← Book details Tasneem Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 23

Sashe 10

Tasneem Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sunje Makarantan Saida Ya tabbatar Sun Fara Exams din Sannan Ya Tafi Asibiti, Sai Yanma Suka Gama duk Ta gaji Ya Dawo Ya dauketa Suka Tafi Gida, Suna Shiga Falo Direct Dinning Ta nufa ta zauna Ta shiga Cin Abinci, Dakinshi Ya Nufa ya Kwanta dan Yau baijin Dadi, Tasneem Na gama cin Abinci Mama Laraba tace "Oya Tashi muje Kiyi Wanka, Ta Turo Baki tace "Ni bazanyi Wanka bah" Mama laraba tace "Kinaso ace miki kazama neh?" Duk wanda beyi wanka ba Wari yakeyi...

Turo baki Tasneem tai tace "Ni To bake Zakimin Wanka bah, Sai kita Gurjeni, Ni Yaya zaimin Yau ko ki bari nayi dakaina ai na iya" Mama laraba Ta Zaro ido Tace "Naeem ya miki wanka??" Gyada kai tai, Mama Laraba Tace "Namiji bayama Mace wanka sai idan ya aureta, Bah Kyau kinji??" Kai Tasneem ta Gyada Dakyar ta shawo kanta Tai Mata Wankan, Ana mata Tasa Kaya ta Nufi dakin Naeem, Ganin Watan Dakin a kashe yasa Ta Shiga Tana Kiranshi a hankali, Tuntube Tayi da wani abu Ta fada Kan gadon, Jitai ta Fada kan mutum Yace Wayyo Jama'a ta Kasheni...

Ummu Farheen✌🏻
N
Aysha Gana💕
[10/15, 8:01 AM] ‪+234 813 184 5457‬: [9/16, 9:53PM]

💥💥TASNEEM💥💥

Na *Ummu Farheen*
+2348131845457
N
*Aysha Gana*
+2347017251433

*101 to 102*

Tuntube Tayi da wani abu ta fada kam gadon, jitai ta fada kan mutum Yace "Wayyo Jama'a ta Kasheni, Ihu Ta saki Tana kokarin Mikewa, Rikota Yayi Ya Matseta a jikinshi Yace "Its all Right nine Naeem" Ajiyan Zuciya Tai Yace "Kinaso ki Kasheni koh?" Ta Turo Baki Tace "Nifah Bansan Kana nan bah" Kuma Faduwa nai, Baice Komai bah Sai ajiyan zuciya Dayake, Lamo tai a jikinshi Tace "Yaya jikinka Zafi bakada lapia ne" Yace "Banida Lapia kuma kinaso ki Karasa ni"...

Kici kicin Kwacewa Takeyi Ya matseta Yace "Ranan Monday Akwai School Sannan Banda Kula Maza Kinji?" Tho Tace a Shagwabe, Yace "Tho dagani" Ta Mike Tadan Tsunguleshi Yace Ouch! Zan kamaki, Wutan Dakin Ta kunna Tamai Gwalo ta Fita, Mama Laraba tasamu Tace "Mama Laraba Ya Naeem Bashida Lapia" Laraba Tace "Inna Lillahi Ya jikin Nashi?" Turo baki tai Tace Oho Nima Bansani bah"...

Kicin ta shiga Tafara Kiciniyan Hada Mai Abinci, Tasneem tace "Mama Laraba meh zakiyi?" Tace "Zan dan daurama Naeem wani abu ne Yasamu Yaci" Turo Baki Tasneem Tai Tace "Uunmm" Ta Fita...

Cikin Minti kadan ta hada Pepper soup din kayan ciki da Zobo, A tray ta daura komai Ta fito, Tasneem tasamu a kasa gefen Kitchen din tana wasa da Teddy dinta, Tace "Tasneem Taso ki kaima Yayanki" Ta turo baki tace "Mama Laraba bakiga Yar Tsanata Tanajin Barci baneh, Ki Bari idan Tai barci", Mama Laraba Tace "kinga Fa baida lapia baici komai Yi hakuri Kinji, Kawota na Kwantar miki da ita kije ki dawo"...

Mikewa tai ta aje Teddyn akan Kujera Tace "Tho Mama Laraba ki Lulubemin ita Kinga fah tanajin Sanyi" Tho Mama laraba Tace Ta mika mata Trayn, Kokarin Zubarwa Take Tace "Kin Rike dakyau kinji?" Tho Tace Ta nufi dakin, Saida ta aje a kasa ta bude kofan Sannan ta dauka ta shiga dashi..

