← Book details Tasneem Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 23

Sashe 2

Tasneem Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dariya Alhaji yayi Sosai Sannan Yace "Tasneem knan Naje Makka sau Hudu" Zaro ido tai tareda rike haba Tace "Tabdi! Alhajin Layin Islamiyan mu koh Bai taba zuwa bah" Alhaji Yayi Murmushi Yace "Tho Zaije shima indai Allah ya kirashi", Gyada Kai tai kawai, Tadau Robanta Tace "Alhaji na tafi gida Kaga Har Yamma tayi kuma Idan na Dade Ya Tasiu Zaimin Fada, Yace Tho, "Gobe ma Zakizo??" Kai ta gyada Mai yayi Murmushi Yace "tho ki gaida Ummanki", To kawai tace Tabar wajan dasauri, Tambaya ne Fal a Cikinta Har ta isa gida, Shagon baba ado a rufe dan Haka ta shiga gidan Goggo, Ta mika mata kudin, A rude Goggo ta kalleta tace "na shiga uku ni Fati Tasneem!"

Tasneem ta kalleta tareda Yamutse Fuska tace "Na'am menene duk kika rude?" Goggo cikeda tashin hankali tace "ina kika samu wayan nan sabin kudin?? Ina fata bah Juye aka miki bah?" Tasneem tai Murmushi taba Goggo labarin Alhaji harda Apple dinda Ya bata, Ta nuna ma Goggo Sauran Tace na Ya tasiu neh, Murmushi goggo tai tace yar Gidan Tasiu, Tasneem ta mike tace "na tafi goggo kada Iya tamin Fada, Goggo tace tho shiknan saida safe"

A Tsakar gidan taci karo da Salame, Tace "Tasneem yanzu baba yace naje dama na duboki" Murmushi tasneem tai tace "ai ina gidan goggo tun dazu" Baba ado daya fito dan Yin Alwala yace "Yaki nan Tasneem" ta karasa Ta gaida shi ya amsa Sannan yace "Tho yaudai Yima Goggo talla ya kare tunda gobe za'a koma makaranta", Tadab turo baki sannan tace "Tho Baba" Yace "Maza aje ai Sallah Magriba tayi" Kamar ta tambayeshi Sai kuma ta share tadau Buta Ta dibi Ruwa tai Sallah, Tana Idarwa Ta nufi Shagon Ya Tasiu, Ta Gaidashi Sannan ta nemi Guri ta zauna, Saida Ya gama Abinda yake sannan Yace "Tasneem ya Akai??" Tai murmushi tareda Mika mai Apple din hannunta, Cikeda Mamaki yace "Aina kika samo wannan tasneem??" Zama tai tabashi labarin duk yanda sukai da Alhaji, Ajiyan zuciya Tasiu yayi yace "Banaso ki kara zuwa Wajan" Tai narai narai da ido tace "Saboda meh Ya Tasiu?" "Kawai" yace a takaice, Shiru tai tana Share kwalla, Ya kauda da kai dan Sam baisan Ganin kukanta, Ganin Kukan Bana Kare bane yasa Ya janyota..

Saida Ya Lallasheta tai shiru Sannan Tace "yaya!" Yace "Na'am Tasneem" Tace "Yaya Dama Ana zuwa makka sau hudu??" Yace "Eh mana indai mutum nada kudi zaije har fiye da haka" Tai Shiru sannan Tace "Tho Yaya Mamanmu Ta taba zuwa??" Yace "meyasa kika tambaya Tasneem?" Tace "tho bakace Babanmu nada kudi bah??" Shiru yayi kamar bazai amsa bah chan kuma ya kalleta yace "Ta taba zuwa Hajji harda Umrah" Murmushi tai tace " Tho mu Ya Tasiu Yaushe Zamu??" Yace "Nifa Surutun ki ke hadani dake" Turo baki tai tace "Shiknan Zan fadama Alhaji ya Kaini tunda kai bazaka bah" Ya zaro ido yace "oh! Danace kar ki kara zuwa wajan Alhajin bakiji bah koh?" Ta Turo baki Batace komai bah, Yace "In gani koh inji Labari Wallahi saina Tattaka ki" Narai Narai tai da Ido batace komai bah, Ganin Yana kokarin rufe shagon yasa ta tashi Ta fita ya rufe a tare suka shiga cikin gidan, Hayaniya Sukaji na tashi daga dakin iya, iya Tace "Mallam Tsintarciyar mage fah bata mage, Banga dalilin dazai sa kace dole sai nayi abinci naba yaran nan bah" Mallan ya kara Harzuka Yace "Dole ki basu, Sai dai idan Bakison zaman gidan nan lapia" "Keh Barin gaya miki akan tasneem da Tasiu wallahi zan iya Sakinki Ki koma gidanku" Dasauri Tasiu yaja Tasneem zuwa dakinsu, Jikin tasiu Yayi Sanyi Sam Baiso yaji iyayen rikon Nasu na fada akansu, Tasneem Tace Ya tasiu muma mu koma gidan mu Arinka bamu abinci Kamar yanda akeba Salame da Shatu, Baice komai bah ya mike..

