← Book details Tarayya Part One Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 51

Sashe 20

Tarayya Part One Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fitowa tayi ta nufi dakinta ta zauna bakin gado tareda jawo bedside drawer ta kalli ledarta tsawon mintuna kafin ta rufe tareda sauke numfashi
Gabaki daya tarasa meya dagula mata nutsuwa ta miqe ta nufi toilet tayo alwalar sallar magrib datayi tazo ta tayarda sallah
Tana gamawa palo ta fito ta nufi qofar fita dan zuwa gurin s salma saidai tana kaiwa qofa ta tsaya takasa shiga sai kawai ta juyo tadawo tana zama a palon sultana na fitowa ta zauna tana cewa,
Yau bazaki gurin ammee bane?

Murmushi yaqe tayi cikin sanyi tace,
Karatu zanyi.

Satar kallonta ammyn tayi kafin tayi magana sukaji qamshinsa yashigo palon tareda sallamarda shikadai yaji abarsa.

Fuska ammy tasaki cikeda farin cikin ganinsa.

Itakam miqewa tayi riqeda tab dinta kanta asunkuye zata bar palon tana kawowa gurinsa kamar alamara sai tuntube
Tab din hannunta ta fadi
Sai kawai yatake ya wucewarsa batareda yanuna yasan da itaba bare tab dinta.

Cikeda mamaki ammy ke kallonsa tana kallon tab din da screen yayi mugun damage mamakinta meyasa ya taketa dan tanada tabbacin yaganta.

Rumanah kuwa tab din taqurawa ido sbd yanayin takawar ya nuna kamar yasan da ita to meyasa?

Kodai laifi tayi?

Sanin babu ikon tambaya ko sanin dalili yasata duqa ta dauka ta wuce dakinta.

Kallonsa ammy tayi ganin baimasan mesukeyiba yasa tace,
Maheer baka lura ka take tab din karatun rumanah ba?

'Dagowa yayi ya zuba mata idanuwansa dasukai wani launi ko bude bakinsa yakasa sai kawai ya miqe yace,
Zan shige saida safe ammy.

Baki sake tasake kallonsa tace,
Maheer akwai abinda ke damunka?

You don't seems alright,
Kodai sultan ne?

Ko abinci bazakaciba?

Juyowa yayi yakalleta daqyar ya iya cewa,
Gud night ammy.

Wucewa yayi yabar palon yanufi part din dayake nasa a masarautar tun kafin yayi aure.

Bayansa ammy tabi da kallo cikin fargabar abinda yake damunsa.

Zaune take gaban mirror ta qurawa tab din ido sbd ko kunnuwa batayiba alamudai sun nuna ta tashi daga aiki kwata kwata.

Hawaye ne taji sun ciko fararen idanuwanta sbd zuciyarta datake zargin laifi tai masa qila.

Aje tab din tayi ta rufe fuskarta da hannuwanta biyu tanajin damuwar hakan duk da tasan batai laifin komaiba saidai tana bawa kanta laifin koda acikin rashin sani tayisa.

Ammy ce tashigo dakin taganta ahaka
To itakuma wannan lafiya?

Cikin mamaki da kulawa tace,
Rumanah meya sameki?

Sunkuyar dakanta tayi tareda girgiza kai murya na rawa tace,
Bakomai.

Bakomai kike kuka rumanah?

Dole akwai wani Abu kitashi kije kikaiwa maheer abinci ina jiranki idan kindawo mayi magana amma kam dole da wani abin.

Tashi tayi asanyaye tareda gyara zaman hular doguwar rigarta ta fito jiki asanyaye.

A babban tray ta jera masa komai ta fito ta wuce zuciyarta cikeda fargaba jikinta har wata rawar tsoro yakeyi amma haka ta nufi inda akace nan ne part dinsa.

Batai knocking qofar palo ba ta murda tashiga sbd sanin baya palo a wannan lokacin,
Kyawu da tsarin palon takalla koina qamshinsa yakeyi da sanyin AC ta nufi qofar bedroom tayi knocking ahankali tareda budewa sanin bazai taba maganaba ko bada ixnin shiga.

Baya dakin shiyasa ta nufi table din dakin kai tsaye ta ajiye tray din tareda bude fridge dindake dakin ta dauko ruwa tazo ta ajiye masa tana juyowa sukai ido hudu yana tsaye bayanta jikinsa ba kaya dagashi sai towel fari wannan karon dogon gashinsa asake ya zuba mata idanuwansa ya kafeta dasu yanda ko motsi zaiyi mata wuya.

