← Book details Tarayya Part One Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 51

Sashe 38

Tarayya Part One Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gyara zama aqoob yayi cikin muryan da ta manyanta da tabbarda abinda zai fada yace,
"Ita da kanta itace zinarin sbd itace kujerar mulkinta,sunanta sunan karagarta daularta itace arziki da kowa ke fatar samu saidai hadarin dayayi Katanga wa arzikin shine soyayyarta wadda itakaice mukulli ga wannan taskar arzikin.

Kallon kallo suka shiga yiwa junansu saidai babu Wanda alamar tsoro ko fargaba yake ataredashi Jamal ya kalli cikin idon aqoob yace,
Shirye muke da mallakar wannan dukiyar kota halin yaya koda soyayyar tatace mun shirya nema.

Murmushi bokan yayi yana jinjina qarfin zuciya da buried tareda rudu irin nasu sannan yace,
"D'ayanku zai fa
a soyayya da ita amma kafin nan sai kunyi jiran
shekara
aya, wanda haka zai kasance kamar ganganci da wasa da rayuwarkune sbd hadarin dajin dakuma tsawon lokacin dakuma mataki uku masu matuqar hadari,
idan kuka tsallake mataki uku da zai faru kafin bayyanarta toh tabbas soyayyar
ayanku zai kulu da ita, sai dai ba soyayyar bace mai muhimmanci dukiyarce mai mahimmanci domin sonda zai gwada mata shi zai sanyanta bu
e mishi alkaryanta da taskar mineelik.

Kallon juna suka sakeyi kowannensu idanuwansa acikeda rashin tsoro ajani yace,
"Toh boka matakai uku da zamu bi dan samun kusanci da ita menene fa'idar haka."?

Mikewa bokan yayi tsaye, ya shiga zagayesu har ya tsaya a tsakiyarsu murmushi yayi yace,
Zakusansu da sharadin taskar arzikin tamuce muduka.

Kallonsa sukayi cike da mamaki da jinjina kwadayinsa saidai zasu iya yin komai da mallakar taskar
kojo ya kallesa
yace,
"Mun amince, zamu raba da kai.

Dariyar
jin dadi yayi yace,
Tareda yarana biyu za'ayi wannan tafiyar tareda rubuta sheda a faifan fatar raqumi da jinin dukkaninmu za'ai rubutun kowa zaibada nashi arubuta a ajiye tarihi ya shaida wannan taskar arzikin mineelik tamuce mu duka.

Babu musu kowanne yafitarda 'yar qaramar wuqarsa dake some a qafafunsu suka 'diga jininsu a 'yar qwarya akai rubutun atake ya ratayesa a bangon dakin.

Yaransa biyu suka shigo yonas da haji yakallesu yace,
Gasunan kuma tabbas akwai haske mai disashe duhu akwai duhu mai disashe haske.

Dayake zuciyoyinsu a shirye suke sun kafe kwa
ayi da son zuciya ya rufe musu ido ba tare da wani bata lokaciba suka amince Jamal dake gyara zaman wuqaqensa dake shanye da dafi kala dabam dabam na macijai da kunamu harma da dafin kada yace,
"Tunda nine zan fara aikin kwada soyayyata dole kasona yazamo mafi nauyi a raqumi.

"Jamal kasonka shine mafi nauyi a raqumi sbd kaine zaka bamu gudunmawa mafi girma a cikin tafiyar,
abinda zai faru idan kuka isa dajin domin jiranta akwai tsoratarwa daga muyagun aljanu da dabbobi masu firgitarwa da suke yawo cikin dajin,
matakin farko zai farane daga kwanaki uku kafin bayyanarta zaku kasance kamar makiyan juna a ranar farko,
Zakiji tsana da qarfin son kashe juna mai qarfi na shigarku saidai karku bari hakan yaci qarfinku sbd dayafi qarfinku zaku kashe junanku cikin rashin imani.
rana na biyu kuwa bazaku ga giftawar tsuntsaye ko wata dabba ko dayaba ko wni iri har kukan namun dajin bazaku ji ba.
a rana na uku da zata bayyana wani mugun zafi da kishirwa zai buwayeku kamar zaku mutu, domin zaku ji har cikin jikinku zai koma kamar babu ruwa da jini a ciki, zuwa yamma ko dare zata bayyana, kai Jamal aikinkane kutsa kai cikin dajin domin ha
uwa da ita duk rintsi duk tsanani babu waiwaya.