Salame ne Tai Sallama A dakin, Langan Da ake sama mallan Abinci ta dire agaban su Tace "Gashi inji Mallan" Cikeda Mamaki Tasiu Yace "Kice Mun Gode" ta Kalli Tasneem tace "Gobe ki shirya Da wuri zamu islamiya" Gyada Kai Tasneem Tai Salame ta fita, Haka Suka Ci Abincin Tasiu nata Sake Saken Abin yi Saboda zaman Gidan, Saida sukai Sallan Isha Sannan Suka Kwanta, Barci Gagaran Tasiu Yayi, Duk Sanda ya tuna Da Mahaifan su sai hankalinshi Ya tashi, Dakyar ya samu Barci ya daukeshi goshin Asuba...

Ummu Farheen✌🏻
N
Aysha Gana💕
[10/15, 7:05 AM] ‪+234 813 184 5457‬: [8/29, 5:31PM]

💥💥TASNEEM💥💥

Na *Ummu Farheen*
+2348131845457
N
*Aysha Gana*
+2347017251433

*16 to 20*

Latin Tashi Yayi Har Saida Tasneem Ta tasheshi, Alwala yayi ya nufi masallaci, Tasneem ta mike knan Zata fito dan Yin Sallah Iya ta shigo dakin a fusace, A Tsorace Tasneem Ta mike, Iya tai mata Wani irin Kallo Sannan tace "Ina Yayanki?" A tsorace Tace "Yaje Masallaci bai dawo bah", Shatu ta banko kofa ta shigo, Tsaki tai Tana Kallan Tasneem tace "Maiya Kawai Ni iya kinsan Abinda ke damuna??" Iya ta girgiza kai Shatu tace "Yarinyan nan duk inda kika bi indai ana Lissafin masu kyau itace ta farko, Yarinya Sai kyau kamar Mayya" Iya Ta doka tsaki tace "inaso na bar Miki Sallau idan Yayanki ya dawo ki fadamai Kada in kara ganinshi a Shagon Mallan" Shatu ta rike kugu Sannan tace "Sannan ke Tasneem duk abinda Za'ayi a gidan nan kezaki rinka yin shi, Ta rike Kunnen Tasneem tace ina fata kinji??" Gyada kai Tasneem tai tana Hawaye, Shatu ta kara Murde ma Tasneem kunne Sannan suka Fita..

Zama Tasneem tai Ta Baza kuka, Kuka take Sosai, Tunawa Datai Idan Ya tasiu yadawo Batai Sallah bah Zai ci mata Yasa Ta mike Ta fito, Bakin Rijiya Taci Karo da shatu tana Fito da kwanonin Wanke Wanke, Tai Tsaki Sannan tace Kina Idar Da Sallah ki fito kiyi wanke wanken nan, Sannan ki Share Gida, Sannan ki tabbata Kinje tuka tuka kin dibo ruwa kin Cika mana Banbu, Kai Tasneem ta gyada dan tasan Halin Shatu tsap Zata mata duka, Dasauri tai alwala ta shiga daki Tana cigaba da kuka, Saida gari yadan Waye Sannan tasiu ya Shigo gidan..

Zaune ya sameta kan Sallaya Tana Rusa kuka, Zama yayi dasauri kusa da ita yace "Lapia Tasneem meyafaru kike kuka??" Kara Rushewa da kuka tai Ya Kura mata ido nadan Mintina, Yace "Fadamin mana Menene??" A hankali Tace Ya Tasiu Ka kaini gurin mamana ni banaso na zauna Anan, Shiru yayi baice komai bah, Ganin kukan bana kare baneh Yasa Ya Shiga lallashinta, Dakyar tayi Shiru Ya mike ya Nufi Shago...

