwarshi, yayinda mahaifin kausar yace yarona katashi ka Zauna daidai.kara durkusar dakanshi yusuf Yayi Kasa bekuma Tashi Ba.mahifan kausar Sunji dadin irin tarbiyarshi matuka.dan haka mahaifin kausar yafara magana kamar haka.

Hakika na yaba da hankalinka Yusuf kuma Nayi matukar farin Ciki Game da Zaben miji nagari da yata tayi, dama nadade ina fatan Hakan.

Allah yamuku Albarka gaba dayanku.

Amin yusuf ya Amsa kasa kasa.

Cigaba mahaifin kausar yayi, idan kashirya Zaka Auri yata katuro mun magabatanka Cikin Satin nan Asaka Ranar biki Zuwa Sanda yata Zata karasa karatunta.

Wata Shida ya Rage ta karasa.koya ka Gani Yusuf?

Baba Yanda kace nima haka Nayi tunani Zuwa jibi Zan Turo magabatana Ngd Allah yakara girma.

Amin mahaifin kausar yace.

Madallah da samun d'a nagari irinka ina alfahari dakai Yusuf mahaifiyar Kausar ta fada.

Ngd mama.

Tashi Sukai suka fita.

Yusuf na ganin Sun fita yatashi tsaye Hannu yadaga Sama yana gdy ga ubangiji mai wanzar da farinciki Cikin Zukatan bayinsa.

Ahaka Kausar ta Shigo ta sameshi Sanarda ita komai yayi Akan yanda sukai dasu Hajiya itama farin ciki tanuna Afili Ahaka Yusuf ya sanar da ita maganar su Yazeed kamar yanda ya Sanar da inno, Cikin ranshi yana rokan Allah ya yafe mishi game da karyar dayayi, So yake ya hada Sunnar mazon Allah S.A.W. tsakanin mutum biyu wanda yake hango babbar Alkairi cikin Al'amarin.

Afili Cewa yayi Kausar mu hada guiwa mu hudu ni dake da Nazir da Leemah Mu hada Yazeed da Feenah aure Nasan Inno Zata Kara mana hikima shiyasa na fada Mata. tunani Kausar take ya'Akai feenah ke Soyayya da Yazeed bayan Feenah Sam Bata jituwa dashi, Kawai nasan Yusuf ne keson hada wannan Auren,toh komadai yayane nima Zanyi farin ciki da hakan Tunda ba karamin dacewa feenah tayi da yazeed ba....kikai Shiru Sweetheart!

Ba Shiru Nayi ba naji dadi hakanne matuka Kuma Zamusan yanda zamuyi.

Inasonki my kausar kinada fahimta.

Murmushi tayi tace kamarka ba tunda kaine ka kawo zancen.

Yusuff saida ya kwashi lokaci mai tsawo tukun yabar garin zariya kan Cewa jibi Zai turo iyayenshi.

Page.....32
Bayan komawar Yusuf kaduna yasanar da mahaifanshi Kamar yanda Sukayi da Mahaifin kausar.

Iyayen Yusuf Sunyi murna matuka dan dama farin cikinsu Ayanzu bewuce Suga Auren Yusuf ba.

Dan haka Ayaune Kwana biyun da Yusuf yace ma Iyayen Kausar tacika. magabatan Yusuf Sunshirya tsaff Zuwa Zaria Ciki harda Abba Mahaifin Yazeed, dashi yazeed din kanshi har Nazir ma wanda Sakon ya isar mishi. gidan Alhji Hafis Suka yada Zango inda Aka taresu da girmamawa da Mutumci.

Saida Aka tanada musu Abubuwan motsa baki daga bisani Abban yazeed yafara magana. toh kamar yanda kuka Sani munzo garin Zaria ne dumin bukatar da kuka nuna game dacewa yadace Yusuf ya tura iyayenshi, Toh Alhmdullah gamu munzo kuma Muna Shedar Yusuf mutumin kirki ne mai hankali da natsuwa.

Dan haka muna nema ma Yusuf Auren Kausar la'akari dacewa ta fito daga gidan Mutumci, idan kun Amince da Hakan.

Uncle din kausar ne yayi gyaran murya yafara mgn.

Alhmdllh Muna matukar farin ciki daku domin munyi maraba da Yusuf tun lokacin da yazo da farko. dama ba wani Abu yasa mukaci ya turo iyayenshi ba saidan Hakan Sunnah ce kuma Al'ada ce....Sannan idan kun Aminci Za'a daura Auren Kausar da Yusuf Ayau din nan Sabida mahaifinta tafiya ta kamashi Zuwa kasar masar na tsawon Shekaru biyu, yana Son yaga daurin Auren yarshi Saikuma yanayin karatunta ya Rage da Saura, Dan haka ya yanke hukunci idan kun Aminci Adaura Auren yaran inyaso kausar din tacigaba da karatunta Amatsayin Matar Yusuf.

