← Book details Tarayya Part One Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 51

Sashe 48

Tarayya Part One Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shima ita ya kalla ta sakar masa murmushi ahankali tareda riqe hannunsa ta lumshe ido sbd abinda taji yana taso mata ta danne yanayin daqyar tasake qaqalo murmushi tana kallon hannunsa dake cikin nata ahankali tabude baki tace,
Karka saki hannuna har lokacinda zan shaqi numfashin qarshena a duniya,
Ka zamo jiqo kuma majingini arayuwata
Ka hanani 'daukar hanyarda zata batardani zuwa duniyar daba tawaba,
Qarfin soyyarka yaci qarfin abinda nakeji ajikina saidai bansaniba ko hakan zai jima shiyasa a yanxu nake roqonka da har abada karka rabu da suhailat sbd itace macen da soyayyarta bazata taba barin cuta ta kutso kai rayuwarkaba..ni tamkar baquwace a rayuwarku ba lallaine na qarasa rayuwa acikinkuba.......

Matse hannunta dake cikin nasa yayi yana rintse idanuwansa dasukai jajir..

Hawayen datake riqewane suka 6alle mata ta kalli fuskarsa datai jajir ya rintse idanuwansa ta shafi fuskarsa hawayenta na tsananta tace,
Maheer abdulshams nagode da soyayyarka gareni..

Bude jajayen idanuwansa yayi yana kallon hawayenta dake gudu sosai yakasa magana sbd radadi da nauyin da zuciyarsa tai masa sai kawai ya rungumota jikinsa.

Ahaka suka kwana cikin wani irin sanyin jiki dana zuciya.

Kwanansu khaleefa biyu a ruwa aranar na uku da yamma sosai suka isa saidai kuma sunsha wahala sosai sbd tuni bakin ruwan yazama border saida sukasha wata irin wuya kafin suka samu wucewa da taimakon wani 'dan asalin qauyensu mamani din.

Bayan wucewarsu duk yanda sukayiwa saurayin bayani bai ganeba sbd basajin hausa ko kadan har gwara nuratu tanaji kadan kadan sbd su mamani da umman rumanah sunayi musu tun suna qanana saidai ya jasu kan mashin dinsa sukayi wani irin mugun overload yajasu dan kaisu cikin qauyen daya samu canji ba laifi.

Tafiya mai tsawo sukayi kafin suka isa qauyen mai tsananin girma da cikar mutane.

Gidan shugaban qauyen yakaisu cikin sa'a lokacinda suka isa yana gida.

Kallonsu aka taru anayi sbd ganin baqaqen labarawa musamman khaleefa dayake cikakken dan Ethiopian asali.

Bayan anbasu guri sun zauna ya fidda tambarin masarautar dasuka fito ya miqawa shugaban ya kalli nuratu yayi mata magana yace,
Kiyi musu bayaninmu yanda zasu gane ko yayane.

Gyara zama tayi muryarta na rawa tace,
Munfito daga qasar Ethiopia ne qarqashin masarautarsu,
Sun siya bayin dasuka fito daga wannan nahiyar tsawon shekara ashirin da biyar yanxu.,
Acikinsu akwai mamani da asma'u dasuka tafi da juna biyu acan suka haifi 'yaya mata dukkaninsu Wanda 'daya daga cikin 'yayan itace ni 'dayar kuma a yanxu itace sarauniyar qasar.

Da wani irin mugun mamaki suke kallonta musamman shugaban garin daya zamto kutti mijin mamani yasake kallon nuratu da gabaki 'daya take kamar yar asalin Ethiopia itama.

Cikin nutsuwa yace,
Ke 'yar wacece acikinsu?

Ni 'yar mamani ce.

Wata irin kabbara tsoffin gurin suka dauka cikeda murna da mamakin wannan alamari kutti yace,
Ina iyayenku?

Dukkaninsu Allah yayi musu rasuwa mamani ko sati batayiba yanxu haka.

Sake daukar kabbara sukayi cikin jimami da tsananin girmama wannan alamari.

Ahankali ta zayyane musu komai gameda rayuwarsu kafin ta gabatarda khaleefa amatsayin Wanda zai karbi takardun dukiyar asma'u da bulama dan neman asalin sarauniya ummu-rumanah.

Bayan dogon koke koken saduwa da baqin cikin rashinsu mamani dasu bulama nan kutti yagabatarwa da su nuratu kansa amatsayin mahaifinta.

