← Book details Yar Lesbian Ce 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 25

Sashe 15

Yar Lesbian Ce 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aha tunda Ka gane ta wajenta Xance Zani kaga babu mai kawo wani Abu Tunda dama chan muna Zumunta da ita,takanje katsina wajena Nima nakanje Yola,yanzune da girma yazo mana Sai Ahankali. da kyau inno lallai maganar Hausawa ta tabbata "Abunda Babba ya hango yaro ko yahau tsani bazai hango ba.

Atoh Aishi Abokinka Ya daukeni Kamar mara wayo karyar boko Kawai.

Inno kinsani dariya Allah dai yakara jamana da kwanakinku.

Amin dan Albarka.

Kinga Tunda Nasan gidan a Yola Saina kaiki da kaina.

Haka Za'ai yusufa Zansaka Ranar Zuwa.

Toh inno. kalli fa hanunka yanda yayi ja! inno ba damuwa Yusuf ya fada yayinda ya tashi Bari nashiga wajen yazeed Inno naga mamy bata kasa.

Bacci take yusufa idan kun gama kacema yazeedu din ina nemanshi toh zan fada mishi Inno.

Fita yayi Ya nufi part din yazeed.

Kwance ya sameshi ido Alumshe daga gani wani Abun yake tunawa.

Kai Sarkin tunani tunanin naka kuma be wuce kan Abu daya ba wanda ka Kasa Sanar dani domin Kana gudun fallasa.

Tashi yazeed yayi Zaune Ashe kasan kai dan fallasa dinne!

Kaini ba wannan fallasa din ba.

Toh wacce?

Zakasani Sai nan gaba.

Tabe baki yazeed yayi toh Yanzu wace Shawara kazo nema?

Kaini Rike Shawararka Inno ta warwaremun komai kuma Nasamu mafita.

Ai dakasani daga Chan ka wuce tunda tabaka Shawara irin ta tsofaffi kuma Ka dauka.

Kwarai na dauka domin na hango Nasara, Kuma nabiyo Nace maka Zani Abuja gobe idan Zaka.

No mai Zanje inyi ni Ka gaida Leemat Kawai.

Matata fa banda ita Kenan?

Yastina face yazeed yayi Idan Kaga zaka gaidata Ai Shikenan.

Ok naji feenah fa?

Hannu yazeed ya daga mishi?tashi katafi malan. dariya Yusuf yayi yace basai ka kureniba Xantafi Akwai lokacin Dazaka nemeni.

Ni bawani nemanka dazanyi katashi ka tafi tunda mace Ka koma harda Saka Wannan jan Abun a hand dinka.

Yusuf Shi har yamance da Lallen daya taba kallon Hanun yayi yaga har yayi ja Murmushi yayi yace Kama tunamun Wani Abu bye Ni gobe da wuri Zan tafi.

Yadai fi maka katafi yanzu ma duk kabi ka'isheni da wani tafiya Sai Kace idan kaje wani Abun Arziki Kake Samu mtsww.

Umm Kodai kissing din matata nayi Ai nafi wani Yusuf ya fada yayin da yayi Hanyar waje.....Oh naman ce Kakarka na kiranka ma.

Ni babu inda Xanje tunda ba zamanta Nake ba.

Ware hannu Yusuf yayi Alamar ko Ajikinshi ya fita yabar dakin.

Kausar gobe bani Zanyi miki kwalliya ba kamata yayi Kije A tsara miki ita domin inason ki kara burge yusuf gobe.

Kinjiki feenah indai kara haukatashi Zakice.

Mai yasa Zaki haukatashi black beauty din face dinki nakeson gobe yaga ta chanza mishi gaba daya.

Nidai kawai kimun feenah Ahakama kinga yanda yake Surutai inaga naje Anmun.

Yes nafison Haka Ai Kausar.

No Ni banaso.

Leemah dake Saurarensu tace besty Rabu da Ita maybe tashirya Zama da kishiya ne! da Sauri Kausar tace Allah ya kyauta mai fatan tsiya.

Ai ba fatan tsiya namiki ba, matan dasuke Tsala kwalliya Akan titi yanzu Zasu Siye Zuciyar mijinki,idan kikai mishi kuwa ba lallai Idan yagansu Su burgeshi ba Sabida yariga ya gani Awajenki, kinfi kowa Sanin halin yan'matan Abuja tunda Kina ganin irin Abun da Suke Akan titi.

Shiru Kausar tayi Cikin Zuciyarta tasan Gaskiya Leemah ta fada but tana tsoron kada Yusuf ya Zuzuce mata.

