← Book details Tasneem Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 23

Sashe 4

Tasneem Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Alhaji yace "Saboda meh?" Kuka ta cigaba dayi batace komai bah, Lallashinta Ya shiga Yi Har tai Shiru Sannan Yace "Tho Yanzu Wajan Wah kike?" Tace "Goggo" wacece Goggo Alhaji ya tambaya Tace "Kakansu Salame neh" Shiru Yayi na Wasu lokuta Zuciyarshi na Suya Sannan Yace "Tho Kina Zuwa Makaranta?" Kai ta gyda Yace "Wani Aji kike??" Tace "Primary Five"..

Iyyeh Kice Babbar Yarinya ce, Dan Murmushi Tasneen tai, Alhaji yasa Aka kawo mata mutumin ta Apple Tai godiya Sannan Ta kalli Alhaji Tace "Alhaji!" Yace "Na'am Tasneem" Ta kara Murmushi Sannan Tace "Ina neh Gidanka??" Yayi yar Dariya yace "kinaso kije neh??" Kai Ta gyada Sannan tace Banaso Nazauna Gidansu Salame, Yayi Shiru Yana Kallanta Yace "Kinaso ki koma gida nah?" Tace eh mana Bah kace zaka koyamin mota ba kuma kace zaka kaini Makka, Murmushi yayi yace "Sosai kuwa insha Allah Tasneem, Mikewa Tai Ta doka Tsalle tana dariya, Shima dariyan Yayi, Ta kalleshi tace Anma Idan Zan koma gidanka harda Ya tasiu da Salame da goggo koh? Kai ya gyada kawai Yana Mata murmushi...

Tace Alhaji Kai meye Sunan Yarinyan kah?? Dariya yayi Sosai, Surutun Tasneem na burgeshi, Shiyasa Duk sanda yake tareda ita Yake Cikin Farin ciki da Annasuwa, Yace Ni banida Yarinya Sai yaro, Ta Bata fuska Tace "ni Bazanje Gidanka bah", Ya gwalo ido yace Saboda meh Tasneem?? Tace Ni Yarinya nakeso sai mu rinka ma Yar tsana Kitso tare nida ita da salame, Yadanyi Murmushi yace "Tho Sai Insa A nemo miki wacce zakuyi tare" Tace To menene Sunan Yaranka? Yace *Faizan* Kyalkyalewa da dariya Tasneem tai tace "Muko Bamuda Wannan Sunan a Kauyen mu Wai *Haizeen* Ta kuma kwashewa da Dariya, Shima dariyan Alhaji yayi Bah Haizeen bai Faizan, Tace "Oho Wannan Sunan na yan gayu, Ta mike tace Na Tafi Kada Goggo tamin fada, Kudi Ya ciro Rafan Yan naira biyar Ya mika mata, Noke kafada tai Tace "Bah ruwana bazan Amsa bah" Yace Haba tasneem Idan baki amsa Bah Raina zai baci, Hannu tasa ta karba tace nagode Sannan ta ruga a guje tai Gida...

Mallan Tagani Ya Fito daga gidan goggo dasauri, Tace Sannu baba, Ya kalleta Yace ina kika Shiga Tasneem Tun dazu Ga Goggo Batada lapia, Bai jira mai zatace bah yabar wajan, Mamaki ne ya cika Tasneem dazu dazu fa tabar Goggo lapia lau, Shiga gidan tai asauri ta leka dakin, kwance ta Samu goggo tana nishi dakyar, Ta shiga dasauri Ta Zauna kusada ita tace "Goggi bakida lapia neh?" Kai Goggo ta gyada dakyar, Mallan ne yayi sallama Ya Shigo, Ya kalli tasneem dake hawaye yace Jeki chan Gidan tukunna, Tho tace ta mike Ta bar dakin..

Shatu ta samu Tsakar gida, Aiko ta balla mata harara, Dasauri Tasneem tabar wajan ta shiga dakinsu, Bata tara da komai a dakin bah har sudaden katifan ta babu, Zama tai a kasa tana karema Dakin Kallo, Ya tasiu ne ya fado mata a rai, A hankali ta sulale ta gwanta tana kuka ahankali, Sunan Ya tasiu kawai take Fada tana kuka, A Haka Barci ya dauke tah..

