← Book details Tarayya Part One Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 51

Sashe 9

Tarayya Part One Complete Hausa Novel · about 8 min read

Babban parlour ne daya tsaru sosai da uwayen nairorin da aka zuba masa gurin tsarasa,
Royal cushions ne purple and golden komai na palon qyallin adon kalar golden din.

Duk haduwa da tsaruwar part din sultana saidataga wannan ma na suhailat yayi kyau sbd ita atunaninta baza'ataba samun part dinda yakai na sultana tsaruwa da kyauba saigashi na suhailat dinma ya tsaru kamarna sultana duk da tanajin labarin haduwa da tsaruwar part din adama kasancewarta itama 'yar adoce sosai.

Kuyanginda aka turowa suhailat 'din sukayi saurin shiga taitayinsu suna mata barka da shigowa.

Hannu kawai ta 'daga musu tareda kallon rumanah tana nuna mata 'dakinsu amah tace,
Kije kiyi musu wanka da ruwa marasa sanyi kuma bamasu zafi sosaiba ki shiryasu sai abarsu su huta kafin anjima suci abinci.

Tana gama fadar haka tamiqa mata hannu ta bata handbag dinta ta shige bedroom dinta.

Dakinsu ta nufa dasu tayi musu wanka ta shiryasu harzata fito suka maqale mata takaisu gurin mum dinsu.

Bata saba da yaraba batama ta6a zama da yaraba tun tasowarta
Daqyar tasamu ta lallabasu ta fito.

Tana fitowa part din tasaki ajiyar zuciya sbd gabadaya a takure take sbd tsoro da gudun aikata laifi.

Kodata koma part din sultana a palon farko ta ra6e sbd ganin alamun har lokacin yarima naciki.

Gab da magrib yafito tayi saurin zubewa amma ko lurada akwai mutum shibaiyiba ya wuce yabar part din da qamshinsa.

Sum sum ta nufi palon ciki ta tararda ammyn zaune har lokacin ta durqusa cikin girmamawa tace,
Ammy a table za'a jera abinci kokuwa anan?

Murmushi tayi cikeda farin ciki tace,
Ajera a table kuma ayiwa maheer honey pancakes da sugarless drink sbd bayacin abinci mai nauyi musamman yanxu da daddare
And kihada masa fruitsalad with less apple sai kikai masa part dinsa kisaka a fridge din Palo nasan idan yafito sallar magrib bazai komaba sai dare.

Wani irin yawu ta hadiye na muguwar faduwar data sameta jin inda aka aiketa itadai batason tayi laifi komai qanqantarsa.

Ficewa tayi tafara kawo abinci a second palo tana jerawa a dining jikinta amatuqar sanyaye.

Honey Pancakes din tayi tareda kawowa dining daidai lokacin aka shiga sallar isha takoma tahado fruit salad ta zuba a glassbowl ta 'daura a tray ta nufi part 'dinsa qafafuwanta har wani hardewa sukeyi sbd yanda jikinta ke rawa.

Tana isa kallo 'daya tayiwa guards din qofar ta juya tayi part din suhailat ta saka cikin fridge tareda sanarda kuyangin palon su sanarda suhailat ankawo fruit salad din yarima.

Kodata koma sallah taje tayo tareda komawa part din sultana tana saka kai da sallama dashi idanuwanta suka faracin karo yana cin pancakes din yana yiwa mahaifiyarsa murmushi.

Juyawa tayi da sauri sultana ta lurada ita amma sanin bayi basa zuwa idan yana guri musamman idan abinci yakeci kozaici yasa tabarta takomawarta.

Sai qarfe tara yabar part din sultana yanufi nasa
Yana zuwa ya tu6e yashiga bathroom dinsa da aka cika masa bathtub da ruwa masu matuqar qamshi da 'dumi ya lumshe fararen oily eyes dinsa tareda kwantawa yana sake jin nutsuwa.

Allah yayisa mutum mai tsananin son rayuwa musamman tajin dadi saidai suhailat bata cika son irin wannan rayuwarba itakuma sbd sunada abubuwan dasuka banbanta ra'ayoyinsu saidai suna qoqarin ganin hakan baitaba rayuwar aurensuba.

