← Book details Tarayya Part One Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 51

Sashe 47

Tarayya Part One Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zare hannunta tayi cikin nasa tareda lumshe ido sbd yanayin datakeji ajikinta har lokacin.

Cikin nutsuwa ammyn tashigo idonta kan rumanah din
Hankalinta ya'dan kwanta ganin ta farka harta tashi zaune.

Qarasowa tayi tareda miqawa maheer hannu ya kama hannun da hannunsa daya cikin nutsuwa yace,
Ina kwana ya ammy?

Murmushi tayi tace,
Lfy klau..tana kamo hannun rumanah tace,
Ya jikin?

Naji sauqi ammy"""ta fada cikin qarfin hali da danne ciwon datakeji.

Miqewa yayi ya fita yana amsa kiran khaleefa dake kiransa kan maganar test result 'dinta dasuka fito.

Ammy dakanta ta kamata takaita toilet tayo wanka da brush tana fitowa taga doguwar riga mara nauyi akan dressing chair ta dauka tasaka ta shirya tana qoqarin busar da kanta sbd wankan tsarkin datayi na haihuwa ammy tashigo tareda nuratu dake daukeda babban tray Jere da breakfast ta ajiye zata juya rumanah takira sunanta ahankali.

Tsayawa tayi tareda juyowa cikin ladabi
Rumanah ta miqa mata hand dryer cikin sanyin murya tace,
Taimakamin.

Ammy na ganin hakan tasan magana zasuyi ta kalli nuratu tace,
Tayi breakfast.

Jinjina kai tayi alamar tou.

Ahankali take busar mata da gashin babu Wanda yayi magana acikinsu.

Tana gamawa ta daure mata gashin tareda ajiyewa a natse.

Miqewa tayi itama ta nufi inda take sallah tana idarwa ta dawo kan couch din dakin ta zauna har lokacin nuratu na tsaye kanta a sunkuye cikin tarin damuwa da kadaici.

Ahankali takamo hannunta ta zaunar da ita kusada ita ta kalli fuskarta kafin ta sauke kanta itama ta qurawa gabanta ido cikin sanyin murya tace,
Kiyi hakuri nabarki alokacinda kike tsananin buqatata,
Kin kuladani kin tayani kuka kin rarrasheni alokacinda na rasa nawa iyayen saidai ni nakasa miki hakan alokacinda kike buqatar wani ataredake..

Kallonta nuratu tayi hawayen datake riqewa suka gangaro mata tace,
Wlh idan nace miki bana buqatarki ataredani na miki qarya rumanah saidai yanayin rayuwa daya kawo bambamci arayuwarmu ayanxu rayuwarki daban take data baiwar datafi kowace baiwa baqin jini sbd mahaifiyarta data.....

Rintse ido tayi tareda budewa idanuwanta na cikowa da hawaye ta juyo ta kalleta cikin sanyin murya tace,
Ada damuke bayi rayuwarmu tafi kwanciyar hankali da nutsuwa tareda dadin gudanar da rayuwarmu,
Rayuwar bayi wata rayuwace mara yanci amma wlh wani lokacin tafi rayuwa irin wadda nasamu kaina aciki,
Nuratu idan zaka roqi Allah abu ka roqi alkhairinsa sbd wlh rayuwata ina baiwa tafimin kwanciyar hankali akan yanxu.

Gangaro mata hawaye sukayi sbd jin tausayin kanta da abinda zata fada tace,
Nuratu na 'yantaki daga yanxu ke ba baiwa bace kinsamu 'yancinki,
Babu wata rayuwar jin dadi da kwanciyar anan dan haka za'a maidaki gida acan zaki samu rayuwar kwanciyar hankali damukai burin samu idan ni bansamuba zan qoqarta gurin ganin ke kinsamu...

Kallonta nuratu takeyi hawayenta na tsananta gudu tace,
Tare mukayi alqawarin komawa gida.....

Zanzo wata rana nima idan nauyin alummar dake kaina ya sauka
Zanzo idan inada rayuwa da lafiya sbd burinane nima nahadu da dangin iyayena dan haka karkiyi wasa da damarki kice zaki jirani kije Allah zai sake sadamu da yardarsa.

Kuka nuratu ta fashe dashi tana girgiza kai tace,
Bansan ta yaya zan fuskanci mutanen da basusanniba nikadai nace musu dukkanin iyayenmu da sauran danginsu da akaje dasu sun mutu ba...

Itama kukan takeyi sosai saidai bazata iya cewa komaiba sbd wannan shine gatan datasan zata yiwa nuratu takoma gida ta fuskanci sabuwar rayuwa cikin amincin Allah.

