← Book details Tasneem Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 23

Sashe 19

Tasneem Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mami Ta nuna ma Tasneem Dakinta Wanda Yake Kusada Nata, Ta Shiga Mata da Akwatunan Kayanta Sannan Ta Fito...Kwanansu Biyu Suka Saba da Gidan Already Abba da Faizan Sunyi Resuming aiki, Dukansu Karfe Bakwai Suke Fita Kowa Ya nufi Nashi Gurin Aikin, Mami Dakanta Takai Tasneem Tai Mata Registration a Dambo Intl School Barnawa, Js2 Aka sata Bayan An Mata Exam Taci, Ahaka Itama Ta fara Zuwa Makarantan ta, Abba Yasama mata Driver dazai Rinka kaita Makarantan Yana daukota, Kullum Idan Suka Fita Tasneem Taje Makaranta Mami Kawai Suke Bari a Gida, Drivern Tasneem Tasa Ya cigita mata Yar Aiki Cikin Ikon Allah Tasamu Mai hankali kamar Sa'a Ta cigaba da Mata Aiki...

Tasneem Tayi Sababin Kawaye Yan Gayu Wanda Iyayensu keji da Kudi, Dukda Itama ba baya Take bah, Saboda Abba Na Wadata ta da Sutura Da abubuwan More Rayuwa Iri Iri, A cikin Makaranta Idan Ana Lisafa Yara Masu Ji da kansu Dole Tasneem Tana Cikinsu, Haka Faizan Shakuwa Sosai Ya shiga Tsakaninsu, Har Mami Takanyi mamaki yanda daya ke Damuwa idan bah Daya, Dukda Ita Tasneem Sam Bata Fahimci Santa Yakeba, Shiko Faizan Kokarin Yanda zai Faranta Mata Yake Ya nuna mata Tsantsar Santa dayakeyi...

Wata Ranan Sati Suna Zaune Duka a Dinning Suna Breakfast, Tasneem da Faizan A Plate daya Sukecin Abinci Wannan Yace Wannan Ya Kwashe, Wannan ma yace Wannan Ya Kwashe, Haka Suketa Shirmensu Mami da Abba sai Dariya Suke, Abba yace "Maza Tasneem ki gama kinga Lokacin Islamiya Ya kusa" Tho Tace Suka cigaba daci suna Hira, Maranta ne Taji Ya murda Tace "Ouch!" Dakarfi, Faizan Ya Kalleta Yace "Yaya Whts wrong?" Mami da Abba Suma ita suke kallo, Ta Turo Baki tace "Cikina ke Ciwo" Mami Tace "Bah Dole Yayi Ciwo bah kinata Dura Abinci Bayan kuma kin qoshi, Sai Biyema Faizan kike koh??" Batace Komai bah sai Cije Lebe Datakeyi, A Hankali Ta Mike Rike da Cikin Ta haura Sama Zuwa Dakinta...

Kan Gado Ta Fada Ta Rike Maran Tana Cije Baki, Ciwo Sosai Yake Mata Har Batasan Sanda Ta saki kuka Mai Qarfi bah, Kuka Take Sosai Tana Cigaba A juye Juye Hannunta Riqe da Maran, Tun Tana Kan Gado Har Saida Ta fado Kasa, Mami Ta Hauro zata Shiga Dakinta Taji Kaman Kukan Tasneem, Ta Bude Kofan dakin Kadan Ta leqa, Kwance Tasameta a Kasa tana Juye Juye tana Kuka, Mami ta shiga dasauri ta dago Tasneem A rude tana Tambayanta meya Faru? Kuka Take Tana Nunama Mami Maranta, Dasauri Mami Ta fito Ta Sauka kasa, Faizan Da Abba suna Kan Dinning Har yanzu suna Hira...

Mami Ta Kwalawa Abba Kira a Rude, Tace Kuzo Tasneeeem, Tasneem, Ta koma Sama dasauri, Faizan Ya mike Dasauri Ya haura Saman, Yanda Mami ta barta Haka Suka dawo Suka Sameta Saidai Wannan Karon Bata Motsi, Idanunta a Rufe Sai Hannunta Dake kan maranta, A rude Faizan ya Sungumeta Yayi Gurin Mota da ita, Mami ta shiga, Abba yace "Zan biku a baya kuje" Kuka Mami Take Tana Shafa Fuskan Tasneem Dake Kan Cinyanta, "Faizan hankalinshi a tashe Ya juyo Yace "Pls Mami stop Crying pls" Ya maida Idonshi kan titi, Yana driving Lokaci Lokaci yana bugun Stearing Motan Tareda Cusa Hannunshi na hagu Cikin Suman Kanshi yana Furzar da Iska, A haka har Suka kai Asibitin...

