← Book details Tarayya Part One Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 51

Sashe 14

Tarayya Part One Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aje wayar tayi tareda kallon Jakadiya data shigo daukeda kaya batai maganaba tagyara zamanta tana jiran jin mai zata fada.

Kai tsaye jakadiya tace,
Saqon tausar zuciya ne daga sultana na aure da yarima maheer yaqara ayau Allah ya sanyaya zuciyarki.

Kasa motsi tayi sai ido data kafe Jakadiya dashi,
Wani irin radadi da ciwo ya ziyarci zuciyarta da mararta alokaci 'daya
Rintse idanuwanta tayi da sauri hawayen dasuka cikasu suka gangaro tayi saurin dafe mararta tareda fara qoqarin tashi sbd jin danshi nabin qafafunta.

Jakadiya ganin halinda tashiga da jinin dake gangarowa daga qafafunta yasa tayi saurin qarasawa gareta daidai lokacinda azaba da ciwon suka taso gadan gadan tasaki wani irin kukan azaba tana dafe cikinta sbd jin axabarda bata taba jiba gurin haihuwa.

Ganin abin yayi muni sosai yasa Jakadiya bada umarnin aje atahoda masu karbar haihuwa sbd tanasa ran qila haihuwarce.

A gaggauce aka kirawosu suka kamata aka shiga daki da ita nan Jakadiya taje ta sanarda sultana
Cikin qanqanin lokaci masarauta ta 'dauka labarin haihuwar da za'ayi saidai kuma masu karbar haihuwar sunkasa sbd jini take fiddawa har lokacin ruwan haihuwarta basu fasheba gashi tafara fita hayyacinta.

Cikin gaggawa jakadiya taje tasanarda sultan abinda masu karbar haihuwa sukace na za'a iya rasa ran suhailat da abinda yake cikinta.

Jin haka sultan dayace kar asanarda yarima sbd karyaqi tarewa da rumanah yau amma jin za'a iya rasa abinda za'a haifa yasa yace asanarda yarima yayi gaggawar bata taimako sbd bayason arasa abinda ke cikin sbd basusan ko meneneba.

Lokacinda ya isa yaga halinda take ciki ransa yayi mummunan 6aci sbd ganin irin jinin data zubar sbd baqin ciki kai tsaye ya fitarda wayarsa yakira khaleefa kai tsaye yace,
Khaleefa ina buqatar tickets na jirgin dazai tashi acikin daren yau.

Yana kashewa ya matso gefenta ya zauna tareda riqo hannunta ya share mata zufa da handkerchief dinsa cikeda kulawa sbd ganin nata yana qara muni.

Fita yayi ya nufi part dinsa ya shirya luggages dinsa ya canza kaya.

Cikin qanqanin lokaci aka shiryasu amah.

Koda khaleefa yasanarda sultan buqatar maheer
Kallonsa sultan yayi yace,
Ka karbo musu ticket shida
Shida mahaifiyarsa da matansa tareda 'yayansa.

Jin haka khaleefa yaje yayi yanda zaiyi ya karbo guda shida 'din koda ya dawo harsun gama shiri tuni jakadiya taje bisaga umarnin sultan ta hadawa ummu-rumanah kaya cikin wasu kyawawan akwatina marasa girma sosai guda uku tasakata ta canza kaya zuwa doguwar Riga baqa suka fito.

Sam baisan abinda yake faruwa aka dauki suhailat dake kwance kamar gawa aka saka mota suka nufi airport.

Sultana da rumanah taredasu amah kuma suka shiga mota 'daya suka Mara musu baya.

Suna isa Sam bai lurada rumanah ba aka dauki suhailat akai cikin jirgi da ita yabi bayansu sultana da yara tareda rumanah da jikinta ke sanyaye suka rufa masa baya.

Amatuqar sanyaye take sbd wannan shine karo na farko data taba fitowa daga cikin masarautar tun duk tsawon rayuwarta.

Ganin yanayin suhailat dakuma ummu-rumanah yasa sultana yanke shawarar qin zuwa Libya binsu zatayi sbd batasan wani irin riqo su maheer din zasuyiwa rumanah idan basa ganin idon kowa duk da tasan ba ruwan maheer da ganin idon kowa akan alamarinsa.

Suna shiga jirgi a darare ta zauna kusada sultana tana kama jikinta kanta a sunkuye har jikin ya daga sama ta rintse idanuwa tareda qanqame jikinta.
#mamuhgee
[7/29, 9:29 PM] Hauwa'u inna: *_TARAYYA_*
_wattpad@mamuhgee_
_Haske writers association
*16*
Not edited.

