← Book details Tasneem Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 23

Sashe 18

Tasneem Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana Idarwa Mum Ta ajemai Abincin, Saida Tadingi Mita Sannan Yadanci kadan Ya Ture, Yarinyan Nan ne Ta kara Shigowa da Sallama, Dukansu Suka Amsa Tareda maida dubansu kan Kofan, Naeem na ganinta Yaja guntun Tsaki Ya kauda Kai, Mum Tadan kalleshi Sannan Ta Kalli Yarinyan Cikeda Murmushi Tace "Ya Farka, Nagode Fah Allah Ya saka da Alheri da Lura dashi da kikai tayi" Dan murmushi tai Tace "Bakomai Mama", Mum Tace "Bansan Sunanki Bah?" Murmushi Tai Tace "Sunana Yusrah", Mum Tace "Nafa Gode Yusrah" Yusrah Ta kalli Naeem Wanda Tun Shigowanta Ya kauda kai Tace "Naeem Ya jiki" Yi yayi kaman Baiji bah, Mum Tace "Tanama Ya jiki" Batare da ya kalleta bah Yace "Dasauki" Tamai Murmushi Tace "Allah Kara Sauki" Mum Ta Amsa da Ameen, Sannan Ta Fita...

Naeem Ya hade Rai ya juya Ya Kalli Mum Yace "Mum I hope Baki Bari Yarinyan nan Ta tabani bah" Mum Ta kalleshi da mamaki tace "To sai meh dan ta tabaka??" Ya kara hade rai Yace "Banaso! Pls mum" Murmushi Mum Tai tace "Idan Ance Tabawa daya knan, Ta tattabaka" Naeem Ya juyo Ya Kalli Mum Yace "WHAT?" Mikewa Yayi dasauri Ya Shiga Toilet Wanka Ya Sake Saida Ya gugurje Jikinshi Sosai Sannan Ya fito, Mum sai Kallanshi take abin nabata Mamaki...

Kwanan Naeem Biyu Ya Warware Sosai, Kullum Sai Yusrah Ta shigo ta gaishe da Mum, Likitoci ma haka Saboda Naeem Yadanyi Aiki Dasu Kafin Zuwanshi Nigeria, Ranan Daya Cika Kwana biyu Aka Sallameshi, Dad yazo ya daukesu Suka Tafi Gida, Yusrah Harda Yar Kwallanta Ranan Da Naeem Zaibar Asibitin...

Alhamdulillah Naeem Yasamu Sauki saidai Yanzu ya zama So Silent Magana sam Bai Dameshi bah, Kullum Yana zaune Shi kadai Sai Hoton Tasneem dayake Tasawa a Gaba Yayita Kallo, Wani Lokacin Har Kuka Yakeyi, Dad Ya Fuskanci Halinda Dan nashi ke Ciki, Sannan yayi Alkawarin Koma Wacece Wannan Yarinyan sai Tazama Mallakin Naeem Dinshi...(Tho Pha!)

**
Faizan ke Driving Sai Baya Mami da Abba Gaba kuma Tasneem, Faizan Yace "Abba Wai Yaushe ne Tafiya Kadunan??" Abba Yace "Ranan Sunday Insha Allah, Saboda mamanka Ta gama Komai nima Nagama" Faizan Yadanyi Murmushi Yace "Allah Ya kaimu" Abba Da mami sukace Ameen, Tasneem Ta juya Ta Kalli Mami Tace "Mami What is Todays Date??" Mami Tace "4th Sept" Menene Baeby?? Zaro ido tai Tace "Mami Gobe Zamu Koma School" Mami tace "Zamu Chanza Gari Zamu Koma Kaduna da zama Sabda Abba Ya samu Transfer Zuwa Chan, Sannan Faizan Yasamu Aiki a Chan, kinga Idan Muka koma Sai Asaki Wani Makaranta Mai kyau Koh" Ihu Ta saki Tana Murna, Faizan Ya kalleta Yace "Kedai Allah Ya Shiryeki" Murguda mai Baki Tai Ta Cigaba Da Murmushi Ita kadai Yayi Kwafa Yace "Zaki Sani dani kikeyi"..

A Bakin wani Babban Boutique Faizan Yayi Parking, Abba Ya Fito Mami Ma ta Fito Sannan Ta budema Tasneem Ta Fito, Turo baki Faizan Yayi Ya kalli Abba Ta cikin Glass din Motan Yace "Ni Abba Baka Budemin Bah" Dan Dariya Abba yayi yace "Oh Faizan Asan An girma dai, Wannan Shagwaban ai sai abarma Tasneem" Kara Shagwabe Fuska Yayi Ya juya Suka Hada Ido da Tasneem Dake Tamai Dariya, Dunkule Hannu Yayi Ya nuna Mata, Ta Kara Kyalkyalewa da Dariya Tamai Gwallo, Abba Ya bude mai Ya fito Sannan suka Dunguma Zuwa Cikin Shagon...

