← Book details Yar Lesbian Ce 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 25

Sashe 8

Yar Lesbian Ce 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tafiya Zanyi mana nagaji da Abunda Akemun Acikin gidan Nan. dad din feenah ne ya kalleta yace Inno kiyi hakuri kizauna ki fada mana me Ake Miki Sai A gyara insha Allah.

Zama tayi tace ni banaso ma a gyara yau din Nan Saina bar gidan Nan.

Hayaniyar inno ta juyo dasu Leemah dake Soyewarsu, tasowa Sukayi Ajere Suka nufo wajenta.

Inno Ya naganki da jaka haka?

Naziru yaron Albarka tafiya Zanyi Inda Ake ganin mutumcinta.

Shidai Yazeed bece komaiba wayarshi kawai yake dannawa ko kallonta beyi ba.

Inno Ki fadamana ko nice ke miki laifi ban Saniba Mamy ta fada cikin Sanyin Murya.

Kallonta Inno tayi tace Ni Fatima bakimun komai ba kedin macen kwaraice ina Alfahari dake, kuma kaima Amadi bakaimun komaiba, laifinku daya dakuka kasa tankwarar da danku kan bakar Zuciyarshi.

Mum ce tace inno ba bakar Zuciya gareshi ba bayason Raini ne.

Oho mai d'a dan bayason Raini Sai Akace nima Rainashi nayi ko inno ta fada tana duban mum din feenah. dad ne yayima mum Alamar tayi Shiru, ya kalli inno yace Inno Hakane Anyi kuskure Amma kiyi hakuri. da Sauri tace nifa baniyin hakuri tafiyata Zanyi.

Cikin Zuciyarta So take Yazeed yabata hakuri Amma Ya nuna kamar baisan tanayiba.

Abba ne yace toh Shikenan Inno Xan kaiki katsina Amma kibari Zuwa gobe da Safe. da Sauri Yazeed yace Abba koni Saina kaita Ayau Idan kana da Wani Abunne.

Galala Inno ta tsaya tana kallonshi ganin Shi Murna ma yake ta tafi...toh yazeed Ashirye kake Yanzu ko?

Abba ya tamabayi yazeed.Abba Ashirye nake kallon Inno yayi yace tashi muje.

Wani irin kallo tamishi tace Wlh naga Alama yazeedu murna ma kakeyi!

Me kikeso nayi Toh?

Me makon Kace nayi hakuri da hawayenka yazeedu.

Chaff yazeed yafada kitashi muje dare nayi fa.

Ai Wlh babu Inda Zanje tunda naga Alama bakin cikin Zamana a gidan Dana kake.

Tashi tayi ta dau jakarta tayi Sama da ita. dariya Su Leemah Suka Saka gaba dayansu. komawa yazeed yayi ya Zauna inda ya tashi, Shi bahaka yasoba yaso ta tafi Ko tabari ya Sarara, Amma bazan kara mgn ba yazeed y fada Aranshi gudun Kada ta tonamishi Asiri yaji jiya Mufeeda tace wancen Xuwan nata inno ta ganta.

Abba daya fara mgn ne y dawo da yazeed daga tunaninshi.

Yazeed banason Inno takara kawo karanka wajena nagaya maka. durkusar da kai yayi k'asa yace insha Allah Abba.

Dad dake gefe yaji Son yazeed yakara Shiga Ranshi sabida yanayin tarbiyyar yaron, cewa yayi Ahmad Ai jika da kaka Haka Suke ba'a hanashi ba kawai inno kishi take da yarinyar daya kawo kwanaki bakuga Abu Kadan maganar yarinyar take ba. dariya Sukai Gaba daya.Abba ya kalli mamy yace waini Fatima yarinyar batai bane?

Tabe baki Mamy tayi tace ai inaga kwanaki yazeed hauka ya fara, yarinyar fa Kamar yanda Inno take Cewa kamar yar kafurai, Sam batada tarbiyya irin ta ya'yan hausawa.

Gaisuwa ma Saida Shi Uban gayyar yasakata tukun ta gaisheni.

Ahhh Lallai dole inno Ta kushe yar mum ta fada.

Leemat ce tace Abba inada picture din matar barifa kagani.

Phone dinta ta ciro tashiga nuna musu pic din mufeeda wanda kausar tamata sending kwanaki. kallonta yazeed yayi ya wurga mata harara ta kauda kanta tana mai gwalo. mamaki Suke yayinda mum tace ai wannan kusanma ta girmeka Son. durkusar da kai yayi yace mum Yanzu bama tare Ai.

Yawwa yarona Sam bata dace da rayuwarka ba.

