← Book details Yar Lesbian Ce 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 25

Sashe 5

Yar Lesbian Ce 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai Wani rawar kafa kake Kamar Yau Zaka fara ganin Feenah din. bahaka bane mum Kinsan nadade banganta ba, Uhum Kaji dashi mum ta fada,Oya tayani Shirya Abincin Nan.

Zaune Suke Yusuf Na fadin wlh Yazeed jina Nake Kamar naje Zaria Ayau! dan Allah katashi katafi mana, duk Ka Wani ishe Mutane kan yarinya karama. bakasan menene Soyayya ba namaka Uxuri kaikam yazeed.

Eh Naji angaya Maka Koda naci Xan Auri Karamar yarinya da Soyayya ne?

Kawai dan ina tausaya ma kaina nane.

Hakane fa yusuf yafada Yana dariya, ina tausaya Maka Ranar da Xaka Zama wawa awajen yarinya karama.

Allah ya kayuta Yazeed ya fada da karfi......inno ce tafito tana tsaka Lfy Ko Halimatu ta karaso ne??

Kallonta Yayi ya wurga mata Harara, bansan kanayi ba Sainaga idonka Akasa, badai Yau Amadi na hanya ba wlh Zaka maimaita duk Abin da kake mun, tsaki yazeed yaja yace Saime toh inno??

Sai Ubanka ya maidani, tsaka yau ina Cikin farin Ciki ka batamun Rai Allah Saiya Sakamun.

Yusuf dake ta faman dariya yace inno nima Wlh yau farin Ciki Nake Sosai...da Sauri Inno tace Ai shi yazeedu ko Ranar idi ce tazo A bakin Rai yake Aini Alhmdullah Zuwa gobe Narabu da kunnama mai Zafin harbi.

Tashi yazeed yayi yace idan kagama biye Mata Kasameni.

Wayyo Sunanka Suri yau tsaka, dariya Sosai Yusuf yayi yace Inno tamu.

Uhum yusufa yushe Zakayi Aure?

Inno Sai yarinyar tagama Karatu. dafatan dai ba katuwa bace irin kafurar yarinyar nan?

Inno Wannan yarinyace kawar Halimatu ce kunama gaisawa da ita, Laaaa Kafso kake so dama? yarinya Mai hankali....dariya Yusuf yayi yace inno ba kafso ba kausar take....Oho Aini ban Iya Sunan yan boko din nan ba. toh inno bari na tafi, duk Abinda Yazeed ke Miki ki fada ma Abba dan yace mun wai Aure yakeso Shiyasa yake Miki haka!

Bude baki inno tayi tana Salati yusufa Ashe Shiyasa Ranar da yakawo Kafura Naganta tafito daga wajenshi tana Sanda????? mamaki Yusuf yayi Cikin Ranshi yace Chafff Inno ta ganshi, Afili Cewa yayi Inno Ai aure yakeso Sosai, Kinsan feenah Kawar Halimatu kuwa?

Kai dan Nan nikuwa nasanta itama tana Miskilanci irin na tsaka.yawwa Inno kawo kunnanki kiji!

Mika kunne tayi Yusuf ya fada mata mgn.

Tashi Naga tayi tana Rawa Tana haka Za'ayi yusufa...

Karfe 5 daidai na yamma driver ya Sauke Su Feenah A mamakenken gidansu Wanda Leemah baccinta take batasan Anzoba, daka mata duka feenah tayi tace tashi Sarkin bacci!

Adan tsorace ta tashi, haba Feenah bayan Nace Agida Xan Sauka kikasa y kawo ni nan.

Ai naga Nan din ba daji bane.

Nidai kirashi ya kaini, Sakko da kanki.

Atare Suka sakko Leemah na Kiran Haruna....daidai Kuma Sanda mortar Nazeer tayi parking A harabar gidan, tare Suka fito da dad Suka nufo Wajen Su feenah. da Sauri feenat ta karasa ta Rungume dad, dady ur wlcm.

Tnx Ummina.

Karasowa Leemah tayi itama tana mishi Sannu, Amsawa yayi Cikin Sakin fuska,,,,Nazir Kuwa gaba daya idonshi nakan Leemah, dad ne yace mukarasa Ciki, Wai tafiya zatai dad feenah ta fada tana kallon Leemah, Aa halimatu muje kici Abinci kihuta sai Nazir ya kaiki Anjuma, toh Leemah tace tabi bayansu jiki A Sanyaye, Shiko Nazir murmushi kawaii yake najin dadi.
page....28
gaba dayansu Sun Hallara Kan dining table din Suna Shirin Cin Abinci. daddy ne yace Hafsat ina yaran Nan ne?