Duk wani zuriar gidan antaru an karbi nuratu da hannu Bibbiyu da zuciya daya da wainda suka San faruwar abin da wainda ma ko haihuwarsu baayiba nan dai kowa yataru ana farin ciki.

Ganin yanayin g
arin yasa khaleefa yanke shawarar wucewa dan sake kutsawa cikin Nigeria dan gabatarda abinda yakawosa.

Kutti ya basa takardun dasuka tsufa sosai ga sanyin ruwa daya soma lalatasu tun wancan lokacin saidai ba laifi yana iya ganin rubutun dake jikinsu atake ya karancesu daganan ya roqi alfarmar tafiya da wani yaron kuttin dayake jin yarensu kadan kadan sbd aiki dayakeyi a border dinsu.

Da mashin din salee suka isa inda zasu samu mota bayan sunyi tafiyar awowi akan mashin din.

Motar dazata kaisu Maiduguri kai tsaye suka hau inda duk hankalin khaleefa yatashi sbd ganin inda yasamu kansa dakuma wata irin azabar wuyar tafiya data fara gigitasa.

Gaf da asuba suka isa Maiduguri kai tsaye wani lafiyayyan babban hotel suka sauka anan yayi baccin wahala ga zazzabin dakeson kamasa na baqar wuyar dabai taba shaba.
#mamuhgee
[8/7, 7:37 AM] ummul aulad: *_TARAYYA_*
_wattpad@mamuhgee_
_Haske writers association
*45*
Not edited.

Saki jikinsa yayi sbd wutar data daukewa jikinsa da wani irin qarfi ammy ta jijjigasa tareda kiran sunanda da qarfi ya durqusa tareda jawota jikinsa ya dauketa gabaki 'daya yabar gurin da ita.

Anso tsayarda nadin sarautar amma haroun ya fitarda saqonta na gaba dake cewa duk abinda zai faru kar a tsayarda nadin dakuma takardarta tagaba dake cewa a raba mara masarautar biyu a rushe Rabin a gina masallacinda yafi kowane girma a qasar Ethiopia.

Hakan yasa aka cigaba da nadin yayinda sultan dake zaune har aka gama bai motsa daga inda yakeba saida aka watse aka gano ya rasu zaune agurin gakuma jinin da aka ganin ya digo daga hancinsa.

Lokacinda su negasi suka rufu akanta dan ceto rayuwarta alokacin ne aka zo da saqon rasuwar sultan Wanda ya girgizasu ya qarasa wargaza dukkanin sauran nutsuwarsu musamman ammy data kasa riqe kukanta maheer yayi saurin rungumeta yana riqe nasa hawayen sbd Allah yasani yana qaunar mahaifinsa duk mugun halinsa sbd koyaya ya zama mahaifinsane.

Cikin qanqanin lokaci rasuwar sultan da halinda assultana take ciki tareda canza karagar mineelik suka yadu 'yan jaridu da kafafen yanda labarai sukaiwa masarautar wani irin dandazo ana yada abinda ke faruwa.

Dukkanin iyalan marigayi abdulshams sun halarto cikin tsananin baqin cikin wannan rana data riskesu musamman 'yayan marigayiya adama dasuke ganin sun rasa uwa da uba.

Da maraice akai jana'izarsa inda dubban alumma na nesa dana kusa suka hallara inda yawan jama'arsa yasa maheer jin sanyi sanyi aransa tareda yiwa mahaifinsa adduar samun rahamar Ubangiji.

Duk damuwar dayake ciki ta halinda rumanah take ciki bai koma gurinta ba sai dare bayan an watse.

Kai tsaye sashen ammynsa ya nufa inda ya tararda ita tareda sauran 'yan uwansa ya qarasa kusada ammyn ya zauna yana kallonta cikin nutsuwa da tausayawa ya riqo hannunta ahankali ya iya furta,
Allah yaji qansa ammynah.

Kwantarda kanta tayi kafadarsa tareda cewa "amin" da muryarta data shaqe kafin ta 'dora da fadin,
Kaje gurin rumanah dan sanin halinda take ciki duk da meenah da jakadiya na gurinta.

Jinjina kai yayi jikinsa na qara sanyi da tuno wani tashin hankalin dayake ciki.

Lokacinda ya isa sashenta har lokacin bata farfado ba sai jinin daya tsaya Wanda suke sakaran jinintane yayi matuqar qasa sosai.

Zaune ya kwana gabanta yana mata addua cikin wani irin hali dabai ta6a tsintar kansa aciki ba.

