← Book details Tarayya Part One Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 51

Sashe 4

Tarayya Part One Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ahaka rana takuma faduwa wani Daren yayi musu a tsakiyar jeji wannan karon kam ya tabbatarda wata duniyar suka fado sbd kalar yanayin dajin ya sauya sosai
Tun yana gani har duhu yasake yi dare Yakuma tsalawa sosai cak ya tsaya tareda yanke jiki ya fadi asma'u dake bayansa ta fado da qarfi kafin ya bude idanu daqyar
Dan taimakonta sai ganin yayi kamar tana gangarawa
Bude idanuwansa yayi awahalce da sauri saiyaga Ashe bakin cliff suke mai tsananin zurfi da ruwa masu tsananin yawa yana miqewa daqyar kafin yakamota idanuwansa suka rufe yasake yanke jiki yafadi tareda fadawa shima.
********
Ahankali ya bude idanuwansa dake gani dishi dishi harsuka bude daqyar suna kallon sama,
Lumshe idanuwan yasakeyi yabudesu yaga tabbas rufin sama bukkar karace yake ciki,
Qoqarin motsawa yakeyi Dan ya yunqura yatashi aka shigo bukkar yayi saurin dagowa.

Tashin namijine kamarsa dago fari tas sanyeda kayan saqi na fulani.

Qarasowa yayi da sauri tareda dafasa yana cewa,
Yi ahankali kana kariya aqafa.

Kallon qafar bulama yayi sai alokacin yaji azaba ya lura da 'dauri amma bai damuba cikin dasashiyar murya da fargabar amsarda za'abasa yace,
Ina matata?

Inane nan?

Ina takardun dake daure ajikina?

Kwana na nawa anan?

Cikeda mamaki da rashin isashiyar hausar fahimtar me bulaman ke fada yake kallonsa kafin ya gyara masa zaman qafar mai 'dori yace,
Kayi hkr sbd bansan mezan fada makaba amsa daya zan iya baka shine kwananka takwas anan sauran tambayar anjima idan mahaifina yadawo ya amsa maka.

Yana fadar haka ya fice
Saigashi yadawo da qwaryar magani da akushin wani irin abinci kamar tuwa kamar kunu ya zauna tareda miqawa bulama yace,
Gashi kaci saikasha magani.

Kallon abincin bulama yayi yaga shi kama ma abincin yayi masa da aman tuwon semo amma sbd yunwa da matsuwar jin inda matarsa take ya karba ya dauke numfashi ya shanye.

Ruwan magani ya miqa masa suma ya karba ba musu ya shanye.
#Mamuhgee
[7/29, 9:29 PM] Hauwa'u inna: *_TARAYYA_*
_wattpad@mamuhgee_
_Haske writers association_
Sashen sultana zaarah aka nufa da Asma'u dake waiwayen qofar sashen da aka baro bulama tanaji ajikinta shikenan sungama rayuwarsa atare saidai jiran lokaci kuma.

Lokacinda aka kaita gaban sultana aka gabatarda ita amatsayin kyauta daga yarima.

'Dagowa tayi cikin wani irin farin ciki da murmushi takalli asma'u cikin sanyin lafazi tace,
Allah yayiwa yarima albarka bisaga wannan kyauta.

Sake kallon asma'u tayi dake durqushe gabanta tasaki murmushin farin ciki murya a tausashe tacewa jakadiyarta.,
Akaita abata 'daki sashen bayi abarta tayi kwana biyu ana koyarda ita aiki kafin tadawo nan tafara aikinta.

Angama sultana.

Daki aka bawa asma'u kuma cikin sa'a aka basu daki daya da mamani suka zauna jigum jigum kowa babu da'din zuciya kafin aka sake zuwa aka tafi dasu bayin bayi kowannensu yayi wanka aka rarraba musu uniform dinsu sukabi layi aka basu abinci kowa da 'yar tasarsa
Anan ne asma'u suka hadu da bulama saidai iyakacinsu kallon juna sbd Layin maza dabam na mata dabam hakama ga dukkanin alamar tsaro da dokokinda suka lura dasu agurin babu bawanda ya isa ko yakeda ikon yiwa baiwa magana sbd tsaro dakuma gudun 6arna irinta zina.

Duk wanda aka bawa samun guri yake a babban filin ya zauna yafara cin abincinsa.

Daga ita harshi ba wanda ya iyacin abincin sai kallon juna suke daga nesa ba ikon magana har aka gama aka gargadasu aka rarrabasu zuwa sassan dazasu riqa aiki kullum.

