← Book details Tarayya Part One Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 51

Sashe 11

Tarayya Part One Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sheshekar kukane yadauki hankalin sultana da jakadiya cikin sanyin jiki suka dubi qofar cikeda tausayawa Jakadiya tace,
Sultana amincewa kibada rumanah shine zai sanyaya mata qunci da damuwar datake ciki na
uwar riqonta sbd natabbarda shine zai nesantata daga uquba da tsangwamarta.,
Koba komai wannan itace iya mafi girman soyayyar dazakiyi mata ta amince mata ta zama mai kawarwa da 'danki sha'awarsa.,
Har abada rumanah bazata ta6a wulaqantaba idan ta hada shimfida da yarima koda kuwa bata haihuba,
Ki qara dubawa sultana.

Shiru tayi tareda rintse idanuwanta cikin rashin madafa da shawara sbd bata fatar rumanah tazama baiwarda za'a riqa kwana da ita tana haihuwa ana kar6e 'yayan daga qarshe kuma asallameta tayi nesa da qasar bazata qara kusanto 'yayantaba.

Wani 6angaren kuma batada wata mafita ko ba6in daya wuce rumanah din Dan itace taga tafi cancanta da jikokinta su fito daga gareta koba namiji bane itadai gwara ace rumanah 'dince ta haifar matasu ba wata baiwarba
Saidai zuciyarta na ganin kamar bata yiwa asma'unta adalcin zaman amincin dasukayiba
Hakama zuciyarta na hango mata wani irin rikici da tashin hankali agaba akan hakan.

Miqewa tayi cikeda damuwa da fargabar rashin madafa,
Masarautarsu has been cursed tun shekara da shekarun dasuka shude,
Duk wani abin alkhairi baya 'dorewa a masarautar,
Sarakunansu hankalinsu da tausayinsu tareda imaninsu yana gushewa daga lokacinda suka hau kujerar mulkin basa da hukunci saina yankewa duk Wanda yayi laifi kisa,
Hannuwa da qafafun sarakunansu na jiqene da jinin mutane,
Sarakunansu are posses,
Duk Wanda ya alaqantu da kujerar mulkin mineelik sai cursed din yashafesa sbd mugun abin daga kujerar yake.,
Jakadiya kinsan me zamantowa uwa ga magajin masarautar nan yake nufi,
Maheer yaqi karbar sunan magajin sarkine sbd kubutardani daga zamtowa cikin makusanta kujerar mulkin,
Yaqi karbar sunan ne sbd kubutarda kansa daga jiqa likkafaninsa da kabarinsa da jinin bayin Allah,
Kinfi kowa sanin tarihin masarautar nan da abinda ke bibiyarta shine zamu 'dauko yarinyar da batada hakkin komai musakata da abinda zata Haifa?

Rumanah kwaqwalwarta bazata iya daukar masifun dazasu biyo bayan zamtowarta mahaifiyar magajin masarautar nanba,
Idan muka sakata cikin wannan masifar muka jiqa hannuwanta da jinin mutane bamuyi mata adalciba,
'Dana yakubatardani da kansa daga wannan masifar shine zamu saka yarinya aciki bayan batasan me hakan ke nufiba.,
Sultan alamarin yariga ya dade shigarsa ayanxu koda 'Dan cikinsa baya tunani biyu kafin ya yanke musu hukuncin kisa,
Masifar tariga tashiga jikinsa bayaji baya gani rashin bin kowane irin umarninsa daidai yakeda fitar ranka....

Cikeda sanyin jiki Jakadiya tace,
Hakan zaki tuna kiyi hkr kibada rumanah idan ta haihu mu tseratarda ita ta hanyar turata nesa inda har abada bazata sake kawo kanta nanba wannan shixai mata Katanga daga zamowa MINEELIK-ASSULTANAH TA BIYU.

Shiru sultana tayi cikeda tsananin tsoro da fargabar abinda suke shirin yi,.

Fitowar rumanah daga bedroom dinta yasasu juyawa qofar.

Sunkuyar dakanta tayi sbd fuskarta datayi jajir sbd kukandatayi.

Wani irin mugun sabon tausayinta yashiga sultana batasan lokacinda tajawota jikinta ta rumgumeba cikin wata irin sanyin murya tace,
Asma'u ki yafemin.

Rumanah kema karki qullaceni.

Batamaji abinda ammyn kefadaba sbd kukanta daya dawo sabo tuntuni take Neman Wanda zai rarrasheta koda tsuntsune sbd mawuyacin halinda take ciki.

