← Book details Tarayya Part One Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 51

Sashe 29

Tarayya Part One Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tunda suka shigo motar hannunsu suke sarqe dana juna saidai babu mai iya magana acikinsu dan kowanne da halinda zuciyarsa take ciki.

Ko acikin jirgi tafiyar babu Wanda yake iya magana acikinsu sbd kowa da abinda yake kai kawo acikin zuciyarsa.

Suhailat dama tuntuni tasan ita farin ciki yaqare arayuwarta daga ranar da mijinta yafara son rumanah musamman yanxu datakejin duniyar dakomai ya fice mata arai gashi ciwon dakecinta yafara fin qarfinta musamman yanxu datake yawan ciwon mara mai tsanani.

Qarfe hudun asuba jirginsu ya sauka a Ethiopia.

Matse hannunta dake cikin nasa yayi ta juyo takallesa da idonta dasukai ja sbd tsananin damuwar dake ziciyarta.

Ahankali ta zare hannunta ta miqe ta wuce gaba su Jakadiya da sauran suka mara mata baya tana qoqarin maida hawayen dake qoqarin zubo mata.

Bayanta yabi da kallo idanuwansa na canxawa
Hannunsa suhailat ta riqo idanuwanta cikeda hawaye cikin rawar murya da kulawa tace,
Zan zamo bangon jinginarka aduk lokacinda kake buqatar hakan.

Rintse ido yayi idanuwansa naqara canxawa suka fito jirgin.

Motar rumanah daban ita kadai da masu tsaronta kuma itace agaba sai sauran nasu lokacin gari baigama haskeba.

Ruwa yaji ankelaya masa yayi saurin bude ido yatashi a matuqar zafafe saiyaga jini kaca kaca a jikinsa da sauri yatashi tsaye aka mayar dashi zaune da qarfi tareda dora masa wata doguwar takobi mai tsananin kyallin sbd kaifinta tsoro bai kamasa sbd dama yasan hakan zata iya faruwa ko yau ko gobe....

Cikin wata irin murya data amsa amo har cikin qwaqwalwarsa yaji ance"""asauke kansa Daga gangar jikinsa a qawata qofar shigowa masarautata dashi kowa ya 'dan'dana kalar mulkin assultana the redblood Queen.

Daga takobin akayi da qarfi za'a sare kansa yayi wani irin yunquri yana hada mugun zufan daya jiqa dukkanin jikinsa yakalli adama dake gefensa itama ta farko tana hada nata zufan da alama itama wani mugun mafarki tayi kamar shi sbd harma tafisa rudewa sbd rawar da jikinta keyi.

Saukowa yayi kan lafiyayyan qaton gadonsa yanajin wani irin tashin hankali na shigarsa busar data cika masarautar tashigo kunnensa kenan su maheer sun iso.
#mamuhgee
[7/29, 9:29 PM] Hauwa'u inna: _*TARAYYA*_
_wattpad@mamuhgee_
_Haske writers association_
*29*
Not edited
Daqyar tasamu tayi bacci sbd ciwon kai koda gari ya waye bata fitoba saida dukkaninsu suka fice aiki tafito daqyar tasha tea takoma daki tayi zamanta ko kallonma a dakinta tayisa duk da rabin hankalinta baya ga kallon.

Daga office ma yau tare suka dawo da wuri sbd driver yaje yadauko suhailat suka biyo suka daukesa suka dawo gida tana kicin ta hango shigowarsu palo ta lafe taqi fitowa
Suhailat na maqale da hannunsa suka wuce sama tana fada masa wani zance sai murmushi yakeyi harda shafo fuskarta.

Harsuka shige bata daina kallonsu ba ta aje freshmilk dinda tazo sha takoma daki a sanyaye.

Qarfe takwas da minti ashirin suke dinner Carolina tazo kiranta inji suhailat tazo suci abinci.

Batai musuba ta miqe ta nufi qofa tafito.

Tundaga nesa take hango wani irin kallo dayakewa suhailat dataci wani irin ado cikin wata doguwar riga mara hannu black sai qyalli takeyi tana masa magana tana dariya shikuma saidai ido.

Riqo hannun suhailat yayi cikin miskilanci yace,
Hmm my wife is this Talkactive and I don't know wow..

Murmushi tayi tareda yiwa hannunsa dake riqe da nata kiss tace,
I love you maheer.

