← Book details Tarayya Part One Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 51

Sashe 30

Tarayya Part One Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shiga tayi taga harda 'dan madaidaicin gadon hutawa mai kyau a dakin sai couches da table harda TV da fridge ga split ac dake aiki
Ta zauna kan couch tareda lumshe ido tana kallon hotonsa dake cikin qaramin frame kan table.

Murmushi tasaki tareda 'daukar frame din qasan maqoshinta ta furta,
Iwe dihalhu.

Cikin kunnenta taji ance,
I heard that.

Saurin juyowa tayi tana ganinsa ta rufe idanuwanta cikeda jin kunyar kanta.

Ya riqo hannunta yana murmushi ya nufi gadon dakin da ita yana cewa,
Karki damu suhailat is kind hearted bazata hanaki mijintaba.

Murmushi tayi tana zaunawa bakin gadon sbd har lokacin bata daina jin kunyar zancentaba.

Janye rigarta yayi yafara scanning din cikinta cikin qwarewa harya gama yayi rubutun dazaiyi fuskarsa batadaina bayyanarda annurin da zuciyarsa take cikiba.

Tayarda ita zaune yayi suna fuskantar juna ahankali yace,
Babynki saura wata hudu yazo duniya yaga stubborn mom 'dinsa mai kishi da antyntah dabatasan tafita son mijintaba ba.

Kallonsa tayi da sauri jin abinda yace bayan baisan meye sirrin tata zuciyarba saidai baisan tayi masa kyakkyawan saniba dahar tagano maganarsa is like yana challenging dinta akan sonda take masa.

Murmushi tasakar masa tareda kai bakinta daidai kunnensa cikin wani irin salo ahankali ta furta,
Kanason tabbatarwane?

Wani irin murmushin jin dadin daya ratsa zuciyarsa yace,
Tabbatarwar nake buqata.

Murmushi tasaki mai qaramin sauti tareda qara 'dora bakinda kunnensa saidataja wani irin numfashin datasan zai 'daga masa hankali kafin cikin ra'da tace,
Umarni ne ko buqata?

Kasa haquri yayi saidaya ha'data da jikinsa ya shafi wuyanta yana sake sakin wani sabon qayataccen murmushin Shima qasa qasa yace,
Duka.

Tashi tayi tana 'yar qaramar dariyar data sake burgesa yariqota tadawo jikinsa cikin wani irin salo tana fadowa ta dora bakinta anasa bayan tayi qoqarin yakice kunyarta da qarfi.

Cikeda mamaki da farin ciki mai tsanani yake kallon idonta tayi saurin rufe masa ido da hannunta 'daya
Nan suka samu damar kissing juna cikeda kewar juna.

Sai rana tsaka suka koma gida har lokacin suhailat bata dawoba babu kowa sai Carolina shiyasake basu damar sakewa a dakinsa sukayi abinda sukaga dama sukayo sabon wanka suka sauko cin abinci
Ko a dining sosai yau Carolina take satar kallonsu tana mamakin irin abinda taga yana faruwa atsakaninsu.

Koda suhailat tadawo suna sama batai shishigin zuwaba tayi wanka dakinta tashiryo cikin qananan kaya marasa nauyi bata fitoba sai lokacin dinner kuma suma lokacin suka sauko
Rumanah na ganinta taji nauyinta sosai
Shiyasa ko kallon inda yakeyi bata sakeyiba ta maida hankali gurin cin abincin ta hankali kwance.

Suhailat ma bata nuna damuwar komaiba saima qoqarin ganin tasake data ringa mata.

Suna gamawa suhailat ta matso kusa dashi ta ranqwafo tai kissing hannunsa tace,
Gud night baby.

Ta juya gurin rumanah dake qoqarin barin gurin tace,
Gud night rumanah.

Cikeda kunya tace,
Allah yatashemu lafiya.

Dakinta ta nufa tabarsu suna binta da kallon girmamawa.

Da kansa yadauketa har zuwa dakinsa ya kwantar da ita ahankali kan gado batareda yace komaiba ya juya yashige toilet.

Kwananta biyu agurinsa ranar na ukun tana sane da abinda suhailat ke nufi shiyasa tun wuri tayi kwanciyarta dan ko agurin dinner tariga kowa tashi tayi musu saida safe
Shima yagane mai suke nufi shiyasa bai damuba ahaka suhailat tagama kwananta biyu saidai kuma kwanan biyu bata yisu cikin lafiya ba sbd wani irin zazzabi da ciwon kai datake fama dashi.