Jakadiya ma cikin tsananin tausayin rumanah din can qasan maqoshi tace,
Ki gafarceni rumanah amma rayuwarki ta birkice daga lokacinda kika haifi 'da namiji sbd qaunar danake yimiki ina miki fatar samun 'ya mace sbd kubuta daga muguwar tsinuwar dakebin makusanta kujerar masarautar mineelik.

Saida rumanah tayi kuka sosai Wanda hakanan yake zuwa takasa tsaidasa saidatayisa sosai kafin sultana ta 'dagota tareda kallon fuskarta tana maida hawayenta takalli jakadiya tareda 'daga mata kai ahankali.

Tasaki rumanah tayi bedroom dinta tanaji ajikinta haqqin rumanah bazai taba barinsuba.

Jiki amatuqar sanyaye ta juya ta fice Jakadiya tabita da kallon tausayi.

Tana zuwa dakinsu ta zauna bakin katifarta tareda rafka tagumi ta fada tunani.

Nuratu ce tashigo dakin tayi saurin isa gurin rumanah din kawai ta rungumeta Tana cewa,
Rumanah karki karaya kisake jajircewa kina haquri da mamani zata daina wata rana ko ance tayi bazatayiba.

Murmushi mai ciwo tasaki tareda kallon nuratu tace,
Mamani uwace banta6a riqeta arainaba.

Zuciyarki nada kyau rumanah Allah yabarki ahaka.

Murmushi tayi tace,
Ummana,abbanah da ammy bayansu kece mutum 'daya dana sani mai zuciya mai kyau Dan haka keda ammy Allah kuma yabarku ahaka.

Dariya sukayi suna qoqarin manta damuwar abinda yafaru.

Ahankali nuratu takalleta tace,
Rumanah kintuna lokacinda muke wasar riqe riqen gudu da ruwa a cup a dakin nan?

Murmushi tayi tareda kallon nuratu sbd wannan wasar itace abinda bazata ta6a mantawaba a quriciyarta,
Itace abinda nuratu ke tuna mata tasakata nishadi amma yau saitaji jikinta yayi sanyi tace,
Meyasa kika tuna wannan yanxu?

Haka kawai na tuna sbd bansaniba kobazamu sake samun damar tunawaba irin haka cikin jindadi.

Qurawa nuratu ido tayi zatayi magana aka shigo dakin.

Kallon qofa sukayi sukaga bayi kusan biyar atsaye saiga Jakadiya tashigo fuskarta a tamke babu alamar wasa takalli rumanah ta 'dauke kai ta juya Tana cewa,
Ku taho da ita zuwa part din gyara yanxunan.

Tana fada ta fice sbd kar tausayin rumanah yashigeta.

Kallon juna sukayi itada nuratu irin kallon da nuratu ke mata na tsananin tausayi yasa tayi saurin kallon qofar da jakadiya ta fita tayi kafin tasake kallon nuratu da tuni hawayen rabuwarsu ya gangaro mata.

Matsowa sukayi suka kama hannunta ko qwaqwaran motsi bata iyayi suka fice da ita.
#mamuhgee
[7/29, 9:29 PM] Hauwa'u inna: *_TARAYYA_*
_wattpad@mamuhgee_
_Haske writers association
*15*
Shiru sultan yayi yana sauraren bayanin Jakadiya ya lumshe idanuwansa ya bude,
Allah yataimaki sultan sarkin dayafi sarakunan qarninsa
Haryanxu baiwa rumanah bata zama cikakkiyar baiwa ga yarima ba""""""
Sune abinda Jakadiya tafada yasaka kallonta kafin cikin 6ayyanarda ikonsa yace,
Asanarwa yarima na sauke zaraah daga yau nabawa adama sultana kuma na dakatarda ita daga matsayinta na matar sultan harsai ranarda ya hada shimfida da baiwar.

Wani irin yawu Jakadiya ta hadiye cikeda rawar murya da girmamawa tace,
Angama da yardar Allah.

Tana fita aka isarda saqon ga yarima.

Aje cup 'din hannunsa yayi tareda rintse idanuwansa dasuka canza lokaci 'daya yabudesu yakalli ammynsa dake zaune taredashi a dining din palonta sunacin abinci.

Lumshe idanuwa sultana tayi ahankali tareda daukesu daga maheer daya qura mata sbd karya gano halinda tashiga ta miqe ahankali ta nufi hanyar bedroom dinta ya riqo hannunta tareda dawo da ita ya rungume ahankali.

Zamewa tayi takallesa tareda sakin murmushin dole cikin kulawa tace,
Karka takura kanka kayi abinda bakada ra'ayin so zan iya qarasa rayuwata akan wannan hukuncin nasa matuqar baka cikin takura maheer.....

Ahankali yabude baki cikeda kulawa yace,
It's okay ammy zanyi abinda yace ba buqatar ki damu da idan inaso ko banaso.

