← Book details Tarayya Part One Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 51

Sashe 13

Tarayya Part One Complete Hausa Novel · about 8 min read

Alarm din gefen gadonsa dake tadashi sallah sbd ba'a shigowa ko palonsa na biyu bare atadashi sallah yasa yakeda alarm na tadashi sallar asuba kawai.

Ringing alarm din yasa ya cira hannunsa daqyar cikin bacci ya danna hasken wutar dakin
Tayi saurin juyowa afirgice sbd takai tsakiyar dakin takusa isa qofa daidai shikuma ya bude oily eyes dake cikeda bacci suka sauka akanta,
Dishi dishi yake ganinta ya lumshe idanun yabudesu itakuma hartayi saurin ficewa.

Tana ganin Jakadiya tsaye wani irin tsoro da mamakinta suka kamata amma saita sunkuyar dakai jakadiya ta miqa mata rigar ta sanya tareda janyo hular rigar ta rufe fuskarta suka fice.

Kallo daya Jakadiya tayi mata tasan babu abinda yafaru tsakaninsu tasaki numfashi tana cigaba da tafiya.

Suna fitowa qofar part din bayinda aka bari da Daren still sunan suka Mara musu baya suka kaita sabon gurinta suka wuce batareda Jakadiya tace da ita qalaba.

Zamewa tayi qasa bakin gado ta ta qurawa window ido ta fada dogon tunani fuskarta cikeda damuwarda tayiwa rayuwarta dabaibayi.

Tadauki lokaci kafin tamiqe tashiga makeken bathroom din dake dakin tayo alwala ta zame kayan jikinta tareda mayar musu da kayansu cikin wardrobe tasaka doguwar Riga tayi sallah.

Koda gari ya waye ankawo mata abinci bata iyacin komaiba hakama da rana ankawo amma takasa koda kallon abincin.

Arayuwa yanxu batada wani sauran buri ko mafarki sbd yanxu ta yarda mafarki baya zama gaskia,
Ita ayanxu tamkar wata dabbace da duk yanda akaso ayi da ita haka za'ayi ta yarda da qaddara tabarwa Allah alamuranta.

Sultana bawani doguwar nutsuwa bace acikin zuciyarta sbd har lokacin zuciyarta da gangar jikinta sunkasa nutsuwa da alamarin tsoro take ciki sosai sbd tana tsoron abinda zai iya juyewa gaba.

Koda gari ya waye Jakadiya tasanarda ita babu abinda yafaru tsakaninsu hakanan tasamu kanta da ajiyar zuciyarta tayi shuru tsawon lokaci kafin takalli jakadiya cikin wata irin murya tace,
Jakadiya zansa acirewa rumanah mahaifa sbd fargabata tana yawa Wanda hakan nabani cewar zata iya haihuwar namiji Wanda nibana mata fatar zamowa MINEELIK-ASSULTANAH kuma kinfi kowa sanin me hakan ke nufi,
Tayi yarinya da riqe wannan matsayin sbd bala'i da masifar dake ciki yafi qarfin shekarunta Dan haka abin zaifi ta6ata.

Shiru Jakadiya tayi kafin tagyara zama cikin son gyara zancen tace,
Allah yataimaki sultana cire mata mahaifa tamkar mun qarasa nakasta rayuwartane,
Ke tamkar uwa kike agareta muyi mata fatar samun 'ya mace ta yanda idan tasamu yantawa akorata nesa da nan taje tayi aure tafara gina wata sabuwar rayuwar.

Ajiyar zuciya sultana tasaki tareda lumshe ido tana fatar Allah karya bawa rumanah cikinma kwata kwata ana dakatarda ita daga zuwa gurinsa ta 'yantata ta turata nesa da nan.

Mamani duk wani baqin ciki da quncin duniya yataru axuciyarta tun lokacinda aka tafi da rumanah ko ruwa ta kasa sawa cikinta jitakeyi kamar zuciyar naci da wutane saidai tana addua da fatar Allah yasa ko cikin 'ya mace karta samu bare na namiji.

Sarauniya adama kuwa komawa tayi tamkar zata mutu sbd baqin ciki acikin dakinta laifi qalilan zakayi tasa arabaka da lafiyarka sbd ta daura damarar yaqi da duk Wanda zaishiga tsakaninta da abinda take buri tun tana qanqanuwarta.

Kamar jiya qarfe goma aka zo tafiya da ita bayan anshiryata cikin rigar da gwara ta jiya da ita suka tafi.

