Sashe 9
Sakacin Waye Part 3 Complete Hausa Novel · about 6 min read
cikin aure ba. Zuciyar bangaren hankali da kyakkyawan tunani ta cigaba da cewa. Kwarai, ina bukatar sanin halaye da dabi’un miji na, na zahiri da badini as a life-time partner. A bangaren halaye da dabi’u, cika alkawari, amana da tsarkin addini ban gama sanin sa ba har yau. Sai aka yi sa’a ni din kuma, wata irin mutum ce mai matukar tsantseni a kan wadannan din, da kuma kiyaye addinin ta matuka. Wato ni Siyama mai son addini ce, mai son kyawun dabi’u ce da son yin ado dasu, inada kokarin kiyaye dokokin Ubangiji tun bayan shiga ta Daar Al-Uloom. Haka kawai wani sabon bahagon tunani mara dadi kuma mara tushe ya bakunce ni a kan sa... Hamzah ba musulmi bane for quite a long time a baya, for almost 38 years of his life ya yi su ne in Christianity, wani addini na wasu rukunin mutane kabilu daban da ba irin nawa ba, mai yuwuwa ne ya taba yin zina (ya nemi mata), mai yuwuwa ne ya sha samun biyan bukatar sa ta dan adam ta hanyar haramun iri daban daban Har ila yau, in aka yi la’akari da yawan shekarun sa kuma a yankin turai, turai din ma a kazamar kasa irin Amurka inda kowa ke yin abinda ya ga dama balle wadanda ba musulmi ba, gashi ko awon jinin nan na zamani da ake yi na kafin aure mu bamu yi ba, tsabar son cika burin zukatan mu ya rufe mana ido, shima kuma Young Abba gaggawar sa da mantuwar sa bata sa ya yi wannan tunanin ba duk bokon nasa, ko mai yasa? Sannan na bar shi ya tara da ni tun a daren mu na farko ba tare da kowacce iri kariya ba (contraception), ya kuma hada bakin sa da nawa ya sumbace ni sau ba adadi, alhalin ban san ko ya taba shan Barasa (giya) da bakin nasa ba!”. “Innalillahi wa’inna ilaihi rajioun!” Na shiga ambata baka da zuci, ina girgiza kai na ina rokon Allah idan Shaidan ne yake son kawo min waswasi, don shiga tsakani na da mijin dana tabbatar ina yiwa wani irin sahihin SO da kauna ta hakika wanda babu irin sa a wannan zamanin, so ne tsarkakakke na samu zuciya ta ke yi wa Hamzah Mawonmase daga Indallahi wanda babu algus ko (material attachement) a cikin sa, to ina rokon sa yayi min iyaka da shi wannan tunanin mara tushe, mara amfani, mara hujja da madafa ko a addini, tunda addinin mu ya hana zargi, ya kuma hana bincike, shaidan ne kawai ke kawowa zuciyata farmaki mai son lalata zaman lafiya ta da kwanciyar hankalin dana samu, na nasarar mallakar abinda rai da zuciya ta ke so, bayan ba kowa ne yake nasarar dacewa da samun tabbatuwar mafarkan sa a zahiri kamar yadda nayi nasarar samun nawa ba. Ni na san ina son Hamzah, kuma ina son komai nasa, amma hakika tun bayyanar sa a ba muusulmi ba na san nafi son addini na ISLAM a kan sa, da kuma tsarkin addinin musulunci cikin jiki na da rayuwa ta baki daya, fiye da ita wannan soyayyar ‘yar asali dana ke yi wa Hamzah. Ko bayan bayyanar sa dana ji cewa ba musulmi bane na yi duk kokarin da zan iya wajen ganin na yakice shi Allah bai bani iko ba, na tabbata ban zabe shi a kan addini na ba. Wanda hakan yau ya tabbatar min (bayan na mallaki Hamzahn ta hanyar aure, zuciyar sa da gangar jikin sa gabadaya sun gauraya da nawa, kanwa ta kar tsami kwannafi ya kwanta) sai na gane cewa ashe dai