← Book details Yar Lesbian Ce 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 25

Sashe 18

Yar Lesbian Ce 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yanzu kwannata uku Awani daji tarasa yanda Zatayi,Sai yau tagane Hanya tashigo Cikin gari dan haka takeson Su taimaka mata ta tsaftace jikinta kafin taje tasha. jin yanda take bayani tiryan tiryan yasa yan'gidan Suka gane Tanada Hankali tausayinta suka ji,Suka nuna mata boket da Ruwa dauka tayi taje Tayo wanka tasaka Sabon kayan data Siya. turare dake Cikin jakarta dashi ta feshe jikinta lokaci daya ta chanza Zuwa Mufeeda dinta Sai yar ramar datayi ta wahala.suma mutan gidan Sunyi mamaki dasukaga ta chanza farar daya gdy tamusu Tare da basu kudi tanufe tashar garin Sokoto dan komawa kaduna.

Akallah Mufeeda takai 2weeks tana jiran yazeed Yazo neman aurenta Amma Shiru,dan haka lokaci daya ta yanke Shawaran Zuwa wajen yazeed din.

Ranar dataje tasameshi ba karamin wulakancin yazeed ya mata ba dan har dukanta yaso yayi aka hanashi, Yamata kashedin kada takara xuwa wajen Aikinshi ko gidansu.haka tafito tana Tunanin kenan bokan Nan be mata aiki ba yasa ta ta wahala Kukan bakin Ciki tayi harta gode Allah.

Asaran kudin datayi Awajen bokan Sunada yawa. yanzu ka koma kamai wulakancin ya maka Asiri ka lalace gara naje wajen wani bokan Na gwada Sa'a ta.

Saida Mufeeda taje wajen bokaye uku duk Abu daya suke fada mata yazeed baya Wasa da ibada Asiri baze kamashi ba,Haka tayita fama saidai ta kashe kudi Abanza a wife.tasha Alwashen Sai Aikinta ya kama yazeed kota halin kaka ne.

Zansan mafita Mufeeda ta yanke shawaran hakan Cikin Zuciyarta.

Su feenah karatu Ake tukuru ba Sanya gaba dayansu yanzu sunmaida hankali kan karatunsu Kasancewar wata daya kadai y Rage musu su kammala.fatansu Ayanzu be wuce Su Samu Sufita da Good Result ba.

Babu Abunda ya Ragu Cikin Soyayyar Leemah da Nazeer sai ma Abinda ya karu.Zuwa yanzu iyayen Nazir da iyayen Leemah Sun San Cewa Akwai maganar Aure Atsakanin yaran nasu biyu.Farin Cikin dasuka nuna baya misaltuwa dan har Walima Mamy tayi Acewarta Abinda ta Dade tanason ya kasance ya kasance.

Rayuwar Kausar da Yusuf ma gwanin Sha'awa Suke yinta.baya wuce 4day's bezo ganin Kausar dinshi ba.

Duk sanda yazo kuwa yana Samu ya rage Zafi Abu dayane Kausar har yanzu taki yarda Shine Yusuf ya kusanceta, Kunya takeji bangare guda tsoron Abunda Za biyo baya take.Leemah tasha mata fada kan tayarda da mijinta babu wata matsala Amma ina taki.

Khadija babu yanda bataiba dan ganin ta dawo Cikin su Amma fir Sunki yarda da Hakan, feenah ce taja mata kunne kan kada takara takowa zuwa room dinsu,ba karamin takaici Ranar khady tayi ba dama haushin feenah takeji,dan haka tasha Alwashin Saita mata Fiye da Abinda tayi mata Ayanzu.

Hankalinsu Ayanzu ya Rabu biyu Ga Exams din dasuke Shirin yi gakuma bangare guda malamin dake koyar dasu islamic yasasu Sunemo Topic Akan matsalar Matan Aure Ayanzu!

Yace Hakane Ze gane cewar karatunshi ya Zauna ko Aa.Zasu gudanar da walima Ranar dazasu fita dan haka Ranar Zasu gabatar da program din.

ZUWA yanzu Atsakaninsu Suke tattauna yanda zasu gabatar da Abun domin sunason faranta Ran malaminsu Aranar walimar.

Mr yazeed har Yanzu be Samu wacce tayi daidai da Ra'ayinshi ba dan haka yanzu ya bar Zaben Allah agareshi.

Matsalar daya yanda Abba ya takurashi yasamo matar Aure yabashi lokaci kankani,yace idan besamu ba Akwai wata yar Abokinshi ita Zaiba yazeed din.

Haka Rayuwa tacigaba Kowa da tashi damuwar Arai.

Yau tunda Inno ta farka take jiran Abba yasakko Kasa.