Yauma a qofar shiga bedroom dinsa ta zame rigar sama da ribbon gashinta ya zubo dakanta yau ta bude tashiga batada kuzari ko kadan ta nufi inda ta ra6e jiya tazauna tareda kwantarda kanta kan gwiwoyinta ta rufe idanuwanta ahankali.

Kwance yake duk yau ko ina bai fitaba iyakacinsa palonsa na biyu inda nan yake cin abinci sbd nan ne dining room dinsa,
Ko suhailat ma so 'daya takirasa awaya tana qoqarin boye damuwarta da kishinsa tagaidasa tabasa su amah sukayi masa 'Dan surutunsu Wanda duk sukeyin abinsu iyakacinsa sauraransu suka gama.

Ammynsa ma yau awaya yagaidata koina bai fitaba yayi kwanciyarsa.

Tun lokacinda tashigo yaganta ya rufe idanuwansa ahankali tareda gyara kwanciya sai alokacin ta fahimci yana 'daki sbd duhu bata luraba amma ko motsawa batayiba tayi Shiru ko tunanin bata iyayi yanxu
Ahaka asuba tayi ta miqe jikinta amatuqar sake ta fice.

Ahankali kwanakin suka ja kusan sati biyu ana kaita amma baitaba ko kallon inda takeba.

Abu 'dayane daya fara canzawa shine qamshinta daya kama koina acikin dakinsa har toilet dinsa Wanda hakan ne kesakashi 6acin rai wani lokacin.

Itakuma ayanxu tarigada tasan bazai ta6a yin komai da itaba shiyasa kowane irin kaya aka bata bata damuwa sawa takeyi.
#mamuhgee
[7/29, 9:29 PM] Hauwa'u inna: *_TARAYYA_*
_wattpad@mamuhgee_
_Haske writers association
*17*
Jikinta har rawa yakeyi gurin zuwa tasanarda mamani,
Da ace bawa nada ikon gudu Dan karan kansa ba sakasa akayi to yau da bazata tafiyaba gudu zatayi domin ta isa gurin mamani da wuri tafada mata kyakkyawar rayuwarda tayiwa rumanah qwanqwasa.

Tana isa babban kicin din ta sake nutsuwa Cikin girmamawa take gaida masu kula da bayin sakewa masarauta girki harta isa gaban mamani dake kwashe farfesun wani qatoton kifi ahankali sbd karya wargaje ahaka ake dorasa cikin inda za'a kaisa,
Murya qasa qasa cikin tsananin farin ciki tace,
Mamani a yau sultana ta 'yanta ummu-rumanah sbd aurawa yarima maheer ita ataqaicema an 'daura au........

Cak mamani ta kafe idonta akan fuskar nuratu 'din babu alamar motsi atareda ita
Cikeda tsoro ta ta6ata tace,
Maman........bata qaraba taga ta yanke jiki ta fadi cikin tsananin tsoro da fargaba takira sunanta da qarfi Wanda yasa masu kula dasu qarasowa da sauri suna tambayar abinda yasameta.

Girgiza kai nuratu tayi idanuwanta na cikowa da hawaye sai dai batasan mezataceba Dan tasan tsabar hassadace ta sumar da mamani.

Ruwa akace nuratu ta 'debo sbd rikicewa ta ciko silver da ruwan masu tsananin zafi tana qarasowa ta zuba matasu amatuqar gigice mamani ta saki wahalalliyar ajiyar zuciya tareda bude ido ta tashi zaune jikinta na wani irin sililin zafi ta 'dago ahankali tana kallon nuratu ta tuno da abinda tafada mata wani irin kuka ne ya kufce mata hadda shesheka ita shikenan rumanah ta mayar mata da burinta mafarki,
Ita sai yaushene bulama da iyalinsa zasu bari taringa samun abinda take burin samu,
Rumanah tasan duk burinta akan nuratu ne tasamu wannan matsayin amma ta shiga tsakaninta da burinta.

Wani sabon kuka tafashe dashi tareda miqewa tana qoqarin cigaba da aikinta sililin jikinma tuni baqin ciki yasa batajinsa ko kadan.

Saidai ita mamani kutti ayau tana rantsuwa dasai ta raba rumanah da duk wani farin ciki dazai shigo rayuwarta kamar yanda iyayenta su asma'u suka rabota da farin cikinta,
Hakama tayi alqawarin shiga tsananin ummu-rumanah da duk wani burinta kamar yanda ta rabata danata.

Jiki amatuqar sanyaye nuratu ta juya tabar sashen kicin din tana tunanin tabbas mamani bazata bari azauna lafiyaba saidai dukda tana mahaifiyarta bazata ta6a bari ta cutatarda ummu-rumanah ba koda hakan na nufin zasu raba hanya ne.

