← Book details Yar Lesbian Ce 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 25

Sashe 2

Yar Lesbian Ce 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Juyawa yayi ya daka mata duka, Afirgice ta tashi zaune, kofa ya nuna mata Alamar ta fita. dan Allah Honey kayi Hakuri Sharrin Shedan ne, tsawa ya buga mata da karfi tashi kifita nace ai kece babbar Shedaniyar, ganin ba Alamar wasa a face dinshi yasa ta hada kayanta tayi hanyar fita....yazeed Yace kuma Wlh kika Bari Wani yaganki you are very Sorry.

Sadaf sadaf tafita Agidan gaba daya....yanzu ya Kara lura da makirci ta hada mishi dan gatanan Ras take tafiyarta,,,Alhmdllh ma tunda babu Abin da yashiga tsakanina da ita. istigifari ya hauyi daga bisani yatashi yayi Hanyar toilet rike da mararshi.

Page...24/25
Kwance yake daga dukkan Alamu tunani ne fal Cikin Ranshi, Alumshe idonshi yake Amma ba bacci yakeyi ba. tura dakin da Akayi ne ya maido dashi daga tunanin daya Lula.... yaya Nazir "mum" tace gobe Zaka kaimu gidan Su mai Kyau muyi weekends Achan.

Shafa kan yaron yayi yace Mubeen Ina ne gidan Su mai Kyau kuma?

Yaya Nazeer gidan Uncle Ahmad inda Akwai Aunty Leemah da inno da Mamy da....katseshi mubeena data Shigo yanzu tayi,eh Mubeen gidan Su bro Yazeed mai Kyau Zaka ce mishi! dariya Sosai Nazir yakeyi yace kune kuka Rada ma yazeed mai kyau ko?

Mubeen ne yake cemai haka, yaya kuma Ai baya dariya Ko? da Sauri Mubeen yace Nidai yamun dariya damukaje da mum, chuno baki Mubeena tayi tace Ai Kadan yake dariyan....toh Nidai yanzu Naji Xan kaiku goben...yeeeh yaya Nazir tnx.

Harzasu fita ya kirasu Twins ita Anty Leemah tana dariya kuwa?

Atare Sukace tanayin dariya, tana mana wasa, kuma tana kawo mana Sweet da Chocolate. wow tanaji daku, kuna Sonta kuwa????

Yeee yaya Nazeer "We Really love her" daga Haka Suka fita da gudu....Murmushi yayi har cikin Ranshi, wani Abu ya tuna Aranshi ya ciro wayanshi yafara dialling Number Feenah. bugu Uku ta daga.

Hello yaya Nazir!

Hy my sister how are you?

I'm fyn bro nd I miss you, miss you more sister, kullum haka kake cewa yaya Nazir, but tunda nazo u have not to visiting me.

I will come sisto Sorry.

Umm bayan Xama muzo Hutu; Oh Haka fa, kinga idan kukazo dakun koma Saina rinka xuwa sosai, Allah yasa d gsk, kin Raina ni ko? dariya tayi tace wace ni Sorry. ina kawayenki ne?

Kausar ta fita saidai Leemah. bani ita mu gaisa....Leemah take!

"Wa"?

Kiyi magana kiji ni bari naje nemo Kausar Feenah ta fada tayi hanyar waje.

Asanyaye tayi Sallama gabanta Sai faduwa yake....Cikin muryar kasaita ya amsa sallamar, My baby hw are u?

Am fine yaya Nazir, Nidai Gsky banason yaya din nan.....dariya yanayin yanda yai maganar yaba Leemah, me kake so kenan?

Kece Xaki samo kisaka Mun tunda zuwa yanzu nasan sakona ya isar miki. kikai Shiru baby Ko haryanxu bansamu waje Cikin Xuciyarki ba? da Muryan tausayi ya karasa maganar Dan Haka Leemah Saitaji yabata tausayi, yaya Nazeer ni kunya nake Ji, dariya Yayi Sosai yace I know baby, karki damu idan mukai Aure Xan Cire miki kunyar nan, Rufe ido tayi Kamar Yana ganinta tace Uhum.... magana Xakiyi baby Abu daya nakeson ji daga bakinki, yaya Nazir inasonka kamar yanda kake sona kuma Na Amince Mu kullah Soyayya wacce tafi tasu Romio da juliat fakat Idan kika gayamun haka ya wadatar dani.....Xaro ido tayi Kamar yana ganinta tace Wlh yaya Nazir ban'iya fadin haka yayi tsawo,,,,, Zaki iya baby inhar kin Amince dani, Kinsan wani irin so Nake miki Leemah, ban taba Son wata ya mace kamar yanda Sonki ke hanani bacci ba, tun Ranar dana Sakaki cikin idona ban kara samun natsuwa ba pls ki Amince mun Mu kulla Syy wadda tsantsar kaunace Aciki, I love you with all my heart Leemah.