Mami Ta kalli Tasneem Tace "Kuje da Faizan kidau duk abinda kikeso", Tsalle Tasneem Tai Ta Shige Ciki Ta Fara jidan Kaya, Faizan na Bayanta Rike da basket, Inta Dauka Saita Wurga Mai, Wani ya Sameshi a Fuska Wani Ya sameshi a Kirji, Wani a Ido, Wani Ya fadi Ya Dauko, Haka taita wuwurga Mai Kayan Kwafa Kawai Yake Tayi Yana Murmushi Shi kadai,

Saida Ta Jida Kaya Sosai, Faizan na biye da ita dakyar Yake Daukan Kayan, Wajan Teddies ta nufa, Wani Kato Ta janyo, Faizan Yace "Ina zaki kai Wannan gunkin?" Ta Juya ta Turo baki Tace "Inaso ne" Faizan Yace "Tab Gunkin?? Ina!" Bata Rai Tai Tana kokarin Yin Kuka Tace "Ya Naeem Ya Saya min Dayawa Kuma....Bata Karasa Bah Yace "Dauka"Hada Rai Faizan Yayi Sam Baisan Yaji ta ambaci Sunan naeem, Haka Ta gama Jidan Abinda zata jida Suka Fito Abba Ya biya Suka Fito, Har Sun Shiga Mota Zasu Tafi Kamar Ance Tasneem Ta daga ido Tako hango Dr Sa'ad Yayi Parking Yana Kokarin Shiga Cikin Shagon, Tada Motan Faizan Yayi, Tasneem Sai Murda Kofan Take Tana kokarin Fita...

Ummu Farheen✌🏻
N
Aysha Gana💕
[10/10, 3:46 AM] 🍹🍬🛍💍Salma🍷💍🛍🍬: [10/7, 5:46AM]

💥💥TASNEEM💥💥

Na *Ummu Farheen*
N
*Aysha Gana*

*131 to 132*

Har sun shiga mota zasu tafi Kamar ance Tasneem ta daga ido Tako hango Dr Sa'ad Yayi Parking Yana Kokarin Shiga Cikin Shagon, Tada Motan Faizan Yayi, Tasneem Sai Murda Kofan Take Tana Kokarin Fita, Bah Wanda Ya Lura da Abinda Takeyi Har Suka bar Haraban wajan, Saida Suka Hau Titi Sunyi Nisa Sannan Tasneem ta Fashe da Kuka, Faizan Ya Juya Ya kalleta a rude Yace "Menene??" Abba dake Baya Suka Hada baki da Mami Wajan Tambayan tah...

Kasa Magana Tai sai kukan data Cigaba, Har Suka Isa Gidan bata daina Kuka bah, Dakyar ta Yarda Ta fito daga motan, Mami ta kama mata Hannu suka shiga Ciki, Dakyar Ta Fada ma Mami abinda Ke Faruwa, Faizan da Abba nafalo duk Hankalinsu a Tashe, Mami Ta Sauko Tana Fada musu Abinda Tagani, Dogon Tsaki Faizan Yayi Ya Hade Rai, "Shi Harga Allah baisan Ana Maganan Naeem din nan" Mami ta Kalleshi da Mamaki, Baice Komai bah Ya Mika ma Mami Kayan Tasneem din Yabar Falon Dasauri. Abbah Yace "Ai datayi Magana Kinga a Wurinshi Zamu San Inda Naeem din Yake" Mami Tace Hakaneh...

Wuri Tasamu Tazauna Ta Kalli Abba Tace "Dama Akwai Abinda Na Manta ban Fadama bah" Abba Ya gyara zama Yace "Inajinki", Mami Tadanyi Murmushi Tace "Faizan Fah San Tasneem Yake Tuntuni, Tun Bata Nan Gidan Yace "Yana Ganinta a Hanya idan Za'a Kaita Makaranta koh Zasu Fita", Murmushi Jindadi Abba Yayi Yace "Dan Nema Ki Kyaleshi Indai Santa Yake Tho Yazo ya sameni Dakanshi" Itama Mamin Murmushin Tai Tace "Kasan Zai Iya" Abba Yace "Ina Nan ina Jiranshi Saiya zo"...

Yini Tasneem Tai Kuka Mami Bah Irin Lallashin da batai bah Haka Abba sam Taqi Cin Abinci, Sunan Naeem da Mama Laraba Kawai Take Kira, Lokaci Lokaci Takan Kalli Zoben Hannunta da Naeem Ya bata, Abba Ya daga Waya Ya Kira Faizan, Daya zo ya Fada Mai Tasneem Taqi Cin Abinci Sai kuka datake, Dukda Ta batamai Rai anma Sam Baiji Dadin Kukanta bah Dakuma Rashin Cin Abincinta, Dakin Ya Shiga Ya sameta Zaune a kasa ga Abinci a gabanta Ta rungume Hannu sai Kuka Take, Ganin Yanda Idonta Suka kukumbura Yasa Ya Rude Ya Karasa kusada ita Ya zauna, Abincin ya janyo ya Ciro Hankiey a Aljihun shi Ya goge Mata Hawayen, Dagowa Tai Ta Kalleshi Ya girgixa mata kai, Sannan Yace "Pls Stop Crying, banaso naganki kina kuka" Bakisan Kukan nan zai iya jawo miki Ciwo bah?? Pls Stop ko nima Kinaso inyi kukan neh??" Girgiza kai Tai Alamar Aa, Abincin Ya dibo a Cokali Yakai Mata baki Takauda Kai...