Kuka sukeyi sosai na rabuwa da juna daqyar rumanah ta miqe ta bude wardrobe ta dauko wata jaka dake daukeda qatuwar sarqar zinari ta miqawa nuratu tareda juya mata baya sbd kukan datake riqewa tace,
Allah ya hada fuskokinmu da alkhairi.

Ta baya nuratu ta rungumeta tana sakin sabon kuka tana cewa,
Kisani zan jira zuwanki har qarshen numfashina.

Daqyar suka saki juna suka fito palonta na biyu inda suka tararda ammy da maheer da khaleefa tareda Jakadiya suna jiran fitowarsu.

Fuskokinsu suka bayyanarda halinda suke ciki.

Ya qurawa fuskarta datai jajir ido kafin ya dauke kai yanajin damuwar ganinta hakan cikin zuciyarsa.

Gefen ammy ta qarasa ta tsaya ahankali ta bude baki tafada musu tafiyar Nuratu din zuwa qasarsu.

Ammy sosai ta yiwa nuratu addua da fatan alkhairi tareda cewa jakadiya nuratun ta sameta kafin washe gari ta wuce.

Bayan fitarta khaleefa yabi bayanta da kallo kafin maheer yayi masa magana da ido suka fita.

Bayan fitarsu ammy ta zaunar da ita tasa aka kawo wani abincin breakfast din.

A palon yarima maheer suka zauna cikin nutsuwa yace,
Khaleefa zaka karbi duk wani bayanin tarihin my queen da mahaifiyar nuratu ta bayar ka kaita har gida kafin ka karbi takardun iyayenta kayi amfani dasu ka nemomin asalinta.

Shiru khaleefa yayi yana sake tauna zancen sbd tafiyar ta jirgin ruwa ce sbd ta ruwa kawai zasubi su bulla garinsu nuratun kai tsaye a yanda akace gashi bai cika son tafiyar ruwa ba saidai kuma dole haka zai daure saidai suyi amfani jirgin dazasu isa cikin kwana biyu.

Acikin daren rumanah tayi kukan tafiyar Nuratu,
Iyayensu sunzo qasar dasu acikinsu gashi su zasu koma batareda ko dayansuba.

Washe gari bayan sallar asuba suka wuce bayan khaleefa yakarbi duk wani tarihi na asalinsu daga hannun anees mai haqqin tattara tarihin sarakunan masarauta Wanda aka ya karbi bayanan daga mamani ya rubuce a littafin tarihi kafin rasuwarta.

Bayan tafiyarsu takira Jakadiya ta miqa mata wani zungureren saqo a rubuce tace takaiwa harooun sarkin fada.

Lokacinda Jakadiya takaiwa harooun saqon yana gama karantawa jikinsa yayi matuqar sanyi da abinda ke rubucen saidai kuma yasan hakan datake shirin yi shine qarshen abinda yake bibiyar mineelik dan haka babu bata lokaci ya fita dakansa yaje gurin Negus sarkin qirar mineelik yayi masa bayani ya karbo littafin zanen karagar mulkin qarnikan baya yadawo yabawa jekadiya takai mata.

Lokacinda Jakadiya takawo mata shirgegen littafin mai nauyi ko budesa batayiba tace,
Kije na zabi lamba ta biyar.

Babu musu Jakadiya takoma ta mayar tana jinjina alamarin rumanah sbd idan Allah ya taimaka abinda take shirin yi shine daidai.

Acikin daren ranar Negus da yaransa suka fara aiwatarda aikin qera sabuwar karagar mulkin mineelik wadda basu ta6a qera abu mai kyau da darajartaba sbd abubuwan dasuka narka ana hadawa dasu gurin qirar.

Lokacinda Jakadiya ta sanarda ammy abinda yake shirin faruwa numfashi ammy tasauke cikin danne fargabarta dan batason tunanin faruwar wani abin saidai zataje tayi magana da sultan sbd shine yasan komai ciki da waje gameda komai na karagar fiyedasu.

Da daddare bayan ko ina yayi tsit sultana ta fito ta nufi sashen sultan kai tsaye aka barta tashiga sanin matsayinta gurin assultana.

Zaune yake hankali kwance yana karatun wani shirgegen littafin tarihi yana shan madara mai zafi da aka kawo masa kullum kafin ya kwanta sbd tana qara lafiyar qwaqwalwa.

Kallo daya yayi mata yasaki murmushi yana cigaba da abinda yakeyi.