Abba ne ya kalleshi Yanzu waka tsayar Toh?

Sosa kai yayi yace Abba inadai nema. toh ka kokarta ka samo kamin ni nasama maka. toh yazeed yace.Leemah jitake Kamar tace Suna Soyayya da feenah, Saikuma tayi Shiru tonuwa da Inno da yusuf sunce Abari su bayyanar da kansu tukun.

Kiran Sunan Nazir da Abba yayi yasa ta dawo daga tunaninta.

Nazir kaifa kanada wacce kakesone Ko kaima Saina nema maka?

Inda inda Nazir ya fara Abba..inadashi Amma Karatu take Yanzu.

Kallonshi Abba Yayi da murmushi yace toh kasanar da iyayen yarinyar kanason ta?

Sosa kai yayi yace bansanar dasuba Abba nabari Saita karasa.

Abba cewa yayi yakamata kasanar dasu Yanda data karasa Saimuje neman Aure Ayi Abun Nan kusa. toh Abba insha Allah Nazir yafada.

Kallon Leemah Abba yayi yace ke Halimatu.

Saida gaban Leemah ya fadi Sosai.tace Na'am Abba!

Ina feenat ne?

Abba tana Sama tace kanta ke ciwo.

Yazeed dake Zaune Cikin Ranshi yace "Ayya Shiyasa banganta ba, Nayi tunanin ma ko'itace taje kirana danaji Ance wai nace Ina Zuwa,Nasan babu memun Rainin Nan sai Ita, Ashe ba ita bace.

Marairace fuska yayi lokaci guda Kuma Kamar bashi yayi maganar ba ya hade rai Yana ni ina ruwanama da ita" maganar Abba ta katse shi. toh Halimatu dake da Ita Kuma Zan dawo kanku Amma Saikun karasa karatun naku. toh Abba Leemat ta fada kanta a kasa.

Kallon dad yayi yace Umar ko kanada magana dasu?

Aa Ahmad Ai duk Abinda Xan fada ka rigani, Yanzu Kawai maganar Feenah ce, Zamuzo neman aurenta wajenka d'ana Ke bukata.

Kallonshi Abba Yayi yace Umar Wani d'a gareka bayan Nasir da yazeed? d'ana d'an wajen Nasir yayana.

Oho Abba ya fada yace mutan yola Zakace, Nayi farin Ciki dajin Wannan Abun,kahada Zumunci Allah ya biyaka.

Amin.

Dad yace Ya kalli Leemah yace, halimatu taso kawar taki kice tazo mutafi.

Toh tace Tayi hanyar Sama.

Feenah na kwance Gaba daya tarasa kanta, bakin Cikin halin dataga Yazeed da mufeeda Suke Kawai take.

Maganganu barkatai take Cikin Ranta!

Ashe Haka mum taji Ranar data ganni ina Aikata lesbian?

Tabbas dole ta Suma adaidai lokacin Nan. hawayene ya fara zubo mata Yayin da take fadin nakara nadama da tsanar Kaina Akan Abunda na Aikata a baya, gashi Yanzu Na nashiga damuwa da bakin ciki kan Abun da brother din Leemah yayi, wai Nan ma Dan ba yaya Nazir bane, narokeka ya Ubangijina Ka gafartamun Abinda na Aikata Abaya,ya Allah kabani ikon danne Sha'awata harxuwa Sanda Zanyi Aure, Na Amince Kuma Xan Auri Kabeer kodan na kare mutumcin kaina.

Yanzu Shi yayan Leemat ya rasa dawa zeyi Zina sai wannan kazamar yarinyar, Allah kadai yasan Sau Nawa Suka aikata wannan badalar. toshe bakinta tayi Sabida kukan daya tawo Mata! ya Allah karka tsayar dani Sheda Tunda ni banga Suna aikatawa gaban idona ba, Abinda nagani kiss. toh kodai maganar Su kausar gaskiyace dasukace yarinyar Zata lalatashi?

Kai "Aa" bayanda mace Zata lalata namiji damachan Halinshi ne Shiyasa yake ma Mutane Wani gani gani.

Numfashi ta Sauke Ahankali Allah kaciremun tunanin wannan Abun,Sukuma Allah kashiryesu.

Tashi take kokarinyi Leemah ta tura kofar, da Sauri Feenah ta goge hawayen fuskarta.

Karasowa Leemah tayi tace besty ya kan?

Yayi Sauki besty yanzuma nake Shirin fitowa.

Ji face dinki yanda duk ta kumbura kuka kikai ko?

