← Book details Yar Lesbian Ce 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 25

Sashe 22

Yar Lesbian Ce 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tashi yake kokarin yi mai ya tuna yadawo ya Xauna.Abba jibi ne tafiyata Xamuje tare da Nazir da yusuf!

Allah ya kaimu my Son.

Amin Abbana,mamy bakice Komai ba.

Allah yamuku Albarka Son Allah ya tsareku gaba daya.Amin Mamy ta. bro yazeed Ina Xaka ne wai??Sister Saudiya Xani Nayi muku addu'a. gyaran murya Inno tayi tana kyafta ma leemah ido. itama leemah kashema inno ido tayi Alamar ta gane.

Laaaa Abba Ai muma jibi Sukace Zamu tafi.

Kallonta yazeed yayi kinga idan kinje Saikiyi addu'Anki ma kawai. dariya Leemah tayi kaima ka karamun da taka ba.

Tunda tafiyarku taxo daya ai saiku hada tafiyar gaba daya ko?

Mamy ke tambayar Yazeed.

Haka kuwa ya dace inno ta fada.

Hararar inno yayi,ya kalli mamy.

Kai Aa mamy tunda itama da kawayenta Zata Gara Suyi tafiyarsu ni banason Shirmen Su. da Sauri Inno tace Amadi kanajinshi fa.

Murmushi Abba yayi kyaleshi tashi kaje yazeed Kowa yayi tafiyarshi daban yama fi.

Tashi yazeed yayi yana fadin yawwa Abbana yasan Halin yara.

Inno data Saki baki yana fita tace Amadi Bazaka daina biye yaron nan ba kenan?

Inno Rabu dashi dakaina Xanje Nahada musu tafiyar.

Murna Leemah tayi tace yawwa Abbana.

Kausar na karasawa gida gaisawa kawai tayi da Hajiya sai yar firar dasukai.Hajiya bari Nayi wanka yunwa nakeji Wlh.maxa yar Albarka Kiyi kixo kici Abinci.Toh mamah.

Yawwa Kausar Kafin kitafi nikuwa maganin dakike Amfani dasu kinajin chanji Ajikin ki?

"Sosai ma Hajiya" kinga maganin infection din nan ma Saura Kadan,Sati biyu kawai nayi Amfani dashi Naji Alamar Sauki,har Asibiti naje Sun tabbatar Mun dacewa banida Wani Ciwo Yanzu Ajikina.kai Alhmdllh Nayi matukar farin ciki Hajiya ta fada tana daga hannu Sama.

Amma mamah ni haryanzu ina fargabar tarewata gidan Yusuf!

Kallonta Hajiya tayi kina nufin duk Rawar kafa din nan da Yusuf keyi Akanki haryanzu babu Abinda ya shiga tsakaninku?

Kausar taji nauyin maganar Amma ya zatayi mahaifiyarta ce itace wadda yazama dole tasan matsalar ta,domin daga Ubangijin daya Halliceta Sai Mazon Sa babu wani wanda yachanchanta ta girmama bayan Su Sai mahaifiyarta da Mahaifinta daga bisani Sauran mutane.

Dan haka babu wani Amfani danta boye mata Sirrinta.

Eh mamah babu Abinda ya shiga tsakanina dashi ina tsoron kada yakasance Nidin ba budurwa bace karashe maganar tayi da kuka.

Jawota Hajiya tayi kan jikinta tana Shafa bayanta,ya'isa yata na fada miki babu Abinda Xai faru tsakaninki dashi Sai Alkairi ki kwantar da hankalinki.

Inason yanxu kisanar dani gaskiya kin taba Aikata wani da Da Namiji ne?

Da sauri Kausar tace Wlh Allah mamah bantaba Aikata Wani Abu dana miji ba.

Indai hakane kuwa Kausar ki daina daga hankalinki Akan Wani Abu na daban.

Shikenan Mamah insha Allah Na daina.Allah miki Albarka ya kareki daga Sharrin mutum da Aljani da dukkan Abu Mai cutarwa.Allah Amin Hajiyata Kausar ta fada tana kissing Hajiya A kumatu.maxa tashi kiyi Wanka.Tom Hajiya.....Namance ban fada miki ba mamah!

Meke nan yata??

Jibi Xamu tafi Saudiyya.

Kai masha Allah Naji dadi Allah ya tsareku.Amn Kausar ta fada tayi Ciki.

Tana Shiga kiran Yusuf na Shigowa wayarta.

Da murmushi ta daga.my wife I miss you Abinda Yusuf yafara fadi kenan.

Miss you more Kausar ta fada kasa kasa.

Meke damunki Sweetheart kaman kinyi kuka.

Zaro ido tayi Kaman yana ganinta banyi ba Sweety Kawai gajiya ne.

