← Book details Tasneem Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 23

Sashe 16

Tasneem Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lokaci Guda Taji San Tasneem ya Shigeta, Cikeda Murmushi ta koma Side dinsu..

Tasneem Ta kalleshi Tace "Mainene Sunanka?" Yadanyi Murmushi Yace "Bakiji Mami ta kira Sunana bah??, Ta girgiza kai Alamar Aa Yace "Sunana Faizan" Tace "Umm Sunan Yan Gayu Ban Tabajin Sunanba" Murmushi Kawai Yayi Ya Xuba Mata Abincin Ya mika Mata, Kurrri Tamai Tana kallanshi Yace "Eat mana Sis ko kinaso nabaki a baki??" Kai Ta girgiza Alamar Aa...

Fork din ta dauka Ta Fara Ci, Idonshi ne Yakai kan Zoben Dake Hannunta, Ya kalleta Yace "Waya baki Wannan Zoben?" Ta Kalli zoben Ta maida Dubanta ga Faizan Idonta cikeda Kwalla tace "Ya Naeem ne Yabani" Murtuke Fuska Yayi Yace "Pls ki Cire Kinga Fah Yanzu bakwa Tare" Girgiza Kai Tai Tana Kallanshi Tace "I promise him bazan Taba Cirewa bah" Baice mata Komai bah Har ta gama, Ya Kalleta Fuska bah Walwala Yace "Muje Wajan Mami"...

Bah Musu ta mike Tabi Bayanshi Har Side din Mami, Suna Shiga Tasneem Ta Saki baki Sai Kallan Gidan Take, Tunda Take bata Taba Ganin Gida mai Kyau Irin Wannan Bah, Duk da Cewa Gidan Naeem ba Baya Yake bah, Amsa Wannan yafishi Kyau da Komai..

Gani Tai Ya haura Sama Ta Bishi Dasauri, Dakinda Ya tura ya shiga da Sallama Itama Ta shiga, Zaune Suka Sami Mami Kan Gado Tana waya, Saida Ta gama Sannan Faizan Yace "Gata" Murmushi Mami Taima Tasneem Tace "Dawo kusa dani kinji" Mikewa Tasneem Tai Tadawo Kusada Mami Ta zauna, Mami Tadan Rungumota Tace "Zaki Zauna Damu?" Kai Tasneem Ta gyada Sannan Tace "Anma Ku fara kaini Wajan Ya naeem da Mama Laraba" Shiru Mami Tai, Faizan ya mike tareda Hade Rai Yace "Idan Muka Fita zaki Ganeh Gidan??" kai Tasneem Ta Gyada Yace "Tashi Muje Tho"...

Mikewa Tasneem Tai Mami Tai Saurin Riketa Tace "Tsaya To mana kiyi wanka, Dakyar Ta Shawo Kan Tasneem Tai Wanka, Driver Tasa Ya Kai Sa'a kasuwa aka Sayo mata Kaya Masu kyau da Tsada, Daya Ta zabar Mata Tasa Sannan Suka Tafi, Yawo sukai Sosai har yanma Tasneem bata Gane Gidan bah, Haka Suka karaci yawon su duk sun gaji suka dawo gida..

'Mami Tace "Nidama Nasan Bazata Ganeh Gidan nan bah, Faizan Ya kalli Tasneem Yana dan murmushi Yace "Duk in bamu Wahala" Mami tace "Sorry!" Baice komai bah Ya mike Yace "Pls Mami am Hungry ina Side dina" Bai Jira mai Zatace bah Ya Bar Falon!, Sa'a Ta kwalla wa Kira, Abincin Ta hado a Tray Ta Nufi Kofan Falon Zata Fita, Tasneem dake gefen Mami Tanacin Nata Tace "Mami in Bita?" Aa keda kikecin Abinci ki bari ki Gama, Zumburo Baki Tasneem Tai Ta Cigaba da Cin Abincin, Dan murmushi mami Tai, Itadai Allah ya Daura Mata san yaya mata Gashi Allah bai Bata bah, Kallan Yanda Tasneem Take Cin Abinci Take Cikeda shawa'a...

Tana Gamawa Ta muke dagudu Tabar Falon, Side din Faizan Ta nufa, Murdan Kofan Tai ta Tura a hankali, Zaune ta sameshi kan Two Seater Ya aje laptop akan Cinyanshi Yana buga Zuma, Dagowa Yayi Ya kalleta Yasakar Mata Murmushi, Karasawa Tai Ta zauna kusada shi Tana Kallan Yanda Yake Bugawa, Saida Ya buga kusan Stage Biyar sannan Yasa Pulse Ya janyo trayn Abincin...