Mahaifin Yazeed ya nisa yace Amma bamuzo da Shirin daurin Aure ba kuma Yusuf din besan haka ba.

Kawun Yusuf ya kalli Abban yazeed yace Ahmad Ina ganin ba matsala tunda Shedune Ake bukata duk gamu A daura Auren kawai idan yaso lokacin dazata Kammala karatun Nata idan Sunada Ra'ayi saisuyi Shagulgulansu. toh madallah Hakanma yayi Abba ya fada.

Sudai Nazir da yazeed mamaki kawai Suke wannan Wani irin Aurene lokaci daya. take Aka umarci Yazeed daya kira yusuf ya Sanar dashi domin Sadaki.

Kiranshi yayi ya Sanar dashi duk yanda Akayi.

Murna Awajen Yusuf bata misaltuwa, Umurtar yazeed yayi daya bada dubu50 Amatsayin Sadaki.

Hakan kuwa Akayi take Aka daura Auren Yusuf da Kausar bisa Sadaki dubu50 lakadan ba Ajalan ba.

Haka kowa yatashi yana farin ciki Cikin Ranshi.

Sun yake Shawara Kausar Xata cigaba da Zama A gida Har Xuwa lokacin dazata Kammala karatu koda da Sati daya ne Sai Ayi Shagalin Biki Akaita dakinta tunda Yusuf bekarasa gininshi ba.

Ahaka Suka hau motocinsu Dan komawa garin kaduna.

Suma Sauran mutanen yan Uwan Mahaifin Kausar Sun tashi Suna murna Ahaka babban parlon ya Rage Saura Mahaifin Kausar, tashi yayi yashiga Cikin gidan A parlo ya Samu Sara Hajiyar Kausar da murna ta tareshi.

Yana Zama yamata bayanin duk yanda Akayi da yan'uwan Yusuf. kallonshi Hajiya Sara tayi Yanzu Alhji kana nufin Kausar Matar Aurece?

Eh ko baki farin cikin Hakan bane?

Ahhh nayi farin ciki Sosai mana Alhji kawai dai yaza'ace Aure irin wannan ba wani Sha'ani.

Hakan bazai Hana idan ta gama karatu kuyi duk Abinda kukeso ba Alhji ya fada yana tashi ki kiramun Kausar din.tashi Hajiya tayi ba'afi minti3 Suka Shigo parlon da Kausar...Xama tayi Akasa kusa da Hajiya tana fadin Gani Baba.

Kausar Abun farinciki ne yasamu, Abaya kinata korafi Akan munki Aurar dake Toh Alhmdllh dama Ance mahakurci mawadaci, Ayau na daura miki Aure da yusuf mijin da kika xaba Amatsayin mijin Aure Ina fatan Zaki farinciki da Hakan, domin ni bana kasar nan Zaki Kammala karatu, Shiyasa na yanke Hukuncin Nan domin Nasaki farin Cikin dana dade Ina fatan kaiwata lokacin dazan Sakaki Shi.

Zaki Xauna A gida Zuwa jibi dazaku koma karatunku, idan kika kammala kika dawo Koda da Sati daya ne Sai kuyi Shagali Akaiki dakinki, da fatan Hakan ya miki?

Kausar da tunda Mahaifinta yafara magana take Surutai Cikin Ranta wanda ita kadai tasan me take fada, dago Kai tayi tace Eh Baba Naji dadin Haka Allah yakara girma.

Amin Alhji ya fada yakara mata da yan Nasihoyi ya tashi yabar parlon. tashi tayi takoma Kan kujiran, jikin Hajiya Sara ta kwanta tana Raira kukanta.

Saida Hajiyar tata Taji Abun yayi yawa tukun tace, kin isheni da kuka ko bakya Son Yusuf dinne?

Cikin kuka take mgn Mamah inason Yusuf, kawai Nasihar da Baba yamun yasani kuka, Sannan Mamah ina kara nadama Akan Abinda na Aikata Abaya, jiya danace miki Zani Asibiti Mamah kinsan mai Dr ya fada mun? girgixa kai mahaifiyarta tayi tace Aa.

Mama Cemun yayi inada infection! ya kamani da yawa, Sannan ya fadamun Hanyoyin da'ake kamuwa dasu, tabbas Hanyoyin daya fadamun harda idan Kana Aikata Lesbian Kana wasa da yatsa, kuma nayi Hakan da khady, Sannan ya fadamun mace Na'iya komawa dis virgin ta hanyar Hakan. mama yacemun infection yana hana haihuwa Shine babban Abinda yafi daga mun hankali,inason yara!