Kwanansu biyu da zuwa jikinsu ya'dan murmure daga yunwa sbd issashe kuma lafiyayyan abincinda ake basu sbd Sam babu yunwa ga bayin masarautar.

Asma'u da bulama iyakacinsu da ganin junansu idan suka hadu gurin cin abinci.

Ganin basuda yunwa kuma babu azabtarwa a masarautar yasa hankalinsu yadan kwanta suka fara maida hankali ga ayyukansu damuwar bulama 'dayace cikin jikin asma'u da mamani.

Sosai asma'u ta dangana ta rungumi rayuwar dasuka tsinci kansu ayanxu tabi uwargijiyarta sbd ganin tana sake mata ba laifi.

Aiki da bauta takeyiwa sultana tuquru babu kyuya ga tsafta da tsananin ladabi.

Tunda sultana zaarah ta lurada cikin jikin asma'u tayi mamaki sosai ziciyarta tashiga wasu wasi takasa hkr ta tsare asma'un ta tambayeta cikin ladabi kanta na qasa tabata labarinsu kaf saidai ta boye mata asalinsu da dalilin barowarsu gida.

Cikin tsananin tausayawa sultana tace,
Karki damu asma'u Allah baya bacci kuma insha Allah za'a dauki mataki akan masu kamo bayin koba yanxu ba nasan zasu dawo.

Sosai sultana tasa jakadiya sassautawa asma'u ayukanta sbd yanayin cikinta daya tsufa kuma sosai sultana keyiwa asma'u kyautar fresh fruits masu yawa sbd anason mai ciki ta yawaita cinsu.

Kasancewarsu kusan sa'anni yasa sosai sultana tasa asma'u tasaki jiki da ita tun tana noqewa harta 'Dan sake idan tagama ayyukanta zata zauna gaban sultana suna 'Dan ta6a fira wani zubin harda jakadiya.

Cikinta na isa haihuwa cikin ikon Allah suka haihu rana 'daya da mamani dake aiki sassan sarauniya adama.

Dukkaninsu 'yaya mata suka Haifa sultana dakanta tasa akai mata iso ga sarki tasanar dashi matar mafi soyuwar bawansa ta haihu tasamu mace.

Shiru yayi cikin jinjina alamarin bayi kuma da haihuwa amma saiya share sbd bayason sanin komai yanxu tunda anriga anyi haihuwar yabawa bulama dama yaje yaga yarsa yayi mata huduba.

Koda bulama yaga 'yarsa hawaye 6alle masa sukayi sbd tarigada tafado daga bayi irinsu shikenan ita rayuwarda Allah yaxabarmata kenan.

Huduba yayi mata kafin ya 'durqusa har qasa yamiqawa sultana cikin girmamawa yace,
Kece kika cancanta daki za6a mata suna.

Yarima daya fito sashen sultan yaqaraso sashen sultana yana shigowa yaji zancensu kai tsaye yakalli yarinyar yakalli sultana yace,
Asaka mata UMMU-RUMANA..

Kallonsa sultana zaarah tayi fuskarta daukeda murmushi tace,
Mahaifiya kayiwa takwara maheer.

Mayar mata da murmushin kawai yayi tareda jinjina kai ahankali ya shafo fuskar jaririyar yace,
Allah ya raya ummu-rumanah.

Yana gama fadar haka ya wucewarsa sultana takalli bulama tace,
Allah yaraya ummu-rumanah.

Amin sukace cikin farin ciki da godiya harda jakadiya.

Yarinyar mamani ma shine yayi mata huduba mamani tasawa 'yarta suna NURATU.

Tunda asma'u ta haihu hankalinsu yasake kwantawa itada bulama tuni suka maida hankali ga bautarsu
Idan zatazo sashen sultana adaki suke barin 'yayansu itada mamani daga baya sultana tace tariqa zuwa da ummu-rumanah
Sosai lokaci yaja tuni ummu-rumanah ta fara girma
Daga ummanta sai sultana da jakadiya tafi sabo dasu sai nuratu dasuke wasa tare a can sashen bayi mahaifinta ta saba dashi sbd ana 'Dan basa damar zuwa ganinta itada ummanta wasu lokutan da haka rayuwa tayi nisa sosai.

Sultan an wayi gari baida amintaccen bawa kamar bulama sbd takai ko fita za'ayi wata qasar da amintaccen bawansa bulama yake zuwa gashi da tsananin biyayya da taka tsantsan sbd sultan nada qarfin mulki da iko sosai da wasu irin dokoki.

Ummu-rumanah nada shekara goma sha hudu cif aduniya Allah yayiwa bulama rasuwa sanadiyar ciwon ciki.