Cikin wani irin yanayi yashigo part din na sultana tareda Jakadiya dake biye dashi daukeda sadakin rumanah 'din fuskar yalwace da farin ciki.

Suna shigowa dukkanin wainda ke palon suka miqe banda sultana da rumanah dake zaune cikin lullubi.

Tsayawa yayi batareda yakalli inda takeba
Ganin haka yasa sultana miqewa tsaye tareda riqo rumanah ta tayarda ita ahankali takawota gabansa suna fuskantar juna
Tanajin yanda dukkanin jikin rumanah yake rawa haka ta saketa tareda saka hannu ta yaye mata lullubin.

Kamar bazai kalli fuskarta ba ya bude fararen oily eyes dinsa akanta,
Karo na farko daya kalli wata mace a duniya yaji gabansa yayi mummunan bugawa ya 'dauke idanuwansa ahankali cikin rashin kulawa yayi Jakadiya wani kallo a hanxarce ta matso tareda miqawa ummu-rumanah tray dinda yake daukeda sadakinta cikin tsananin girmamawa tace,
Allah yataimaki amarya ummu-rumanah ga sadakinki Allah yayiwa aure albarka.

Hannuwanta dake cikeda awarwaro da zobunan zinari ta 'dago yana rawa sosai ta karbi tray din har lokacin kanta na qasa bata dago takalli kowaba.

Sultana ta miqawa tray din batareda tace komaiba sbd bazata iya maganaba itadai duk yanda sukazo haka zata bisu sbd tasan wannan shine fate dinta.

Karba sultana tayi tareda sakin murmushin qarfin hali tace,
Allah yayiwa aure da rayuwaki albarka ummu-rumanah bulama.

Mayar mata da lullubinta akayi suka dunguma zuwa gurin sultan .

Acikin dubban taro aka gabatarda ummu-rumanah bulama amatsayin sabuwar matar yarima.

Jama'ar gari da wasu masarautun sun jinjina kyawu irin na ummu-rumanah sbd ayanda tarihin sarakunansu yake zuwar musu shigowar mace mai tsananin kyawu a cikin zuriar sarauta baya zamtowa alkhairi.

Ana gama gabatarwa aka mayarda rumanah gefenta tareda sabbin bayi da kuyangi goma.

Bayan angama shagalin sultana ta shirya dukkanin kayanta tareda sa jakadiya tasa ayi mata booking ticket na flight dinda zai tashi da dare zuwa Libya.

Wanka yayi yashirya cikin fararen qananan kaya transparent marasa nauyi shiyasa mur'dadden jikinsa yake kusan a bayyane sbd shi Sam bayajin damuwar komai sbd auren bai sakasa akansaba sbd yasan bazai ta6a takura kansa ya canza sbd waniba, baya buqatar wata mace arayuwarsa bayan suhailat so bayajin yanada wani lokacin 6atawa gurin zama yana yiwa mata ciki saikace wani injin.

Damuwarsa 'dayace barin sultana masarautar zai ta6a martabarta da qimarta a idanuwan mutanan da mineelik ke mulki dakuma mutanen masarautar mahaifinta.

Kwanciya yayi tareda lumshe ido.

Suhailat kwananta biyu bata fito part dintaba sbd nauyin ciki dakuma rashin son kusanta kanta da duk inda zataga ummu-rumanah kokuma zancenta sbd batason kishinta yafi qarfinta qarshe tayi abinda zata zubarwa kanta mutumci tabarwa kanta da 'yayanta abin fa'da gashi maheer ma anyi mata iyaka da ganinsa sai baiwarsa tasamu ciki shiyasa ta kama kanta a part dinta tasamu ta haihu ta tattara takoma Georgia ko zata samu hankalinta yadan kwanta.

Zaune take a palo tana waya da mum 'dinta cikin sanyin murya tace,
Mum inason nazo gida na haihu agurinku sbd nasan anan ne nida abinda zan Haifa zamu samu soyayya da qaunar yanda muke buqata....

Cikin rarrashi mum dinta tace,
Suhailat my dear kiyi hkr tunda kinsan a inda kike aure,
Idan kin haihu I promise to come by Allah's grace my dear,
Kicire damuwa da tunanin komai sbd condition you're in.,
Wen is your edd???

Saura sati hudu.

Ok akwai sauran time ma ashe?

Yes mum,
Mum can you just give me a minute I will call you back someone is here.
Chapter 13 · 0% Book details