Inaga ko basu gama huta gajiya bane mum ta fada tana kokarin Serving din Nazir dake wajen... ya kamata Akirasu ko? daddy ya fada yana kallon mum.

Kallonshi tayi tace da Nabari ne Saci nasu daga baya.

Nazeer ne yace Ai gara kawai Aci gaba daya mum!

Banza tayi dashi, ganin Haka yasa dad yace ma Mubeena ta tashi ta kirasu, tashi tayi ta tafi da gudu Zuwa Sama. ba'afi Minti5 tsakaniba Suka Sakko Atare....daddy Yana ganinsu yace duk gajiya dince Haka yarana, Murmushi Leemah tayi ta Sunkuyar da kai qasa, yayinda Feenah tace dad Akwai gajiya Wlh.

Ai kun kusa gaba daya daurewa Zakuyi dad yafada. tashi feenah tayi tafara Zuba Nasu Abincin, Sunaci Suna fira banda Leemah da duk take jinta A Takure musamma data dago taga Nazir take fuskanta, Haka dai kawai ta daure tana ci gashi duk Sanda Zata dago Saisun hada ido Atare Kuma Suke Sakar ma juna Murmushi... mum ce ta dago tace Nazir Anjuma Zan Aikeka gidan "Umma" ka kaimata Sako.

Shirun data jine yasa ta kalleshi, gaba daya Hankalinshi baya jikinshi magana Suke da Leemah da ido ga wani kallo dasuka tsare junansu dashi!

Mumy ce ta Saki Spoon din hanunta ta dan bigi Kafadar dad tana nuna mishi Su Leemah, daga gira dad Yayi Sama yana murmushi lokaci daya Kuma yayi gyran murya Ehmmm...gaba daya Suka juyo Suka kalleshi ganin Su Ake kallo yasa Leemah taji Kamar ta nitse Awajen, durkusar da kai tayi Kasa.

Nazir kuwa Inda inda yafara yace Mum maga kikai? dad ne yai Saurin cewa ba magana tayiba nine nakusa kwarewa, Hafsat tashi muje kiban Ruwa, tashi mum tayi Sukabar wajen ita da dad. feenah kuwa da dama tunda Suka Zauna ta lura da yanda Suketa mgn da ido da Hanci??itama tashi tayi tace Alhmdllh nakoshi....tashi Leemah tayi da Sauri besty jirani Nima na koshi, da Sauri Nazir yace baki koshi ba Common Xauna ki karasa,marairace Fuska tayi kamar Xatai kuka Allah yaya Nazir na...Kafin ta karasa yace Naji kin koshi Xauna muyi mgn, Xama tayi.

Yace feenah dawo kema tare Zamuyi mgnr, dawowa tayi ta Xauna Nazir ya kalli Twins yace kuje Baba ladi ta Shiryaku Xankaiku gidan Su mai Kyau!

Ai da Sauri Suka tashi Sukai Cikin gida.

Juyowa yayi yana kallon feenah Sisto Nariga Nasan Kinsan ina matukar Son besty dinki ko?

Umm ni bansaniba feenah ta fada tana yatsina face...Kara juyowa yayi yana kallonta Haba my Sis Nasan kinsan komai kuma bakya karya kigaya mun gsky.

Eh Nasani Yaya Nazeer kawai Haushin boyemun dakayi Nake ta karashe mgnr harda Dan Hawayenta....haba Sis Menene Abun kuka kuma, Nifa daman Nabari ne kidawo Nagaya miki kamar Surprise Haka, kinsan bana boye miki Abu itama Leemah ban so tasaniba Nakasa daure ma Zuciya tane yasa Nagaya mata.

Turo baki tayi tace Naji Amma dafatan Son tsakani da Allah kake mata? dariya tabashi yace irin Son danake miki Shi nake mata, Aa yaya Nazir nafison Nata yafi Nawa...Shiru yayi yace toh kitayani addu'a tasoni fiye da komai, toh yaya Nazir Zanyi.

Leemah ce tace karfa mum tafito! bayan Sun gane komai feenah ta fada tana dariya..Atare Suka Zaro ido fada musu kikai Leemah ta tambayeta?

No kune kuka tona kanku kallon juna Kamar wani Xai dauke dayanku din nan.

Nazir yace Ai Hakan ma yayi kinga Sai Amana Aure da wuri!

