Sashe 19
Tarayya Part One Complete Hausa Novel · about 8 min read
Qofar ta kalla bayan ya wuce ta rintse idanuwanta ahankali tareda fitarda numfashi ahankali kafin ta miqe ta taka daqyar ta dauki doguwar rigarta ta zura kan rigar baccinta ta nufi qofa tana qoqarin daidaita tafiyarta duk da zafinda takeji.
Saukowa taringayi ahankali harta gama saukowa ta nufi dakinta
Tana kaiwa tsakiyar palon tayi ido hudu da sultana zaune ta zuba mata ido cikeda mamaki.
Sunkuyar dakai tayi idanuwanta na cikowa da hawayen tsananin kunya da nauyin ammyn.
Juyowa sultana tayi ahankali cikeda mamaki takalli inda yake zaune yayi tamkar baimasan da isowar rumanah dinba ya danna kira asibiti.
Kasa maida kallonta tayi kan rumanah sai kawai ta miqe ta nufi dining.
Jiki sanyaye ta qarasa daki tafada toilet sai kawai tasaki siririn kukan kunya da ciwon da jikinta ke mata.
Wanka tayi da ruwan zafi sosai kafin ta lallaba ta fito tayi sallah ta shirya cikin sauri sauri ta fito kai sunkuye.
Kallonta ammy tayi cikin sanyin murya tace,
Kizo kiyi breakfast mutafi munyi latti.
Kai ta daga ta nufi kicin a darare ammy tabita da sabon kallo harta shige tasake juyowa takalli maheer dako gefensu yaqi kallo,
Mamakin duniya ne ya taru akanta gashi Sam ko fuskarda zatai masa wata magana yaqi bata bare taji makomar rumanah daga garesa.
Daqyar ta iya shan tea da biscuit ta fito daidainan Carolina tagama fitar mata da kayanta zuwa mota.
Kodata fito ammy ta nufi waje sbd sunyi latti sosai dan haka ba kowa a palon saishi azaune yana waya
Qofa ta nufa riqeda qaramar jakarta tana qoqarin wucesa yakara mata qafa ta kwashi wani mugun tuntube ta fada masa ya aje wayar hannunsa tana qoqarin tashi ya matseta da hannunsa daya tareda kallon cikin idonta ya dauke gira daya cikin izza yace,
Ance kitafi ne?
Kallonsa tayi da sauri kafin ta Girgiza kai.
Hannunta yakamo yasaka mata wata Leda tareda sakinta ya miqe yafita batareda ya waiwayo ba.
Bayansa tabi da kallo kafin ta dawo da idonta kan ledar daya saka ahannunta taga magungunane
Sake dagowa tayi takalli qofar fuskarta da mamaki.
Qofa ta nufa ta fito tana sake damqe ledar maganin a hannunta ta nufi motar da tagansu.
Driver ne zai kaisu dan haka dukkaninsu baya suka shiga yana tsaye yana kallonsu aka tayarda motar
Dagowa tayi ahankali ta saci kallon gefensa idonsu yashiga cikin na juna tayi saurin sauke kai tareda sake damqe ledar maganin daya bata.
Suna fita yafidda key ya nufi hospital sbd tuni suhailat ta damu dayazo daukarta
Shikuma ji yake da bayada aiki sosai ammynsa xaibi Libya sbd damuwar sultan yasan haryanxu tana ranta.
Yana isa asibitin yahadu da doctor dinda ke kula da suhailat sukayi magana da sauran rubuce rubuce suka nufo gida.
Tun ahanya takeson tambayarsa maganar rumanah saidai zuciyarta na gargadin bakinta da furtawa sbd sanin bazaiso maganarba karma ta bata masa rai da kiran sunan an aura masa baiwa.
Suna isa gida ta tararda komai fes tashiga dakinta tayi wanka ta shirya cikin simple kaya marasa nauyi ta nufi bedroom dinsa.
Cikeda mamaki ta tsaya tsakiyar dakin tana sake bude hancinta sbd dakin wani qamshi yakeyi na dabam Wanda ta tabbar bana maheer bane.
Zama tayi bakin gado ta rafka taguma tana wasi wasin tunani
Ganin qamshin zai iya buga zuciyarta yasa ta miqe tabar dakin sbd dama bayanan yana ajeta ya koma asibiti.
