← Book details Tasneem Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 23

Sashe 11

Tasneem Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya Kura mata Ido Na kusan Minti Biyar Sannan Yace "Ina Sanki Tasneem Bana fatan Naji ko Naga Abinda zai Rabani dake, Hannunta Ya rike Ta Kalleshi Suka Hada ido yace "I Love You Ok" Murmushi Kawai Tai Batace Komai Bah, Yace My Love koh ke Bakya Sona?? Bakyaso Muyi aure Wata Rana mu haifi yara??

Dan Dariya Tai Tasa Hannu ta rufe Idonta Yayi Murmushi Yace "Bakyaso?" Tace inaso, Wani Kayataccen Murmushi ya Saki Ya Kunna Motan Suka Kama Hanya, Suna Tafiya Tana Bashi Labarin Scul, Hold Up ne Ya Rikesu Sai Shagwaba Take Ita Yunwa Takeji, Kamar Ance ta juya Tako Hango saurayin Nan Cikin Motarshi, Hada Ido sukai ya Mata Murmushi, Murguda mai Baki tai, Sai Kawai Gani Tai itama Ya murguda Mata, Gwalo Ta Sake mai, Shima Ya mata, Dariya Ta Saki dai dai sanda Hanya ta bude, Naeem Yace "Lapia?" Tace "Wannan baturen neh kemin Gwalo"..

Mamaki Fal Fuskan Naeem Yace Gwalo kuma? Ina Yake? Juyawa tai taga wayam bah kowa Ta juyo tace "Ban Ganshi bah" Baice Komai Bah Har suka iso Gida, Food Flask din kawai ta dauka ta fito Tabar Jakan, Tana Shiga Falon Dinning Ta nufa Kai Tsaye, Mama laraba dake falo tace "Tasneem bako Sallama Bare Gaisuwa kin Tafi gurin Abinci? Turo baki tai tace "Nayi fah Bakiji baneh" Abincin Ta soma Zubawa, Naeem Yayi Sallama rike da jakanta, Mama laraba tace "Oh Manya Fa an Fara zuwa makaranta, jakan kuma yayanki ne Zai Rinka dauko miki"..

Batace Komai ba sai Saka Loma take, Dan Murmushi Naeem yayi Ganin Yanda Take cin Abincin Tana Lumshe Ido Alamar Taji Yunwa, Dakinshi Ya Nufa dan Rage kayan Jikinshi...

Haka Tasneem Ta cigaba Da zuwa Makarantan ta, Shakuwa Sosai Ya shiga tsakanin Yusrah Da Tasneem, Ta fara Fahimtar Turanci Sosai, Ga Maida Hankali da Tasneem Tai Ga Karatun, Shakuwa Sosai ya Kara Shiga Tsakanin Tasneem Da Naeem, Every Week end Yakan Dauketa Suje Shopping Da Wuraren Shakatawa Sosai, A Haka har Tai Wata Shidda a Gidan Naeem, Yanzu Suna js1 Second Term...

Yau Yakama Saturday da Wuri Naeem Yatashi ya shirya cikin Shadda Golden, Sai Hula Kalar Shaddan, Kayan sun matukar Mai Kyau Ya Fito sai baza kamshi Yake, Tasneem Da mama laraba na palour Zaune Suna Kallo ya fito, Tasneem Ta mike dasauri Tace "Ya naeem Ina zaka?" Yace "Anguwa" Tace "Tho nima zani" Kai ya girgiza Yace "Aa Kiyi Hakuri bazan dadeba zan dawo kinji, Turo baki tai ta rungume Hannayenta Ta Shiga Daki dagudu Tana kuka, Mama laraba tace "Kyaleta zoka Wuce" Dan murmushi Yayi ya mata sallama ya Shiga mota Yadau hanyan Gangara Hayin Mallan...

Ummu Farheen✌🏻
[truncated by WhatsApp]
[10/9, 7:44 PM] 🍹🍬🛍💍Salma🍷💍🛍🍬: [9/20, 7:15AM]

💥💥TASNEEM💥💥

Na *Ummu Farheen*
+2348131845457
N
*Aysha Gana*
+2347017251433

*105 to 106*

Turo baki Tai ta Rungume Hannayenta ta shiga Daki dagudu tana kuka, mama laraba tace "Kyaleta zoka wuce" Dan Murmushi Yayi Ya Mata Sallama ya Shiga mota Yadau Hanyan Gangara Kauyen Hayin Mallan, Koda Ya Isa Direct Gidan Mai Gari ya Nufa, Saida Ya mika Gaisuwa Sannan Ya gabatar da Kanshi...