Rudewa tayi tarasa yanda zatayi sbd hakanma yasake tabbarda akwai abinda tayi sai kawai hawaye suka ciko idanuwanta suka fara gangarowa ta durqusa qasa ta sunkuyar dakai cikin muryar kukan datake riqewa tace,
Yi hakuri ina neman afuwar laifina.......sai kawai kuka Mara sauri ya sake mata.

Sosai takeyin kukan yana tsaye yana kallonta kamar mai kallon wani show.

Matsota yafara yi tayi saurin rintse ido harya qaraso gabanta ya riqo hannunta na dama ya miqar da ita tareda kallon cikin idonta dahar lokacin ke tsiyayar hawaye yamaida kallonsa ga hannunta da dama dake cikin nasa yayi masa muguwar matsar da azaba tasata kallon cikin idonsa da sauri
Idonsa ras cikin nata yake kallonta batareda yasake mata hannunba.

Sabbin hawaye ne suka gangaro mata ahankali daqyar tasake furta,
kayi hakuri..

Sassauta riqon hannunta yayi tareda matsawa baya kadan yana kallon hawayenta dake tsiyaya.

Da hannunsa daya ya shafosu yakalla ya matsota jikinsa sosai yakai bakinsa saitin kunnenta can qasan maqoshi yace,
Kinyi kama da albinon malaminki da wannan hawayen.

Dagowa tayi takallesa ko qyaftawa batayi tana tsaida hawayenta kamar bashi yayi maganarba yaqara qasa da muryarsa yace,
Kallon fa?

Sauke idanuwanta tayi cikeda kunya tanason zamewa ta fice amma ba hanya sbd ya matseta jikin bango.

Cikeda mamaki da wani irin kallo dake nuna annurin fuskarsa yake kallon kunyarta data bayyana fili
Yasa hannu ya juyo da fuskarta tayi saurin rufe ido fuskarta dake fidda wani kyallin Hutu yaqurawa ido har zuwa qaramin bakinta dake qirjinta dake gugar nasa ya sake matseta yana zame band 'din dake daureda dogon gashinta
Gashinta ya zubo har gefen fuskarta
Yasa hannu ahankali ya janye tareda yasake tura kansa cikin wuyanta murya a shaqe yace,
Bazaki zubamin abincin ba saiya huce and I don't eat hutaccen abinci.

Saurin dagowa tayi takallesa saidai ko juyowa baiyiba ya qarasa kujera ya zauna
Akaro na farko da wani sahirtaccen murmushi ya kufce mata Wanda yasa kumatunta lotsawa akan idonsa ya dauke gira 'daya tareda dauke kai.

Qarasowa tayi ta duqa ta bude masa tareda daukar ruwan data dauko ta mayar fridge din dakin ta canzo masu sanyi sbd wainnan sun huce.

Wayarsace ahannunsa yana duba wani saqo kamar bashine yasata aikinba.

Zuba masa ruwan tayi a glass cup ta aje masa ya miqa hannu yakarba ya kurba kadan ya dago yakalleta tayi saurin sauke kai.

Cikin nutsuwa yaci abincin kadan kafin yace,
I need a coffee.

Kwashe kayan tayi tafice dasu cikin sa'a ammy bata palo tashiga kicin ta aje ta hado masa coffee takoma.

Yana toilet kodata shiga yana waya ta ajiye tray din ta dauki cup din ta miqa masa yana karba ya hada da hannunta ya riqe yana cigaba da wayarsa kuma bai kalli fuskarta ba.

Kan jikinsa ya fixgota ta zauna tacigaba da wayarsa yana sipping coffee dinsa hankali kwance harya gama wayar ya aje coffee din tareda kallonta yace,
Me kike jira haryanxu?

Da sauri takallesa cikeda mamaki ganin har lokacin matse take ajikinsa ko hanyar tashi babu.

Sunkuyar dakai tayi cikin rawar murya kamar zatayi kuka tace,
Zantashi.....

Sai hawaye.

Lumshe lazy eyes dinsa yayi yabude yana bin hawayenta da kallo a kasalance ya daga hannu ya shafo hawayen yana tattara gashin kanta daya barbaje.

Sakin kukan datake riqewa tayi batareda sanin dalilin yinsaba,
Zagaya hannuwansa bayanta yayi ya rungumeta tareda rufe idanuwansa.