Sun isa Libya da qarfe shida na yamma motocin masarautar mahaifanta sukazo daukarsu cikin qanqanin lokaci suka isa babbar masarautar mai tarin dukiya da adalci
Masarautar mineelik saidai ta nuna musu girma da iko tareda dukiya wadda ta hada data mulkin mutanen da ba'a gani sbd dukiyarsu nada alaqa data mutanen daba nasuba amma a fagen adalci da qaunar talakawa da basu yanci basu kamosu ba ko kadan.
Saida suka sauka fadar sultan jalaluddeen suka gaidashi tareda gabatarda rumanah amatsayin matar yarima maheer yasawa aure albarka kafin suka isa babban sashen sarauniya salma matar sultan jalaluddeen mahaifiyar sultana zaarah.
Sosai aka hau hidimarsu duk da manyanci daya kama sarauniya salma tayi farin ciki da murna sosai ganin rumanah amatsayin matar yarima maheer sbd lurada nutsuwarta.
Sashe guda aka ware musu acikin part din sarauniya salma mai daukeda palo da bedrooms guda biyu dasukaji gyaran tsadaddun decor.
A babban palon s salma sukaci abincin dare tareda ita kafin kowannensu ya nufi dakinsa.
Tubewa tayi tashiga wanka ta jima tana dumama jikinta kafin tafito ta shirya cikin kayan bacci tayi sallolinta harzata kwanta taje ta dauko ruwa tazauna bakin gado tareda fiddo maganin daya bata tasha takwanta cikin qanqanin lokaci bacci yayi gaba da ita.
Bacci tayi sosai mai dadi sbd gajiyardake jikinta bata farkaba sai bayan sallar asuba ta tashi tayo alwala tayi sallah tasake komawa ta kwanta.
Qarfe tara ta tashi tayi wanka tashirya tafito cikin doguwar riga black mai adon red sequence stones.
Dakin sultana ta nufa ta tararda ita tana waya tajira harta gama ta gaidata cikin girmamawa.
Cikeda kulawa sultana ta amsa tareda cewa,
Ya jikinki?
Shiru tayi takasa bata amsa sbd nauyi.
Shikenan tashi kije zansa afara kulawa dake harkiji sauki sosai sbd haryanxu jikinki bai nuna kin warkeba.
Kamar munafuka ta fito sbd tsananin kunya da nauyin ammyn datake ji musamman data riga tasan tabbas ammy tasan meya faru tsakaninsu.
Kodataje gaida s salma acan tayi breakfast dinta har akazo kiranta ta tashi tabisu tanaji tana gani aka hau gyaranta da gashinta kullum cikin sakata cikin ruwan zafi da wasu irin magunguna ake kuma kullum sai anbata 'danyar madara tasha cup daya da safe gashi aiki ko daya anan batayi saidai idan taji jikinta yayi tsami da yawa taje dakin sultana tahau aikin gyara mata kayan wardrobe da wankin toilet duk da akwai masuyi amma wani lokacin tafison tanayi.
Satinsu biyu tasaba sosai da kowa,
Sultana mamakin rumanah takeyi bata taba tunanin zataga rumanah tasake hakaba shiyasa ba bata lokaci tasa aka dauko wani Mexican malamin wata collage yana zuwa koya mata karatu.
Sosai tayi fresh abinta ta dire dakyau kyawunta tuni yaqarasa bayyana sbd Hutu da gyaran da ake mata kamar kullum.
Wanka tafito ta shirya cikin kayan bacci riga da wando tazauna bakin gado tareda jawo bedside drawer taqurawa ledar da kullum saita kalla ido tareda lumshe fararen idanuwanta tanajin hannunsa ajikinta lokacinda zai saka mata ledar ahannu.
Sake lumshe ido tayi tareda zamewa ta kwanta ahankali tana jin wata irin kasala.
Sosai ta warke takoma tamkar batai ciwoba sun cigaba da rayuwarsu kamar da tuni tafara zuwa aikinta hankalinta kwance sbd ganin maheer yamanta da wata maganar aure da aka daura masa,
Abinda yake damunta yake hana mata bacci wani bi 'dayane,
Maheer Sam bai cika nemantaba kamar da ataqaicema yarage sha'awa sosai sbd wasu lokutan tana lure da inda baya taba mata da yanxu yana tabawa saidai ita Sam bataso musamman nonuwanta Sam batason yana yawan tabasu sbd batason suyi laushi da wuri gashi dama shayarwa tafara lausar mata dasu.