Mai Gari bai Manta Dashi bah, Sunyi Gaisuwar Mutumci Sosai, Naeem Ya gyara zama Yace "Dama nazo ne akan maganan Tasneem ko Mallan ya dawo?? Koh Yayanta" Mai Gari ya kalli Liman Suka hada ido Sannan Liman Yace "Gaskiya Mallan Bai dawo bah, Sannan Yayanta Kuma Tabbas Munji Labarin Yadawo Anma Sam Bai nememu bah, Dan Ance Ranan Da Ya dawo Ana Fadamai Cewa Kanwar ta Bace Yabar garin Yana Kuka"...

Girgiza Kai Naeem Yayi Yace "Tho Dan Allah Bah wanda Yasan Inda Yake Makaranta?? Nadai San ance Zaria Neh ABU anma Nemanshi Yanzu dakamar wuya, Domin Makaranta ce mai Girma, Mai Gari Ya Gyada Kai Yace "Hakane, Yanzu dai Ka Bari tukun Har Sai Allah Ya Kawo Mallan din", Naeem Yace "Tho bakada Waya Saina Rinka Kiranka inaji??" Mai Gari Yace "Mallan Liman Bashi Numbern ka Kwa Rinka Waya", Liman Yace "Tho Ranka Ya dade" Karanto ma Naeem numbern Yayi Yana Rubutawa, Sunyi Sallama Ya Musu Alheri Sosai Sannan Yadau Hanyan Komawa...

Direct Gidan Sa'ad Ya nufa, da Fara Ya Tarbeshi, Saida Suka Natsu Sannan Naeem Ya Fadamai duk Yanda sukai da Maigari, Sa'ad Yace "Hakan ma Yayi anma Naeem Yazakai da Mum dakacema Kamaida Ita Gida? Ina Tsoron abinda zaije yadawo fah", Tabe Baki Naeem Yayi Yace "ah dnt worry babu abinda zaije yadawo insha Allah,"...

Hira Suka dan Taba Daga Bisani Naeem Yamai Sallama Ya Dau Hanyan Gida, A Haraban Gidan Yaga Tasneem Kwance Ruf da Ciki a kan dan karamin carpet Tana Rubutu, Ya Karasa Da Murmushi Yace "My Love Nadawo Assignment kikeyi neh?" Turo baki tai Ta mike ta zauna Ta juya Baya, Sam Naeem Ya manta Fushi Take, Rarrafawa Yayi yadawo gabanta ya riko Hannunta Yace "Haba my love banaso kina Fushi dani am sorry kinji?", Turo Baki tai idonta Ya ciko da kwalla Tace "Koba Kai Baneh Kaki Zuwa dani", Naeem Yace "Am Sorry Inda Naje bai kamata Naje Dake bah, But kibari next week end sai muje Yawo koh??" Kai ta Gyada Tana Murmushi...

Littafin Hanunta Ya Amsa Yace "What are you doing??" Tai Murmushi tace "Assignment" Yace "Can i help you wit it??" Kai ta Gyada, Zama Ya Gyara Ya Shiga Solving mata Maths din Yanayi Yana Bata Tayi Yagani, Saida Ya Tabbatar ta iya Sannan Sukai Assignment din"...

Ranan Monday da Safe Tasneem Ta fito Shirye Ciki kayan Makarantan Tah, Dinning ta Zauna Ta Fara Breakfast, Shiru bah Naeem, Ta mike Tai knocking a Dakin ta Shiga Kai Tsaye, Kwance Tasameshi Yana Barci Hankalinshi Kwance, Hannu ta daga Zata Kai mai duka Sai kuma Tafasa Dabara ya fado mata, Toilet ta shiga Ta debo Ruwa Ta Yayyafa Mai a Fuska, Zumbur Ya Mike dan Ya matukar tsorata, Ganin Yanda Yayi Yasa Tasneem Kyalkyalewa Da dariya..

Hade Rai Yayi ya kira Sunanta a hankali, Ta Kalleshi Tana Cigaba da dariyan, Yace "My love why this?" Ta Turo baki a Shagawabe Tace "Tho bah kai baneh Kaki Tashi kai Breakfast ta kaini School", Mamaki karara a fuskarshi Yace "School kuma?, Shi Ali Drivern menene anfanin Sa??" Ta Bata Fuska Tana Bubugawa a kasa Tace "Nidai kai nakeso ka kaini" Baice Mata komai bah yadau Bargo ya lullube daga Kai har kafa..

Zaro ido tai da Mamaki, Hannu tasa Tana kokarin Janye bargon anma ta kasa, Dakyar Allah Yabata Sa'a Ta Janye Ta Yar, "Ohhh! My Love Rigima, pls kibari nai Barci ga Ali kice Yakaiki I promise you idan kunyi closing ni zanzo nadaukeki" Turo Baki Tai Ta Fita tana gungunai"...