Mazan yanzu Suma idan baka haihuwa wulakanci Suke maka, bama hakaba Sam baka Samun kwanciyar hankali wajen yan'uwanshi da Mahaifiyarshi.

Narasa yanda Zanyi mama Sam be dace yusuf ya Aureniba Domin Ni din baxan bashi farin Cikin daya dace dashiba, Naso nafada mishi Abunda na Aikata kamin na aureshi mama yanzu nasan tabbas idan yaji Sakina Zaiyi kuka mai karfi ya kwacemata takasa karasawa.

Kankameta Hajiya tayi tana tausaya ma yar tata cikin Ranta tace tabbas nayi Sakaci, Na takema y'ata Hakkinta A baya duk dacewa Aure lokacine Amma nima na Aikata babban kuskure gashi najawo ta fada Aikata mummunan Abu ina Murna ta Bari yanxu ga Sakamakon Abinda ta aikata nan.

Afili cewa tayi ya'isa Kausar kinga Shiyasa ko kadan ba'ason Asab'ama mahallici domin duk maiyin hakan watarana Saita kife dashi, Amma tunda kin tuba Allah ya gafarta miki insha Allah.

Yanzu wannan kaddarace ta Sameki, kin Aikata kuskure babba kausar Amma kisani Allah SWT shi yasan Abinda ke boye Ki Saka Aranki Zaki haihu kamar kowacce mace.kuma ba Lallai kinzama dis virgin ba, Abinda nakeso dake wannan yakara Xama Horo Kan Abinda kikai Abaya.

Sannan Idan kinga Zaki fada ma Yusuf dinne kifada mishi ai yaron yanada Hankali Xai fahimta.maganar Infection Ayau Xamuje Islamic-Chemist din Chan dake kusa damu ya hada mana magungunanshi.

Ni matsalata yanzu gyaran jikin Ki Anje Anwani daura Aure tun yanzu.

Amma Shima Bari Akwai Wasu Abubuwan daxan baki idan kinje Skul din lokacin dakike da lokacin Kanki Sai kiyi Amfani dasu Akwai nasha dana Turare duka.

Gyaran jikin idan kikadawo Sai Amiki.

Idan yaso tarewan Sai Akaishi Zuwa Sati biyu domin a gyara munke Sosai. kuma yusuf din Ko Zuwa Yayi dubaki Kada Kibari ya kusanceki duk da nasan ma Akwai Su feenah Adakin kinji dai na fada miki kibari har Sanda Zaki tare.

Kausar magan ganun mahaifiyar ta Su Suka Sanyaya mata rai domin ta yarda dacewa Hajiyarta Xata tsaya wajen ganin ta magance mata damuwarta. toh Hajiya insha Allah nacire damuwa Araina.Allah yamiki Albarka Kausar dita.Amin hajiyata. daga Haka Kausar ta tashi tashiga Ciki.

Leemah ce Rike da waya da Alama kokarin kira take....Hello!

Feenah Kinji Abinda nakeji kuwa?

Daga bangaren Feenah cewa tayi besty mekenan?

Yanzu Naji Su Abba Suna magana wai Andaura Auren Yusuf da kausar Leemah ta fada! daga inda Feenah take Ido ta fiddo waje tace Nimafa Naji yaya Nazir yana maganar kausar da mum Amma Ni bankawo da Kausar Akeba, wai dgske Kausar Aure tayi Kenan.

Leemah dariya tayi tace toh gashima Abba na maganar Aikuwa Kinsan gsky ne.

Ajiyar Zuciya feenah tayi tace Wannan Aure Kamar Angaji dakai!

No ba Haka bane feenah wai Babanta keson yaga Auren yanzu kuma tafiya ta kamashi, but Za'ayi bikin daga baya Sukace.

Koda Naji Amma Anya lfy Kausar bata kiramu ta fada mana ba?

Feenat Nasan lfy qalau Amma inaganin tana Cikin damuwa ne, mai Zai hana mushirya gobe muje Zaria dagachan Saimu huce Skul jibi.

Hakan yayi Leemah bari Nafada mawa mum ko?

Ok Nima Bari nasanar da Mamy Sai goben.

Ok besty bay.

Yusuf gaba daya yau Cikin farin Ciki yake Wanda baya misaltuwa.

Godiya kawai yake ma Ubangiji Akan wannan Sabuwar Rayuwa daya shiga Ayau.
Chapter 9 · 0% Book details