← Book details Tarayya Part One Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 51

Sashe 26

Tarayya Part One Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bazata iya tsayawa takurataba dama sbd fita haqqin su biyun ne yasa tace taje dan haka babu wata damuwa tace,
Shikenan kibawa Carolina din takai masa.

Ta juyawarta tabar gurin itama rumanah dakinta takoma ta kwanta.

Juyawa yayi dakinsa yana zuwa ya zauna ransa amasifar 6ace.

Kiran suhailat ne yashigo wayarsa da farko bai dagaba saidata sake kira ya daga
Cikin kulawa tace,
Sorry baby I......bata qarasaba yace,
I need a coffee.

Ajiyar zuciya tasaki kafin tace,
Kitchen taje tasaka Carolina ta 'dora mata tana gamawa ta zubo masa a coffee cup ta nufi dakinsa.

Tana shiga taqarasa jikinsa ta zauna tareda miqa masa yakarba yafara sha yana duba saqo a wayarsa koda yagama yamiqa mata cup din ta ajiye kan table yace,
Ruwa.

Tashi tayi taje ta dauko masa yasha ta karba ta ajiye tareda komawa jikinsa tana cewa,
Baby are you ok?I mean you......jawota jikinsa yayi ya rungume tareda sakin ajiyar zuciya sbd jin 6acin ransa ya ragu sbd 'yar kulawar data nuna masa.

Murmushin jin dadi tasaki tana cewa,
Ok ok I got it,you're missing me right?

Wani irin murmushi yasakar mata sbd girma da ko yaushe take qarawa a idanuwansa dan yasan tana fadane dan tabawa kanta matsayi dakanta idanma bai bataba sbd ta cirewa kanta damuwa bayan shi yana iya hango damuwar a idanuwanta.

'Daga kai yayi tareda matso da fuskarta tasa yana goga hancinsu yace,
I always missed this sweet voice of mrs m.a shams idan bata kusa.

Dariyar jin dadi tayi soyayyarsa naqara shigarta ya hade bakinsu yana zura hannunsa cikin rigarta ta riqe hannun tana daria tace,
Heyy kana sakani waiwayi plsss.

Daka tawa yayi yana kallonta
Tayi dariya tareda maida bakinta kan nasa ba musu yasake matseta jikinsa yana shafata daganan ya dauketa suka koma kan gado.

Kasa bacci tayi sbd tunanin baici abincinba ta tashi zaune tareda saukowa gadon ta nufi qofa ta fita taje
dining ta dauki abincin datasan dominsa akayi taje kitchen tayi warming dinsa kafin ta jero a tray tareda komawa daki ta canxa riga zuwa doguwar riga mara hannu da wani sahirtattan qamshi ta dauka ta nufi saman.

Kai tsaye ta bude qofar palon tashiga ta nufi qofar bedroom dinsa tayi knocking ahankali.

Shiru babu alamar za'a bude tasake knocking lokacin suhailat ta taso daqyar daureda towel dinsa sbd bazata iya mayarda kayanta batai wankaba.

Cikin muryar gajiya tace,
Carolina is that you?

Muguwar faduwa gaban rumanah yayi
Tray din hannunta yafara rawa tayi saurin ajewa kan table din palon ta juya salin alin tabaro saman tadawo dakinta
Tana zuwa ta kwanta tana adduar bacci sbd sotake yayi gaggawar daukarta batareda zuciyarta tasamu damar wani wahalallen tunani ba.

Ita kuwa suhailat najin shiru jikinta yabata rumanah ce takasa budewa ta juya sbd babu dadi tabude mata qofa a wannan yanayin datake ciki.
#mamuhgee
#vote and follow pls.
[7/29, 9:29 PM] Hauwa'u inna: *_TARAYYA_*
_wattpad@mamuhgee_
_Haske writers association
*27*
Aje basket din hannunta tayi tana sake qaqalo murmushi tace,
Ashe kece babu lafiya baby baifadaminba kawai yafadamin numbern dakin ne,
Sannu ya jiki?

'Daga kai tayi ahankali tana cewa,
Alhmdllh.

Shiru dukkaninsu sukayi babu wacce numfashinta bai fita da sauri sbd ganin 'yar uwarta.