Washe gari koda akaga bata farkaba hankula sukai matuqar tashi musamman da jikinta yayi wani irin fari fari Kore Kore ga 'yan jarida dasuka kasa suka tsare a masarautar sunason ganawa da sarauniyar data kafa sabon tarihi a qasar daba tataba.

Duk wani kalar likiti na turai da gargajiya an nuna qwarewa amma abu yaci tura gashi alamunta na sake 6aci ranar da akai uku aranar gabaki dayansu suka tattara suka nufi Georgia..shi,ammy da jakadiya data samu 'yancin rayuwarta itama sai sauran 'ya'yan da kowace takoma inda take aka bar sabon sultan dan gabatarda mulkinsa cikin aminci.

Suna sauka kai tsaye motar asibiti tazo daukarsu aka wuce asibiti dasu cikin tashin hankalinda yafi na farko sbd saki jikinta daya farayi.

Matsayinsa a babbar asibitin garin yasa ana isa da ita dukkanin likitocin dake nan suka taru aka fara qoqarin gano matsalar cikin gaggawa cikin tashin hankali da mamakin yanayin matsalarta sbd basu taba cin karo da irin hakanba.

Ammy daqyar ta iya zama gida saidai gabaki 'daya hankalinta da damuwarta na asibitin gabaki daya cikin kwana ukun ta rame tayi wani irin sanyi ko doguwar magana bata iyawa.

Har gari ya waye likitoci na kanta duk wata dabararsu da qwarewarsu sun nuna dan ganin ta farfado saidai Sam bata farfado ba saidai fatarta data fara komawa daidai sbd jinin da aka saka mata kusan leda biyu hakan yasa suke sakaran idan fatar ta gama komawa daidai ta farka.

Daqyar yake iya hadiye yawun bakinsa sbd tsananin bushewar bakinsa da maqoshinsa,
Duk wata nutsuwarsa da tunaninsa sungama barin jikinsa idanuwansa tuni suka qanqance ko gani bayayi sosai da idonsa dukkanin abokanan aikinsa sun tausayawa halinda yake ciki shiyasa suma gabaki daya hankalinsu tashe yake da ganin ta farfado 'din.

Khaleefa aranarda suka wuce aranar yasauka Ethiopia ya tararda abinda ke faruwa kasa kwana yayi duk da rashin lafiyarsa washe gari yabi jirgin asuba sbd yasan aminin nasa na tsananin buqatarsa.

Har yamma bata farkaba khaleefa ma saukarsa garin alhaji babaye yakirasa sbd news din dasuka gani gameda abinda yake faruwa a qasar nan yaqara yasanardasu abinda yake faruwa nan hankalinsu yayi matuqar tashi suka fara shirye shiryen tahowa cikin gaggawa.

Qarfe goma na dare ta bude idanuwanta dasukai wani irin shigewa sukai nauyi da ja.

Atake dukkanin likitoci suka sake hawa kanta cikin gaggawa da nuna qwarewa tareda fatar samun nasarar sanin matsalarta.

Kasa miqewa yayi sbd saki ga gabobin jikinsa sukayi sbd fargabar abinda za'a fada masa saidai khaleefa ne ya dafasa yana jinjina masa kai alamar qwarin gwiwa ganin halinda yake ciki.

Wasu sabbin dogayen hours suka 'diba suna qoqarin gano matsalar wadda suka gano daga qarshe wadda tayi mummunan 'daga hankalinsu haka suka ringa fitowa jiki amatuqar mace zuciyoyinsu ba dadi sbd dukkanin hotunansu da test test dinsu sun tabbatar musu da abu 'daya.

Dr Edward ne yafito qarshe yana zare glasses dinsa yakalli maheer da khaleefa yace,
Can we talk in my office pls..

Tashi tsaye maheer yayi tareda kallon qofar dakin da take yakalli Dr Edward din yana rintse idanuwansa da abinda za'a fada masa yace,
Just tell me dr Edward I c........

Dafasa Dr Edward yayi cikin tsananin tausayi ganin daqyar yake iya bude bakinsa yayi magana cikin sanyin murya yace,
I'm really sorry Dr m.a shams matarka ta rasa gangar jikinta bazata taba gara aikiba ma'ana tanada rai tana gani tana numfashi tanaji saidai bazata iya motsa jikintaba ko kadan bare magana har abada.

Wani mugun jirine ya dibesa khaleefa da Dr Edward sukai saurin nufarsa zasu taresa ta rigasu taresa cikin kulawa da tausayawa.
Chapter 48 · 0% Book details