← Book details Tarayya Part One Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 51

Sashe 10

Tarayya Part One Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kalaman Jakadiya sundaki zuciyarta matuqa ta rufe idano ahankali ta budesu jajir sbd quncin zuciya amma tabbas babu yanda zatayi ita baiwace kuma yar bayi kamar yanda Jakadiya ta fada
Hannu tasa tashare hawayenta bata qara motsiba suka fara aikinsu ganin ta zame rigarta tashiga cikin ruwan madara da lalle dake cikeda bathtub suna zuba qamshi.

Jakadiya Juyawa tayi tafice takoma part dinda aka warewa baiwarda duk aka zaba akusadana suhailat yake Saidai baiyi girman nataba.

Duk wani abin jin dadi da hutawa da more rayuwa ansaka sbd so ake jikinta yariqa murmurewa fatarta tasamu isashen Hutu da kulawa ta yanda yarima zaiji dadin mu'amala da ita.

A cikin bedroom dinda ke part din wardrobe din dakin cike take tab da wasu irin kayan barci marasa kyawun gani basa qirguwa,
Hakama braziers masu daukar hankali dakuma panties,
6angaren turaruka kuwa duk wani turare mai tsada da qamshi ansiya har gaban mirror bai daukesuba aka zuba wasu a wardrobe.

Suhailat Jakadiya ta tambaya duk wani Abu da yarima yafiso ta 6angaren tayar masa da sha'awa zuwaga auratayya bisaga umarnin sultan,
Cikeda damuwa ta zayyanowa Jakadiya shinefa aka nemi turaruka masu matuqar tsada da kayan barci.

Saidata tabbatarda gyaran komai yakammala takoma gurinda ake shirin rumanah din ta tarar sungama shiryata cikin wata irin doguwar riga maroon colour dataji wasu irin tsadaddun adon sequence stones sai rawa take tana qyalli.

Mayarda kallonta tayi zuwaga fuskarta cikin tsananin mamaki da fargabar zallar kyawunda sultanace kawai take gani da kwatankwacinsa zuciyarta tayi mugun bugawa cikin zuciyarta tace,
Ya Allah kabar wannan fuskar mai tsananin kyawu da kwarjini ta dauwama ahaka karka wanke kyawun fuskarnan da jinin bayinka.

Cikeda umarni tace,
Ku rufeta mutafi daga yau rana bazata qara ta6a fatartaba harsai yarima yagama da ita idan ya gundura da ita,
Hakama daga yau idan tafara kwana barayar yarima duk bawa namiji yabari tsautsayi yasashi kallonta anyiwa zakunan fita yaqi alqawarin namansa.

Sam bata jinsu sbd damuwa da qunci dayayiwa zuciyarta yawa
Haka aka rufeta aka kamo hannunta suka jata.

Part din da'aka ware mata aka kaita har cikin bedroom Jakadiya ta kaita ta janye lullubinta tareda kallonta fuskar tamke da kakkausar murya tace,
Daga yanxu kinshigo kenan bazaki sake fitaba sai ranarda kika haihu,
Daga yanxu dokace mai tsanani babu Wanda yakeda ikon ganinki sai yarima kawai,
Akwai komai na buqata kullum dare zanxo narakaki barayar yarima harsai ranarda kika samu ciki saiki fara shiri daga yanxu
Zanje bayan sallar ishai zandawo nakaiki yarima baya jira Saidai ajirasa.

Ficewa tayi tabi bayanta da kallo idanuwanta na qoqarin cikowa,
Kukan datake dannewane tuntuni ya kufce mata ta zame qasa tafara wani irin kuka tana shidewa,
Kuka takeyi sosai tana qanqame jikinta cikeda tsoro,fargaba da baqin cikin rayuwardata tsinci kanta dakuma wadda zata fara daga yau bayan anfara kwanciya da ita duk lokacinda akeso.

Sbd kuka muryarta shaqewa tayi tashare hawayenta tareda mi
qewa ta nufi toilet din bedroom din tayo alwala daqyar take gani sbd kumburin idanuwanta da fuskart.
4 hours later.

Kasa kallon kanta tayi ta rintse ido jiki amatuqar sanyaye sbd kayanda ke jikinta,
Riqar baccice kalar black Wanda babu wani sashe na jikinta da rigar ta suturta,
Bra da pant dinda aka sata sakawa duka suma black ne aka daure dogon gashinta dashima aka gyara hatta turaren hayaqi mai wani irin qamshi anyiwa gashinta bare jikinta aka daure tsakiyar kai tareda 'dora mata wata doguwar tiga mai hula data rufe koina ajikinta aka rufe fuskarta da hular tareda bata wasu takalmi masu laushi ta zufa anatse Jakadiya tace,
Mutafi,Allah yadatar dake da samun ciki acikin daren yau.