Tasneem Ta dauka Tana Kokarin Dannawa Yace "Meh Zakiyi?" Turo Baki tai Cikeda Shagwaba Tace "Nima Zan buga ne" Yadanyi Murmushi Yace "Tho kin Iya neh?" Girgiza kai Tai Alamar Aa Sannan Tace "Anma ai naga Yanda kakeyi" Baice Mata komai ba Ya Fara Cin Abincin shi, Tana Ganin Haka Ta Janyo Laptop din ta soma Shige Shige!, Game din Taga Ya bace, Shige Shige Take tayi Ta goge Wanchan Ta Goge Wanchan, Ganin Barnan Datamai Yasa a Aje System din Sadaf Sadaf Tabar Falon, Kiran Sunanta Yake Tanaji Ta Arce a dari da sittin....

Zakumin Afuwa na Rashin Posting Ina Karatu ne Ranan Talata Xan Fara jarabawa, Ina baran Adduar ku Fans..Thanks

Ummu Farheen✌🏻
N
Aysha Gana💕
[10/9, 10:21 PM] 🍹🍬🛍💍Salma🍷💍🛍🍬: [10/4, 6:00AM]

💥💥TASNEEM💥💥

Na *Ummu Farheen*
N
*Aysha Gana*

*123 to 124*

Tana Ganin Haka Ta janyo laptop din ta soma shige shige, Game din taga ya bace, Shige shige take tayi ta goge Wanchan ta goge wanchan, Ganin barnan datamai yasa ta Aje systen din sadaf sadaf tabar Falon, Kiran Sunanta Yake Tanaji ta arce a dari da Sittin...

```Naeem Fah?```

Zazzabi ne Sosai Ya rufe shi a Cikin Jirgi, Bah Karamin Tashi Hankalin Mum Yayi Bah, Rungumoshi Tai Ta daura kanshi akan Kafanta, A hankali Take Shafa mai baya Har Barci Ya daukeshi Dakyar, Dukda duk Wanda Yaga Barcin Yasan Bana dadin Rai baneh....

Karfe Bakwai na dare Jirginsu Ya sauka, Ma'aikatan Jirgin Sukai Waya aka taho da Ambulance, Suna Saukowa Mum Ta hade da dad Yana Jiransu, Ganin Naeem Kwance akan Gadon Ambulance Yasa Ya zare ido Yace "What Happen to my son" Shiru Mum Tai kanta a kasa Tana Hawaye, Baice komai Ba Tasa Kayansu a Booth din Motan Ta Shiga Yaja Suka Fara bin Motan Asibitin...

Tafiya suke lokaci lokaci Yakan Furxar da iska Tareda Dukan Stearyn Motan da Hannunshi na Dama, Saida Suka iso Asibitin Yanayin Paking Ya Juya ya kalleta Yace "If any Thing Happen ti my Only son...Gwafa Yayi Ya fita tareda Banko Kofan Ya Shiga Cikin Asibitin, Mum Mutuwar Zaune tai Hawaye Kawai ke Gangara daga Idonta, A Hankali Take Furka "Am Sorry Son!, Am Sooo Sorry" Fashewa Da kuka Tai Tana Tuna Irin Korar Dataima Tasneem da Mama Laraba...

Saida Tai Kukan Mai Isanta Sannan Ta mike Ta shiga Asibitin, Tana Shiga Litikan na fitowa daga Dakin, Dan Tsayawa Tai Duka Wuce Sannan Ta Murda Kofan Dakin a hankali Ta Shiga, Kwance Ta Sameshi Ana Samai Drip, Sai Gefenshi Magunguna da aka Cicire guda Daya, Alamar an Bashi, Idonta ya ciko da Kwalla Ta Karasa Bakin Gadon Ta zauna, Hannun Tasa Ta shafa Suman Kanshi Tadanyi Murmushi Hawayen Dake Makalle a idonta Suka gangario Tace "Am Sorry Son, Nama Alkawari sai Tasneem Ta dawo gareka I promise you"...

Gyaran Muryan dataji a bayanta ne Yasa Tadan Juya A hankali, Wata Likita ce Ta Shigo Da Sallama, Sanye da Dogon Riga Abaya Sai Lap code dake Saman Rigan, Fara ce Sosai, Saika Kalleta Sosai Zaka ganeh Yar Nigeria ce, Mum ta Kalla Tace "Sannu Mah" Gyada Kai kawai Mum Tai, Ta kara Murmushi Tace "Ya Jikin Naeem din?" Mum ta Kalleta da mamakin Hausan datai Tace "Dasauki" murya a Sanyaye, "Allah kara Sauki" Tace "Ta murda kofan Dakin Ta fita Tana Mai Jin Dadi, Lallausan Murmushi Ta saki Ta koma Office Dinta Tanata jin Dadi...