Zaune ta Sameshi gefen Gado daure da Towel Yana Tsane Ruwan kanshi, Daga Gani Yanzu ya fito daga Wanka, Sakin Trayn Tai ta Kwalla Ihu, Fitowa tai dagudu Ta rungune Mama Laraba tana Muna Mata dakin, A Rude Mama Laraba Tace "Lapia Tasneem Menene?" Dakin Ta Cigaba da Nuna Mata tana Kara shigewa Jikinta, Naeem Koh Gabanshi ne Fadi Jalabiya ya zura ya fito a rude, Mama laraba Tace "Lapia??" Naeem Yace "Bansani bah Tana Shigowa ta Yarda Trayn ta Fito Tana Ihu"..

Tsugunawa Yayi Kusada Ita Ta matsa Dasauri tana Kokarin Guduwa, Ya Kamota Ta kara kwalla ihu, Ya Riketa Sosai Yace "Tasneem menene" Kokarin kwacewa ta cigaba dayi, Mama Laraba Tace "Tho zo nan ki fadamin" Bah musu ta koma Gurin Mama Laraba, Tace "Tho Fadamin menene?" Matsar Kwalla ta fara tana Kallan Ya Naeem Tace "Koba Ya Naeem Dan Iska b..., Bata karashe ba Mama laraba ta rufe mata baki tace "Kar na sake ji"

Kunya ne ya Kama Naeem Yadan Kalleta Yace "Menayi?" Ta Turo baki a shagwabe tace "Koba kai bane Bakada kaya sai zani" Dariya Naeem ya Guntse Ya mike, Mama Laraba Tace "Kedai Wallahi Allah Ya shirye ki!" Bah Nace ki rinka sallama in zaki shiga dakin mutum bah??" Tace "Tho fah Mama Laraba nayi" Anma ai cewa nai sai ance ki shiga koh??" Batace komai bah Ta turo baki ta koma Tadau Teddynta Ta fita Wajan mai gadi...

Mama Laraba Tace "Ashe bakaji dadi bah?" Yadan Sosa Keya Yace "Eh Anma Alhamdulillah nasamu Sauki, Tace "Tho Allah ya kara sauki, Yace Ameen tareda komawa dakinshi...

Haka suka yini Tasneem sai kumbure kumbure take taki ta kula kowa dakyar Naeem Ya shawo kanta suka fita yayi mata shopping Sosai sai dadi takeji suka dawo gida...

Exams ya fito Tasneem tayi kokari sosai, Har ya mata registration an dinka mata uniform Ranan monday Zata fara zuwa, Dadi gurin Tasneem ba'a magana, da Tsalle ta samu baba mai gadi tana fadamai, Ya tayata murna sosai Da yi mata addua...

Siyaiyan Makaranta Ya mata tun daga kan socks, takalmi, jaka, litattafai dadai sauransu, Suna dawowa ta nunama Mama Laraba tai Murna sosai tareda sa Alheri..

Ana Gobe zata Fara zuwa Makaranta, Ta Shiga dakin Naeem da Sallama, Kwance ta sameshi saman gado yayi ruf da ciki yana Danna Laptop dinshi, Amsa Sallaman Yayi batareda ya kalleta bah, Ta Hayo gadon ta aje litattafan a gabanshi, Kwanciya tai ta daura kanta a bayanshi tace "Ya Naeem baka rubutamin suna bah" Idonshi na Kan Laptop din Yace "Oh! my love Case!, Kinzo ki hanani aiki koh?" Ta Turo baki tace "Ya Naeem ka rubuta min sai in tafi" Yadanyi Shiru yace "Tho Ki Bari in Gama Kinji my love?"...

Kai ta gyada Tayi lamo a bayanshi, Chan ta Sarkalo hannunta na dama a wuyanshi tace "Ya Naeem kai menene sunan babanka??" Dan Murmushi Yayi Yace "Sunan babana Umar" Tai Dariya Tace "Sunan Abokin Ya Tasiu" Ta kara kallanshi tace "Mamanka fah?" Yace "My Love kinaso ki hanani Aiki koh??" Ta turo baki Tace "Tho Ina mamanka da Babanka??" Koh Kai bakada Mama da Baba?? Zaro Ido yayi...

Ummu Farheen✌🏻
N
Aysha Gana💕

[10/9, 7:44 PM] 🍹🍬🛍💍Salma🍷💍🛍🍬: [9/17, 10:18PM]

💥💥TASNEEM💥💥

Na *Ummu Farheen*
+2348131845457
N
*Aysha Gana*
+2347017251433

*103 to 104*

Ta Kara Kallanshi tace "Mamanka fah?" Yace "My love kinaso ki hanani aiki koh?" Ta Turo baki Tace "Tho ina mamanka da Babanka??" Koh kai bakada Mama da Baba?? Zaro ido Yayi Yace "My Love bakin nan naki koh?" Mikewa tai tana kumbure kumbure tabar dakin, Dan Dariya Yayi Yadau biro ya rurubuta mata sunanta Ya Fita Ya aje mata kan Dinning...