Abba na sakkowa ta tareshi Amadi katashi lafiya ko?

Lafiya qalau inno yanaganki da kaya haka?

Yawwa Amadi yola Nakeson Zuwa Ayau din nan!

Yola kuma inno me Zaki Achan?

Yau naga ikon Allah tsareni Zakai da tambaya,danfa Kada kanemeni ne yasa nafada maka dayanzu na tafi ma ni.

Mamy dake Sakkowa tace Ayi hakuri mamah munason musan wajen wa Zaki!

Wajen Aminiyata zani Nafisatu kakar Nazir.

Ayya inno Zumunci Zaki hakan yayi dadai Ai.

Aikuwa fatima nadade banga Nafisatu ba gara Muma murinka Zumunci da Sauran lokacin daya rage mana.

Allah yakaro muku tsawoncin Kwana da lafiya mai Amfani Abba ya fada.Atare inno da mamy Suka Amsa da Amin!

Inno yazeed ne Zai kaiki ko?

Da Sauri tace Aa nikam bana gayyar Sode, Yusufa ne Zai kaini jiya na sanar dashi,idan danta tsaka ne nikam na yafe,hakanan yaje yasakani a Rami.

Inno tunda dai Zuwa jibi Zamuje kibari muje tare kada adaura ma yusuf Nauyi.

Aaa nikam bazani daku ba Amadi dan ina tsohuwa Kawai Saina Shiga Cikin Maza.tafiyar ku daban tawa daban.Kuma yusufa yaron kirki shine yace Zai kaini bawani Nauyi kawai nadanje Mu gaisa Kwana biyu ne nadawo.

Toh inno ba damuwa Allah ya tsare Hanya bari nafita nayo miki tsaraba yar kadan.

Allah yamaka Albarka Amadina Saukin kan Nan naka A Nono kasha, Shikuwa Yazeed Chan yabiyo dangin uwarshi dan ba fatima yabiyo ba itama Akwai Saukin kai. dariya Mamy tayi ta tashi tabar wajen yayin da Abba yafita yimata Siyayya.

Atare Abba da Yusuf Suka shigo bai wani zaunaba yace inno tafito.fita tayi Su mamy namata rakiya har saida motarsu tafita tukun Suka koma Ciki.

Page...41/42
Misalin 5 na yamma inno Suka karasa garin yola. gidan Alhaji Ibrahim Suka nufa gida mai tsohon tarihi da nagarta.

Cikin farin Ciki da doki Inna Nafisa ta taresu.

Cikin lokaci kankani iyalan Inna Nafisa Suka karaso gidan.nan Aka Zauna Anata firar yaushe gamo.

Bayan Sunci Abinci Anhuta Yusuf Y yashirya domin komawa kaduna.

Inna Nafisa ita ta dakatar dashi da Cewa Haba Dan nan Kamar Ana korarka Yanzu idan ka Kama Hanya kaduna dare Zai maka Sosai Kai baka tsoro garin nan ne?

Sosa Kai Yusuf yayi Inna gobe inada Aiki Sosai A Office Shiyasa.

Likita bokan turai kayi dai hakuri Xuwa gobe koda da Safe ne Saika tafi.

Shikenan inna nabari Allah ya kaimu.

Amin Inna Nafisa tace yayin da tashiga neman babban jikanta Kabeer (My Siriki??) Akan ya Sama ma Yusuf wajen Kwana.

Karasowa Kabeer yayi Cikin ladabi ya gaida Inno da fara'a ta Amsa yayin da ya juya ya mika ma Yusuf hannu.gaisawa Sukai Cikin girmamawa tunani Yusuf yashiga yi Cikin Ranshi" wannan Shine Kabeer din kenan.

Ba laifi ya hadu daka ganshi kaga mai ilimi, gashi da kyau kasancewarsu Fulany, Ammaa Gaskiya nafison feenah ta Auri yazeed domin wlh sunfi dacewa Kuma ni inaganin Alkairi Cikin Aurensu." Katse shi Kabeer yayi muje ko.

Ok.Ok.

Yusuf Y fada Suka fita.

Inno fira Suke Sosai da inna irin firarsu ta tsofaffi.

Inno Cikin Ranta taso ta bar maganar daya kawota Xuwa gobe Amma Ina batajin Xata iya daurewa maganar takai gobe.

Nikuwa Nafisatu wannan Shine kabeer din Dan wajen Naziru?

Eh Shine Kinga yayi Saurin girma Halan, Haka yayan Zamani Suke Kiga tabarakallah da Anhaifosu Lokaci kankani kiga Sun girma.

Gaskiya Kam Ainima mamakin danake Kenan, Shine Za'a Aura ma Takwarar taki kenan?