"I love you too yaya Nazir" kettt ta kashe wayan.....tashi yayi daga kwancen dayake ya daga Hannu Sama "Alhmdllh ya Allah" farin ciki ne falll yacika Xuciyarshi tashi yayi ya nufa part din Mamy da karfin guiwan Shi......
fitowarshi daga wanka kenan daure da towel Sai Dan karamin dake Hanunshi yana goge jiki.....Inno ce ta turo kofar tashi da karfi har saida yadanji tsoro, ganin Itace yasa ya daure face yaja tsaki. tsaka ma tayi tsaki Allah ya tsine mata ballantana mutum Dan Adam makaryaci inno ta fada tana kallonshi, be ko kalli inda take ba ya fara taje kanshi da kum..... gafa mutun har mutum Amma Yayi kyan banxa...kallenta yayi ya galla mata Harara, Bazan fasa cewa Amadi ka Harara ba wlh.... kasan ma me yakawoni? be tanka mata ba....kwantar da murya inno tayi kamar ba ita tagama Zaginshi ba.....yazeedu dan Albarka jiya kace Xaka kawomun kudi baka kawo Mun ba Shine nazo Amsa, kayi hakuri Idan dan narabaka da kafurar yarinyar nan ne, gani nayi ka wuce Ajinta koni tsohuwa nafi yarinyar nan lasting Ayanda naganta, kallonta Kawai yazeed yake yanda take Surutu Kamar Radio, yazeedu idan ma kana ganin Zan gaya ma Amadi Abinda kake mun ne Wlh "Aa" waye ke fishi da jikanshi Ai sai wawa.

Inno yanzu kudi kikazo dai nabaki ko?

Eh yazeedu yaron kirki Allah yabaka mata yarinya daidai yanda Xaka more Rayuwarka, tsaki yaja, inno batai magana ba tunda Abu tazo nema gunshi, tashiyayi ya bude wani Dan karamin Box ya ciro kudi ya mika mata, yawwa yazeedu yanzu kashirya ka kaini Dan Allah. gaskiya Inno kincika takura Wlh babu inda Zani kibarni naji da Abunda Ke damuna. dan iska ba gara Abun yayita damunka ba tunda baka da Mutumci, Kana wani mun magana da gadara Kamar ba gidan dana nazo ba, ko Kuma Angaya Maka Nima sakarkarun yan matankace?

Ni koxanyi Soyayya Ayanzu Ai nafi karfin nayi da kamarka, dogon baza Kawai.

Kwafa yazeed yayi yace Zaki kara neman Abu aguna, Allah ya Sawwake mun na nimi Abu Awajenka,kudin naka ma danasan bawani Albarka Xasu yimunba Sabida baakin ranka....Amadi ya kusa yadawo ya maidani garinmu...daga haka tafita ta jaaa kofar da karfi....tana fita yace gara kitafi din ko mutum ya huta....wayarshi ya ciro ya kira Yusuf yace yaxo ya Sameshi.

Atare Suka Shigo dakin, ganin Leemah A kwance yasa Kausar tace Halumcy kin gaji ne Haka....Batama San Anayi ba, ta Lula kogin tunanin Nazir dinta, ganin idonta Abude kuma batajuyo ba yasa Kausar ta kalli feenah tace, feenah Wannan qalau take kuwa?

Nima shi nagani. besty Lfy kuwa?

Shiru ba Amsa, atare Sukayi kanta Haleemah Suka fada da karfi...Afirgice ta tashi tana Zaro ido.

Ajiyar Xuciya Sukai atare, kausar tace iskanci muna magana kinyi Shiru kin bamu tsoro.

