← Book details Yar Lesbian Ce 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 25

Sashe 21

Yar Lesbian Ce 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Amma kwa hada matan nan daku Wanda kanku yake Aduhu haryanzu baku waye ba?Ku bakusan duniya ta chanza ba kuna yawo cikin lullubi kamar wasu Munafukai??wlh nidin nan dakuke gani n.a. tsakanina da namiji babu wata Amana domin shi ba dan goyo bane ba,ke matukar ma Naga Zaimun wata gargada sainace Ya Sakeni nikuma na bidi Wasu ga mazan Nan suna Yawo Kamar janfer a jos.

Ni iya Abinda zan fada Kenan.

Mai gabatarwan ce ta Amsa toh Allah ya kyauta Zan'Iya cewa kawai Anan.

Malama Feenah Umar Faruk bisimillah.

Yazeed da kanshi ke durkushe besan Sanda ya dago yana kallon yanayin yanda take tafiya Kamar batason taka Kasa.Subhanallah 1yr danayi kadai banga yarinyar Nan ba kalli yanda takara girma da Kyau dan tsaki yaja inama Ruwana da ita.

Cikin natsuwa ta karasa Wajen..Sallama tayi Cikin Xaxxakar Muryarta Wanda ta dira Cikin kunnan yazeed!

" She is So Cute nd She have a Nice Voice" Cikin Ranshi yayi maganar Amma Sai yaji Yusuf yace Allah ko?

Kenan Afili Nayi maganar.

Kallon Yusuf yayi yace yes kallitafa nadade inason wakokinta wayarshi ya Nuna mai Wata mace.dariya Abun yaba Yusuf Sosai yace Kawai ka Aureta.

Tsaki Yazeed yaja yabar maganar.

Magana feenah tafara.

Haba malama Khadija Koda yake bakibani mamaki ba domin Kowa yasan Halinki da tarbiyarki.

Wainan Abun da yan'uwana suka fada aiba kwance Xani a kasuwa bane, Gyara kayanka Ai baya Xama Sauke mu Raba.dakike cewa bamu San halin mazan nan ba toh kinsan duk Namijin dayake sonka baxai wulakantaka ba.domin Manzo S.A.

W.

Yace (duk Wanda baya kishin matarsa bazai Shiga Aljannah ba) kuma dakike maganar kishiya ai Allah bai Hana mutum ya Auri mace fiye da daya ba.

Saurara kiji Abinda Allah S.W.A. ya fada Cikin Al'Qur'an *FAMKIHU MAZADA LAKUM MINAN NISA'I MASANA WA SULASA WA RUBA, FA IKIFTUM ALLAH DA'ADILU FA WAHIDATA AU MA MALAKAT AI MANUHU*! ( ku Auri Abinda yamuku dadi nadaga mata biyu biyu,ko uku uku,ko hudu hudu.idan kunsan bazakuyi Adalci Atsakaninsu ba toh ku auri guda daya kokuma Abinda hanunku ya mallaka na daga kuyangi) dan haka Malama Khadija Kinji Allah be hanasu Auren mata hudu ba,
Sadai idan bazasuyi adalci atsakaninsu ba.kuma dakike magana Akan fita har Kina cewa wai muhada kanmu da matan Annabawa kona Sahabbai!

Kwarai kuwa dole mutun musulmi yayi koyi dasu, domin sudin iyayen Mumunai ne Kuma Su tsarkaka ne.

Sayyidina Aliyu Allah yakara mishi yarda yace.... (babu yadda Za'ai mace tafita daga Dakin mijinta batare da wata babbar lalura ba,kuma idan ya kasance ma Xata fita tanemi Xanin baiwarta ko maiyi mata wanke wanke ta daura tayanda babu Wani namiji dazai ganta yayi Sha'awarta)Amma saikaga Matan Xamanin nan Idan Zasu fita unguwa Ansha ado Abinda batamawa mijin nata.

Kuma maganar dakike kan Sauran matan Kasashen dasuka Cigaba inda Xa'aga mata a Governor Ko wasu mukamai ai Manzon Allah yace duk jama'ar dasuka Shugabantar da mace baxasu Rabauta ba Ranar Alkiyama.kuma kince tsakaninki da namiji babu wata Amana dayayi Miki gargar Saikice yabaki takarda toh wannan Kuma Sai idan Kinyi Auren.

Allah yasa mudace.daga haka takoma ta Xauna.

Masha Allah jama'a suka rinka fadi yayin da Wata malama ta taso ta Rufe taron da Addu'a Su feenat Sun Samu kyauta masu yawa Dan Har kujeron maka Aka basu.daga Haka taron yatashi Cikin farin ciki.

SU mammy Sun dau hanyar komawa Yayin dasu Leemah Sai Xuwa gobe.