Eh Shine da Zasuzo Nan da jibi kan maganar, Amma dazun Naji Nazirun yana cewa Zaiyi tafiya dan haka Abari Zuwa Nan da Sati biyu, Kinga Zuwa lokacin takwarar tawa ya Rage Saura Sati daya ta Kammala karatun nata.

Kallonta Inno tayi Au kina Nufin yanzu Sun daga tawowar?

Eh Sun daga ta.

Madallah inno ta fada Cikin Ranta domin Abubuwan Suna Xuwa mata Cikin Sauki.

Afili cewa tayi Ai kabir din daga ganin shi yaro mai Hankali ne,ga natsuwa Amma bansan me yasa me Sunanki bata Sonshi ba! juyowa inna tayi tace bata Sonshi Kamar ya?

Wato basu fada miki gaskiya ba Kenan ko?

Inno fadamun kinsan yaran nan basu dau tsowo da Muhimmanci ba.

Aa kedai Nafisatu inaganin gara kiji daga bakinsu domin Abun ya shafeni Sai Aga Kamar Nayi Shishshigi.

Kai Aminiyata Dan Allah kada kirufemun mana. toh shikenan bari kiji wannan komawar dasu Nafisatu Sukayi karatunsu, Kafin Su tafi tazo ta Sameni Tana kuka,lokacin ta dagamun hankali na matuka,Na tambayeta ko lafiya.Shine take cemun dan Allah na Sanar da mahaifinta ita batason Kabir tanada wanda take So, Nayi mamaki data fada Amma kinsan yaran Zamani idan basa son Abu Aka tilasta musu Nan da nan Saisu kama ciwo, dan haka nace mata toh waye takeso Wanda ya wuce dan uwanta.

Budar bakinta tacemun wai yazeedu jikana dan Wajen Amadi!

Nayi Salati nace ni bazan iya tunkarar Mahaifin ta da maganar ba domin Za'aga kamar Dan yazeedu jikana ne Shiyasa nakeson kashe maganar wancen Auren.

Alokacin tagama magiyarta nace badaniba tayi hakuri ta Sanar da Umar da bakinta.toh kinji bansan ko tasanar dashi dinba.

Haka yazeedu yanachan duk ciwo yake Anrasa gane Kanshi Saini dana san ciwon Son Nafisatu yake, dana fada ma iyayenshi Cewa Sukai ba haka bane wai Nafisatun da an tsayar da magana da dan'uwanta tayaya Za'ai haka.

Dan haka na Sharesu ban kara magana ba Allah yasa Aurenta da kabeeru Shine mafi Alkairi ba shikenan ba!

Sauke Ajiyar Zuciya innah tayi ikon Allah Ashe maganar da Nazir karami yazomun da ita kwanaki Gaskiya ce????yazo y fadamun cewa Nafeesat nada wanda takeso Alokacin nan banzatar da Zancen nayi.

Allah Sarki inno ta fada Mai yuwuwa lokacin danace ta same iyayenta da maganar Shine ta kasa fada musu,Shine ta fada ma dan'uwanta.

Da Sauri innah tace toh Aikuwa bazaiyu ba,Kafin Alhaji Ibrahim ya Rasu Saida ya gargadeni da kada nayarda ko bayan Ransa Ayima jikokinshi Auren dole, Hanya mafi Sauki gobe Zan Samu Naziru da maganar Asan yanda Za'ayi.

Aa kedai Aminiyata tunda Anyi niyar Abu Kawai Amusu Aurensu.

Aa inno ban yarda Ashiga hakkin yarinya.....Kabir daya Shigo yanzu ya katsesu.

Xama yayi gefen kakarshi.inna da inno Naji Abinda kuke tattaunawa, Nima dama Nazo nafada muku damuwata, tun lokacin ina karatuna A London muka hadu da Wata yarinya Saida nasa Akaimun bincike Akanta kafin nafara Soyayya mai karfi da ita, dan Allah kutaimakeni ni ita nakeson Aure,nadade dasanin Feenah bani takeso ba domin wani Xuwa da baba yasani nayi naganta tare da yazeed dan haka banma karasa Ciki ba nadawo garin yola.

Inno dakejin Kamar ta tashi ta taka Rawa tace haba kabeeru kuyi ma iyayenku biyayya Ku auri juna,Zakuga Albarka Abun Agaba.

Inno inada wacce nakeso Kuma itama feenah tanada wanda takeso kuyimana adalci kuba Kowa Wanda yakeso dan Allah.dafashi innah tayi ka kwantar da Xuciyarka indai ina raye Sainaga burin kowannenku ya Cika.

Tashi kaje ka kwanta.tashi Kabir yayi yana fadin Allah yakaro muku lfy.
Chapter 18 · 0% Book details