Suhailat cikin jikin rumanah din take satar kallo dan kuwa batasan haka take kishin mijintaba saidataga cikin dan kuwa Allah ne kadai yasan irin ciwo da radadin datakeji axuciyarta saidai tana qoqarin fincikewa sbd batason zubarwa da kanta qima a gurin mijinta da 'yayanta harma da rumanar datake kishiyarta.

Rumanah kuwa jitayi duk atakure take da wanzuwar suhailat din gashi nurse tagama abinda takeyi ta fice.

Hakanan takejin bata iya kallonta sosai sbd ganin take zuciyarta da shaidan zasu hasaso mata maheer atareda suhailat din Wanda hakan na matuqar girgiza zuciyarta.

Cikin kulawa suhailat ta miqe ta bude basket din ta hada mata black honey tea sai pancakes da toasted chicken datai laushi sosai ta zuba matasu a plate tareda aje matasu yanda zata iya ci.

Cikin sanyin murya rumanah tace,
Nagode amma inaso zanshiga toilet....

Wayar suhailat dince tayi ringing ta sauka da sauri sbd mum 'dintace batareda taji mai rumanah din ke fadaba ta fita dan amsa wayar.

Ganin ta fita yasa rumanah sauke qafafunta qasa ahankali ta sauko ta nufi toilet din dake dakin ahankali sbd jiri.

Tana kaiwa tsakiyar dakin wani irin jiri ya dibeta daidai shigowarsa dakin.

Saida tajita jikinsa tayi saurin sakin ajiyar zuciya sbd ta sadaqarda cikinta yagama zubewa idan ta fadi.

Bude idanuwanta data rintse tayi takallesa cikin fargaba sbd ganin kallon dayake mata murya na rawa tace,
Toilet zanshiga.

Yanda ya dauke gira daya yasa tasan menene azuciyarsa tayi qasa dakai cikin tsananin sanyin murya tace,
Yi hakuri bansan zan.....

Just shut up"""yafada yana daukarta gaba 'daya ya bude toilet din suka shige.

Sauketa yayi ahankali kamar kwai
Ta dago takalli fuskarsa taga ba wasa tasaki 6oyayyan murmushi cikin zuciyarta tana cewa,
Ko fushi kyau yake masa.

Brush ya miqa mata ta karba tayi tana kallonsa sbd kallonsa yanxu matuqar nishadi da nutsuwa yake bata tana gamawa ya miqa mata towel tareda jawota jikinsa yazare mata kayan jikinta itadai ido kawai take binsa dashi sbd yau ko ta6insa nutsuwa yake bata.

Da yake shower ce bai shigaba ita kadai tashiga tayi wankan shikuma yana tsaye gaban mirror yana goge inda rigarsa ta baci da ruwan allurar dayaje yiwa wani patient kafin yashigo dakin.

Tana gama wankan ta dauki towel ta daura tareda zare shower cap din kanta ta tsaya gaban madubin da yake dubawa tana fuskantarsa.

Wasu kayan yasanya mata saidai bada bra ba duk saiyaji ransa yabaci da yanda kayan patients din sukai mata kyau amma bai nunaba yasake gyara mata gashinta ya dauketa suka fito tana kallonsa gira 'daya ya dauke yace,
Wannan kallon fa matata tana nan so be carefull bata hadani da komaiba.

Murmushi daya bayyana fararen haqoranta tasaki tareda sake qanqamesa tana fitarda sautin murmushinta ahankali
shima murmushin gefen baki yasaki suna kawowa tsakiyar dakin sukai ido hudu da suhailat dake zaune tayi musu kallo 'daya ta dauke kai tana qoqarin danna kira awayarta.

Saurin saukowa jikinsa rumanah tayi sbd taji nauyin suhailat din sosai koba komai ka girmama mai girmama kansa ta zauna bakin gado tana suuke kanta qasa.

Kallo 'daya yayiwa suhailat yagano halinda take ciki yaji tabasa mugun tausayi sbd baisan lokacinda ta dauka azauneba gashi sun dade aciki gashi qila batasan yana cikiba.

Hannu yakai yakamo hannunta tareda miqar da ita ya matsota gabansa yana kallon cikin idonta datake qoqarin 6oye halinda take ciki cikin kulawa yace,
Are you ok?

Kai ta 'daga masa batareda yakallesaba
Yayi kissing forehead dinta yace,
I will be in my office""yasa kai yafice yabarsu.

Jawo abincin rumanah tayi tafara ci hannunta na rawa sbd rawar da zuciyarta keyi.