Aa bacci nadanyi Leemah. bacci Kuma idonki yayi jaaa haka, kodai bro yamiki Wani abune dakikaje kiranshi? dan tsaki feenah taja tace Kinfi kowa Sanin banason tambaya irin haka, yayan naki menene hadina dashi dazaimun wani Abu.

Murmushi Leemah tayi tace Kuma hakane fa, kitashi dad nakiranki Xaku tafi.

Toh Feenah tace tashirya ta sauka Kasa.

Yazeed na ganinta gabanshi Yafadi Dan tayi Wani fiyaut,Kamar ba'itace jiya tagama mishi Rashin Kunya ba!

Jiyayi Yanason Sanin Meke damunta gashi ba dama.karasawa tayi parlon tana gaida su Mamy, Amsawa Sukayi Suna mata ya jiki.

Hada ido tayi da Yazeed ta wurga mishi harara Cikin Ranta tace jishi Kamar bashi yagama iskanciba! ai dama mubeen dinne yaje kiranka daya tona.

Shima Magana yake Cikin Ranshi "mema yasa nake damuwa da yarinyar Nan?

Wama yasani ko kallon iskancinta ta gama idonta ya koma haka jarababba kawai" dad ne yace kutashi mutafi ko.

Tashi sukai gaba dayansu har nazir Sukai hanyar waje daidai Sanda Yazeed yakara kallon Feenah itama Akai Sa'a tajuyo Atare suka Sakarma junansu Wata harara Sai a idon Mamy.

Tabe baki Mamy tayi tace Sukuma wa'inan ko lafiyarsu Oho.

Fita sukai suka Shiga katuwar jeep din dad Nazir yashiga tukasu yayin da Feenah ke gaba kusa dashi, Su mum Na baya tare da Twins.

Yusuf A birnin Zariya! besha wahalar kai kanshi gidan Su Kausar ba, Tunda dama location ta tura mishi.

Kiranta yayi Ya Sanar da'Ita ya karaso.

Me gadi tasaka ya Shiga dashi part din da'aka tanada dan Saukar baki, ba karamin kayata wajen Akai ba dan Yusuf tsayawa Kawai yayi yana kare ma babban parlon kallo. bama Sai angaya maka gidan Sara dubai kazoba.

Zama yayi adaya daga kujerun da'aka Zagaye parlon dashi gabanshi fruits ne makil.

Wata yar matashiyace tashigo Sanye da uniform da Alama Aiki take Agidan, daret wajenshi ta nufa ta mai Sannu da zuwa amsawa Yayi, Kausar din tace tanazuwa.toh yace.

Tafara yayyanka mishi fruits din daga bisani ta fita.

Ba'afi mintina10 ba tsakani Saiga Kausar tashigo face dinta dauke da Murmushi, Sanyi take cikin wata doguwar riga Arabic gown ce mai launin Brown, red din mayafi tasaka ta Zagaye Saman kanta dashi yayinda takalmin kafarta ya kasance Jane, dankunne da Sarkar wuyanta zuwa Abin hanunta suma duk jane.ga Wata kwalliya data tsantsara kamar Zata zaben sauraniyar Kyau...tsayawa Yusuf yayi yana kallonta Gani yake kamar ba kausar ba domin gaba daya ta chanza mishi.

Iskar data hura mishi a Ido ita ta dawo dashi Cikin hankalinshi.

Tashi yayi tsaye yana facing dinta.

Kinyi Kyau my Kausar, Murmushi tayi tace Tnx my Yusuf.

Zama Sukayi Atare tana mishi ya Hanya.

Waye ya gayamiki masoyi na ganin Akwai tafiya Xuwa wajen masoyinshi. hakane kuma Sweetheart bakaci Komai ba.

Inajiran kizo kibani, karka damu Soon.

Kinsan yau gaba daya nazo da Shirina, domin ni Ayanda nake Ayanzu baki Adaura mana aure Ayau Natafi dake ba. dariya kausar tayi Sosai tace kacika Xumudi.

Kece kike ganin haka yusuf ya fada Yana daukan Ayaba dake kusa dashi.

Kawo na bare maka ko.

No Indai kika bare kece Zaki bani dan haka kawai na hutar dake.

Haka sukaciga da firarsu Cikin kulawa da Nuna Soyayya tsantsa, ta Yanda kowannesu yake ganin bazai iya rayuwa ba dayanshi ba. bari nakira maka Su Hajiya Ku gaisa, Kina nufin daddy ma Yana nan?

Eh mana.

Gyara Zama Yusuf yayi yace gara dana Saka manyan kaya kuma nazo da Shirina.dariya Kausar Ta fita tanayi.

Ba'adau Wasu lokutaba Iyayen Kausar Suka Shigo Cikin parlon.
Chapter 8 · 0% Book details