Tashin farko dayayi mata test cikin wata uku ya bayyana ajikinta Wanda ya basa mamaki ta yanda bai taba luraba ita kuma dama tasan da abinta kawai taga tunda bana farko bane kuma akwai wadda tafita buqatar kulawa tunda ita natane na farko shiyasa kawai tabarwa kanta.

Rungumeta yayi cikin nutsuwa yace,
Thank you suhailat.

Shafo fuskarsa tayi cikin qaunarsa tace,
Why are you thanking me?

Sbd you're always given me happiness.

Murmushi tayi tareda taba hancinsa tace,
Ka godewa Allah not me.

Ina godewa Allah koyaushe daya bani best wife datake qaunata,
Ina fatan komai na zama anan gaba zaki cigaba da sona bazaki barniba.

Hakanan taji faduwar gaba tareda tausayin kansu tace,
I promise to be with you and support you komai rintsi komai wuya koda akan abinda kakesone.

Rungumeta yayi jikinsa da zuciyarsa na shiga wasi wasin komai zaizo gaban.

Ranarda cikin rumanah yacika wata bakwai na suhailat yacika wata biyar mumman saqo ya iso daga mineelik na 'daukar rumanah da suhailat dan zuwa haihuwa.

Lokacinda yakira ammy yasanarda ita atake tafara shirin komawa mineelik 'din tsoro da fargabar data danne na dawo mata sabo.
#mamuhgee
[7/29, 9:29 PM] Hauwa'u inna: _*TARAYYA*_
_wattpad@mamuhgee_
_Haske writers association
*31*
Not edited.

Kallon adama dake qoqarin saukowa gado yayi yaga yanda jikinta ke rawa saidai Sam bata tata yakeyiba mafarkinsa ya girgiza tunaninsa da zuciyarsa matuqa sbd su mutane ne dasuka yarda da mafarki,
Basason 'yaya mata sbd muguwar aqidar dasuke ciki ta wani irin mulki da ake gudanarwa na tsantsar iko kowa yasan mulkin mace a mineelik masifa ce dabaza'aso maimaitawaba sbd jinin matansu bazai iya controlling na abinda yake tareda throne dinba kamar namiji shiyasa mulkinsu yake zama tamkar masifa ko annoba sbd mulkine na tsantsar zubarda jini Wanda babu yaro ba babba bare mata bare maza,ba tsoho ba tsohuwa.

Alqawarine yadauka bazai taba bari mace ta mulki mineelik ba koda zai rasa ransane sbd yasan duk macen dazata hau zaiyi wuya basuyi ajalin junaba dayaga haka ya roqi Allah yayi gaggawar daukar ransa.

Cikeda rudu adama takallesa tana goge fuskarta dahar lokacin take gumi tace,
Sultan nayi mugun mafarkinda gwara nayi mutuwar qasqanci a hannun 6arayi dana fuskanci irin abinda Nagani a mafarkin.

Bai kalletaba bare yatsaya sauraran abinda take fada sbd tunanin daya cika zuciyarsa akaro na farko arayuwarsa dayaji mulki yafara fita ransa sbd duba da irin mutuwar da sarakunan mineelik keyi yayi tunanin zai iya tsallakewa ya sauka mulkin salin alin batareda fuskantar irin qarshen sauran sarakunan ba shiyasa ya tattara duk dagewarsa akan ganin maheer ya karbi mulkin amma yaqi gashi matarsama ta haifi namiji arabasa da wannan masifar abu yaqi yiyuwa ta wani 6angare ga daular shiefffs na jiran rashin magajinsu su zamo bayi a qarqashinsu Wanda yafison ya sare kansa daga gangar jikinsa dayaga wannan baqar ranar yanzu kuma ga wata masifar nason 6ullowa sbd baisan me mafarkinsa na assultana yake nufi ba.

Hannunsa ya daga ahankali ya shafo fuskarsa cikin mamaki saiyaga zufa ne ke tsatsafo masa,
Rabon da yayi zufa a rayuwarsa harya manta.

Irin tarbarda akayiwa isowarsu ta qara sanyaya jikin rumanah sbd tafara fargabar itama me zata Haifa sbd ganin irin dubban jama'ar dasuka dogara da abinda zata haifa.