Ummu Farheen✌🏻
N
Aysha Gana💕
[10/10, 3:46 AM] 🍹🍬🛍💍Salma🍷💍🛍🍬: [10/8, 6:41PM]

💥💥TASNEEM💥💥

Na *Ummu Farheen*
N
*Aysha Gana*

*135 to 136*

Faizan Hankalinshi a tashe ya juyo yace "Pls Mami Stop Crying pls" Ya Maida idonshi kan titi, Yana Driving Lokaci lokaci yana Bugun shearing Motan tareda Cusa Hannunshi na hagu Cikin Suman Kanshi Yana Furzar da Iska, A haka har suka Kai Asibitin...

Ko Kwakwaran Parking Faizan beyi bah Ya fito ya bude baya Yadauketa Ya Shiga da ita Asibitin, Nurses neh sukai Saurin Amsan Tah Akai Emergency da ita, Mami a Rude Ta Shigo Ta kalli Faizan Tace "Ina Take?" Dakinda Aka Shiga da ita Ya nuna Mata, Ta Kalleshi da mamaki Tace "Aina Kasamu Jini??" Kallan Jikinshi yayi sai a sannan Ya lura da Jinin daya batamai Riga, Ya kalli Mami a Tsorace Yace "I dnt Knw" Batace Komai Bah, Abba Ya shigo Asibitin, Mami Yasamu Zaune Tayi Shiru, Yace "Ina Tasneem din??" Tace Tana Emergency Har Yanzu basu Fito bah, Sun Dade Sannan Likitan Ya Fito Yamusu Bayanin Period Zata Fara Shine Yazo mata da Ciwon Mara, Likitan Ya kalli Abba Yace "Shawara Anan Alhaji amata Aure da Wuri, Saboda Yawancin Mata Idan Aka musu Aure Suka Sadu da Mazansu Yawanci Suka dena, Abba ya kalli Mami Suka Hada Ido, Yace "Tho Mungode Likita"...

A Kofar Office din Suka Samu Faixan Yadawo Siyan Magani, Ya Kalli Abba yace "Abba meke Damunta" Shiru Yadanyi Sannan Yace bkmai kawai ciwo neh, Duka a Tare Suka Shiga Dakin datake Kwance, Barcinta Take Tasha Sai Drip da ake Kara Mata...

Kwananta Uku a Asibiti aka Sallamesu, Mami Tayi Mata Bayanin Yanda abin Yake, Tasneem Sai Kunya Takeji Mami na Dariya, Kwana Biyu Ta Kara bataje Makaranta bah, A Kwana biyun Ta Ware Sosai Ranan na Uku Ta koma Makaranta...

Naeem ne Zaune a Wani Gurin Shakatawa, Iska ne ke kadawa Mai dadi, Wurin Zagaye da Flowers masu Daukan Ido, Kowa nata harkan Gabanshi, Naeem Koh Kanshi nakasa Hannunshi Rike da Hoton Tasneem Sai Papern Datai Drawing dinta Ita Dashi, Kallan Rubutun Datai a Kasa Yake Yana Kara maimaita Kalmar a Ranshi, Ganin Mutum yayi Ya xauna kusada shi Yadan juya ahankali, Yusrah Yagani Zaune Tana Kallanshi tana Murmushi, Kauda Kai Yayi yaja Tsaki, Tadan Rankafo Tace "Haka Naeem ban Chanchanci Haka daga gareka bah Naeem...

Gyara Zama Yayi Ya juya Baya, Yusrah Ta Marairaice Fuska Kamar mai Kuka tace "Dan Allah Naeem Kaimin Magana konaji Dadi pls" Ina Matukar Sanka Narasa Yanda Xanyi pls karka bari sanka Ya hala Kani, Ya juyo fuska a murtuke cikin Fushi Yace "Ya halakaki Mana So What, I Hate You Yusrah, I hate You! Ki Fita Daga Rayuwana mana Dole ne Saina Soki nace Bana sanki, Ki Barni Naji da Abinda ke damuna pls" Yana Fadin Haka Ya mike Yabar Wajan...

Fashewa da kuka Yusrah Tayi ta bishi da Kallo harya Bace, Drivern daya Kawoshi Ya Tukashi Zuwa Gida, A Garden Yasamu Dad Yana Hutawa, Har xai Wuce dad Ya kira Sunanshi, A Hankali ya Taka Har zuwa Inda Yake, Dad ya nuna mai Kujera Yace "Sit" Bah Musu ya zauna kanshi a kasa, Dad Yayi gyaran murya Yace "Lokaci Yayi Naeem dazaka Cire Komai a Ranka, Bana Jin Dadin Ganinka haka, Munyi Magana Da Management din Hospital Din nan Sunce Ran monday ka Koma Aiki, Tunda dama kai ka gujesu, Naeem Ya Dago dasauri Yace "Butttt...