Qarasowa tayi kusadashi ta zauna cikin girmamawa ta gaidasa tana kallon littafin dayake karatu tace,
Meyasa haryanxu bazaka sauke dukkanin wani tunani na sharrin shaidanba ka fuskanci gaskia ka bita,
Ka tubarwa ubangijinka ka ajiye duk wata niyya da qudirinda bana alkhairi ba wlh Allah zai karbi tubanka sbd shi mai yafiyane ga bayin dasuka tubarmasa.

Wani irin murmushi yasaki tareda rufe littafin ya ajiye gefe ya kalleta yace,
Baiwarki kuma matar 'danki tayi babban kuskure na aikata abinda ta aikata sbd kaf tarihin mineelik babu wani sultan da aka taba muzantawa saini sultan abdulshams jinin ajani....

Numfashi tasauke cikin takaici da baqin cikin halinda mijinta yasamu kansa idanuwanta na cikowa da hawaye tace,
Son zuciyar kakannin kakanninka shine yasamu ahalinda muka tsintsi kanmu aciki karka bari zuciya takaika aikata irin kuskurensu.....

Katseta yayi da cewa,
Meya kawoki ki fada kai tsaye sbd nasan akwai abinda yakawoki a wannan lokacin.

Kallonsa tayi ganin Sam idanuwansa da zuciyarsa sun rufe..

Cikin sanyin murya tace,
Assultana na shirin canza mineelik gabaki 'daya da wata......

Da sauri ya kalleta yana ajiye cup din hannunsa sbd girgiza da zuciyarsa tayi.

Cikin bayyanarda tsananin tashin hankalinsa yace,
Zata aikata wani babban kuskuren sbd rusa karagar gabaki 'daya na nufin rusa rayuwarta sbd zata rushene tareda jininsu jamal na qarshe daya hau karagar yayi mulki akanta......

Shiru yayi zufa na karyo masa sbd yasan dagashi sai itane suka rage aduniya wainda suka taba zauna karagar har sukai mulki akanta,
A bangaren jini kuwa shikadaine jininsu na qarshe dayayi mulki akan mineelik ita 'din ba jininsu bace akwai yiyuwar abin bazai shafetaba koya shafeta saidai ta nakasta amma shi babu tantama rayuwarsace ke rawa jinin qarshe nasu jamal.

Wannan rumanah gabaki 'daya rayuwarta ta zame masa masifa mai barazana bai taba tunanin ko namiji zai iya fuskantarsaba ya girgizasa bare 'yaya mata daya dauka marasa amfani saigashi ko acikin 'yaya matan ma baiwace take barazaga rayuwarsa,
Bazai Bari su aikata hakanba dole ya juya musu zancen..

Gyara nutsuwarsa yayi cikin vasarwa yace,
Karku bari ta aikata hakan sbd rayuwartace acikin hadari dan kuwa haqqine na qarshe zai fita akanta.....

Murmushin baqin ciki ammy tasaki tareda girgiza kai hawayenta suka sauko tace,
Yanayinka da kulawar daka nuna yasamin kokwanto akan amsarka dan haka mun dangana munbarwa Allah komai zamu barta takawo qarshen mineelik duk abinda Allah ya qaddaro zamu runguma mu dauki dangana.

Miqewa tsaye tayi zata fice ya riqo hannunta akaro na farko dayaji tsoro da fargaba sun ziyarci zuciyarsa ya bude baki daqyar yace,
Karki bari ta aikata sbd rayuwatace a hadari kuma tatama na cikin hadari.

Hawayenta suka qara gudu ta sunkuyar dakai tanajin zuciyarta na karyewa sbd qaunar mijinta uban yayanta saidai kuma kodan sbd 'yayanta da jikokinta zataso akawo qarshen masifar mineelik.

Zame hannunta tayi ahankali tace,
Allah yazaba mana abinda yafi zama alkhairi.

Ficewa tayi jiki asanyaye zuciyarta na sake karyewa saidai bazata bari ta karayaba hakan da rumanah zatayi shine daidai insha Allah.

Zaune yake bakin gadonsa yayi shiru tareda zurfi cikin tunani Sam bayajin nutsuwa a zuciyarsa wani irin rashin sukuni yakeji..

Ahankali tashigo dakin rungume da abeel jikinta amatuqar sanyaye sbd jikinta datake yana tsananta dan ko yanxu kafin tafito saidata yanke jiki ta fadi jini na fita hancinta saidai bata fita hayyacinta ba kuma ta hani Jakadiya fadawa kowa abin yafara tsanani.

Qarasowa tayi ahankali ta kwantarda abeel kan sofa tadawo gefensa ta zauna ahankali tareda dafa hannunsa takalli fuskarsa.
Chapter 47 · 0% Book details