Jakadiya ce agaba sai ita abaya bayi kusan guda biyar sun zagayeta suna kama rigarta dake Jan qasa.

Duk takunta 'daya kamar zuciyarta zata fadone ta buga sbd bugawa da tsananin tsoro da baqin cikin datake ciki,
Akaro na farko arayuwarta zata kwana da namiji ba mijintaba kuma duniya da kowa zasusan ana kwana da ita harta haihu,
Tabbas da ubangiji bai halastawa uwayen gijiyoyi bayinsuba da ayau tafison a raba kanta da wuyanta abawa dabbobi jininta data cika wannan umarnin amma sa6a musu da bijire musu tamkar ta bijirewa ma'aikintane sbd shine ya halasta hakan.

Wani irin tsaro ne na musamman a part din yarima ga wasu irin hasken fitilu masu kyau da burgewa haka duk fadin masarautar idan kacire uban gayya sultan part dinsane ne kawai mai palo hudu kafin akai master bedroom dinsa.

Cak suka tsaya bakin qofar shiga
Jakadiya tajuyo ahankali tayiwa bayinda ke bayansu kallo daya
Suka ja baya suka tsaya tareda sunkuyar dakai kafin tajuyo takalli guards din bakin qofar cikin girmamawa suka wangale qofar ta saka qafa tashiga.

Wani irin numfashi rumanah tasake sbd kukama yanxu yagaji yagudu yabarta zuciyarta da idanuwanta sun bushe sauke numfashi kawai take yi akai akai sai jikinta dayake wata irin rawa ko Abu bazai iya tsayawa ahannuntaba.

Numfashi tasauke ahankali tareda 'daga qafarta tashiga ahankali tareda rufe ido tabude sbd rayuwarta ta canxane daga yanxu data sako qafar palon yarima maheer ibn abdulshams abdallah.

Har lokacin fuskarta rufe takeda hular rigar dake jikinta ahankali take takawa faduwar gabanta da rawar jikinta na tsananta harsuka isa palon qarshe Wanda dagashi sai bedroom dinsa.

Abakin qofa Jakadiya ta tsaya tareda juyowa tayi mata kallon mintuna uku kafin tazagaya bayanta ahankali tasaka hannu ta zame doguwar rigar mai hula
Tasaka hannu ta zare ribbon dinda aka 'daure gashinta
Gashin ya zubo kan kafadunta ta juya mata baya cikin sanyin murya tace,
Kishiga ki kwanta a gadon dake dakin kijira isowarsa.

Shiru tayi tareda Jan numfashi ahankali tasauke sbd barazanar barin qirjinta dayakeyi.,
Daqyar ta iya daga qafafunta dake rawa
Rawa hannunta keyi sosai takasa bude qofar bedroom din
Ganin haka Jakadiya ta matso tareda dafata cikin kulawa tace,
Karkiyi gardama da qaddara ki nutsu kibi umarni kiyi biyayya Allah ne kawai yasan dalilin komai dake faruwa.

Bude mata qofar tayi tareda juyawa sbd batada dama da iko tareda hurumin ganin makwancin yarima.

Akaro na farko da wani yayi mata magana da sigar lallashi tun bayan data zamto za6abbiya.

Ajiyar zuciya tasauke tareda saka qafarta cikin dakin Jakadiya ta jawo qofar ta rufe ahankali kafin ta juya ta fice da doguwar rigar ahannunta.

Komai na 'dakin white and golden ne,
Sanyin AC da qamshin dakin da mai dakin tareda nata data shigo dashi suka taru suka sauyawa dakin yanayin qamshi mai dadi kasancewar turarukan arabian oud akayi mata amfani dasu sabanin nasa dasuke designers na turawa.

Daqyar qafafunta suka kaita bakin couch dake bedroom din ta sulale qasa ta jingina kanta jikin kejerar tareda rufe idanuwanta.

Qarfe goma da rabi yafito part din sultana ya nufi part dinsa guards biyu ba bayansa yana isa masu tsaron qofar sukai saurin budewa yashige.
#mamuhgee
[7/29, 9:29 PM] Hauwa'u inna: *_TARAYYA_*
_wattpad@mamuhgee_
_Haske writers association_
*12*
Akan nuratu jakadiya ta tsayarda idanuwanta tana nazarinta sbd zama da rumanah yasa itama takeda nutsuwa daidai gwargwado......