Afili tace Allah yakaimu Sainaje.dariya Suka kwashe dashi feenah tace Eyya my Kausar kedai bakison kishiya.

Feenat batada dadi yanayin yanda Ake fada.

Hakane Amma Akwai nagartattu har yanzu.

Toh Allah Ya hadamu dana gari.

Amn.

Ni Wai Wannan tarkacen Maisuke Kara miki Kullum Saikin sha banga Kina kiba ba bare naga kin chanza, dama gyaran jikin Kawai muka Samu mai yi tazo tarinka miki Anan.

Lallai Feenah Ki gwada Sha Zakiji Chanjin Dana Samu Ajikina, gyaran jiki gara idan mun koma kinga yanzu munashiga Rana Kuma gyaran yan Sudan ma yafi.

Waye yace miki Anan babu yan Sudan Kausar?

Feenah ina Kika gansu toh?

Nidai Nasan baza'a rasaba.

Shikenan idan Ansamu Saimu fara.kudai fara keda Leemah nikam banyi.

Eh tunda da kyanki Ai bakya bukatar gyaran jiki daman.

Hmmm feenah tace.

Leemah ce rike da Cup tayo wajen feenah, gashi kisha kiji besty.

Mene wannan Leemah?

Abin Kausar ne wannan, Akwai dadi yanzu Nasha Kamar Zuma Wlh.

Kallon Leemah Kausar tayi tana gumtse dariya.karba feenah tayi tafara Sha Wow Akwai dadi kuwa Wlh.

Eh mana ai nafada miki Leemah ta fada.

Tafff yau daki Zanje nabiya kudi na Zauna domin bazanyi kwanan Xaune ba Kausar ta fada tana dariya.

Me yasa kikace haka Leemah ta tambaya?

Sabida bakusan Me yake Saniba Shiyasa kuka dauka Kuka Sha wato kwadayi dadi.

Zaro ido??feenah tayi Nashiga3 me yake Sawa Kausar?

Ku kuka Sani tunda kunsha Ai Zakusan me yake Sawa.

Wayyo Leemah kece kikaja koma miye.

Ni ba ruwana mai yasa dana baki bakice bakya Sha ba.

Tuni har feenah ta fara Hawaye Shikenan kila Yau mutuwa Zanyi. dariya kausar tayi mai Arhar hawaye Kawai toh tshokanarku Nake.

Kinma kanki Leemah ta fada tayi Kan bed.

Ita dai feenah bata yarda ba Haka itama tayi kan bed daniyar bacci.

Kausar saida ta gama waya da Angonta ya Sanar da'ita gobe da wuri Zaizo tukun taje ta kwanta itama.

Page....38
Misalin karfe 2 Yusuf ya'isa garin Abuja.

Skul din su Kausar ya nufa Kai tsaye.

Yana Xuwa yayi parking Car dinshi yashiga Ciki.

Room dinsu ya nufa yana Knocking ba'a dau lokaci ba Kausar ta taso ta bude mishi.

Subhanallah Yusuf yafada Cikin Ranshi.

My Sweetheart Come in ka tsaya waje why. daidaita Natsuwar Shi yayi ya sakanmata Murmushi Oya Muje.

Ciki yashiga feenah da Leemah Suka gaidashi.Amsawa yayi Cikin kulawa yace feenah kinyi wuyar gani duk Sanda Nazo Ace kin fita...Kamar bazatai mgn ba daga bisani tace Eyya.

Shiru yadanyi domin yasan Halinta ba magana Xata tsaya Suyi ba.yazeed yana gaidaki.

Nikuma Kodai Leemah kake Nufi?

Kedai yace! tabe Baki tayi ta tashi Xata fita.

Haba my feenah kince yau Xama Xakuyi Ayi fira daku kuma Zaki fita.

Oh Sorry Kausar yanxu Zan dawo.

Ok kada kidade pls.

Batace komai ba tayi waje.

Kallon Leemah yusuf yayi leemah brother dinki da besty dinki Suna bani wahala fa. dariya Leemah tayi Sorry yaya Yusuf Very Soon komai Zai Xama lbr.

Kinjiki Saikace kuna wani Abu Naga daga ke har Kausar din bakwa wani kokari kan Wannan Abun Kodai Baku Amince da hadin bane? da Sauri Leemah tace kai yaya Yusuf inaga duk nafiku doki kan Wannan hadin kawai dai mubi komai Ahankali Har Su furta da bakinsu.