ni Siyaman da sauran hankali na, ko ta ina aka je aka dawo za’a tarar ba makahon so nake yi wa Hamzah ba, irin wanda zai hana ni gano kyawun halayya da nagartar dabi’a ko akasin hakan cikin dabi’un sa. A’ah, So ne gangariya kuma tsaftatacce daga Allah wanda ba zai hana ni ganewa idan ya yi ba daidai ba. Na kuma fahimci cewa. Soyayyar dana ke masa a baya ta samu dan ‘tasgaro’ (cikas) daga lokacin da na same shi a ba musulmi ba! Wato ta samu dan nakasu. Karfin SO da sabo da son ne kawai ya dorar da ita, yet ina son abina a yadda na same shi din har gobe, musamman da ya zo ya rungumi musulunci nan da nan sanadi na. Wannan ya taimaka wajen farfado da sumammen son (karbar musuluncin da yayi), duk da cewa barin da aka yi, ba duka aka kwashe daidai ba wato hausawa suka ce ba’a bari a kwashe dai-dai, duk da hakan ina son sa har gobe da dukkan rai da zuciya ta, ina addu’a da fatan Allah ya inganta imanin sa ya cigaba a zama miji na a gaba dayan ragowar rayuwata ta gaba, amma kaso 30% cikin dari a cikin motar sa ya kwaranye. A lokacin da yake gaya min wata sadara…...mai taken; “Ni Hamzah dan addinin christianity ne!”. Ni na san Hamzah ya riga ya musulunta a yanzu, zunuban sa na baya an shafe su, shi da wanda aka haifa cikin addinin musulunci yanzu basu da maraba. Sai ma shi da ya fi mu rangwamen zunubi. Ya koma tamkar jariri sabuwar haihuwa. Amma duk da wannan tabbacin dana ke da shi na kasa nutsuwa a rai na, na rasa me yasa wannan bakon tunanin ke damuna yana addaba ta a yanzu; ba abinda nake so irin in tabbatar cewa Hamzah ba ya neman mata, ba kuma ya shan Barasa ko da kuwa karya zai gaya min, ina son samun wannan tabbacin daga bakin sa ba daga kowa ba, don samun nutsuwa da kwanciyar hankali na. Abubuwa da yawa sun taru sun hana ni kwantar da hankali na in mori wannan moment din yadda ya kamata, wanda kowacce mace sau daya take samun sa a rayuwar ta, wanda ya kamata yafi kowanne farin ciki a rayuwa ta wato (satin farko na amarci). Mai yuwuwa saboda can a kasan zuciya ta ina da damuwar Abba na a karkashin rai na, wadda yanzu ta zo ta kara lullube ni ta hana ni enjoying komai, bayan cikar mafarki da buri na na yin auren soyayya da samun irin mijin da nake mafarkin samu a kamanni da suffa, all my dreams are born alive now (duk da ban gama saninsa ta fuskar dabi’un sa ba) tukunna, amma wani hanzari ba gudu ba, duk da samun cikar mafarkan nawa ina son samun albarkar mahaifi na a cikin aure na da kuma yardar sa da amincewar sa ga mijin da Allah ya zaba min, ko in ce; ni Siyama na zaba da taimakon Young Abba, ba don komai ba sai don samun dorewar albarka cikin rayuwa ta, ba zan so nima yaran da zan haifa a gaba su yi min irin kafiyar dana yi wa Abba ba ya kasa tankwara ni, har a karshe ya zabi ya kore ni duk son da yake min. Don haka zan roki Hamzah in ya huta, mun gama amarcin mu yadda ya kamata ya yarda muje gun Abban Abuja, koda kuwa zai tsire mu ne, ko ya jefa mu a wuta ya kona sabida ya samu ya huce fushin sa. Hakan zai fiye min kwanciyar hankali fiye da in cigaba da rayuwa a kan fushin mahaifi na. To amma shin ban makara ba??? Ita ce tambayar da na dade ina yi wa kai na tun bayan cikar mafarkai da burika na. *****