_Fans Ita kuma Wannan Fah??_( mudaije zuwa)

Bayan Isha Tasneem Nazaune itada Sa'a a falo ta kunna mata Mbc3, Takurewa Tasneem Tai a gefe hankalinta Sam Baya Wurin Kallon, Faizan ne Ya shigo Falon da Sallama, Sa'a Ta amsa tareda Mikewa Tabar Wajan, Ganin Halin da Take ciki Yasa Ya karasa Ya zauna kusada ita Yace "Sis Whats Wrong Meke Damunki??" Girgiza kai Tai alamar bah Komai, Gyara Kwanciyar datai Kan Kujeran Tai, Anan Yaga Hawayen Dake Kwance Kan Fuskanta, Gabanshi ne ya fadi Yace "Pls Sis Kidaina Kuka kinji"...

Handkie Yasa Ya Goge Mata Hawayen dake Fuskanta Yace "Tell me Why are You Crying??" Kallanshi Tai ta kara fashewa da kuka tace "Ya Naeem" Wani kololon Abu yaji a Kirjinshi da makoshin Shi Ya danne Yace "Tho yanzu ai Baya nan ki daina kuka kinji?" Duk Abinda Yake Miki Nima Zan Miki" Kara Goge Hawayen Dake Fuskanta Yayi yace "Bulala nazo namiki fah" Ta zaro ido Cikeda Shagwaba tace "Menayi" Dan Murmushi Yana San Shagwabar Ta, Ya kwaikwayi Yanda Tai magana Yace "Koba ke Bace dazu Kika Goge Mun Abubuwana Na System" Ya kare Maganan Yana Turo baki Tareda Rungume Hannu, Kyalkyalewa Da dariya Tai Tace "Kamar Ya Naeem" Dan gintse Fuska Yayi Ya Sasauta Murya Yace "Ki daina Fadin Ya Naeem Kinji Am now Your Brother"...

Kai kawai Ta gyada a Kalleta Murya a Sanyaye Yace "I Love You Tasneem, I love You soo Much" Dagowa tai dasauri Ta kalleshi, Duk da Bayau Ta Saba Jin Kalman Bah, Anma Nayau sai Ya mata nauyi, Muryan Mum Sukaji Tana Cewa "Ku tashi Kuban Guri inyi Kallo, Su o'I An Girma ba'a San an Girma bah" Turo Baki yayi ya mike Yace "Nidai Mami Bakya Sona yanzu bakomai" Yanzu Ko irin Babyn nan ma kin daina kirana, Dariya tai Tace "Kai Yanzu Kazama Kato Ka Girma" Ta Rungumo Tasneem Tace "She's Now My Baby"..

Dariya Tasneem tai Ganin Yanda yake Bubbuga kafa a kasa yana Turo baki, Mami Tace "Ahan kan Na manta Tomorrow by 9pm Abbanka fight dinsu Zai sauka Zamuje mu taroshi, And kai nakeso Kai Driving Muje" Ihu Ya saki Kamar Karamin Yaro Yace "Nima Wanda yake Sona Zai Dawo" Yabar Falon Yana dariya tareda Dagama Tasneem Hannu..

Tasneem Ta kalli mami Tace "Mami nima Zan Raka ku" Mami Tace "Aa Tasneem Ki Bari Idan Mukaje Muka dawo i promise you zan Kaiki Yawo" Girgiza Kai tai Tana Turo baki, Mami Tace "Oh Allah! Tasneem Rigima, Faizan Rigima" tace "Shiknan naji zamuje Tare" Rungume Mami Tai Tana Murmushi...

Ummu Farheen✌🏻
N
Aysha Gana💕
[10/9, 10:21 PM] 🍹🍬🛍💍Salma🍷💍🛍🍬: [10/4, 9:11PM]

💥💥TASNEEM💥💥

Na *Ummu Farheen*
N
*Aysha Gana*

*125 to 126*

Tasneem ta Kalli Mami Tace "Mami nima Zan Raka ku" Mami Tace "Aa Tasneem ki Bari Idan Mukaje Muka Dawo i promise you zan Kaiki Yawo" Girgixa kai tai Tana Turo Baki, Mami Tace "Oh Allah! Tasneem Rigima, Faizan Rigima" Shiknan naji zamuje Tare" Rungume Mami Tai Tana Murmushi...
Chapter 16 · 0% Book details