← Book details Tarayya Part One Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 51

Sashe 12

Tarayya Part One Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yau rashin sukuninta yafi na kullum sbd har dare yasakeyi jikinta bai koma daidaiba ko cup tariqe hannunta rawa yakeyi data duba taga dare yakusa yi sai gabanta yafadi saidai tana bawa kanta hkr da qwarin gwiwa
Babu abinda takeson gani yanxu kamar nuratu,
Tana tsananin buqatar Wanda zatai magana dashi koda so dayane ayini.

Da daddare tun gurin kaita Jakadiya ta lurada yanda take cikin tsananin damuwa tashareta suna isa tashige itakuma tadawo.

Zaune yake akan cauch 'din datake lafewa gefen yana aiki da apple laptop,
Fararen kayan baccine ajikinsa as usual ya miqe qafarsa akan glass center table dake gaban couch din.

Ba haske adakin sosai saidai tana iya ganinsa yana iya ganinta.

Tsayawa tayi takasa qarasawa kujerar sbd ganinsa agurin.

Aikinsa yakeyi hankali kwance batareda yanuna yasan da alamar wani mutum adakinba bayan kansa.,
Saida yagama ya ajiye laptop din tareda miqewa ya nufi lafiyayyan royal bed dinsa ya kwanta Kansa na sarawa.

Saida yakashe wuta yana kalli ta qarasa ta kwanta qasa ahankali.

Gurin datake yaqurawa ido itama ahankali tabude idanuwanta ta qurawa gadonsa ido akaro na farko
Duk da akwai duhu adakin.

So kusan hudu yana gwada ta6ata kozai iya kwanciya da ita amma Sam zuciyarsa na qyanqyami da hakan Wanda hakan yayi matuqar tunxura sultan yayi wani irin fushi mai muni tareda yanke wani irin mummunan hukunci aransa yace adaren yau idan yarima bai keta budurcin baiwa rumanah ba washe gari su saurari hukuncinsa.

Koda saqon yaje masa baidamuba matuqar hukuncin kona menene bazai shafi ammynsaba.

Jin sanarwar abinda sultan yafada ya tsananta damuwarta da quncinta saidai batada Wanda ko fira dashi bare Wanda zata tattauna damuwarta dashi shiyasa taqara rungumar qaddararta tana jiran hukuncin yanda za'a cigaba da yanda akaso da ita.

Sama sama Cikin bacci take jin kukan yara da manya,
Mazaje da mata tareda wata irin iska mai daukeda hayaniya na amsa kuwwa ako ina na cikin masarauta da wajenta koina na amsawa a fadin garin.

Bude ido tayi ahankali tareda kallon inda take tayi ido biyu da maheer duqe agabanta yana idanuwansa sunyi wani irin mummunan ja wata irin damuwa da tashin hankali tareda neman mafita take hangowa acikin idanuwansa.,
Da sauri ta sauko daga gadon taji qafafuwanta sun nitsa cikin ruwa ta sauke idanuwanta ta duba a firgice tayi baya jikinta na wata irin rawa ganin jini kwance yana gudana.

Kallon maheer tayi da sauri ya girgiza mata kai cikin wata irin murya mai ciwo da sanyi yace,
mineelik assultana the redblood Queen.

Zaro idanuwa tayi cikin tsananin tashin hankali jin abinda yace,
Rawa jikinta yadauka
Ihun datake ji tun farko yafara yawa cikin kunnenta yana neman gigitata ta fita da sauri tafara gudu cikin jinin daketa gudu kamar ruwa ako Ina na bangon masarautar stains ne na jini,
Tana fitowa babban filin harabar palace din taga gawarwaki harbabu gurin saka qafa su zaka taka dole ka wuce ga ruwan sama dake sauka sosai Wanda suke qarawa jinin dake zube koina gudu.

Wata irin busa taji anyi wadda ta amsa kuwwa koina
Nan take taga mutane nata taruwa kamar tururuwa sbd mugun yawansu,
Haka suka cigaba da taruwa suna kallon wata babbar qofa dake been sama inda sultan ke fitowa idan zai fito yayi magana inda kowa ke iya ganinsa.

Kutsawa tafarayi Cikin mutanen tana bin mutanen da kallo
Nan tafara girgixa kai ganin ba jama'ar daularsu bace kawai hardana wasu daulolin,
Wanda alamu suka nuna da qarfin mulki aka mallakesu ana mulkarsu harsu har sarakunansu.