Ada Sam basu damesaba shima amma yanxu yanason tabawa tarasa meyasa hakan.
Wannan karon sbd ganin uwar datasha dakuma tiyatar da akai mata yasa tayi allurar shekara biyu sbd tahuta mahaifarta tasake qwari.
Fitowarsa wanka kenan daureda towel wayarsa tayi ringin yakalli wayar kamar bazai daukaba saikuma ya daga.
OK kawai yace ya aje wayar ya shirya cikin kayan shan iska ya sauka.
A palo ya tararda baqon nasa yadauki remote yana canza tasha yace,
Uhumm.
Gyara zama mutumin yayi cikin girmamawa yace,
U wanted to see me sir.
Batareda yakallesaba ya karbi coffee dinda suhailat ke miqo masa murya a dake yace,
I need a first-class vip ticket......
Kallonsa suhailat tayi da sauri cikin mamaki tace,
Zuwa ina?
Libya"""yafada kai tsaye yana sipping coffee dinsa idonsa nakan TV.
#mamuhge
[7/29, 9:29 PM] Hauwa'u inna: *_TARAYYA_*
_wattpad@mamuhgee_
_Haske writers association
*22*
Not edited
Da sabon mamaki tasake kallonsa,
Libya?
Amma baby mezakajeyi a Libya yanxu?
I mean is everything OK?......
Dakatawa yayi dashan coffee din ya ajiye tareda juyowa yakalli gefenta cikin izza yace,
Ammy na Libya kike tambayan mezanje yi acan?unbelievable.
Miqewa yayi yabar palon sbd bayason damuwa da tambayar dazeta iya bata ransa.
Bayansa tabi da kallo cikeda mamaki saidai batajin dadin tambayar datai masaba itama sbd mahaifiyarsa nacan baikamata ta tambayi mezaije yiba.
Miqewa tayi tabisa dan basa hkr saidai koda taje waya yakeyi haka ta zauna jiran yagama.
Zaune suke a qaramin palon baqin s salma itada Mr aarib suna karatu harsuka kammala ya kalleta cikin sakin fuska yace gobe bazai samu damar zuwa ba qila sbd yanasaran zaiyi tafiya idan baiyiba zaizo.
Gyada masa kai tayi cikin sakewar fuska ita suka fito kusan atare yana sake maimaita mata wasu English words daya koya mata itakuwa sbd ta sake fahimta bakinsa ta qurawa ido tana daga kai ahankali fuskarta asake sbd ba laifi sunsaba da Mr aarib.
Tab dinda ake mata karatu da ita ya miqa mata ta amsa tana murmushi tace,
Thank you.
Cikin jin dadi yace,
Ure welcm.
Juyawa yayi ya fice ta nufi qofar palon s salma na gaba tashiga har lokacin fuskarta daukeda murmushi tana shiga palon ta tsaya cak tareda juyawa da sauri sbd qamshin dataji yacika palon.
A fuskarsa idonta ya sauka yana zaune yana mgn da s salma gabanta yayi wani irin faduwa wani irin yanayi yashigeta na fargaba ko fuskar gaidasa bata ganiba ta hadiye wani yawun fargaba ta daga kafa daqyar ta isa gabansu kanta a sunkuye ta gaidasa batareda yakalletaba ya 'dan daga hannu
Juyawa tayi ta wuce sbd yau babu batun fira a gurin s salma.
Tana isa palonsu ammy na zaune tana kallon wani English program
Zama tayi tareda aje tab dinta tana cewa,
Ammy yace qila gobe bazaizoba.
Ammy na kallon TV tace,
Eh ai gwara karyazo yanxu yajira bayan kwana biyu tukuna sbd maheer dake qasar baku hadu a palon ammee ba?
Eh yana can.
Murmushi tasaki tareda kallonta sbd jin amsar dan batai cikakkiyar kama da tambayar datai mata ba
Maida kallonta tayi kan TV tana cewa,
To yayi kyau.
Miqewa tayi ta nufi kicin jikinta duk ya mutu tasha ruwa ta tsaya jikin fridge tsawon mintuna tana sauraron bugun zuciyarta daya canza yaqi daidaituwa tun lokacinda idonta ya sauka akansa.