Wani irin kallo sultana ta 'dago tayi masa cikeda mamaki da takaicin abinda yake shirin yi kafin ta bude baki tayi magana cikeda nuna isarsa da matsayinsa yace,
Lij(sadaukin kuma amintaccen mayaqin meneelik) duk wanda ya nuna rashin gamsuwa da hukuncin sultan ko a fuskane ko wanene shi arabasa da abinda yafiso ajikinsa,
Idan nace ko wanene ina nufin kowanene,
Jakadiya kije ashirya sabuwar surukar sultan nanbada jimawaba zata zama uwar magajin meneelik.

Yana gama fada ya miqe yashige palonsa na hutawa tareda manyan masarauta dazasu tattauna wani abin,
Wasu majiya qarfin samudawa suka tsaya qofar Dan bata tsaro.

Kai tsaye ya miqe yabar palon batareda fuskarsa ta nuna meke cikin zuciyarsaba.

Sultana ma miqewa tayi jikinta amatuqar sanyaye zuciyarta cikeda takaici da tunanin rashin ganin amfanin 'yantawarda tayiwa rumanah tunda hakan baisa ta tsirar da ita daga masifar datake gudar mataba ta haihuwar namiji a wannan masarauta ta mineelik.

Jakadiya kuwa wani irin zufa take yarfewa Tana qoqarin ganin ancika umarnin sultan saidai itama damuwarta da tsoronta yahana farincikinta wanxuwa musamman idan taduba yanayin tsoro da fargabar dake yawan samunsu idan sukayi tunanin rabon dazai shiga tsananin yarima da rumanah.,
Wannan masarauta batada tarihi mai kyau,
Jinin mutanen da ake kashewa yananan yana bibiyar duk wani hakkinsa,
Masiface acikeda masarautar wadda babu Wanda yasanta saisu dasuka ginu acikinta
Har abada bazata ta6a yiwa rumanah fatar shiga cikin jerin wainda masifar zata cigaba da shigarsuba aqarshe tabasu qarshe mai matuqar tausayi da kokawa saidai tasan bawa baya wuce qaddararsa,
Duk dubararsu da qoqarin kubutarda ita idan Allah yace tana cikin masu wannan mummunan qaddarar saita shiga.

Zubewa sultana tayi kan daya daga cikin kujerun palonta na farko sbd bazata iya qarasawa na biyunba tareda 'dagawa kuyanginta hannu nan suka watse cikin girmamawa.

Dafe goshinta dake daukeda adon sarqar zinari tayi tareda rufe ido tarasa wane irin hali zuciyarta take ciki sbd takasa riqe tunani ''daya dazatayi cikin biyu auren maheer da rumanah kokuwa korarda sultan yamata gefe 'daya kuma tsoro ne fal yafi cika mata zuciya.

Ya Allah kadubi maraicin rumanah kazaba mata kyakkyawar rayuwa agaba.

Tana cikin wannan halin Jakadiya tashigo 'yan mata biyar na bayanta 'daukeda manyan trays suna qyalli kamar zinari suka jeru sanku sunkuye.

Kallo daya Jakadiya tayiwa sultana 'din tasan tana cikin tension murya asanyaye tace,
Allah taimaki sultana anshirya zuwa gurin shirya sabuwar amaryar yarima maheer sa albarki akazo karba.

'Dago fuskarta datai ja tayi takalli jakadiya batareda tace komaiba ta miqe tashiga bedroom dinta tafito da wani madaidaicin akwati yana kyalli.

Zama tayi tareda aje akwatin batareda takalli jakadiya ba murya ba kuzari tace,
Allah yasawa aure albarka.

Amin jakadiya tace tareda kai hannu tabude akwatin.

Sarqoqin zinari ne masu nauyi da marasa nauyi nakai dana qafafu taredana wuya da awarwaro har kusan basa qirguwa.

Hannu Jakadiya tasa tana zarosu tana zubawa acikin tray dinda suka shigo dasu harsaida tray din yacika suka fice,
Sashen adama suka isa tana zaune cikin royal kushins din dasuka qayata palonta cikeda girmamawa aka iso mata da saqon zuwansu Jakadiya tace sushigo.

'Yan matanda ke bayan Jakadiya 'daukeda manyan trays din takalla cikeda mamaki sbd alamu na sakawa aure albarka zaka bayar.,
Wane zaiyi aure kuma ayau batareda tasaniba?

Lallai ana wasa da ita amma karsu damu da zarar ta 'Dora mazaunanta akan kujerar mulkin mineelik tayi alqawarin bawa dabbobin dake zagaye da qasar naman wainda suke wasa da alamarinta.