Bazaka kallesa ka gano 6acin ransa sbd kyakkyawar fuskarsa koyaushe bata nuna 6acin ransa amma Tsananin 6acin ran dayake ciki ayau yafi na kullum sbd sultan nason ganin iyakarsa koyaushe da mahaifiyarsa yake amfani Dan cimma buqatarsa garesa Dan yasan aduniyarsa babu kamar mahaifiyarsa agurinsa.

Yau wani irin sabon turare Jakadiya tasa aka kawo daga gidan turaren dake qasar Wanda yafi kowane turare dadin qamshi da hanawa duk namijin daya shiga hancinsa nutsuwa.

Farar rigar bacci yau aka zabo mata daga closet tasaka akaro na farko da aka hanata saka bra jakadiya dakanta ta bita koina da turaren ta feshe kafin suka fito.

Kamar koyaushe tana shiga Jakadiya ta juya ta fice daga part din.

Ahankali ta nufi gurin kwananta.

Hasken blue and red bulb ya gauraye dakin.

Cak ta tsaya tsakiyar dakin bugun zuciyarta na canxawa har kirjinta yana dagowa amma takasa juyowa.

Akaro na farko daya qurawa wata mace daba matarsaba lazy eyes dinsa,
Dogon wandon kayan baccine kawai ajikinsa fari qal mai matuqar santsi da laushi,
Wani irin murdadden namijine maji qarfi da kyawun gabbai sbd yawan yin geam ya bude duk wani qarfi na jikinsa.

Abayanta taji tsayuwarsa numfashinta ya tsananta fita hannuwanta da qafafunta suka fara rawa ta rintse ido.

Bayanta dayake fari qal yaqurawa ido da gashinta daya rufe wuyanta yanaji qamshinta na shigarsa yanason ta6o wani bangaren na sha'awarsa akaro na farko dataji muryarsa cikin wani irin taushi da aji yace,
Juyo.

Juyowa tayi ahankali tareda sunkuyar dakai tanajin wata irin muzanta na shigarta sbd tanajin kallon dayake bin jikinta dashi na qyama.

Kusan atare suka rintse ido suka bude sai acikin idanuwan junansu ta mayarda nata ta rufe da sauri tareda sunkuyar dakai.

'Dauke idonsa yayi tareda juya mata baya.

'Daga qafa tayi duk ilahirin jikinta rawa yakeyi zata wuce yariqo hannunta.

Barin jikinta numfashinta ke qoqarin yi tayi saurin Jan boyayyan numfashi yadawo jikinta saidai tuni qafafunta suka kasa riqeta ta zube qasa kan gwiwoyinta tana dafe qirjinta dake bugawa da qarfi haryana mata zafi.

Tattara numfashi tayi ta dafa table din dake tsakar dakin ta miqe har lokacin numfashinta bai daina fita da sauriba jikinta bai daina rawaba ta fuskacesa kanta na sunkuye.

Sake kafeta yayi akaro na biyu.

Hannu ya daga yamatso da ita sosai har kirjinsu na haduwa musamman idan numfashinta ya taso sosai qirjinsu ke haduwa.

Ahankali yadauke fararen idanuwansa daga fuskarta zuwa qirjinta dake gugar nasa.

Hannu yadaga ya dora akafadunta yana kallon idanuwanta dake rintse hawaye na qoqarin fitowa cikinsu.

Ahankali ya zame siririn hannun fingilalliyar rigar dake jikinta data gama bayyana komai na surar jikinta.

Zamewa rigar tayi tafadi qasa
Rintse idanuwansa yayi tareda ja baya ya juya tareda kallon jikinsa ganin tsikar jikar jikinsa ta tashi abinda baitaba yiba kenan tun tashinsa.

Bakin gadonsa ya isa ya zauna tareda zamewa ya kwanta rigingine ya rufe idanuwansa batareda yasake kallon sashen datake ba.

Daukar rigarta tayi tamayar jiki amatuqar sanayaye ta matsa inda take rabewa ta lafe hawaye suka gangaro mata ta goge ahankali tareda rufe ido.

Har asuba tayi babu Wanda yayi bacci acikinsu tanajin anyi kiran farko ta miqe ta nufi qofa tana fita Jakadiya na isowa taqare mata kallo bataga alamar komaiba tasaki ajiyar zuciya afili kafin tamiqa mata doguwar rigar tasa suka wuce.

Yau ko palon farko bai iya fitaba sbd bayason magana ko 'daya yau sultana ma saidai yayi mata massage
Fruits 'dinda ke cikin small fridge
Din bedroom din kawai ya iyasha Sam yau ko apatite bayada.
Chapter 11 · 0% Book details