Page...44
Washe gari tunda Safe Su feenah Suka fara Shirin barin makarantar.

Haka kuma dalubai Sai Shigowa Suke Suna yaba bajinta irin tasu feenah, Kusan daidai kone Wa'inda Suke Cikin Skul din da basuzo wajen Su feenah Neman Alfarmar Su Zama kawayensu ba.

Kausar da Leemah Sune masu Amsa musu wanda feenah ita dai Saidai tayimusu Murmushi,Anan ne Suka gane Ashe friends din Su3 basuda matsala da Suna masu kallon Rashin fahimta.Sundai gane Acikinsu Feenah itace marason magana wasu Suna fadi Aransu Miskila ce wasu kuma Suna ganin Tanada Class ne.

Leemah duk wa'inda Suka Shigo Saita Sanar dasu bikin Kausar. da Haka drivern Su Kausar yazo inda Zai Aje Su leemah A kd Kafin ya wuce da Kausar Zaria.

Mota Suka Shiga yayin da driven ya kwashe Gifts din na musamman da Aka ba Su,Dan ma Su Mamy jiya Suntafi da Wasu.

Cikin mota Gaba dayansu Suke kara jin dadin irin Kayutar Xuwa Makka da Akai musu.

Kausar ce tafara magana Nifa Nafison nafara Zuwa Kafin bikin Nan. dama Ai yafi my Kausar daga Chan basai muwuce Sudan dinva.

Haka kuwa Leemah kin kawo Shawara mai Kyau,Amma Ina Zamu Sauka a Sudan kike gani?

Hotel mana Ko kuma gidan Hajiya...wama take?

Gara dai Hotel din feenah ta fada ataikace!

Shikenan Hakan ma yayi yaushe Suka Shirya mana tafiyar Kausar ta tambaya? bari muga Leemah ta fada tana ciro wata takadda.

Kai Ashe jibi nema tafiyar.

Kai haba Kausar ta fada tana karbar takaddar.Kaai d gaske kuwa Lallai Xamusha gajiya.

Kallonta feenah tayi gajiya Ake da ibada See you.dariya Kausar tayi nidai bance ba Naga Yau Xamu koma gida,jibi Muje Saudiyya Xuwa 1week muhuce Sudan,da mundawo Biki Xa'a fara Kinga Kuwa bamuda Hutu.

Zubaida kawai!

Feenah ta fada tana Tabe baki.

Allah ya kawo wanda Zaiyi maganin wannan bakin naki.dariya Leemah tayi tace Amin.

Haka Sukayita firarsu gwanin Sha'awa.

Tafiyar Awa daya da Rabi yakaisu kaduna.

Bari mufara Aje feenah ko.eh yafi kufara Ajeni domin wlh kun isheni daman. dariya Sukayi kausar tace iro Unguwar Dosa Zaka Ajeta ka gane gidan ko?

Ahhh ai kinacewa Unguwar Dosa na gane.yawwa Kaimu Chan daga Nan gidan Hajiya fatima inda kake kai Hajiya Xaka Aje Leemah.Toh toh Toh ba damuwa Ai iro ya fada lokacin dayake parking kofar gidan Su feenat. fita tayi Kausar nafadin sai Mun hadu,Allah yakaimu feenah ta fada tayi Cikin gida.

Leemah wannan Matar brother din Naki Saimun chanza ta.kinban dariya Ai Shima brother din nawa Halinshi ne Kinga vasaisu dafa kansu Suci ba.

Lallai kam Su dafa kansu Amma wannan Shan kamshi haka,ke Nifa har yanzu banma yarda Suna Son junansu ita da yazeed ba,kinsan dai idan da gaske ne babu yanda Xa'ai feenah takasa fada mana.

Mtsww ke Wlh Kausar din Nan kincika maida Abu baya,ke duk pictures da Video's Dana nuna miki basu gamsar ba. toh Leemah bakya ganin tunda mukazo yazeed baizo Abuja ba sai jiya,jiya dinma basu wani haduba bakiga yanda Nazir da Yusuf Suke rawar kai ba har Saida muka hadu dasu Sukaji dadi,Toh babu yanda Xa'ai Ace Feenah Na Soyayya da yazeed kuma Sukaasa haduwa Ajiyan Nan.

Oh My God Kausar har yanzu baki gane boye Al'amarin suke ba basason fa Kowa ya Sanine,ke dakanki kinsan inno bata fadin maganar da ba daidai ba,kuma yusuf din daya fada mana Shima karya yayi kenan?

Ke bama Wannan ba Sau Nawa Ina ganin feenah da bro Yazeed Sun kebe Suna magana idan duk wannan be isheki sheda ba pictures din Dana Nuna miki Ai sun isa.