Shafa fuskarta yayi yace,
Ok time to eat.

Juyawa rumanah tayi jiki sanyaye sbd zuwanta gurin zai rage musu jin dadine kawai musamman suhail
at dataga tana cikin farin ciki sosai.

Bayanta yabi da kallo a sace harta shige dakinta sbd tun fitowarta yaganta sbd dama hankalinsa na nutsuwarsa nakan qofar.

Abinci Carolina tazo ta dibarwa rumanah babu Wanda yace tasake kiranta sukaci abincinsu suka yakoma sama suhailat taje ta taya Carolina shirin baccinsu amah.

Yana kwance idanuwansa a rufe suhailat tashigo ganin kamar yayi bacci yasata komawa dakinta tayi kwanciyarta.

Tundaga ranar rumanah taqara nesanta kanta dasu sbd ganin sunfara mantawa da wanzuwarta a gidan
Dama aikinta yaqare tunda tasamu cikin da akeso.

Sati 'daya kenan basu saka juna a ido ba sbd qauracewa musu datayi har gwara suhailat tana zuwa dubata duk tadawo aiki sbd sanin lafiyarta musamman yanxu da Cikin yaqara fitowa.

Yau da wani irin ciwon kai da zazzabi ta wuni ko ruwa daqyar take iya sha sbd komai taci sai amai.

Qarfe tara suhailat tashigo dakinta dubata taganta kwance lamo tayi shiru jikinta yayi matuqar zafi.

Cikin kulawa da tausayawa tace,
Subhanallah bakida lafiya haka shine baki fadaba.

Cikin dasashiyar murya tace,
Kaina ne yake ciwo sosai.

Fita dakin suhailat tayi da sauri ta nufi dakinsa
Koda tashiga yafito wanka yana zaune sanyeda wandon bacci mai tsantsi black bai sanya rigarba yacika dakin da qamshinsa da sanyin AC yaqarawa da'di yana zaune kan kujera ya dora qafafunsa kan table yana waya da ammy.

Cikin 'yar damuwa tace,
Baby rumanah batajin dadi sosaifa tace kantane yake ciwo sosai and the condition she's in kasan ba'ason tana fama da damuwar ciwo ko yayane.

Aje wayar yayi batareda yakalletaba a miskilance yace,
Mezan mata?

Zaunawa tayi kusa dashi tareda dafasa tace,
Baby pls kadubata kasan maganin dazaka bata baza'a barta cikin halinda take cikiba wlh daga gani kuka ta yini tanayi....

Wani kallo yayi mata jin abinda tace kafin ya dauke kai yace,
Idan tabaki tausayi har haka ki kawota naga abinda zan iya yi.

Miqewa tayi tafice cikin jin dadi.

Daqyar rumanah ta tashi tabiyota tana tafiya ahankali sbd Sam har cikinta jitake yayi mata kamar ya kumbura ya danne saman cikinta.

Koda suka isa dakin rumanah sauke kanta tayi har kusa dashi suhailat takaita ta zauna
Shi ko kallon inda suke baiyiba yana duba Abu cikin laptop din dake gabansa.

Cikin kulawa suhailat tace,
Bari naje nasa carolina ta hado miki abinda zakici kafin kisha magani,ta fice.

Shiru tayi numfashinta na fita da sauri jinta kusadashi sosai
Shikuwa aikin gabansa yakeyi sai dai ganin yana neman fara shirme yasashi rufe laptop din yajuyo ya qura mata idanuwansa.

Jin kallonsa na yawo ajikinta yasata 'dagowa ahankali takallesa nan take idanuwanta suka ciko da hawayen masifaffiyar kewarsa dake cinta.

Yana kallo hawaye suka gangaro daga Cikin idanuwanta ya lumshe ido yasake budesu akanta
Hannu ya miqa mata babu musu takama tareda fadawa jikinsa tana sakin kukan datake riqewa duk kwanakin.

Rungumeta yayi tareda rufe ido yana jin nutsuwarda yarasa duk kwanakin tana dawo masa.

Qanqamesa tayi tana sake shigewa jikinsa sbd sabuwar kewarsa dake shigarta dukda tana jikinsa din.

Sun jima ahaka kafin ta dago fuska ta kallesa shima ita yake kallo tasaki murmushin cikar buri
Ya shafo fuskarta zuwa lips dinta yace,
Kukan da aka yini tanayi na ciwon gske ne kona kewar ammy ne?