Sorry kinji.Uhum kawai Kausar tace.

Albishirinki!

"Goro my Honey" jibi ne tafiyarmu Saudiyya nida Yazeed da Nazeer.

Wow what a Wonderful Story lyk Sweet.

Ajiyar Xuciya yusuf yayi dan nace Zanyi tafiya kike murna Haka?

Waye ya fada maka kawai dan inaganin Xamu tafi tare gani ga mijina Shiyasa na fada haka.

Me kike fada haka? ina fada maka jibi muma Xamu tafi.

Wow yusuf ya fada are you Sure?

Yeah Kausar tace!

Naji dadi matuka dole tafiyata ta dawo nida ke.

No Honey mu hada gaba dayan mu dai. yes Yusuf yafada da karfi hakan ma yafi.

Wayyo Xaka fasamun kunne.

Am Sorry my.dariya Kausar tayi kama kunenka.

Shima dariya yayi kin mance wa'azin jiya dakikai ko?

Au na mance.kin kyauta Ai.

Uhum Uhum Kausar tace kaman irin Xatai kuka din nan.

Menene Kuma Sweetheart?

Ni Wanka fa Xanyi ka hanani.

Sorry kice dai kinason nazo namiji oya Shirya ina Xuwa.Rufe ido tayi ni banaso.

Zakiyi bayani idan kikaxo hannu ba wanka bama har.......kashe wayan Kausar tayi jin duk Zai kashe Mata jiki.Hanyar toilet tayi face dinta dauke da murmushi.

Page..45/46
Zaune Suke babban parlon Abba mamy inno and Leemah.

Inno naji tana magana idan ni baka yarda da Zancena ba Ai Ga Halimatu nan Ka tambaya Amadi.

Kafin ma Abba yakai ga tambayar Leemah tayi Sauri tace Abba Wlh da gaskene bro Yazeed da feenah Suna Soyayya.Kasan dai yanda bro yake da yaya yusuf baya boye mishi komai,kuma Kasan yanda nake da feenah idan ma baka yarda ba Abba Bari ka gani.wayarta taciro ta Shiga Nuna ma Abba pic din feenah da yazeed har wanda take bacci kan jikinshi a mota.

Girgiza Kai Abba yayi yanxu dai na Shirya muku tafiya Anjuma da Karfe 8 Zaku tafi.

Haba Amadi inno ta fada ya muna magana mai Muhimanci kana wani xance.

Sallamar Kausar ya hana Abba cewa komai.

Da gudu Leemah ta tashi tayi kanta.my kausar harkun karaso.

Kardai ki ballamun yarinya mamy ta fada daga Nesa.dariya Sukayi suka karasa. har Kasa Kausar ta tsugunna tana gaida Mamy da Abba.Amsawa Sukai Cikin kulawa.Mamy tashiga tambayar ya Hajiya.Mamy lafiyansu qalau tace Agaidaku.muna amsawa.

Juyawa Kausar tayi ta gaida Inno.Cikin Kulawa inno ta Amsa ma Kausar.

Mamy ce tace Ai ba karamin birgeni kukai Ranar walimanku ba.

Yarana Akwai hazaka.Allah yamuku Albarka.

Amn Sukace Gaba daya.

Abba yace Ai Wajen Aiki daya ma Zan Sama musu.yeee Leemah ta fada.Abba dama bro yazeed ya daukemu a Asibitin Shi.

Nima haka nake gani mamy ta fada.Shikenan idan kun dawo Saiku Kai mishi takkadunku ya duba Ai.

Thanks Abba Kausar ta fada Kai adurkushe.

Kausar waye ya kawoki ne?Leemah ta fada?

Yusuf ne ya Shiga wajen yazeed yanzu.

Waini ina Nafeesatu Abba ya tambaya.da Sauri Leemah tace Abba Ai tace Xatazo yanzu duk ta nan Xamu wuce.

Inno ganin Xa'a Shiririntar da wanchan magana yasa ta kalli Kausar.kafso Dan Allah Nafeesatu ba budurwar tsaka bace??

Gaba daya parlon Sukasa dariya.

Kausar tace eh Suna Soyayya Amma babu wanda Sukeso yasani. kallon Abba mamy tayi kajifa mutane duk Hakan Suke fada,Anya Abban Leemah ba Gaskiya bane kuwa?

Koma dai menene bari Nakira yazeed din Suzo Shida yusuf.

Kafin ya daga wayar ya kira Su feenah Sukashigo tare da yaya Nazir,mum,dad Sai Twins.

Ai gaba daya parlon yakara hargetsewa Leemah da Kausar Sukai Kan feenah.