A Hanya Ali Driver Yace "Yaukam Tasneem kinyi Latti" Ta turo baki Tace "Tho ba Yaya Nace Yakaini ba Yaqi", Murmushi Ali Yayi yace "Tho bagani bah" Batace Mai Komai Bah ta maida Kallanta ga Titi, Ido Suka hada da Baturen nan Cikin Hadaden Range Rovern shi Baki, Sanye Yake da Suit Fari kar, Gashin Shi luf Luf Kamar na Yan india...

Murmushi Ya mata Ta Galla Mai Harara, Maida Dubanshi Yayi kan Titi Yana Murmushi ahankali, Ta Turo Baki Tareda tsaki, Ali Driver Yace "Duk Rashin Kaiki Makarantan neh Haka??, Batace Komai Bah ta Kara kallan Window, Ko Alamarshi Batagani bah, Sai bin Motoci take da Kallo har Suka Kai Makaranta...

Yusrah ta Fara cin Karo da Ita a Bakin Gate din makarantan, Murmushi Sukaima Juna Suka Shiga Cikin Makarantan, Saida Aka Tashi Break Yusrah Tace "Kullum Inaba Ummana Labarinki Tace tanaso Taganki" Murmushi Tasneem Tai Ta dauko joter a Jakanta Tace "Ki Rubuta min Address dinku sai Nace Yaya Naeem ko Ali Ya kawoni" Bah Musu Ta rubuta mata Tasa a jaka...

Kamar Yanda Naeem Ya Mata alkwari Ana tashi Ta fito taga motanshi Yayi parking yana jiranta, Dan Murmushi tai ta karasa ta Shiga, Ya Kalleta yana murmushi Yace "My Love rigima, Shine kika Tafi Bako Sallama koh?" Batace Komai ba Ya Ja motan suka Dau Hanyan gida...

Haka Rayuwa yacigaba da tafiya, Gari ya waye, Rana ta Haska, Dare Yayi Kullum Rayuwa Sai kara tafiya Take, Yanzu Tasneem Tana Js2 Second term, Ta kara Girma Tayi Tsawo, Yanzu Tana shekara Sha Uku, Naeem Yakan Kira liman yaji Labarin ko akwai wani Labari gameda Tasiu ko Mallan, Amma Shiru...

Yau Kamar Kullum da Sassafe Ta shirya Tana Breakfast a kan Dinning, Naeem Ya fito Dasauri Yana kokarin Fita, Ta Kalleshi tace morning Ya Naeem! Sai a Sannan ya Lura da ita, Yayi Murmushi Yace "Oh Sorry My love Inada Emergency Theater ne a Asibiti, Tai murmushi Tace "Ok saika dawo" To Kawai Yace ya fita Dasauri, Mama laraba ta fito dauke da Breakfast din Naeem, Tasneem Tace "Ai Ya Tafi wai Yana sauri" Ta mike Tace "Nima Natafi, Mama laraba tace "Adawo Lapia"...

Tana Dawowa Ta Shiga Falon Dasallama, Decorating Falon Akai Ko Ina, Sai Wani hadaddun Cakes Tagani Guda Uku Akan Center Table, Yanda akai Decorating Falon Da cake din Ya matukar Burgeta, Karasawa tai Tana Kallan Cake Din, Daya an Rubuta "Tasneem is 13" Daya kuma An Rubuta "My Love is 13" Sai dayan aka Rubuta "Naeem and Tasneem" Idonta taji an Rufe Zatai magana Naeem yakai bakinshi Daidai saitin Kunnenta Yace Shhhh!..

Ummu Farheen✌🏻
[truncated by WhatsApp]
[10/9, 7:44 PM] 🍹🍬🛍💍Salma🍷💍🛍🍬: [9/20, 4:00PM]

💥💥TASNEEM💥💥

Na *Ummu Farheen*
+2348131845457
N
*Aysha Gana*
+2347017251433

*107 to 108*

Idonta Taji an Rufe Zatai Magana Naeem Yakai bakinshi Daidai Saitin Kunnenta Yace "Shhh", Gyalle Yasa Ya Rufemata Ido, Sannan Ya Rike Hannunta Har Dakinta, Idonta Ya Bude, Dakin Tabi da Kallo, Komai na dakin an chanza, Komai Pink akasa, Sai Manya Manyan Teddys da Aka Sa A Gefe Gefen Gadon, Dagudu Ta karasa Ta Dauki Daya Ta Rungume, Bangon Dakin Duk Hotunan ta ne Da Batasan ma Duk Sanda aka dauketa bah...
Chapter 11 · 0% Book details