Sam bayason wanka a shower saidai a bathtub sbd yafison koyaushe yakwanta cikin ruwa tsawon mintuna goma sha biyar zuwa ashirin kafin yayi wanka,
Itakuma suhailat Sam batason wanka a bathtub saidai shower shiyasa haryau baisamu irin rayuwarda yakesoba sbd basu ta6a wanka atareba
Kwata kwata batama shiga toilet din bedroom 'dinsa sbd 'duk girma da fadin toilet dinsa bayason ganin ruwa ko yayane a qasan toilet dinsa itakuma idan tashiga toilet saita gama jiqa koina take fitowa.

A bangaren rayuwar aurensu kuwa Sam bata iya kwana a 'dakinsa sbd komai dare idan suka gama abinda sukeyi a bedroom dinta take kwana sbd daga ita harshi kowa yafison ya kwana shikadai akan gado shiyasa yawanci zata raba dare a bedroom dinsa susha love dinsu kafin tayo dakinta.

Bayan sun jima da aure yazo yasaba baya iya kwana sai ajikinta amma itakuma dukkanin cikin datakeyi bayason kwanciya dashi hakadai yama cirewa ransa kota haihu basa kwana tare saidai su raba dare tare.

Bude idanuwansa yayi ahankali tareda kallon ruwan sbd qamshin dasuke fitarwa yakalli gaban mirror din cikin toilet din yagansu kaloli kusan guda goma masu kalar qamshi dabam dabam.

Saidayayi mintuna kwance cikin ruwan kafin yayi wanka ya fito daureda brown towel sabo qal ya tsaya gaban mirror tareda goge jikinsa ya fesa Hugo black men's spray tareda gyara sumarsa da lafiyayyar qasumbar dake kwance a farar fatarsa fuskarsa ya fesa mouth spray mint flavour ya nufi closet ya dauko kayan bacci white colour yasaka tareda nufar makeken lafiyayyan royal bed dinsa dayake gyare da komai white da kusan eight pillows masu laushi.

Wayoyinsa ya kashe tareda ajesu a bedside drawer ya kashe wuta yabar bedside lamps masu duhun haske.

Kwashe komai tayi tasake gyare palon tayiwa ammy Saida safe ta nufi gefensu na bayi anatse.

Tana zuwa babu kowa a dakin ta kwanta bayan tacire uniform dinta tasaka tsohon uniform dinta sbd sune tamayar na bacci dama idan akaga uniform dinka sun mutu ana baka wani.

Kodasu mamani suka shigo idonta biyu amma ta lafe tanaji mamani nata fada tana zaginta
Ta share hawayenta tareda rufe ido tana danne kukanta.

Tundaga ranar kusan itace take wahala da suhailat da 'yaranta sbd kullum ita sultana ke aikawa tana yiwa yaran wanka takuma kaimusu abinci ta Jere a dining safe rana dare saiya zamto ayyuka sunmata yawa danma babu laifi suhailat na sakar mata fuska sosai hakama yaran ba laifi suna yarda da ita ba kamar kowaba sbd kullum ita ake sawa ta daukosu takawo gurin sultana su yini kokuma gurin sarauniya adama.

Sati 'daya da zuwansu yarima yana zaune gaban sultan sbd kiransa dayayi cikeda girmamawa yake sauraren mahaifin nasa.

Cikin iko da umarni sultan yace,
Aure zaka qara maheer ibn abdulshams.

Shiru yarima yayi cikin tsananin mamaki tsawon lokaci harsaida mataimakin sultan yasake maimaita masa kafin ya 'dago manyan oily eyes dinsa yakalli haris abdallah mahaifin khaleefa kuma mataimakin sultan yace,
Ina bawa sultan da mataimakinsa hkr sbd babu sha'awa ko burin qara aure arayuwata.

Wani shu'umin murmushi sultan yasaki tareda sake maimaita zancensa.

Shima maheer cikin girmamawa yasake maimaita amsarsa.

Kallonsa sultan yayi yasan sarai waye maheer saidai bazai barsaba zaiyi amfani da qarfin ikon mulkinsa dakuma ikonsa na mahaifinsa akansa.

Batareda yakallesaba yace,
Maheer ibn abdulshams zabin farkone nabaka na qarin aurenka.

Rufe idanuwansa yayi ahankali yana danne 6acin ransa yace,
Ina qara bawa sultan hakuri akan wannan buqatar tasa sbd idan nayi auren bansan yaya zan iya kwatanta adalcin kulada mata biyu ba.

Murmushi sultan yasake saki tareda kallon sarkin gida dake tsaye da sauri yafice ya nufi hanyar part din sultana.