Twins Sukai wajen inno,Mamy ta tashi tana taren Aminiyarta mum yayin da Abba ke fadin Aminina Umar Faruk bako waya. duk lokaci daya kuma suka koma Suka Xauna Aka Shiga gaisawa.

Dad yace Alhaji Ahmad katara mutane A parlon naka.

Inno najin haka tace Umaru Gara ma dakazo ai domin magana mai Muhimanci Akeyi. toh Toh Alhmdllh Dad ya fada,Ai Saimu cigaba.

Abbane ya kalli feenah yace Yata Angama karatu lafiya?

Alhmdllh Abba feenah ta fada Cikin Sanyin muryarta.

Masha Allah Abba ya fada.

Yanxu Sai maganar Aure ko kuma neman Aiki? durkusar da Kai kasa feenah tayi tace Aiki Abba.

Ahhh ban yarda ba yata nafison kufara Aiki kuna dakunan maxajenku.

Feenah batace komai ba.Abba yace yanzu wa kika tsayar Amatsayin mijin Aure?

Saida tayi Shiru nadan lokaci daga bisani tace Abba yaya Kabeer!

Toh Shikenan Kinga dama gobe mukeson Xuwa Yola din Xamusan Abinyi Allah yamuku Albarka.Amin duk yan wajen Suka fadi.Inno kallon feenah tayi Nafisatu kifadi tsakaninki da Allah kada Ki cutar da kanki.

Kallon Inno feenah tafarayi dan bata gane me take fadi ba.harara ta Sauke mata takara daure fuska.

Haushi inno taji tace kin harara kanki ni Gata nakeson nayi miki.ganin inno Xata fadi wata magana yasa Abba cewa kutashi kushiga ciki feenah.tashi tayi Leemah da Kausar na binta a baya.

Waikai Amadi meyasa kakemun Hakane yakamata fa muba yaran nan Abinda Zukatansu Suke so ba san Ranmu ba.

Haba inno bakiga yanxu Agabanki na tambayeta ba tace Kabeer ne Xabinta.

Dad ne yace wai meke faruwa ne?

Da Sauri Inno ta kwashe komai wanda yusuf ya fada mata game da feenah da yazeed harma da karinta ta kara ta fadama dad.kallon kallo Aka shigayi tsakanin dad da mum.

Inno ce ta katsesu idan ban fada daidai ba Ai ga Nazeer Nan Shima ya Sani.

Kallon tambaya Daddy yayima Nazeer.

Eh daddy Akwai Soyayya atsakaninsu tun Kafin nafara Son Leemah!

Toh gashinan kunji ni nasani andade Ana Boye Abu Anan gidan Amma ku kunki yarda,Wata kila saikun gani da idonku Xaku yarda.

Aa inno bawai munki yarda bane yanzu Agaban idonki Mukai ma yarinya magana ta fadi wanda takeso kuma.Amma bari mukira yazeed muji ta bakinshi.

Itama Feenah adawo da ita Suyi magana tare dad ya fada.

Mubeen jeka kira bro yazeed mumy ta fada yayin datace Mubeena ta kira su feenah.

Kusan Atare Su feenah Suka Shigo parlon tare dasu yazeed.

Xama Sukai gaba dayansu.dad ya kalli feenah Ummina kin tabbatar Kabeer Shine wanda kike So?

Eh dad ba tuntuni kuka tsayar da maganar ba!

Kuna waya dashi ne?

Aa dad inaganin ko yanada aiki Sosai yasa baya kirana.

Amma kun taba Xama kunyi magana ta fahimta dashi?

Sunkuyar da kai tayi kasa Aa dad.

Wannan ya Nuna cewa dan kibi umarninmu yasa Zaki Auri Kabeer. da Sauri feenat ta dago kai Aa dad inason Shi ma.kinasonshi Kuma Akace kuna Soyayya da dan'wankin yazeed.

Wani bugun Zuciya taji lokaci daya Hawaye yashiga Xubo mata.

Tambayarki Nayi ummina ba kuka nace kimun ba. dad Wlh kudaina kama maganar Inno daga ta ganni naje gyaramai daki Shikenan take fada ma mutane wai Soyayya muke. dariya Abun yaso ba Leemah,Kausar,Nazeer da yusuf ganin yanda inno ta bude baki gaba daya.

Nice namiki Karya munafuka sau nawa Ina kamaku Kuna Zance?Rannan harcemun kukai nabar wajen ina takura muku.

Amadi Shiyasa nace maka kasaka Abun hangen Nesa kaki yau gashi Ana karyatani Akan gaskiya ta. feenah jitake Kamar ta shake Inno domin Arayuwarta babu Abinda ta tsana irin batai Abu ba Ace tayi.

Dad Ni Wlh karya.....da Sauri mum ta bige mata baki.
Chapter 22 · 0% Book details