← Book details Tasneem Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 23

Sashe 8

Tasneem Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Baice Komai bah ya mike Ya Shiga Dakinshi, Zama Tai a wurin Ta saki kuka, A nan Taci kukanta Har Barci ya dauketa, Abin Duniya yayima Naeem Yawa, Wayanshi Ya Dauko Ya Danna Layin Sa'ad, Bugu Daya ya Dauka, Cikin Wani Irin Murya Naeem Yace "Dr Kana Gida neh??" Sa'ad Yace "Lapia dr Naeem" Naeem Yace "just Answer mie" Eh Dr sa'ad Yace Naeem baice komai bah ya kashe kiran..

Yakai Kusan Minti Biyar A kwance Dakyar yasamu Ya Tashi Ya Shiga Toilet, Wanka Yayi ya fito, Blue Jeans Yasa Da Black Top, Feshe Jikinshi Kawai Yayi da Turare Ko Combing Kanshi beyi Bah Ya fito, Kwance Ya sameta gefen Dinning Tana Sharan Barci, Tausayinta Ya kamashi, A Hankalin Yabar Falon Ya Fita, Motanshi Yahau Mai Gadi ya bude mai gate, Yadanyi Slow Ya kalli me Gadin Yace "Pls Ka kula da Tasneem Na barta tana Barci karka bari taje koh ina" Tho An gama ranka ya dade Cewar Mai gadin, Ya fita Yaja Motan Dagudu..

Gudu Yake Sosai Har Yakai Gidan Dr Sa'ad, Horn Yayi Mai gadin Ya bude Mai Gate ya Shiga, Parking Yayi sannan Ya Kira Dr Sa'ad A waya Yace ya Shigo, Dasallama Ya Shiga Falon, Zaune Ya Sameshi Shida Matarshi da dan karamin Dansu da bai wuce Shekara uku bah, Suka Gaisa Sannan Matarshi ta basu guri, Naeem yayi Shiru Yana Wasa da car Key dinshi..

Sallaman Matar sa'ad Yasa Yadan dago tareda Amsa wah, Tray ta aje Cikeda Kayan Ciye Ciye, Ya kalleta Yayi Murmushi Yace "Dama kin Barshi am Ok" Tace "Lallai ai ba'a zuwa Nan gidan ba'aci abinci bah" Baice komai bah Ta Tashi Tabar Wajan, Sa'ad Ya kalli Naeem yace "Whts Wrong Naeem, Naganka Cikin Damuwa, ina Tasneem?" Tana Gida Kawai Yace, Sa'ad Ya matso Yace "Naeem Fadamin meke faruwa?" Ya dago ya kalli Sa'ad idonshi ya ciko da kwalla yace "Zasu Rabani Da Farincikina Sa'ad, Ya rikemai Hannu yace "Pls Sa'ad Karka bari Su rabani da ita I So much Love her pls"...

Sa'ad Yace "What Did You Mean Naeem Yimin Bayani Yanda zan ganeh, Labarin Tasneem kaf Yaba Sa'ad Sannan ya Fadamai Yanda Sukai da Mum dazu, Ajiyan Zuciya Sa'ad Yayi yace "Naeem dole kabi Umarnin mahaifiyan Kah, Menene Abin Danuwa ai Babu komai Idan ka maida ita Saika Rinka zuwa dubata koh" Girgiza Kai Naeem Yayi Yace "Sa'ad kaima ka goyi Bayan na maida Tasneem Haba mana Sa'ad, Ina Santa, Ina Tausayama Rayuwarta, Inaso Nasama Mata farinciki, Inaso Na Zame mata Kamar Iyayenta Data rasa, Shiru Sa'ad Yayi Cikeda tausayin Abokin Nashi, Lallashin Shi Ya Shiga yi akan Ya maida ita inyaso Ya rinka zuwa Yana dubata, Sun Aje Akan Gobe da Sassafe zasu Tunda bah wani nisa baneh...

Tasneem koh Naeem Ya fita ba dadewa Ta Tashi, Dube dube Ta Shiga yi cikin Gidan Dakinshi Ta shiga Bai nan ta Fito ta leka kicin Nan Ma baya nan, Da kuka Ta Fito Haraban Gidan Tana kwalla mai Kira, Ganin bah motarshi Yasa ta Zauna Dabar Ta Saki kuka mai Karfi, Mai gadi ne Ya nufeta Dasauri Yana tambayanta meya Faru? Batace mai komai bah Sai kuka datake tana kiran Naeem, Yace "Yi Shiru Ya fita Neh Yace Bazai dadeba Zai dawo", Dakyar Ya shawo Kanta Ta Tashi Ya kaita Kan benchn Shi Suka Zauna, Ganin Taki Sakin Jiki Yasa Ya Shiga bata taysuniya Tanata Dariya, A Haka Har Ta sake tanata bashi Labarin Kauyensu...