Tsaya to idan zama da rumanah yasa takeda nutsuwa ba kamar mahaifiyarba me zai hana su dauki Mai nutsuwar gabaki daya.

RUMANAH"""shine sunan dayazo ranta atake tasaki murmushi cikin farin ciki sbd tasan sultana idan taji ta inda jikokinta zasu fito bazataji damuwaba.

Sallamarsu tayi tareda juyawa kar tsaye ta nufi hanyar zuwa gurin sultan.

Tana zuwa akai mata iso cikeda girmamawa ta zube gabansa cikin bayyanarda farin cikinta tace,
Allah yataimakeka ansamu baiwa mafi nutsuwa da kyawu acikin bayin masarautar mineelik,
Baiwa ummu-rumanah 'yar tsohon aminyaccen bawanka bulama.

Shima wani irin murmushi yasaki tareda kallon Jakadiya yace,
Allah yayi saina hada zuria da bawa mafi soyuwa agareni
Aje ashiryata yau za'a fara rakata turakar yarima
Bulama Allah yaji qanka da rahamarsa,
Jakadiya kije idan ta haifi namiji ina miki albishir da akwatin dalolin amurka.

Miqewa tayi tana zuba godia da farin ciki tareda adduar asamu biyan buqata.

Lokacinda ta isa gurin sultana ta zube gabanta ta zauna cikin farin ciki tace,
Allah yataimakeki Ansamu wadda nasan zakifi kowa farin cikin fitowar jikokinki ta tsatsonta.

Kallon rashin fahimta sultana tayi mata cikin qoqarin Kore damuwarta sbd jin ansamu mafita.

Baiwa ummu-rumanah ta wajenki itace nakega tafi cancanta da'a za6a sbd ganin nutsuwa dakuma shakuwar dake tsakani.

Wani irin kallo sultana ta jefi Jakadiya dashi cikin mamaki da takaici.

Datasan rainon datakewa rumanah na idan tasamu sanin asalintane daga mamani ta 'yantata danta koma gida cikin yan uwanta ne.

Dauke kai tayi cikin bada umarni tace,
Kije kinema masa wata banda rumanah.

Kallonta Jakadiya tayi da sauri cikin mamaki tace,
Allah yataimaki sultana naga tafi kowace baiwa cancanta tazamo uwar jikinki koba komai tunda 'danki ne ba wani akace akaiwaba.

Girgiza kai tayi tareda juyawa takalli qofar bedroom dinta da rumanah ta fito cikin nutsuwa daukeda zanin gadon data cire ta fice tana mamakin kallonda suka biyota dashi kamar ta canza.

Laundry din masarauta ta nufa takai kayan ta karbo wasu sabbin zannuwan gado masu laushi farare qal tana fitowa mamani ta shigo part din laundry din daukeda kayan wankin adama itama takawo.

Saurin matsawa tayi tana cewa,
Mamani sannu da aiki.

Tsayawa mamanin tayi tareda kasa danne baqin cikinta da takaicinta akan rumanah din sbd ko yauma dai ba'a zabi nuratu ba sbd ko wanka batayiba.

Cikin takaici tace,
Rumanah tunda kika zuga nuratu Dan karmu samu farin ciki kema bazaki ta6a farin cikiba arayuwa,
Keda iyayenki kunzamarmin muguwar qaddara sun mutu sunbarmana masifa gashinan kin shiga tsakanina da yata kin shiga tsakaninmu da farin cikinmu....

Rintse idanuwanta dasukai jajir tayi Cikin dannewa tace,
Kiyi hkr mamani bawa baya wuce qaddararsa ko.......

Shaqota tayi cikin tsananin baqin ciki jitakeyi kamar ta cire takaicin iyayenta na shekara da shekaru akanta ta huta.

Hawayen wahala rumanah ke fitarwa sosai batareda tayi yunqurin kwatar kantaba.

Motsi yasa mamani sakinta ta kwashi kayanta ta wuce zuciyarta na tafarfasa.

Kukan datake riqewa tana shiga bedroom din sultana tasakesa zuciyarta na quna,
Sosai take kuka tana shesheka sbd yanxune take 'dandana maraici da quncin dake cikinsa,
Wannan karon harcikin ranta takejin qunci da radadin abinda mamani ke mata shiyasa takasa danne kukanta duk yanda taso.
Chapter 10 · 0% Book details