Saida aka taru harbaka iya qwaqwaran motsi sbd taro da yawan jama'a aka sakeyin busa nan guri yayi tsit ko kukan tsunstu babu kowa yamaida kallonsa ga qofarda sultan zai fito itama tayi saurin kallon qofar daidai lokacinda aka wangale qofar wadda tafi kama data zinari sbd kyalli.

Cikin wata irin doguwar Riga maroon colour tana ja da qasa tafito daga cikin qofar ta bayyana
Gashinta azube yake har bayanta yaji adon sarkokin zinari nakai har zuwa kafadunta hakama wuyanta sarkace har saman cikinta ta zinari,
Wani irin kyau da kyalli take fitarwa daidai hannuwanta a lalace suke kaca kaca da jini har jikin rigartama haka
kujerar karagar mulkin mineelik Wanda keta tsiyayar jini wasu irin samudawan guards suka ajiye mata tasaki wani irin qayataccen murmushi zata zauna......

Cikin wani matsanancin ihu takira sunanta da qarfi tana cewa,
Rumanahhhhhh karki zauna a wannan kujerar......rumanahhhhh
Zama tayi cikin wani irin iko da mulki nan gari yadauki ihun sunanta.

Amatuqar gigice sultana ta zabura daga baccinta tana tareda lalubar bedside lamp takunna da sauri jikinta na muguwar karkarwa tafara karanta innalillahi tana hada wani mugun gumi.,
Wannan mafarkin nata babu alkhairi acikinsa,
Meya hadata da wannan mummunan mafarkin?

Tsoro da fargaba taji yana shigarta tayi saurin saukowa tafada toilet tayo alwala tazo tafara jera nafiloli kafin asuba tayi.

Har gari ya waye bata sake ko kwanciyaba bare rintsawa,
Abinda tagani amafarki tamkar wani gargadine ga abinda suke shirin yiwa rumanah bata fatar ko acikin bacci tasake irin wannan mafarkin bare ya tabbata.

Dan haka ta yanke shawara komai zai faru shirye takeda daukar hukuncin sultan.

Qarfe goma sha 'daya na rana saqon kiran sultan yazo gareta babu bata lokaci ta miqe cikin shirinta da adonta ta nufi part dinsa kuyanginta na biyeda ita,
Duk inda ta gifta kafin ta qaraso anrabe anxube qasa ana gaidata cikin matuqar girmamawa harta isa tun a qofar palon farko suka dakata itada Jakadiya data fito tarbonta suka qarasa.

Tana isa jikinta yayi mugun sanyi sbd ganin yanda kowa ya dauke wuta sai mizurai akeyi sbd ran sultan ya baci kuma kowa yasan hukuncinsa ba sauqi ba kyau haka itama ta isa kujerar dake matsayin tata tazauna bayan ta kwashi gaisuwa.

Maheer ransa amatuqar bace yake sbd baisan hukuncinda sultan zai yankeba akan ammynsa.

Cikin kakkaisar murya yakalli Jakadiya yace,
Inason jin dalili qwaya 'daya daya daga yarima Wanda ya hanasa cika umarnin sultan dinsa.

Cikin rawar murya Jakadiya takalli yarima zata maimaita masa abinda sultan ya tambaya batareda yakalli ko dayansuba kai tsaye yace,
Banada sha'awar kowace mace bayan wadda igiyoyin aurena suke kanta.

Wani numfashin bacin rai sultan yafitar yana kallon yarima sbd yasan daga yau hukuncinda zai yanke akansa yagama da rayuwarsa gaba daya cikin isa da mulki yabude baki yace,
Jakadiya atambayesa yana buqatar qarin lokaci kokuwa shikenan......

Cikin tsananin dauriya da danne fargabarta da fargabar abinda zai biyo bayan abinda zatayi tabude baki tace,
Ina neman afuwar sultan amma baiwa rumanah ta haramta garesa daga yau sbd na 'yantata daga wannan lokacin harzuwa qarshen rayuwarta,
Daga yanxu ita ba baiwa bace sbd haka ta haramta ga kowane namiji idan ba mijin aurentaba.

Cikin wani irin mugun mamaki da 6acin rai dabai taba yiba yake kallonta jin abinda tafada,
Ta 'yanta baiwarda yabada umarnin yarima ya kwana da ita kenan 'danta takare daga aikata abinda baiso
Tabbas zasu 'dandani hukuncin sultan daga ita har 'danta.