Leemah ce ta marairaice fuska Aa nifa Sai feenah tasamu miji Zamuyi Aure Rana daya...dariya Nazir yayi yace wato Ku Haryanzu yara ne, banda Abunku Ai gara daya taga auren daya Sabida idan Rana dayane daya bazatakai daya gidan Aurenta ba.

Waye ya fada maka yaya Nazir?

Aikoda Rana daya mukai Aure Sai Nakai Leemah gidanta kafin na wuce Nawa.

Nazir ne yace kinmanta Kabeer Xaki Aura kuma yola Za'a kaiki,ba Lallai Na yarda baby taje yola Aranar Aurenmu ba...da Sauri feenah ta tashi tana cewa Ai bazaka Rabamu ba dan yanxu kasamu mun Amsheka, daga Haka tabarsu Zaune A wajen.

Juyawa yayi yana kallon Leemah baby kawarki Akwai Rigima, Uhum bata Rigima Kaidinne Kake Sakata Rigima, Umm Na lura bakwason Laifin junanku Toh ya Soyayya ta yanzu Aranki???

Shiru tadanyi daga bisani tace tasamu waje babba Acikin Zuciyata, kallonta Nazir yayi kamar ba ita tayi mgnr ba ta wani fuske, Cikin Xuciyarshi yace Lallai Leemah irin macen danake muradin Aure ce, Afili cewa yayi Alhmdllh my baby Yanzu kinga kamin Ki koma Skul Sai Asaka mana Rana...Xaro ido tayi tace da wuri Haka?

Eh mana bakiji Hausawa nacewa Abari ya wuce Shi ke kawo Rabon wani ba?

Hakane but yaya Naz..but what?

Nazir ya katseta da Sauri.

Kabari lokacin daxa'a Saka Ranan feenah da kabeer Sai Asaka tare da namu.

Kin kawo Shawara mai kyau baby Shiyasa nake kara Sonki,duk da kin barni Cikin tunaniki, kullum dake nake Kwana kuma dake nake tashi.

Nima Haka yaya Nazir.

Kin tabbata?

Kallonshi tayi Suka hada ido ta kashe mai Ido daya tace Ummm, Ajiyar Zuciya Nazeer yayi Dan wani irin farin ciki yakeji wanda baya misaltuwa.

"I love you So much my baby" Nazir ya fada yana Mata Murmushi.

"love you more my baby" Leemah ta bashi Amsa kasa kasa.

Xancire miki kunyar Nan Soon duk da Naga Alamar nama fara kokari Wajen cireta....dariya Leemah tayi ta tashi tace kada Su mum Su Sakko, tashi Shima yayi ya rakata Har kofar Room din Feenah yace kishirya Anjuma Nakaiki gida.

Ok tace tashige Ciki.

Inno ce tsaye Kan yazeed Tana fadin Haba tsaka ka kiramun ita Naji ko tana inane.

Inno nace miki wayata Bazata iya Zama A kunanki ba dan Allah kitafi ki bani waje yazeed ya fada yana nuna mata Hanyar Sama.... tsaka! tsaka! tsaka!

Sau nawa nakira ka?

Oho yazeed yace ke kikasan tsaka.

Kwafa Inno tayi tace yaro yarone ina tausaya maka Ranar da Zaka Shigo hannuna, Xakayi nadamar yimun wannan Abun Dan Ubanka,yanzu namaka Uzuri dan nagane dalilin dayasa kakemun wannan Abun...Amma muje Zuwa ni inno jikar Saluhu da balaraba Nakusa Na dana maka tarkon da bazaka iya tsallakeshiba.

Kallonta yazeed yayi yace iyaka kice idan Abba ya dawo Xaki fada mishi, Toh Sai me?

Haka kace ko?

Eh Haka nace mtsww kizo kitafi koma ma huta.

Fatima kayimawa tsaki bani ba...muxuba ni dakai.

Tashi yayi yana toshe kunanshi...daidai nan Abba yayi Sallama Cikin parlon.

Suman tsaye Yazeed yayi dan yasan yau Inno Sharri Xataimishi ba kadan ba. da karfi Inno tace Ayirirerere yau Ga dana Ya dawo huta Roro. ...da fara'a Abba ya karaso kusa da ita ya gaidata amsawa tayi Cikin walwala da Sakin fuska, Abba ya kalli yazeed my Son lfy kuwa?

Sannu da dawowa Abba!

Yawwa Son duk kuna lfy ko?

Alhmdllh Abba.
Chapter 5 · 0% Book details