Ummu Farheen✌🏻
N
Aysha Gana💕
[10/15, 7:50 AM] ‪+234 813 184 5457‬: [9/8, 9:29AM]

💥💥TASNEEM💥💥

Na *Ummu Farheen*
+2348131845457
N
*Aysha Gana*
+2347017251433

*81 to 85*

Sun Dade Yana Bata Tasuniya, Chan Sukaji Horn Din Motar Naeem, Dasauri Mai Gadi Ya bude mai Ya shigo, Turo Baki ta kauda Kai, Parking Yayi Ya fito, Mai gadi yamai Sannu da zuwa, Ya amsa Cikin Sanyin Murya, A Hankali Yace "Tasneem!" Kauda Kai Tai Rungume Hannunta ta Turo baki Tareda Kauda Kai, Dan Murmushi Yayi Ya Karasa Kusada Ita Ya duka Yace "Nayi Laifi My love Bazan Sake bah", Bata Kalleshi bah ta kauda kai, Hannunta Ya rike Ta kwace Ta tashi Ta Shiga Falo, Binta Yayi Ya Sameta Kan Kujera Tanata Kumbure Kumbure, Yayi Dariya kasa kasa Yace "Am Sorry baeby, Kinji!, Kira na Akai a Asibiti kinji", Kai Kawai Ta gyada Tace "Ya Naeem Meyasa kake kuka dazu?, Kaima zaka tafi kabarni ne Kaman Yanda ya Tasiu Ya Tafi?" Gabanshi ne Ya fadi Tuna Kalaman Mum, Ya kirkiro Murmushi Yace "Aa Bazan Barki Bah, I Will Always Be Wit You"...

Murmushi Tai Ta rungumeshi Tace "Ya Naeem Karka Tafi Ka Barni Kaji?" Dakyar ya iya gyada Kai Hawaye Cike a idonshi, Sassauta Rikon Yayi Ya Kalleta Yace "Muje Na Siyo Miki Yar Tsanan Koh?" Dariya Tai Tace "Eh Muje" Hannunta ya Kama har Bakin Mota, Ta Kalleshi Ta Turo Baki Tace "Ni Ya Naeem Wanchan motan zamu Shiga" Ta nuna Heneci arsh, Yace "Tho ai Wanda Zamu Shiga Yafi Kyau da Tsada" Tace "Nidai Wanchan" Yace "Tho An gama My love" Keyn Motan Ya dauko Suka Shiga Yaja Suka bar Gidan...

Suna Cikin Tafiya Ta Kalli Naeem tace "Ya Naeem Nima Ka Koyamin Na Rinka tuka kah" Dariya Yayi A hankali Yace "Tho Zan koya miki anma Bah Yanzu bah" To Sai Yaushe? Yadan Kalleta yace "Sai Kin Kara Girma Kinji?" Kai Ta Gyada Ta maida dubanta ga Titi, Sun Kusa Zuwa Shopping mole Din Ta Kara Haduwa Da Wannan Saurayin, Yana Cikin Motarshi Yana ja anma idonshi nakan Tasneem, Murguda mai Baki tai Ta kauda Kai Tareda Dan Sakin Tsaki, Naeem Yace "Menene kike Tsaki?" Tace "Wannan baturen Na Ranan da Yaketa Kallona Shi na Kara Gani" Yace "Ina Yake?" Juyawa Tai da niyan nuna mai Shi amma Taga Wayam, Juyawa Tayi ko yana Bayansu Anma bata ganshi bah, Tace "Ban Ganshi bah ya Tafi", Kai Naeem Ya gyada Dai dai da Isan Su Wajan yayi Parking Suka fito...

Shopping Sosai Naeem Ya Mata Tun Daga Kan Kayan Sawa Zuwa Kayan Ciye Ciye, Manyan Teddys Ya sai mata guda biyu tanata murna Tanajin Dadi har suka dawo gida...

Dakinta ya kaimata Kayan Ya koma Nashi Dakin, Yana Kwanciya komai ya dawo mai sabo kan maganarshi Da Mum, Dafe Kai Yayi Yace "Mum Why!" Bazai iya Fita ya musu take away bah dan Haka Ya mike Ya hada mata Oat dan Yaga Tanaso Sosai, Ya kaimata, Ta Amsa Tana Murmushi, Saida Yaga Tasha Sannan Ya koma Dakinshi..

Haka Ya wuni Sukuku Har Dare, Saida Ya tabbatar tayi barci Sannan yadau Babban Trolley Ya Shiga Dakinta, Kayanta Ya saka Ciki duka da Kayan Ciye Ciyen Daya Siyo mata, Set Daya ya barmata Wanda zatasa Dasafe, Ya Fita da Trolleyn Yasa a Bayan Booth...Dare ya Tsala sosai Komai Shiru, Duk wani abu mai Rai ya kwanta Yana Hutawa Ko yana barci, Naeem ko Sai safa da marwa yake a Cikin dakinshi, Lokaci lokaci yakan Shafa Gashin Kanshi ya Saki ajiyar Zuciya dakarfi, Dakyar yasamu barci Ya daukeshi..