Shiru sukayi cike da al'ajabi suke kallon kallo sabida jin abinda zai faru dasu wanda suke gani kamar fa
ar bokane,
Kallon bokan jamal yayi cikin nutsuwa yace.

"Wannan indai shine sharu
an mun amince.

Murmushi boka yayi sannan yace,
Tafiyace mai zuwa babu tabbacin dawowa abin bautarku ya kubutar daku.

"Toh ni dai har yanzun abinda nakeson ji shine me zamu mata musamu dauko dukiyar mu mallaketa" Inji Amari.

Kallon Jamal bokan yayi cikin murmushi ba shi yayi tambayar ba amma ya maida idanunshi kan jamal,
aukar duwatsunshi yayi ya watsa har lokacin idanunshi nakan jamal,
juyawa yayi yace,
"Lokacine zai nuna mana abinda zai faru ynz zan baku wasu madaurin dantse ku
aura gudun karku cutar da kanku.

"Wannan zai kareku daga cutar da juna, sannan babu wani abinda zai cutarku nagama daku sai ranar da yasamu nasaran isa birnin Sarauniya mineelik, zamu karasa aikinmu nakarshe."
Mikewa sukayi baki
aya suka fita koda suka isa bakin kofa, kallon jamal yayi cike da tausayi, sannan yace.

"Duk bayan lokaci mai dan tsayi ina son Babbanku yazo ya fa
a min cigaban da kuke samu."
Kallon 'yayansa yayi ya jinjina kai cikin muryar jarumta da bankwana yace,
Abin bauta yasa musake haduwa.

Haka sukayi bankwana dashi suka tafi.
****
Tunda suka tafi, kaman yanda bokan ya fa
a musu haka ya faru, sabida sun
aura
anbar wani kudiri a ransu, ranar farko, suna kwance sai suka fara jin shashekar kuka, kamar na yaro kaman na babba haka aka cigaba da razanasu da wani irin mahaukacin kuka, kafin aka samusu dariya irin na bantsoron nan, can da dare yayi tsakiya, sai kana kwance a cikn tantinka za'a zo ana kiranka daga kan ajani aka fara,
yana kwance ya dunkukune a marufinshi yaji an tsaya abakin tantinsa ana cewa.

"Ajaniiiiiiiiiii"
D'auke numfashinsa yayi cak, tsabar tsoron, haka aka kewayasu ana razanasu.

Wasa wasa sai da suka kwashi fiyye da wata biyar ana tsoratasu da abubuwa a gurin tuni suka saba da rayuwa adajin sbd dama dukkaninsu sunsaba da rayuwa a daji dan haka yanzu gida suka dauki dajin sbd burinsu abune dazasu iya komai akansa.
lokacin da suka cika wata shida Ajani yaje ya fa
awa boka abinda ya faru, nan ya zauna ya fa
a mishi abinda zasuwa Mineelik dazaran ta fa
a soyayya da Jamal.

Bokan ya cigaba da cewa,
" Matu
ar mukace muna son dukiyar baxata bamu cikin lumana ba.

Karshe rabaku xatayi da
an uwanku amma idan mukayi haka toh babu wata damuwa sannan zan nema muku abubuwan da zakuyi amfani dashi, karka bari
an uwanka yaji labarin dan matukar yaji bazai yarda yayi aikin ba."
Gya
a kai ajani yayi sannan yabar garin ya koma dajin, nan suka cigaba da zama ga tsoratasu da ake ga kwanakin kamar baya tafiya, duk sun kaqu da faruwan haka,
Da zaran sun zauna hiransu kenan, akan yanda zasu juya dukiyarsu da suka samu, daga gareta, a hankali lokacin yana tafiya wasa wasa sai gashi har saura kwanaki bakwai zata bayyana,
......

Bayan kwana hu
u wata rana da safe suka tashi da mugun fa
a kaman zasu kashe junarsu, kaman dai yanda bokan ya fa
a musu, karshe rabuwa dasu Jamal yayi ya koma gefe dan ya hassaso wannan rigimar yana cikin alamomin bayyanarta nan yatunatar dasu nan kowa yayi nesa da 'dan uwansa suna fidda wani irin gumi najin wani irin qarfi mai razanarwa na son kashe dan uwansa.
rana tabiyu kuwa sun tashi da babu giftawar tsuntsaye ko
aya tareda wani irin tsoro mai firgitarwa dayake shigarsu wanda suka tabbarda natane amma haka suka dinga daurewa cikin wata irin jarumta.