Mintuna qalilan akayiwa Jakadiya iso tashigo tareda zubewa qasa tana gaisuwa.

Cikin mulki da nuna ikonsa yace,
Jakadiya aje yau awanke masa baiwar datafi kowace kyau 'daya cikin biyar 'din danace agyara akai masa daga yau aringa kaita kowane dare harsaitayi ciki,
Kuma daga yau an dakatarda matarsa zuwa gurinsa sai baiwarsa tayi ciki
Idan ya kaucewa umarnina Jakadiya ki sanarda sultana zaarah na sauketa daga matsayinta na sultana kiyiwa adama albishir da samun sabon matsayi.

Yana fada ya miqe nan dukkanin su haris abdallah suka miqe yashigewarsa palonsa na musamman.

Cikeda girmamawa Jakadiya tace,
Angama sarki mai adalci.

Miqewa tayi da sauri ta fice sbd ganin halinda yarima yashiga sbd tsananin 6acin ransa da baqin cikinsa daya kasa 6oyuwa.

Miqewa yayi yafice kai tsaye part dinsa ya nufa tareda bawa guards din qofar part dinsa gargadin duk Wanda yayi motsi mai qarfinda harzai shigo part dinsa yadamesa arufesa tsawon shekara guda.

Jin haka yasa akayi sanarwa tuni kowa ya nutsu yashiga taitayinsa.

Jakadiya kuwa cikin qanqanin lokaci tasa aka tara dukkanin wata baiwa dake masarautar mai shakatun dabasu wuce sha takwas,sha tara zuwa ashirin da uku da hudu.

Koda aka kira duk suka halarta banda rumanah dake bedroom din sultana tana jera kaya acikin closet.

Duk iya damuwa da rashin mafita sultana naciki sbd tun binciken farko Jakadiya tace bataga wadda ta daceba gashi sultan yace yau.

Zaune kawai take amma hankalinta nakan halinda maheer yake ciki yanxu.
#mamuhgee
[7/29, 9:29 PM] Hauwa'u inna: *_TARAYYA_*
_wattpad@mamuhgee_
_Haske writers association_
*13*
*_JAN HANKALI_*
*_'Yan uwa masu zantuka akan wannan littafi masu dadi da marasa dadi tareda cin fuska duk inason Ku luradafa_* *_akowane lokaci mai rubutu idan zai isarda wani saqo na halin rayuwa tofa dolene saiya fara kawo 6atancinsa da 6arnarsa kafin yazo ga darasin ciki tareda gyaransa Dan haka please muriqa bari muna ganin inda aka dosa kafin muriqa fadar ra'ayoyinmu._*
*Not edited*
Komai bakinta baida kuzarin furtawa koda yanadashi 'din baida ikon furtawa sbd hakan na nufin ruwan sama zai wanke jininta bayan anraba jijiyoyin dasuka riqe kanta da wuyanta
Saidai bazata iya hana zuciyarta qunci da radadin zuciya ba sbd sai ayaune ta sake tabbatarda ita baiwace Mara 'yanci gaba da baya.

Kai tsaye part din gyara taga sun nufa nan shakkunta da wasi wasinta ya tabbata kenan itace zata zama.....

Kasa qarasawa tayi ta rufe idanuwanta da qarfi hawaye na 6alle mata.

Daganan kasa daga kafafunta tayi haka suka jata kamar makauniya suka shiga da ita.

Zaunarda ita sukayi tareda fara zame mata kayan jikinta har lokacin bata iya 'daga koda Dan yatsanta bare ta iya 'dago fuskarta.

Shigowa Jakadiya tayi kallo daya tayi mata tagano tsananin dukan da firgici yayiwa zuciyarta tayi saurin dauke kai cikin bada umarni tace,
Ku shiryata shirinda har abada yarima zai riqa tuna qamshi da kyawunta kuma Ku kwantarda hankali kuyishi anatse.

'Dagowa tayi ahankali takalli jakadiya daidai lokacin hawayenta suka samu tsinkewa.

Cikin zafi da daure fuska jakadiya tace,
Karkiyi mana kuka sbd ke baiwace da akeda ikon kwana dake aduk lokacinda akaso kuma akeda ikon yin yanda akeso dake Dan haka ki saurara da kyau
Idan kikayi mana garaje anan wlh abincin kaji za'ayi da jininki.
Chapter 9 · 0% Book details