Da Asusubah Ya Tashi yayi Sallah Yayi Wanka, Dakin Tasneem Ya leka Ya sameta Sai barcinta take, A Hankali ya soma tashinta, Ta Mike Zaune a tsorace Ta kalleshi tana Yatsine Fuska, Yace "Tashi kiyi Sallah Kiyi Wanka Yau Zamuje anguwa da Sassafe" Jin Maganar Yawo yasa ta mike Ta fada Toilet Shi kuma Yabar dakin, Tea Ya hada Mata Da Bread Ya aje kan Dinning, Chan Sai Gata daure da Towel Ya kalleta Yace "Ke Nakefa Jira" Kamar xatai kuka tace "Banga kayana bah" Yace "Wanda xakisa yana kan Gado sauran nakai dakina na boye miki" Tho Tace tareda komawa dakin..

Dafe Kanshi yayi dake Sara mai, Sunan Allah kawai yake Kira a ranshi, Chan Sai gata ta fito Ta Zauna kan Dinning Din, Yace "Ga Tea Bamuda Time" Bah musu Ta dauka ta Fara sha, Chan Ta kalleshi tace "Ya Naeem kai bazaka Sha bah??" Yace "Nasha kafin ki fito" Ta gyada kai Ta Cigaba dasha, Saida Tagama Tas Sannan Ta dau Cup din takai Kitchen Sannan Ta dawo ta dafashi Tace "Nagama"...

Car key Dinshi ya dauka suka Fito, Tana kokarin shiga gaba Yace "Koma baya zan dauki wani Abokina" Bah Musu ta Koma baya, Yaja Motan suka bar Gidan, Gudu Yake sosai akan Titi, Tun Kafin Yakai Gidan Ya kirashi a waya akan ya fito, Suna kaiwa Suka Daukeshi Suka dau Hanya...

Ummu Farheen✌🏻
N
Aysha Gana💕
[10/15, 7:51 AM] ‪+234 813 184 5457‬: [9/10, 1:37PM]

💥💥TASNEEM💥💥

Na *Ummu Farheen*
+2348131845457
N
*Aysha Gana*
+2347017251433

*86 to 90*

Sa'ad Yadan Kalli Naeem Ya kafta mai Ido Sannan Ya Juya Ya kalli Tasneem Yace "Tasneem Menene Sunan Kauyenku??" Tai Shiru Tareda Rike Haba Tace "Umm Hayin Mallan, Gangara" Sa'ad Yace "Lallai Kice Keh Yar Garin Mallan neh" Murmushi kawai Tai Batace Komai bah, Sa'ad Ya juya ya kalli Naeem Ganin Yanda Hankalinshi Yatashi Yasa Yace "Park the Car let me drive" Bah Musu Naeem Yayi Parking Sa'ad ya amsa Suka Cigaba da Tafiya...

Tasneem Sai kallan Titi Take Tana Zazzare ido, Ganin Sun nufi hanyar Kauyensu Yasa Ta Kwala Ihu Ta kalli Naeem Tace "Ya Naeem Zai Kaini Gida Dan Allah Kace karya kaini" Naeem baice Komai Bah Sai idonshi daya Ciko da kwalla, Maida Kanshi Yayi Yana Kallan Titi, Kuka Tasneem Take Sosai Tana Rokon Sa'ad Akan Ya Tsaya Karya Kaita, Sun Shiga Kauyen Suka Samu Wasu Mutane Zaune, Sun Gaisa Sannan Naeem Yace "Dan Allah Gidan Mallan Ado Ladan Muke Nema" Mutumin Ya musu Kwatance Sukai Mai Godiya, Tasneem Ta Matso Kusada Kujeran Naeem Idonta Taf da Hawaye Tace "Ya Naeem Kaima Zaka tafine Ka barni?" Ya Naeem Su Iya dukana zasu rinka yi, Ta kara fashewa Da Kuka, Rintsa Ido Naeem Yayi Hawaye Suka Gangaro daga Idonshi, A Hankali ya Share...

Wani Razananen Ihu Tasneem Ta Saki Lokacin da Sukazo Bakin Kofar gidan, Sa'ad ne Yayi Parking Ya Fito, Kofar Gidan Sa'ad Ya Shiga doka Sallama, Yakai Kusan Minti Uku Yana Sallama, Wani Makocin Sun ne ya fito Yama Sa'ad Sallama, Sa'ad Ya mika mai Hannu Sukai Musabaha, Mutumin Yace Bawan Allah Lapia?? Sa'ad Yace "Dan Allah mai Gidan nan muke nema" Mutumin Yace "Oh Mallan?" Ai Kwana Hudu Knan da Sakin Gidan, Sun Bar Gidan Gaba daya, Sa'ad Yace "Dan Allah ko ina Ya koma?"...
Chapter 8 · 0% Book details