Lafewa tayi tana qoqarin goge hawayenta ya miqar da ita tareda zame mata doguwar rigar sama yabarta data ciki ya cirata sama ya suka nufi gadonsa yazura hannu ya kashe lamps din dakin tareda dora hannunsa akan siririyar rigarta ya zame.

Kallon agogo ammy tayi taga qarfe goma sha biyu harda rabi tasake fitowa amma Sam rumanah batanan ta aika gurin s salma batacan Sam hankalinta yaqi kwanciya sbd ganin kukanda rumanah din keyi dazu.

Hakanan ta hakura takwanta tareda mamakin maheer bama na rumanar ba.
#mamuhgee.
[7/29, 9:29 PM] Hauwa'u inna: *_TARAYYA_*
_wattpad@mamuhgee_
_Haske writers association
*24*
Not edited
Sheraton bamako hotel forth floor room 302 shine dakinsa da ako yaushe yake sauka idan yana qasar.

Babban suite ne dayaji tsari irin na rayuwar dayakeso akoda yaushe.

Zama tayi a darare kan sofa tareda aje handbag dinta tana kallon tsarin dakin.

Tun kafin ya isa yayi musu shopping kayan buqatarsu shiyasa yakalli agogon hannunsa yana 6ata fuska .

Knocking akayi ahankali sbd gudun kar ayi disturbing dinsu
Ga mamakinta ganin tayi ya miqe ya nufi qofar bayan tasan abaya budewa kowa qofa idan kagaji da knocking ne kashigo koka jira amma saigashi yatashi yaje yabude kuma hannu kawai yasa yakarba ya rufe qofar ya aje kan gado yafara 6alle ma6allan rigarsa.

Sauke kai tayi ganin murdadden jikinsa yafara bayyana
Yana gama tubewa ya nufi toilet.

Ya jima yana wanka kafin yafito yabude kayan ya dauki brush da toothpaste yakoma yayo brush yana dawowa ya fitarda turarrukansa da yayi shopping yayi shirin bacci bayan ya fitarda fararen kayan baccin daya siya yasaka ya fidda wayarsa yakira suhailat datun dazu take kiransa.

Miqewa tayi itama tashiga toilet tayo wanka ta fito daureda towel gashinta daure tsakiyar kai sbd karya jiqe gurin wanka.

Duk wani nauyi da kunyar duniya jitake kamar suna kanta sbd mayen kallon daya tsareta dashi tun fitowarta kuma lokacin waya yakeyi da suhailat.

Rigar bacci tagani kan kujerar gaban mirror tadan juyo takallesa ya dauke gira 'daya yana cigaba da wayarsa.

Da mamaki take kallon turaren Prada royal pink for women da shine turarenta,
Ya akayi yasan sunan turaren datake shafawa gashi tamazo da nata suna cikin handbag.

Wanda ya siyo din ta shafa ta dauki rigar tadaga batai mamakin ganin yanayin rigarba datafi kama da babu sbd tun a mineelik da ake sakata sakasu tasaba dasu.

Daga zaunen ya miqa mata hannu na musu tazo ya jawota ya ajeta kan cinyarsa ya zare ribbon 'dinda ke 'daureda gashinta gashin ya zuba yacigaba da wayarsa da suhailat yana cusa hannunsa cikin gashinta zuwa wuyan rigarta.

Cikin nutsuwa suhailat tace,
Zan kiraka gobe insha Allah gud night.

Aje wayar tayi tareda rintse ido da qarfi hawayen dasuka ciko mata suka gangaro kan fuskarta sbd yanayin yanda maganarsa ke fita qasa sosai ta tabbarda akwai abinda yakeyi da matarsa dan mum ta sanarda ita da rumanah yaje.

Share hawayenta tayi tareda miqewa ta nufi 'dakin yaranta takwanta kusada fammah tareda jawota jikinta a hankali tace,
Ya Allah kabani ikon juriya da adauke kai kan abinda bazai shiga haqqinaba nima kodan karna barwa 'yayana abin takaici da kunya.

Rumanah dake lafe jikinsa ta 'dago takalli fuskarta dake kallonta qasa qasa da murya yace,
Kinsa matata ta ajemin waya for the first time banine na aje mata ba.

Wani irin lumshe idanu tayi Wanda yasashi kafeta da ido kafin yakai bakinsa kunnenta qasa qasa yace,
Are you trying to seduce me da wannan idon?
Chapter 20 · 0% Book details