Chan cikin barci taji Ana Salati da karfi, Ta tashi dasauri Ta leko, Mallan tagani a tsakar gidan da iya, Abinda taji mallan din na fadi yasa kafafuwanta Suka soma rawa, *Goggo ta cika* Kuka Tasneem Ta fashe Dashi da karfi, Salame tazo kusada ita, Itama kukan take, Tasneem ta kalli Salame cikin kuka Tace "Shiknan na rasa goggo na rasa ya tasiu" kuka suke Sosai, Dagudu tasneem ta fita ta shiga gidan goggo, Kwance ta sameta an lulubeta da zani, Kara Fashewa da kuka tai ta zauna dabas a wajan, A haka akaima goggo sutura aka kaita gidanta na gaskiya...

Damuwa taima tasneem Yawa dukda karancin shekarunta, Bata aikin komai sai kuka da ambatan Ya Tasiu da goggo, A haka har akai kwana uku, Tun daga ranan rayuwa ta chanza ma Tasneem, Kullum cikin Tsangwama take a gurin shatu da Iya, Kullum sai ta dibo Ruwa Ta share tsakar gida da wanke wanke, Duk ta rame ta lallace Kullum idan Mallan ya tambayeta sai tace ba komai, A haka har Ya Tasiu yayi wata uku da tafiya, Goggo kuwa Wata biyu da rasuwa..

Ummu Farheen✌🏻
N
Aysha Gana💕
[10/15, 7:34 AM] ‪+234 813 184 5457‬: [9/2, 6:23AM]

💥💥TASNEEM💥💥

Na *Ummu Farheen*
+2348131845457
N
*Aysha Gana*
+2347017251433

*41 to 45*

Yau Juma'a Mallan Ya fito Cikin Sauri zashi Masallaci a kofar gida Yaci karo da Alhaji Sani dake chan Kasan Layin su, Suka Gaisa Alhaji sani yace "Dama Mallan Akwai Maganan Dake tafe dani neh" Mallan Yace "Tho muje Masallaci idan muka dawo sai mu tattauna" Alhaji ya washe baki yace "Tho Bismillah ya nuna mah Mallan tsohuwar abesfan shi" Suka Hau suka tafi Masallaci..

Suna dawowa Mallan Ya Shiga Gida ya dauko musu tabarma, Sun zauna Mallan Yace "ina jinka Alhaji" Alhaji Yayi gyaran Murya yace "Dama game da Yarka ce Tasneem" Mallan Yace "Tho Inaji Ina fata dai lapia?" Murmushi Alhaji Sani Yayi Yace "Mallam Idan Baxaka damu bah inaso a bani aurenta" Kurrri Mallan yayima Alhaji Yana Kallanshi Sannan Yace "Alhaji ina baka hakuri Tasneem Yarinya ce Shekaranta Sha Daya, Kuma Yarinyan nan amana ce a gurina, Bazai yuwu na zartar da hukunci akanta bah ban nemi shawaran Yayanta bah, Dan Allah kai hakuri, Alhaji ya mike Batare dayace da mallan komai bah yabar wajan Fuuu...

Duk abinda ake Shatu naji Wacce ta boye a xaure tana sauraronsu, Dasauri ta shiga gida tahau kiran Iya! iya!! Kina ina? Iya ta fito tana cewa "Haba shatu wannan wanne irin kira neh", Kurya ta suka shiga Shatu taba iya Labarin duk yanda Mallan sukai da Alhaji Sani, Tsaki ta doka Sannan tace ina mamakin Mallan Wallahi, Gaskiya bazai taba Yuwuwa bah, Kinga Fah idan Alhaji sani ya zama surukin mu zamuji dadi yanda yakeda tarin dukiyan nan, Shatu Tace "Gaskiya neh iya" Anma iya dama ni aka aura mai kinga fa gidanshi gidan hutu ne, Iya ta dungureta tace "Dalla chan Wawiya Inafa hutu, Mutumin da ke dukan matanshi Sannan Ki dora katan Tukunya koh kin manta yaya gareshi" Shatu tace "eh hakaneh" tho yanzu menene abin yi?? Iya tace Zan kirashi ne dan wallahi bazan bar damar nan ta wuce mu bah, Dama mallan zaiyi tafiya Lagos wai zaije Saro kaya, Kinga kamin ya dawo ai shiknan, Shatu ta kyalkyale da dariya tace "ho Iyan mu!"..