Toh Shikenan Jiya inno kecewa 3months masu Xuwa Xa'aje Ayi maganar feenah da kabeer a yola.Xaro ido Sukayi Kausar tace da gaske?

Eh mana my wife Amma kada kudamu Akwai Allah Sa'annan inno takawo Shawara Mai Kyau.

Me tace?

Tace Xataje Yola Amma bansan me Zatai ba.

Kai ita kakus din Nan kada taje tabamu matsala fa.

No Leemah inaganin inno tafimu Son wannan Abun ya yihu Kada kudamu Nasan dalilin da Zai kaita insha Allah dalili mai Kyau ne.

Allah yasa Toh!

Amin Leemah yazeed yana gaidaki.

Bana Amsawa bayan tunda muka dawo yaki Xuwa mun Visiting.

Sorry Sister inaga duk Cikin buye mana dinne bayaso yafiye Xuwa Ku gane.

Lallai kam Leemah ta fada tana kokarin tashi.

Marairaice face Kausar tayi Leemah ina Xaki kuma?

Ke miye Naki na damuwa bayan gaki ga Rabin ranki.

Rabu da ita Leemah maybe Saceta Xanyi ko. dariya Leemah tayi yaya Yusuf inma ka saceta Ai halal dinka ka Sata.

Shiyasa kike burgeni kanwa ta.

Aikuwa Leemat ta fada tayi Hanyar waje da Sauri Kausar ta taso Haba Leemah miye haka Ina Zaki?

Sorry my Kausar feenah tamun text yanzu Xan tayata divan kaya.

Pls karku dade.

K Cutie yanzu Zamu dawo daga Haka tafita.

Tsayawa Kausar tayi taki komawa Ciki kuma taki juya baya. tasowa Yusuf yayi yana Murmushi yakarasa kusa da Ita.

Jikinshi ya manna A bayanta yasakalo da hanunshi Xuwa kan k'ugunta.

Kinyi kyau my Sweetheart.

Wannan dress din yabani Sha'awa kyanki yakara fitowa I love you So much Sweet wife.lumshe ido tayi tanajin dadi Cikin Ranta da Allah yabata miji mai kaunarta kamar Haka.

Juyo wa tayi tana fuskantarshi Thank you my Sweetie nd I love you More.

Rungume ta yayi Sosai but my Kausar why...katseshi tayi Yayin data Zame jikinta Zauna ka huta ta fada yayinda ta koma ta Zauna.

Kusa da ita ya karasa Shima ya Zauna. drink din Dake gabansu ta tsiyaya mishi A Cup ta mika mishi.

Ni Saidai kibani Yusuf ya fada yana kashe mata ido daya.

Murmushi tayi tashiga bashi yana sha.

Kurba Kadan yayi yace is Ok.Nidai kashanye duka.

Nidai ya isheni ya fada yana yin irin maganarta.

Dariya yabata lokaci guda kuma tazaro ido...What is dis my Yusuf ta fada tana nuna dan yatsanshi.

Kallonta yayi da murmushi Lalle ne.

Mai ya hadaka da Lalle kuma? bansan yana jaaa haka ba Shiyasa Na Saka mata!

Ido tafito dashi waje take kuma tace wace?

Shiru yadanyi daga bisani yace Kairat Mana.

Kairat!

Who is She?

Dan dukan goshin shi yayi yace Am Sorry ban miki Bayanin ta ba....Me kake So Kace kuma? ya kike daga Hankali haka bafa Wani Abu bane Xuwa 1week inaga Xai fita.

Marairaice face tayi takara matsawa kusa dashi pls wace Kairat Sweetie?

Cikin Ranshi yayi Murmushin Nasara Lallai Mata Akwai kishi jita yanda ta Rude lokaci daya...pls tell me Something About her. yarinyar Uncle dina ce data nace wai tana Sona, Yanzu data ga Nayi Aure inaga tajanye maganar, jiya tazo gidanmu tana Lalle, takasa Saka Sauran Shine tace Nayi helping dinta, bansan Zai b'ata ni haka ba yasa Nayi mata.kuma dai itama tana dan taimaka mun dawasu Abun idan tazo,Tana hadamun breakfast tana gyaramun daki kinga ai yakamata nima Nayi Mata Abinda take So ko.? tunda yafara magana Kausar tafara Sake Sake Aranta.

"Me kenan yace budurwanshi ce Ada, Sannan kuma yace tana taimaka mishi.
Chapter 15 · 0% Book details