Cikin girmamawa Jakadiya ta katseta da cewa,
Sultana zaarah ta 'yanta baiwarta ummu-rumanah ayau kuma ayau sultan zai aurawa yarima maheer ita akan sadaki tiren zinari,
Sultana ta bada nata tiren saka albarkar aure saurake gimbiya adama ina fatar ba'a shiga cikin lokacin hutawarkiba.

Cikin wani irin yanayi na mamaki ta kalli Jakadiya tace,
Aure tsakanin yarima da baiwa?

Kozansan dalilin wannan auren na gaggawa?

Allah yataimakeki maganar dai 'dayace.

Rintse ido tayi tareda Jan numfashi cikin takaici
Sam sultan bazai bari tashaqi numfashi mai dadi ba sbd wannan masifar tasa tason haihuwar magajin mineelik,
Meyasa koyaushe yake son 6ata mata aiki idan yayi nisa,
Tana qyalewane ta lafe sbd bokanta yace mata sa'arta ba yanxu takeba saizuwa gaba takwantarda hankali tajira sbd ba'a taba haihuwar namiji ba a masarautar yayi duba yaga tabbas mace ce zatayi mulkin mineelik bayan sultan takuma tabbatarda itace macenda zatayi mulki amma badan hakaba da tuni tasaka anbinne sultan da ransa takaiga cikar burinta.

Murmushi tasaki tana 'dauke gira 'daya tace,
Allah yayiwa aure albarka.

Sarkar jikinta data kanta taredata qafafunta tasa baiwarta nuratu ta cire ta daura akan tray din suka miqe suka fice.

Nuratu duk ilahirin jikinta rawa yakeyi gurin cire mata sbd tsananin farin cikin data shiga jin zancen,
Ta matsu tagama yiwa sarauniya adama yankan fruits taje tafadawa mamani sbd yau tun safe adama tasakata aikin abinci kusan kala biyar sbd 'yarta meenah zata zo hutun makaranta daga Sydney.

Part dinsa ya isa cikin wani irin yanayi da babu mai iya gano maike zuciyarsa ya zauna kan sofa tareda rintse idanuwansa yana shafo sumar kansa.,
Miqewa yasakeyi ya nufi bathroom yashiga cikin bathtub bai tsaya bata lokaciba yayi wanka yafito ya zauna gaban mirror yana goge jikinsa,
Shiri yayi cikin Ethiopian royal kaftans black and golden wainda yasaka ranar daurin aurensa da suhailat.,
Turare yafesa tareda saka takalmi ya fesa turare tareda gyara gashinsa mai 'Dan tsawo ya 'daure tsakiyar kai yasaka hula batareda yakalli kansa a madubi ba ya nufi qofa ya fita inda guards kusan guda goma da fadawan sultan suke jiransa Dan masa rakiya har gurin daurin auren.

Zaune take kan kujerar mirror ita kadai kamar koyaushe shiru tayi nisa cikin tunani tareda qurawa kanta ido.

Qura mata ido Jakadiya tayi kafin tayi gyaran murya tareda yiwa 'yan matan alama da ido cikin nutsuwa suka zo gaban rumanah data miqe cikeda ladabi tana gaida Jakadiya suka Jere matansu.

Sam bata shiga ko saka kanta ga duk abinda tasan bai shafetaba shiyasa ko inda aka ajiye kayan bata kallaba ta sunkuyar dakanta tana jiran umarni daga jakadiya sbd tasan dole akwai abinda yakawota.

Fuskarta Jakadiya take kallo tace,
Ayau sultana zaarah matar sultan abdulshams sarkin masarautar mineelik ta 'yantaki ummu-rumanah bulama sbd ki auri 'danta 'yarima maheer Wanda za'a daura miki aure dashi yanxu nanda mintuna qalilan.

Kallon Jakadiya tayi da kyau taga fuskarta babu wasa ko raini yasa tayi qasa da kanta sbd tasan babu abinda zaisa Jakadiya tafadi abinda bahakaba sbd dokace a masarautar duk Wanda yayi kuskuren qarya aka ganosa allurar dabazai qara maganaba ake masa shikenan yazama kurma shiyasa duk tsanani duk wuya ba'a qarya a mineelik.

Shiru kawai tayi sbd haryanxu batajin kanta amatsayi na an 'yantata tunda za'ayi auren manufa da ita,
Aurenda tasan dalilinsa Dan haka babu abin murna a 'yancinta.

Riqota sukayi zuwa toilet batai musuba jiki asake tabisu.
Chapter 14 · 0% Book details