Sati biyu da Faruwan Haka da Asusubah Mallan ya tashi dama tun da daddare ya hada kayanshi, Yana dawowa Sallan Asubah Yasamu Tasneem tana Fito da kayan Wanke wanke, Ya kalleta yace "Tasneem meh zakiyi??" Kanta na kasa tace wanke Wanke, A Fusace ya kwalawa Iya kira ta fito tana gungunai, Ta kalleshi tace "Lapia kake kirana da Asubahin nan" Yace "Haba Kina ko jin tsoron Allah??" Na lura tun bayan rasuwan Goggo yarinyan nan duk ta Chanza batada Walwala kuma nasan duk ke kike takura mata" To bari kiji, Yarinyan nan na hana tayi duk wani aiki a gidan nan daga yau" Iya tace Wallahi bazai yuwu bah mallan, Haka yarinya zata zauna bazatai aiki bah, baice komai bah ya shiga dakin ya dauko jakan kayanshi, Ya kalleta yace nidai na fada miki, Sannan idan na dawo naji wani abu tho Wallahi a bakin aurenki...

Kallanshi Tayi da mamaki, Sannan ta tabe baki ta koma daki, Ya kalli Tasneem yace "Allah ya miki Albarka, ki Cigaba da hakuri kinji?" Kai ta gyada Yayi Murmushi yace "meh zan siyo miki?? Tayi Murmushi Har Saida dimple dinta ya lotsa Sannan tace "Yar tsana" Yace shiknan Saina dawo, Adawo lapia Tace ya fita...

Gari na kara Haske Iya ta Yafa Mayafinta ta nufi runfar Alhaji Sani a kasuwa, da Sallam ta shiga ta samu guri ta zauna, Sun gaisa Sannan tace "Mallan ne Ya aiko ni" Yace Wani mallan?? Tace "Mahaifin Tasneem" Hade fuska yayi yace lapia?? Tadanyi murmushi tace "Akan maganan auren Tasneem ne yace Ya amince Sannan baiso ya wuce gobe, Yayi tafiya yau, Yace Liman ne waliyin tah, Alhaji sani ya washe baki yace tho madallah, anma gobe ai yayi wuri, Iya tace bah komai, Koh bakai mata lefe bah babu matsala ka mata a dakinta, Alhaji yace tho Shiknan, Hannu yasa a aljihu ya ciro kudi Dubu Hudu yaba iya yace gashi aci goro, ta amsa dasauri tai godiya tace karka Manta dai Gobe da anyi azahar sai a daura, Alhaji yace tho bah damuwa, Da murna iya ta dawo gida tana ba shatu labari...

Tasneem naji ta fashe da kuka dagudu tazo ta tsugunna gaban iya tace "dan Allah iya kiyi hakuri duk abinda kikeso zan miki wallahi" Tureta Shatu tayi taba cewa Aure kamar anyi an gama yarinya, Kuka tasneen take sosai Tana ba iya hakuri, Salame ce tai Sallama Ta dawo daga Islamiya, Wurgar da jakan hannunta tai Ta karasa kusada tasneem tace menene? Cikin matsanan cin kuka tasneem tace "iya ce zatai min Aure", Salame tace "Aure??" Iya Ta harareta tace "To zoki hana" Fuu Salame ta shige dakinsu, Kuka tasneem take sosai kamar ranta zai fita...

Iya ko Mayafinta ta yafa Ta nufi makota tana fada musu maganan auren tasneem gobe, Bayan la'asar Wasu datijai Suka kawo kaya, Atamfa guda Uku, Shadda daya, da leshi daya, Sai takalmi daya da sarka, Iya sai murna take, Dubu daya ta basu tukuici Suka tafi, Nan tasneem ta kara tsurewa ta Cigaba da kuka, Har dare kuka take, Zazzabi ne mai zafi ya dauketa wuraren tara na dare, Kuka take sosai a dakinsu tana kiran Sunan mallan da Goggo sai ya tasiu, Iya ta fito a fusace Ta rufeta da duka, Saida tai mata lillis sannan ta turata waje, Duk da ruwan da ake tsugawa...

Rakubewa Tasneem tana cigaba da kuka, Rawar sanyi take Sosai, Dakinsu ta nufa ta dauko Kudin da Alhaji ya bata ta fita daga gidan, Gudu take tana kuka tana cigaba da kiran ya Tasiu, Gidan gonan alhaji ta nufa anma a rufe, Cigaba da gudu tai tana kuka kamar ranta zai fita ga Ruwa da akae tsugawa, Bata ankara bah taji Wata mota na mata horn da karfi, Daburcewa Tayi ta kasa guduwa kan kace meh Motan nan tayi ciki da ita...Innalillahi wa inna ilaihi rajiun...

*This is just the beginning!!!*
Chapter 4 · 0% Book details