Anji mutuwarsa duk da kasancewarsa bawa hakadai asma'u da rumanah suka dangana da rashinsa saidai rasuwar ta ta6a asma'u sosai,
Ta rasa lafiya da nutsuwar zuciya tun tana daurewa tuni ciwo ya kwantarda ita hakan tasa rumanah karbar ragamar aikinta a sashen sultana.

Kwanciyar hankali tuni ta qauracewa rumanah ganin babu uba ga uwarta na jinya sosai
Sultana ma tana cikin damuwar ciwon asma'un Dana matuqar tausayin rumanah sbd jin asma'u takeyi tamkar 'yar uwarta ta jini rumanah kuwa dama amatsayin 'ya take agareta sbd tun tana shan nono tayi sabo da yarinyar.

Anyi maganin har andanga anbarwa Allah ikonsa amma jikin yaqi sauqi ganin haka sultana ta 'yantata nanda nan aka shelar an 'yanta baiwa asma'u.

Rumanah ga abin farin ciki amma Sam batajinsa ita kadai tasan yanda takejin zuciyarta ganin mahaifiyarta sai qarayin nisa takeyi.

Cikin dare Allah yakarbi rayuwar asma'u tabar 'yarta cikin wannan duniya mai ababen tsoro.

Rumanah kam zuciyarta bushewa tayi sosai tabawa kowa mamakin rashin kukanta har aka kai asma'un aka dawo.

Sultana zaarah lokacinda ta aika kiran rumanah tana zuwa ta durqusa gabanta kallon rumanar tayi batasan lokacinda hawaye suka taru a idonta ba tayi sauri shigewa qurya sai alokacin rumanah tasaki wani kuka daya tokare qirjinta ta zube agurin tanayinsa jakadiya tayi saurin jawota jikinta tana lallashinta.

Andauki tsayin lokaci kafin rumanah tasaba da rayuwa ba iyayenta ga 6angare guda mamani Sam bata qaunarta bare ta rage maraicin rashin uwa sbd da mamani da nuratu take kallo amatsayin jininta.

Sultana zaarah kuwa sosai take nuna qaunarta rumanah wanda itama rumanah tana qaunarta sbd ita take gani tana rage kewar ummanta.

Da haka rayuwa taja harsuka qara zama 'yan mata ta maida hankali sosai ga bautawa ummy kamar yanda take kiran sultana zaarah.
********
ABDULSHAMS IBN ABDALLAH MUHD shine sultan na yanxu dake mulki a meneelik wani yanki na babban birnin ethopia kamar yanda kakanni da iyaye suka bar masa,
Mulkinsu wani irin tsauri da zafi dashi ga wani irin qabilanci dasukedashi sbd Sam basa bayi ko borori da 'yan qasarsu saida akawo musu na wata qasar su siya shiyasa yawanci bayin masarautar daga qasashe dabam dabam suke mafi yawansu Nigeria sbd rashin tsaro na zama Dan qasa da 'yan Nigeria sukedashi.

Tun lokacin mulkin kakanni a wannan zuriar ta ABDALLAH muhd basuda yawan 'yaya maza saidai mata wanda hakan yayita kawo barazana ga barin sarauta da mulki daga zuriar.

Duk wani kalar arziki na duniya Allah ya hore musu shi kobana sarautataba amma banda yaya maza daqyar cikin yardar Allah suka samu namiji 'daya cikin 'yaya mata goma sha biyu da sarkin yakedasu daga matansa uku.

ABDULSHAMS shine yazamto namiji daya kuma ya gadi sarautar bayan rasuwar mahaifinsa ABDALLAH.

Tun yana yaro qanqani mahaifinsa yake cusa masa qaidoji da hukunce hukunce masu zafi sbd karsuyi sake sarauta tabar gidansu matuqar ba magaji sbd arubuce yaje a aje duk ranarda suka wayi gari sarki ya mutu ba magani to masarautar da duk wanda ke cikinta zasu zamo qarqashin ikon masarautar kilaimee tamkar bayi dundaga kan matan sarki da 'yayansa har bayinsu sbd wata tsohuwar muguwar gabace atsakanin masarautun.

Hakan yasa duk wanda yayi mulki basa tsayawa kan matansu da qwarqwarori suke qarawa amma duk da haka sunada qarancin maza sosai sai arzikin 'yaya mata.

Yanxu lokacin mulkin sultan abdulshams yanada matuqar zafi da tsanani amma duk da haka baiyi na iyayensa da sauran sarukan dasuka gabata.
Chapter 4 · 0% Book details