Ajiyar Xuciya itama Leemah tayi tace bacci fa nake, hada ido Sukai feenah da Kausar atare kuma Sukace bacci Ido Abude?..dafe kai tayi tace ba bacci nakeson nace ba, toh mekikeso kice feenah ta wurga mata tambaya?

Ina tunani ne wai lokaci ba wuya gashi har Zamuje hutu da mun dawo Saikuma tafiya gida gaba daya...Kausar ce tai saurin cewa naki wasane, aini inajin dadin hakan Sabida da mun gama karantun Nan Sai maganar Aurena da Yusuf daga baya Saiya samamin Aiki....dariya Leemah tayi tace ikon Allah kowa da damuwarshi, Ita dai feenah bata yarda da Abinda Leemah tace ba, tabe Baki tayi tace toh bani phone dita besty kin Rungumeta Kamar kin Samu baby.

Atare dukansu Sukayi dariya.

Karasowar yusuf Yayi daidai da fitowar inno daga Cikin gida, tana ganinshi ta washe Baki yusufa Kaine?

Shima dariya yake yace inno nine, ina Zaki haka?

Kasuwa Zani yusufa, inno ko nazo nakaiki ne?

Aa Fatima ta Samo driver yanzu ma Shi Zai kaini, toh Inno Adawo lfy, yawwa madallah yusufa.

Inno Yazeed naciki?

Tsaka yana Ciki tun jiya yake dacin Rai,Sabida yakawo kafura gidan Nan nakoreta, Yusufa yazeed ya haukacefa dan bakaga matar daya kawo jiyaba Xatai Sa'ar Fatima,Shine dan nakoreta yake bakin ciki....dariya Sosai yusuf keyi yace Inno kinyi daidai dakika koreta Haka dama nakeso, eh aishi wawan besan gata ba, Shiyasa yake cika Yana batsewa.

Inno bari nashiga nasanar dashi Gata kikaimai, daga nan kace mishi uwarshi ta samomun driver, toh inno Xan fada Mishi.daga haka yayi ciki,Inno tafita.

Shiga yayi ya Sameshi kwance rike da mara.

Dr ya dai? dagowa yayi ya kalli yusuf ya mayar d kanshi, karasawa Yusuf yayi kusa dashi, yanxu naga inno Xataje kasuwa, tace nacemaka mamy ta sama Mata driver...karamin tsaki yazeed yaja yace ina ruwana ni: gsky Inno tana son kasuwa jiyama kace ka kaita fa!

Ummm yazeed yace.

Meyasa kace nazo kasan ba magana Xamuyiba, Naga Allamar tunda kasamu Su inno suka amince da maganar Mufeeda shikenan Kake Wani Kara Shan kamshi.

Cemaka tayi Sun Amince?

Ni bamuyi maganar da itaba, Amma Nasan dansun Amince dinne Kake mana yanga. ...

Cije Lebe Yazeed Yayi yanaa runtse ido.

Wai kai meke damunka ne?

Kodai Ciwon kanne haryanzu?

Eh Shine Yazeed yaba Yusuf Amsa a kufule.

Allah yabaka hakuri Yusuf yafada yana kunshe dariyar dake cinshi. yazeed ne yajuyo yace Yusuf Ashe dama mata haka Suke?

Xaro ido Yusuf Yayi yace Mai Mata Sukai maka?

Shiru yazeed Yayi nadan lokaci daga bisani ya kwashe Abinda yafaru dashi game da Kausar ya fada mishi, gaba daya babu Abinda ya Rufe ma yusuf....da mamaki Yusuf ke kallon Yazeed yace Shiyasa Kake ta Wani Rike mara, ba kasamu Abinda kakesoba?

Kuma ai ka rage Xafi kadan....tsaki Yazeed yaja ina gayamaka Nayi Sabon Allah jiya kanamun Shirme!

Yusuf ne yace toh ai ba lefinka bane kaidin mata ne ya Afka maka, Yanzu kayita neman gafarar Allah, da Sauki ma tunda baka Shigeta ba, Sannan yakamata Xuwa yanzu kasamo Matar Aure, Sabida nafi Kowa sanin matsalarka game da ciwon mara, kaga kafin Ka gagara moruwa yadace Kayi Aure.
Chapter 2 · 0% Book details