Shatu na ganin ya fita ta leko tace oya Tashi muje, Bah musu Tasneem ta mike Tabi bayan Shatu, Tsaye Tama Tasneem dole Sai ta wanke kwanukan, Salame ta fito daga dakinsu Tace "Lah Shatu Tasneem Fa bata iya Wanke Wanke bah ki kawo ni inyi," Hararanta Shatu tayi sannan tace "Bar nan wajan Ko ki Sani", Salame Ta hade rai tace "Allah Shatu idan Baki kyale Tasneem bah yanzu zanje na Fadama baba", Shatu najin Haka tabar Wajan dasauri ta nufi dakin iya..

Salame ta kalli Tasneem tace kyaleta kawo ni nayi, Tare da Tasneem din Sukai Wanke wanken, Iya ta fito a Fusace Tace "Lalla Salame, Albasa dai batai halin Ruwa bah Wallahi", Salame ta turo baki tace "meh nayi??" Iya Ta galla mata Harara tace "Ban sani bah, Tho Wallahi bari kiji duk randa na kara saka tasneem aiki a gidan nan kika hana saina hadaki keda ita na zane", Zaro ido Salame tai tace "Iya bakyau fah A islamiya mallamin mu yace Kaji tausayin Wanda bashida mama da baba" Iya ta kara Galla mata Harara tace "tho uwata Yimin Wa'axi, In banda ke doluwace Yarinyan nan ta hana kinsamu Soyaiyar mahaifinki" Jin Muryan mallan Yasa Sukai Shiru Tasneem ta koma dakinsu Dasauri..

Bakwai nayi ta shiga dakin Mallan Har kasa Ta durkusa ta gaida Shi ya Amsa Fuska a Sake, Yace kin karya?? Kai ta gyada Alamar Aa!, Iya ya kwalawa Kira ta shigo tace gani, Kallanta yayi cikeda Mamaki Yace "Ina Abin karin Tasneem??" Tsaki tadanyi sannan tace yana Daki taje ta dauka, Ya kalli Tasneem yace je kidau na Tasiu kikai mai Sannan ki dau naki, Tho tace Ta mike Ta Nufi dakin...

Saida ta shasha Dunguri da zagi gurin Shatu da Iya Sannan Suka barta ta dauka Ta kaima Tasiu Sannan Tadau nata, Tana Gamawa Ta Shirya cikin Kayan islamiyan tah, A Tsakar Gida Sukaci karo da Salame Suka Wuce...

Suna Dawowa Tasneem ta kalli Salame tace lah! Salame na manta pencil dina a aji, Salame tace "Tap bazan jiraki bah Ni na tafi, Kije ki dauko", Murmushi Tasneem tai tace tho Sannan Ta Koma dasauri, Gidan Gona Ta nufi, Tana zuwa Alhaji na zuwa, Kyalkyalewa da dariya tai tana kallanshi Har Yayi parking motarshi, Ta karasa dasauri tace Alhaji nima Zaka koyamin mota??

Ummu Farheen✌🏻
N
Aysha Gana💕
[10/15, 7:09 AM] ‪+234 813 184 5457‬: [8/30, 5:44AM]

💥💥TASNEEM💥💥

Na *Ummu Farheen*
+2348131845457
N
*Aysha Gana*
+2347017251433

*21 to 25*

Murmushi Yayi Yace "Tasneem bah Gaisuwa??" Tadan yi Dariya tace au! Ina kwana? "Lapia lau" yace Sannan Yace "Ya gida Ya Ummanki da Abbanki?" Shiru tai idonta ya kawo kwalla, Alhaji Hankalinshi ya tashi yace "Tasneem menene?" Tace "Ni bansan Ummana Da Babana bah" Alhaji ya girgiza kai cikeda tausaya wah yace "Sun Rasu neh??" Ta kara Girgiza kai Alamar Aa!, "Tho ina suke?" Cewar Alhaji, Tasneem ta gyara Zama tace "Nima ban sani bah, Kullum idan na tambayi ya Tasiu Sai yayi Shiru ko kuma ya Fara kuka" Shiru Alhaji yayi Cikeda tunani, Katseshi tai dacewa "Na tambayi Baba Ado shima yace Yasan Su, Shima idan nace aina Suke Sai Yayi Shiru" Ta kalli Alhaji tace "Alhaji tho kai kasan su??" Girgiza kai yayi Alamar Aa...
Chapter 2 · 0% Book details