Lokacinda mamani tayi ido biyu da rumanah da cikin dake jikinta wani mugun jiri mai qarfi ya 'dibeta nuratu tayi saurin tareta tana kallon idanuwanta dake cikowa da qwallar baqin ciki tace,
Mamani lafiya?

Kasa riqe hawayenta tayi sbd baqin cikin daya rufe zuciyarta tace,
Har abada bazanyi lafiyar zuciya ba sbd bulama da asma'u har bayan barinsu duniya basu bar kurwata ta zauna lafiya ba bayan duk balain dasuka sako rayuwata aciki dan haka wlh bazan zauna nashaqi numfashi mai dadiba sai ranar dana gama lalata dukkanin zuriar da suka bari aduniya....

Sakinta nuratu tayi cikeda mamaki da baqin cikin halin mahaifiyar tata muryarta na rawa tace,
Mamani dazaki cire abinda yake ranki gameda rumanah dakin cire sbd zai kaikine matakin halaka sbd yanxu tariga ta taka wani matsayinda duk Wanda yayi mata wani ganganci zai iya rasa rayuwarsa sbd dukkanin burin daular nan da zagayenta akanta da cikinta yake dan haka ki nesanta kanki da ita sbd gujewa rasa rayuwarki..ke mahaifiyatace ina sonki fiyeda komai amma bazan iya kallo ki cuci rumanah ba dan haka karkiyi abinda zai barni da rashin zabi face na fadi gaskiyar dazaki rasa rayuwarki.

Tana gama fadar haka tabar gurin cikeda damuwa
Duk murnarta da farin cikin ganin rumanah din ya 6aci sbd mamani.

Kukan 6aqin ciki mamani tasake tana tsinewa bulama da asma'u ta juya ta nufi gurin adama da sai alokacin zata fito tarbon.

Kallo daya tayiwa cikin rumanah taji tari mai qarfi ya sarqeta kamar ranta zai fita
take ta gigice da gudu akaje aka kawo mata ruwa ta karba tasha idanuwanta dasuka firfito sukai jajir sbd tari numfashinta na fita da sauri ta juya tabar gurin nanma idonta ya sauka kan na suhailat dake tsaye gefen Maheer ai take taji qaramar hauka na neman kama zuciyarta tana isa palonta na farko dukkanin bayi da kuyangin part din suka fice sbd gudun laifi lurada halinda take ciki.

Mamani data sake biyota da ruwa ta miqa mata har lokacin itama jitake kamar ta cinnawa mineelik wuta kowa ya babbake ya mutu ko zataji abinda ya tsaya mata a maqoshi ya fada.

Karbar ruwan tayi tasake sha tana cewa,
Burina dana gina tun ina budurwa bazai taba rushewaba kan baiwa 'yar bayi,
Babu Wanda bazan iya raba gangar jikinsa da kansaba kan burina sbd burina shine burin karagar mineelik..

Cikin tsananin damuwa da baqin cikin mamani daya kasa dannuwa aranta tace,
Duk inda bulama da asma'u suka sauka saisun bar masifar data addabi kowa awajen
Shiyasa bazan numfasaba saina tabbarda na tarwatsa rayuwar rumanah da abinda ke cikinta.

Kallonta adama tayi da jajayen idanuwanta baqin cikinta na ninkuwa tace,
Ko bulama ne aduniya bai isa ya shiga tsakanina da hawa throne din mineelik ba bare 'yarsa dan haka ni adama ayau ina sake daukarwa kaina alqawarin kawarda ko wanene ya shiga hanyata ta cimma burina
Idan nace ko wanene ina nufin ko wanene ciki bancire kowaba.

Cikin takaici mamani tace,
Allah yasa gurin haihuwa ta mutu daga ita har abinda zata haifa kowama ya huta.

Kobata mutu gurin haihuwa ba ta haifi namiji saiya mutu kozan rasa rayuwatane"""adama ta fada
tana miqewa tsaye.

Tsayawa tayi tareda juyowa takalli mamani itama mamani ita takalla sai alokacin kowannensu yadawo nutsuwarsa jiki na rawa mamani ta zube tana sunkuyar dakai
Adama fuskewa tayi sbd duk duniya daga ita sai bokanta ne suka San da sirrinta sai yanzu da 6acin rai yasata fadar abinda ke ranta saidai kuma ga alama tasamu wadda zata riqa amfani da ita Dan cimma burinta musamman da kusancinsu da rumanar zasuyi amfani tunda tana yiwa mamani kallon uwa.
Chapter 30 · 0% Book details