Ajiyar Zuciya Kausar ta Sauke Shikenan Amma.....katseta Leemah tayi kidai Xauna Xakisha mamaki idan kika gansu da kanki kya Rantse kice dama Chan Atare aka haifesu.dariya Kausar tayi Xanso Naga feenah an yazeed waje daya.

Murmushi Leemah tayi daidai Sanda Aka karaso gidansu.

Toh my Kausar Sai mun hadu pls kigaida Hajiya Sosai.

Tom insha Allah my halimcy bye I will miss you.

Me too bye.

Daga haka tayi ciki Su Kausar Sukayi gaba.

Tana Shiga Twins Suka taso da gudu Rungumeta Sukai ur Wlcm Aunty feenah Suka fadi Atare.

Thanks Cuties muje kada Ku yardani.dariya Sukai mubeena tace Aike babbace bazaki fadi ba.

Waye yace babba baya faduwa Mubeena?

Mai Kyau ne ya fada mana.

Tsaki feenah taja tunowa datayi wa Suke kira mai Kyau, Shikenan ka dawo yanzu Zasu isheka da Xancen banza.kallonta Mubeen yayi daidai Sanda Suka Xauna kan kujera.

Aunty feenah ke bakyason mai Kyau ne?

Yana dariya yanzu fa,kuma yace Xaije Saudiya ko mubeena?

Eh mana kuma Xai Siyo mana Aunty balarabia.

Nidai kutashi ku kira mum pls.

Tashi Sukayi Suka tafi da gudu.Cikin Ranta take fadin wai wani Aunty balarabia ya Xauna yana gaya musu Shirme.

Mum ce ta Sakko Oyoyo My daughter,tashi feenah tayi ta Rungume mum.mumy ya gida?

Lfy my daughter ya Hanya.Alhmdllh mum.kinga yanda kika kara kyau my daughter kaman ina kusa dake Lallai Leemah na kulamun dake.dariya feenah tayi Kai mum.mumy kinji jibi Zamu tafi.Kai dama da wuri Aka shirya muku tafiyar kenan?

Eh wlh mum daxu naji su Kausar Suna mgn a mota.

Amana addu'a.insha Allah mum.Nazir dake Shigowa yanzu Sister yaushe kika dawo?

Oh yaya Nazir ka Zauna mana. dariya yayi yakarasa ya Xauna ya Leemah ta? duka Mum takai mishi Mara kunya Kawai Agabana kake Xancen budurwa.

Am Sorry mumy.

Yawwa mumy mun hada tafiya Zuwa Saudiyya Nida yusuf da yazeed.

Kai Haba yaushe kuma?

Inaganin Xuwa gobe ko jibi.

Lallai kun kyauta kunga Saiku hada tafiyar dasu Feenah gaba daya.kallon feenah Nazir yayi Sister kuma tafiyan yanxu ne?

Eh jibi ne Amma kuyi tafiyarku daban. matsawa yayi kusa da kunanta Sister ya haka Kibari muje tare dan Naga Leemah da Kyau. tabe Baki feenah tayi ta tashi Mum bari Naje Wanka.ok daughter kiyi Saikizo ga Abinci.

Maika fadama yarinyata kasa ta tashi?

Sosa Kai Nazir yayi mum bakomai.kai kasani dai Garama dad dinka yazo Afara maganar Aurenka mu huta. dariya Nazir yayi mumy tawa ni kadai.

Kajika Sauran yaran nakaisu bola.

Nidai bance ba mum dinmu.

Xaune Suke gaba dayansu a parlo da Sallama takarasa.Oyoyo Halimatu Oyoyo Halimatu.

Karasawa tayi ta hau Cinyar Inno.kai daughter karasamun Uwar tawa Xaki?

Abba Wane ni Sannuku da gida,Sweet Mamy Hy, bro Miss you.

Murmushi Mamy tayi Allah ya Shiryamun ke.Amin Abba ya fada Suna dariya.

Kallon yazeed inno tayi tsaka bakaga gudan jinina bane? mtww wai tsaka ni wlh Abba kaja mata kunne tafita harkata!

Kaci gidanku yazeed Mamy ta fada tana nunashi da Hannu.

Sunkuyar dakai yayi Sis ya Skul din?

Nifa fishi Nake dakai bro Yazeed kaki kaje ka ganni Sanan yanxu Ina maka magana kayi Shiru.

Sorry Sister kece daga Xuwa Kika nufi wannan tshowuwar.

Ayeririri inno tayi guda yau nagane kishi irin na yazeedu dama Nadade danasanin kishina kake Cikin gidan nan Shiyasa kake Alfarma,Aurene dai kayimun tsufa Akai kasuwa.dariya duk Sukayi, banda yazeed da yaja tsaki Mtsww kinada matsala wannan tsohuwar Wlh.
Chapter 21 · 0% Book details