Suhailat ma batareda takalli fuskar rumanah din ba tace,
Zantafi office am getting late Allah yasauwaqa.

Tana gama fada ta dauki handbag dinta ta fice hawayen datake riqewa suka gangaro mata ko office dinsa bata biyaba ta wucewarta saidata isa office dinta ta rufe siririn kuka ya balle mata amma dannesa tashigayi sbd bataga dalilin kukanba tunda dama tasan tanada kishiya meye abin jin zafi dan taganta da ciki bayan itama Allah yabata nata 'yayan ba juya yayitaba.

Saidata samu nutsuwa tayi masa text tace ta wuce office and she's very late so shiyasa bata biyo office dinsaba.

Tana ficewa rumanah ta aje breakfast din sbd dama turawa kawai takeyi.

Yana gama karanta text dinta ya aje wayar tareda lumshe fararen oily eyes dinsa.

Yinin ranar dukkaninsu a darare sukayisa sbd kowanne da abinda ya maqalewa zuciyarsa.

Baibar asibitin ba yau sai qarfe goma na dare lokacinda rumanah tayi bacci kenan.

Koda yakoma gida suhailat bata nuna damuwar komaiba a fuskarta itada 'yayanta su maqalqalesa suna masa oyoyo
Yayo wanka bai sauko cin abinciba sbd yaci pizza tareda rumanah a asibiti.

Koda suhailat taji cewar yayi dinner murmushi kawai tayi tace,
Ok bari nacewa Carolina tasaka a fridge.

Kodata dawo dakin yana kwance wayarsa a kunnensa yana magana da antynsa wadda yake biwa tana qara basa haquri akan abinda yafaru shidai kunnuwane kawai nasa baya iya zuba dogon zance.

Kwantawa tayi ajikinsa tareda rungumesa ta rufe ido alamar bacci
Yayi mamaki sbd basu cika kwana daki dayaba koman dare wani lokacin dakinta take komawa ta kwana.

Koda yagama wayar tayi bacci yakalli fuskarta kafin ya lumshe idanuwa fuskar rumanah daya baro tana barci tafado masa yasake rungume suhailat ajikinsa yana kamar rumanah ce ajikin nasa.

Washe gari ma tare sukaje asibitin saidai ko zama batayiba gaisawa kawai sukayi ta wuce gurin aikinta sbd ganin irin kallon da maheer kewa rumanah sbd sai yanxu cikinta yafito dakyau sbd kayan da aka canxa mata sunso kamata saikuma basu kama 'dinba.

Bayan wucewar suhailat nurse 'din dake kula da ita ta fita sbd idan yashigo fita sukeyi.

Kallon 'dan cikinta yayi batareda ya amsa gaisuwartaba ya dauki file dinta yafara dubawa.

Qamshinsa daya cika dakin ta shaqa tana lumshe ido cikeda qaunarsa mai zafi dake cin zuciyarta.

Yana gama dubawa ya kalleta a miskilance yace,
Did you bleed today?

Girgiza masa kai tayi kala kallonsa ya juya yafice baisake cewa komaiba.

Numfashi tasauke a sanyaye ta zame takwanta.

Kwananta biyar a asibitin akayi discharging dinta tunda suka kamo hanyar gida numfashinta ke fita da qarfi
Jin tayi tafison komawa Libya gurin ammy hankalinta zaifi kwanciya acan.

Suhailat ma tunda tasan zasu dawo gida anyi discharging dinta jikinta yake sanyaye.

Carolina tagyarawa rumanah dakinta tun na farko sosai.

Qarfe goma sha biyu suka iso tareda driver sbd shi theatre zaishiga.

Koda suka iso gidan tuni kayanta dayayi shopping online suka iso har ankai mata dakinta
Itadai suhailat tana bedroom dinta sbd ita bata iya munafurciba arayuwarta bazata iya tsayawa tana rawar jiki akan abinda tasan ba haka bane cikin zuciyarta,
Abinda tasani shine bazata qi rumanah ba bakuma zatai munafurcin nuna mata soyayyar qaryaba saidai zata mutumta ba sbd mijintane ya ajiyeta kuma as along as babu Wanda ya wulaqanta wani acikinsu to zasu zauna lafiya babu takura saidai batai alqawarin ringa zaunawa suna fira tareba gwaradai nesa nesa da juna saisunfi mutunta junansu.
Chapter 26 · 0% Book details