'Dagowa yayi yakalli wazirinsa cikin wani irin yanayi na nuna rashin damuwa yace,
Ta 'yanta baiwarta sbd ta rahamtata ga 'danta sbd bayaso nikuma zan halasta masa ita ayau sbd umarnin sultan baya bin iska,
*_KUJE ABADA SANARWAR 'DAURIN AUREN YARIMA MAHEER IBN ABDULSHAMS ABDALLAH DA 'YANTACCIYAR BAIWA UMMU-RUMANAH BULAMA_* nanda awa biyar duk Wanda baizo ya shaida 'daurin aurenba nakoresa daga qasata sai bayan shekara biyar yadawo.,,
*_SULTANA ZAARAH BAYAN 'DAURIN AURE ZATA KOMA GURIN IYAYENTA BAZATA DAWOBA SAI MATAR YARIMA MAHEER RUMANAH TA HAIHU._*
#mamuhgee
[7/29, 9:29 PM] Hauwa'u inna: *_TARAYYA_*
_wattpad@mamuhgee_
_Haske writers association
*14*
Gyara tsayuwa suhailat tayi daga bakin tafkeken windon bedroom dinta iska na daga curtains suna ta6o har fuskarta sbd sosai take buqatar iskar sanyin AC bazai mata ba she's feeling suffocated already.

Gyara tsayuwarta tayi akaro na ba adadi tana tsananin buqatar Wanda zai bata kulawa ayanxu sbd wani irin kishin mijinta dakecin duk wani jini dake yawo acikin jijiyoyin jikinta,
Tana tsananin so da qaunar maheer,
Maheer na respecting relationship dinsu sbd 'yaya dakuma zaman fahimta dasukeyi Saidai maheer na buqatar macen dazaiji dadin yin rayuwarda yakesonyi da ita Wanda bata fatar yasamu hakan daga wata macen bayan ita,
Yanda labari yazo mata baiwa rumanah ce aka za6a
Tsoronta na qaruwa aduk lokacinda ta tuno kamanni da tsarin rumanah din Saidai kuma bata tunanin tafi bata tausayi sbd sanin waye maheer bazai ta6a iya kwana da wata mace ba musamman wadda ba matarsaba.

Girgiza kai tayi tana mayarda dogon gashinta daya barbaje baya ta zauna bakin lafiyyan gadonta tana cewa,
Ya Allah ka yayamin wannan azabar danakeji cikin raina
Hawayen datake dannewa tun lokacinda zancen yazo mata suka 6alle ahankali tafara fitarda sautin kuka tana rufe fuskarta.

Kallo daya yayiwa gefenda take ya nufi bedroom yashiga ya tube yashiga cikin bathtub yakwanta tareda rufe ido yana qoqarin samun nutsuwa azuciyarsa har tsawon lokaci kafin yayi wanka yafito 'daureda towel milk colour yanufi closet yadauki kaya yashirya cikin kayan bacci ya fesa turare mai sanyin qamshi ya nufi gadonsa ya kwanta hankali kwance cikin nutsuwa tareda shigewa lallausan duvet ya zira hannu yakashe wuta ya lumshe ido sbd shi baimasan ta yaya zai saka zancen sultan aransaba bare harya cika kwata kwata shi ba mutumne mai yawan maganaba idanuwansa da kallonsa suke bada magana ko umarnin abinda za'ayi kuma shima mutumne dazai iya 6ata lokacinsa gun abinda baima shafesaba kokuma abinda baidauka da mahimmanciba shiyasa ko kallo baiwar bata ishesaba idan sungaji da kawota zasu daina Dan Kansu ko yanxu yabartane aringa kawota sbd abinda sultan yafada akan ammynsa if not baisan yama za'ai yaringa kwana daki daya da wata macenba bayan ko matarsa basa kwana daki daya.

Tunda yashigo ta lafe jikin kujerar tareda tsayarda duk wani motsinta ta sunkuyar dakai numfashinta na tsananta fita
Tana rabe kanta sunkuye yayi duk abinda yakeyi ya kwanta tana ji tana jiran taji ya tunkarota amma ko kallon inda take baiyiba harya kwanta.

Ajiyar zuciya tasauke ahankali hawaye masu sanyi suka gangaro fararen idanuwanta bada damu data sharesuba sbd duhune adakin ta kwantarda kanta kan gwiwoyinta hawayenta nacigaba da gangarowa.

Asubar farko Jakadiya tazo ta tsaya palon qarshe riqeda doguwar rigar dazata rufe kayan barcin dake jikinta.

Miqewa tsaye tayi jikinta ba qwari sbd kuka da rashin bacci ta nufi qofa.
Chapter 12 · 0% Book details