Langwabar dakai Yayi yace "Plsssss" A Hankali Ta bude baki Yasa Mata, Saiya Lallabata Sannan Take amsan Chokali Daya, Ahaka Har Tadanci Abincin, Duk Abinda Sukeyi Mami da Abba Suna Bakin Kofa Suna Kallansu Sai Murmushi Sukeyi, Tasneem Ta Kalleshi Tace "Na Koshi" Yace "Are You Sure?" Kai Ta gyada mai Alamar Eh, Ruwa Ya kara bata Tasha, Sannan Yayi murmushi Ya lakaci hancinta Yace "Mai Kukan Banza Kawai" Itama Murmushin tai, Ya mike yace "Ki Shirya Muje Wani Guri" Yana Fadin Haka ya fita Dama Already su Mami sun bar Wajan...

Kaya Tasneem ta Chanza Cikin Wanda Ta zabo dazu, Riga da Skirt Pink Tasa Ta Daura Blue Hijab akai, Kayan sun mata kyau Sosai, A Falo ta Tarar dasu Mami, Dagudu Tai Hanya Fita Sannan Tace "Abba! Mami Mun Fita da Ya Faizan Bye" Mami Tace "Take Care Baeby" A bakin Mota ta Hadu Dashi yana Jiranta, Ya Shiga ita Ta Shiga, Tada Motan Yayi Sannan ya Kalleta Yace "You look Subab!" Murmushi kawai Tai, Ya Kalleta Kasa Kasa Yace "I love You" Dariya tai Tasa Hannu Ta Rufe Fuskanta, Shima Dan Dariyan Yayi yace "Kice Uh Love mie pls" Girgiza kai Tai Alamar Aa Yace "Why?" Kara Girgixa mai Kai Tai, Murmushi yayi Ya Ja motan suka bar Gidan...

Yawo Sukai ranan sosai, Ya nuna Mata Wurare Dayawa, Wani Gurin idan Sukaje Sai tace "Ta taba zuwa Itada Naeem" Tun Tana Kiran Sunan Naeem Yana Bata Fuska Harya Ware Sukai hira Sosai, Kayan ciye Ciye Yasai Mata Dayawa sai Daf da Magriba Suka Dawo Gida Tasneem cikeda Jin Dadin Yawon da Sukai Yau...

Shirye Shirye Mami Take Sosai na Barin Katsina, Komai Datake Buqata ta dauka Har an Tafi dasu, Sauran Funitures Kuma da Kayan Kitchen Duk Tace "Sa'a Tazo ta daukan ma mamanta" Kayan sawansu Kawai ta hada sai Yan Abubuwan da Ba'a Rasa bah, Rannan Sunday da Sassafe Suka Daga Zuwa Kaduna Garin Gwamna...

Ummu farheen✌🏻
N
Aysha Gana💕
[10/10, 3:46 AM] 🍹🍬🛍💍Salma🍷💍🛍🍬: [10/7, 2:11PM]

💥💥TASNEEM💥💥

Na *Ummu Farheen*
N
*Aysha Gana*

*133 to 134*

Shirye Shirye Mami Take Sosai na barin Katsina, Komai datake Buqata ta dauka Har an Tafi dasu, Sauran Funitures kuma da Kayan Kitchen duk Tace Sa'a Tazo tadaukan ma Mamanta. Kayan Sawa Kawai Ta Hada Nata dana Tasneem saina Abba, Sai yan Abubuwan da Ba'a Rasa bah, Ranann Sunday da Sassafe Suka Daga Zuwa Kaduna Garin Gwamna...

Tun a Hanya Tasneem Tai Barci, Batasan an iso Gariba Saida Suka Shiga Gidan, Jidatai Mota ta Tsaya Yasa Ta bude ido a hankali, Ganinsu Tai a Cikin Wani Hadadden Gida, Haraban Gidan ma kadai Abin Kallo neh, Mami Ta Bude mata Ta Fito Suka Shiga Cikin Gidan, Sakin Baki Tasneem Tai Tana Kallan Gidan, Faizan Ko sai Dariya Yake qasa qasa Ganin Yanda Ta saki Baki Tana Kallo, Mami ta Galla mai Harara bah Shiri Yayi Shiru Yabar Falon..
Chapter 18 · 0% Book details