Da Sassafe Ta tashi Tashiga wanka, Mama Laraba ta Rike baki tace "Oh Yau Tasneem wanka ake kamin ace Lallai Yau Yan gidan nan Zasusan za'a Fara zuwa makaranta" Tana Fitowa tadauko Uniform din ta aje akan gado, Fita tai Tasamu Mama Laraba a Kitchen tana kici kicin daura Breakfast, Tace "Mama Laraba Kizo ki nunamin Yanda akesa Kayan Banso inyi Latti", Dan Dariya Mama Laraba tayi Tace "Tho kije Ina zuwa" Tho tace Ta Fita Anan ne Taga Litattfan Tadauka tana Turo Baki ta Nufi Dakin...

Mama Laraba ce ta shirya ta Tsaf, Riga Da Skirt ne, Blue Skirt Sai light Blue Riga, Da Dan Karamin Baby hijab Fari, Kayan Sun Matukar amsar ta, Mama Laraba Tace "Kinga Yanzu Tunda Za'a Fara Makaranta dole Zaki Fara Kitso", Batace Komai bah Ta Goya Jakanta Ta Fito, Mama Laraba Tace "Tho Kyadai Tsaya Kiyi breakfast koh?" Dai Dai nan Naeem Ya fito Cikin Suit Brown da Farin Shirt Sai Red Bod Tie, Kayan sun Amsheshi Sosai, Gashin Kanshi Sai Kyalli yake..

Bata Kalleshi ba Ta Nufi Dinning din ta zauna, Mama Laraba Tai Serving dinta ita Dashi, Kadan Tasneem Taci Ta mike, Ya Kalleta Yace "Ina Zaki?? Kyadai Jira na Gama koh?" Batace komai bah Ta dawo ta Zauna a Palour tana Turo Baki, Dan Murmushi Yayi Ya cigaba da cin Abincinshi...

Saida Ya Gama Tsaf Yama Mama Laraba Sallama Sannan Ya Kalli Tasneem Yace Muje Koh? Turo baki tai ta mike Yana tafe Tana binshi a baya Har bakin Mota, Muryan Mama Laraba Taji Tana Cewa "Tasneem ga food flask dinki kin Manta, Ta Karaso Ta mika Mata Tace "Allah Ya kiyaye a dawo lapia" Ameen Tace Ta shiga suka kama hanya...

A Hanya bah Wanda Yacema Wani Har Suka kusa School din, Kallanta Yadanyi Yayi Murmushi Sannan Yace "My Love Fushi kikeyi dani??" Batace komai ba Ta Turo baki ta Maida Kallanta ga Titi, Dariya Yadanyi mara Sauti Yace "Tho Am Sorry kinji My Love, Bazan Kara Bah and Na miki alkawari kina Dawowa zan Fada miki kinji??...

Batace komai bah Still har suka kai Makarantan, Fita Tai Shima Ya fito Suka Shiga Cikin School din, Saida Aka bata Class Ya Rakata Har Ajin Yaga Ta Zauna Sannan ya Mata Bye Bye, Ga Mamakinshi Yaga Itama Ta daga mai hannu Harda Murmushi, Yana Tafiya Wata dake Kusada Kujeranta tace "Kema Yau kikazo??" Kai Tasneem ta gyada Itama Tace "Nima Yau nazo"...

Sunana Yusra Kefa? Tasneem Tace "Nikuma Tasneem" Bell akai ringing na Fita Acembley Suka Fita Tare, Ranan Tare Sukai Yawo itada Yusrah Ta Koya Mata Wasu abubuwa da bata Sani bah Haka Itama Tasneem Ta koya ma Yusrah...

Ana Tashi Suka Fito a Tare Har bakin Gate, Nan Tasneem Ta hango Motan Naeem, Ta kalli Yusrah tace "Ga yayana Bye sai Gobe" Yusrah Ta dago Mata Hannu Itama Tace "Nima Ga mamana Chan", Motan Ta shiga Naeem ya hade rai Yace "Har kin Fara Yin Kawaye koh?" Ganin Yanda Ya hade rai Yasa ta Tsorata Tace "Itafa ta fara min Magana", Yace Harda Maza koh? Ta Girgiza kai Dasauri tace "Aa ban Kula kowa bah" Ajiyan zuciya yayi Yace "Banaso ki kula kowanne Namiji kinji?? Har Uncles Dinku Indai bah Tambayanki Sukaiba Akan Karatu" Kai ta Gyada Sannan tace "Tho"
Chapter 10 · 0% Book details