Dad Ya Katseshi yace "Shhh! Banasan Musu Naeem, I promise You idan Har Ka Koma Aiki Sannan ka Cire duk wata damuwa a Ranka, Ni dakaina Zanje Nigeria na nemi duk Inda Tasneem Take i Promise, And She Wil Insha Allah be Your Wife", Naeem ya dago Fuskanshi Dauke da Murmushi Yace "Dad are You Serious??" Dad Ya gyada kai yace "Nataba Maka Wasa??" Naeem Ya mike ya rungume Dad Yana Dariyan Farin Ciki Yace "Thank you dad! Thank You, You d best dad Ever" Ya sakeshi Ya Shiga Cikin Gidan a Guje Yana Kwallawa Mum Kirah...

```To Fans ya kuke Ganin Mum Zatai reacting Idan Taji Wannan Zanchan??```

Ummu Farheen✌🏻
N
Aysha Gana💕
[10/10, 3:46 AM] 🍹🍬🛍💍Salma🍷💍🛍🍬: [10/9, 9:00AM]

💥💥TASNEEM💥💥

Na *Ummu Farheen*
N
*Aysha Gana*

*137 to 138*

Naeem ya dago fuskanshi Dauke da Murmushi Yace "Dad are you serious??" Gyada kai Yayi Yace "Nataba Maka Wasa?" Naeem Ya mike Ya Rungume Dad Ydba Dariyan Farin Ciki Yace "Thank you dad! Thank You, You d best dad Ever" Ya sakeshi Ya Shiga Cikin Gidan a guje Yana Kwallawa Mum Kirah...

Tana Daga daki tajiyo Kiran Naeem, Yanda Yake kiranta Alamar da Alamar Farinciki Yasa Ta Tashi Dasauri Ta tari dan Nata, Tana Fitowa Sukai Kicibus Yana Kokarin Shiga, Murmushi Ya Sakar Mata Ya Rungumeta, Turus Mum Tai Yaushe Rabonda Koh Murmushin Naeem Tagani, Itama Murmushin Tai Tace "Tel me Son meya Faru??" Yadanyi Dariya Ahankali Yace "Mum dad Promised me Idan na Fara Xuwa aiki zaije Nigeria Ya nema min Tasneem" Murmushin Murna Mum Tai dan Ta Gaji da Ganin dan nata a Wani Hali, Yanzu ta Yarda Sosai Naeem Yakesan Tasneem, Mum Ta shafa Suman kanshi Tana Murmushi Tace "Am Very happy, Allah Yasa Rabon muce" Naeem Yace "Ameen Yabar Wajan Cikeda farin Ciki...

Tun Daga Ranan Naeem Ya Saki jikinshi Yadawo Naeem dinshi nada, Ranan Monday da Sassafe Ya Shirya Cikeda Farinciki Zai Tafi Asibiti, Mum Tayi Tayi Ya Tsaya Yaci Abinci Anma Ina! Haka Ya tafi Asibitin. Doctrs da Nurses harma da Cleaners Sunyi Murnan Ganinshi Sosai Ciki Harda Yusrah dake ta Kokarin Nuna Mishi Murnan ta Yana Sharewa, Haka Ya Cigaba Da Aikinshi Kullum Sai Yusrah Ta dameshi...

Sati biyu da Komawan Naeem aiki, Dad Ya karbi address din Garinsu Tasneem a Wajan Naeem, A Sati na Uku Dad ya Dau Hutu a Wajan aiki ya taho Nigeria. Har Airport Naeem ya raka dad Saida Yaga jirginsu ya tashi Sannan Ya koma Asibiti...

Naeem ne zaune a office dinshi Yana duba Foldern Wani patient, Knocking Yaji a Kofan, Yace "Yes come in" A Hankali ta murda Hannun kofan ta Shigo, Bai Dago bah Ya cigaba da Abinda Yakeyi, Jin Shirun Yayi yawa Yasa Ya Dago kai, Yusrah Yagani Tsugune a Kusa Dashi idonta taf da Hawaye, Ya hade Rai Yace "What dah hell are you doing in my Office" Hawayen Dake Maqale a Idonta Suka zubo, Tace "Naeem ina Azabtuwa da Sanka, Dan Allah karka bari sanka ya zama Ajalina Dan Allah, Ina Sanka ina matuqar Kaunarka. Ta Fashe da Kuka mai Tsanani Kanta a kasa, Kauda Kai Yayi Yadanyi Tsaki, Ta dago Tace "Kasoni koda Rabin wanda nake maka neh Dan Allah"...
Chapter 19 · 0% Book details