Rana mafi tashin hankali shine ranar bayyanarta tsananin zafin da ake yaja sukaita fad'uwa, gashi sun shanye ruwansu, dakyar Jamal ya mike yace.

"Yaku Y'an uwana wannan itace rana mafi hadari ageremu saidai ina fatar mana samun nasara."
Daqyar su kojo suka rarrafo gurinsa suka rungume juna cikeda tsoron rabuwa da juna saidai burinsu ya zarce komai.

Daqyar suka rabu da juna yana rangaji yana faduwa yana tashi sbd yunwa,zafi da qishirwa dake neman lahantasu ya nausa dajin inda ranar suka fara ganinta baisan inama yake jefa qafafunsa ba sbd azabar dayake ji cikin hanjinsa da cikinsa.

Duhun dare nayi yana isa gurin saidai ba'a cikin hayyacinsa ba sbd tuni yafara ficewa hayyacinsa atake ya yanke jiki gurin yafadi yana fitarda numfashi daqyar.

Ahankali kunnuwansa suka fara jiyo amo da sautin sarqar zinarin qafarta sanye take cikin kaya ruwan makuba fuskarta na fitarda wani irin annuri duk da cikin duhune atake yaji wani sanyi na yaye masa yunwa da wahalarsa suna barinsa ahankali.

Cikin wani irin takun nutsuwa da wata irin haiba ta nufo hanyar taku kadan tayi ta tsaya cak tareda lumshe fararen kyawawan idanuwanta.

A hankali ta juyar da kanta tahangosa kwance ba alamar yana numfashi.

A hankali takalli jikinta ahankali ta rikide ta sauya zuwa wata kyakkyawar bafulatar baqar Ethiopia sarqoqin jikinta na zinari suka koma duwatsun dandaye masu qaramin kyau ta nufosa numfashinta na wani irin sarqewa sbd wannan shine karo na farko data taba ganin wani biladama wadda take tabbarda shine Wanda ta dibi shekaru da qarnika tana jira.

A hankali ta durqusa gabansa tareda daga daga dogon hannunta ta ta6a goshinsa atake ya bude idanuwansa yana kallon fuskarta bai san lokacin da ya sume ba,
ruwan dake cikin goranta ta fulanin daji ta
auka ta watsa mishi, a hankali ya bu
e idanunshi sai akan fuskarta.

Cikin idanunta ya kalla kamar wanda aka
iga mishi ruwan gold, lumshe idanunshi yayi.

"Sannun ko" tace mishi...

Wani irin sauti yaji daga muryarta wanda yakusan sake sumar dashi yayi wani irin jarumtar daidaita numfashinsa da nutsuwarsa yayi kalar wanda ke cikin tsananin wuya ya daga mata kai daqyar alamar amsawa yana jan numfashin qarya daqyar.

Kasa wata maganar tayi tasauke kai tana kallon qafafunsa dake
cikin takarmin fatar damisa.

Sunkuyar da kanshi yayi ahankali kwalla na zuba daga idanunshi cikin muryar tsananin damuwa da baqin ciki rayuwa yace.

"Me yasa kika taimakeni?
me yasa baki barni na mutu ba?
na gaji da rayuwar duniya gwara na mutu nabar duniyar nan."
Kallonsa tayi cikin sauri da nutsuwa da laushin murya tace,
"Koma Ya-yane dai rayuwarka tana da amfani,
ka daina cire tsamani da rayuwa, dan ko bada
e ko bajima zaka amfani rayuwarka tana da amfani."
Kuka ya fashe da shi yans kwa
a kanshi da bishiya yana cewa,
"Kaicon rayuwa dan ina maraya shine bazanyi rayuwa kamar kowa, gwara mutuwata."
Duk ya jiwa kanshi ciwo,
tausayinshine da mamakin bil adamane ya kamata musamman ace yaganta mace cikin wannan dajin da tsakar dare amma bai nuna shakku ko tsoro da fargaba ba kodai yasan da fitowartane?
Chapter 38 · 0% Book details