Soke kanta tayi sbd sarai tagano 'dan ammy yake nufi ba ammy ba.

Murmushi yasaki sbd qin dago kanta datayi sbd kunyar zancen sbd ta tabbarda yariga yagane shine kukanta shine murmushinta.

Dago fuskarta yayi tayi saurin rufe idonta ya zura hannu cikin rigarta ahankali yashafo cikinta
Ta bude ido tana kallon fuskarsa.

Da ido yanuna mata cikin yayi kicking tanajin motsin itama musamman yanzu da hannunsa ke kan cikin saitaji qaunar cikin da maishi sun sake shigarta ta dora hannunta kan nasa dake kan cikin suka kalli juna sbd sake motsi da Cikin yayi.

Suhailat data shigo basusan tashigonba ta tsaya cak tareda kallonsu jikinta na 'dan rawa tayi saurin aje tray din tsakiyar dakin ta fice ko dakinta bata komaba dakinsu amah taje takwanta kusada fammah tareda Rungumeta ajikinta tana kiran sunayen Allah.

Basuyi tunanin suhailat zata dawoba hakama basu lurada abincinda takawoba yabata fruits din dake gabansa wainada suhailat takawo masa tuni tasha kadan yabata magani tasha tana kwance jikinsa daganan ko mintuna nawa batayiba bacci ya dauketa dama akwai na bacci sosai aciki sbd yanayinta daya nuna bata samun isashen bacci.

A jikinsa tayi bacci yazare mata doguwar rigar jikinta yazare mata bra yabarta da pant yasaka mata rigarsa ta bacci duk da ta mata mugun yawa ya kwantarda ita kan gado tareda rufeta bayan yayi kissing idanuwanta dake rufe.

Kan kujera yakoma yabude laptop dinsa yanason cigaba da aiki amma yakasa yayi crossing legs yadauki fruits 'din data rage yana sha idanuwansa nakanta ya zuba mata yana kallonta nutsuwa nasake shigarsa.

Washe gari kusan tare suka tashi hannunsa cikin nata suka shiga toilet sukayo alwala sukazo sukai sallah daganan bacci suka koma Wanda ita rabon datai irinsa ta manta shikuwa banda kallon fuskarta da cikinta babu abinda yakeyi daga baya yasake shigar da ita jikinsa ya lumshe ido bacci yadaukesa.

Qarfe bakwai suhailat tayi shirin zuwa aikinta ta fice ko breakfst bata tsayaba apple kawai taci bayansu amah sun wuce school.

Sai qarfe goma suka sauko tana gefensa sanyeda jallabiyarsa datai mata mugun yawa ta nufi dakinta da sauri sbd batason haduwa da suhailat da rigarsa ajikinta.

Shikuwa black Gucci trouser ne ajikinsa da black shirt fuskarsa sosai take bayyanarda annashuwar da zuciyarsa ya nufi dining yana waya da sultan dake sanardashi abinda ya 'daga hankalinsa na cewar sufara shiri kowane lokaci zasu iya dawowa gida sbd rumanah a mineelik zata haihu.

To kawai yace sbd kai karshen zancen dan zai iya samun matsala da sultan din idan yace aa.

Wata doguwar Turkish gown tasaka Maroon wadda tayi mata kyau matuqa musamman da cikinta yafito tayi rolling kanta ta sanyo loafers black tafito tana fidda siririn qamshin daya zama tamkar na jikinta.

Kai tsaye dining ta nufa itama tunkan taqaraso ya zuba mata ido yana kallonta musamman murmushin dake fita fuskarta dayafi 'daga masa zuciya.

Tana zuwa kusada shi ta zauna tareda duba abincin ta zuba masa Wanda tasan yanaci ta dibi chips kadan taci da mango mango juice mara sanyi ko kadan sbd tuni yasawa Carolina dokar karta kuskura kaiwa rumanah Abu mai sanyi.

Suna gamawa ta sanarda Carolina zata fita ta fice Kodataje yana cikin Mercedes-maybach exelero 'dinsa da alama shine zaiyi driving din
Taqaraso tashiga sukabar gidan.

Asibiti suka nufa,suna isa kai tsaye office dinsa suka nufa
Suna shiga ya nuna mata quryar resting room din dake cikin office din yace tashiga yana zuwa.
Chapter 29 · 0% Book details