Sashe 24
Sakacin Waye Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
yi musu ba nayi yadda yake so, ya zaunar da ni, ya dauko dryer din ya jona ya hau drying gashin nawa, daya daga abubuwan da yake so a cikin halittar Siyama kenan; gashin ta na asalin fulanin Mambillah yana kayatar da zuciyar sa. Ya yi wa Siyam alkawurra da dama wadanda har yau bai gama cika su ba, sabida sabon gap din data sanya a tsakanin su na rashin dalili wato fushin da ta tsira. Daya daga abubuwan da na ke so a tare da Hamzah kenan, duk da shortcomings dinsa (musamman ta fuskar kula da addini) kula min da gashi na da yake yi da kan sa (at his leisure times). Ya gama busar da gashin da dryer din, ya kama shi ya tufke daga tsakiyar kai na, sai na koma cute kamar kankanuwar yarinya, ya saki jelar ta kwanto lambam a wuya na, ya dawo ya hada fuskokin mu wuri guda, yana sunsuna ta, karan hancin sa mai tsayi yana gugar nawa karamin hancin, goshin mu a hade da juna, hannayen sa duka biyun zagaye da kugu na, bakin sa daidai nawa kamar mai shirin sumbata ta ya soma magana a matukar tausashe. “Kin daina fushin Siyam? Kin huce da ni ko? Kin ga ni ban san laifin dana yi miki ba. You are just punishing me for nothing. Jiyan nan jiyan I was…. I was…” (so yake ya ce he was drunk a jiyan amma ya kasa). Sai ya kifa kan sa a kafaduna ya soma hawaye. In ya tuna Allah kadai ya san irin zagin da ya yi wa Siyama sai ko ni kaina. “Ki yi hakuri Siyam ki yafe min don Allah. Na yi alkawarin haka ba zai sake faruwa ba, in sha Allahu. Yau za’a cire min filallika? Punishment din is too severe……”. Hawayen da suka kwanta cikin idanun sa sun gama nuna nadamar sa koda bai furta duka ba. Na yi dan murmushi, na russunar da kwayar ido na kasa. Hamzah sai ya sumbaci saman idanun nawa da sauri kafin na kai ga bude su, idon sa a kan kirji na da suka tasa sosai suka yi kamar baloon. Yana mamakin Siyam da yadda har yanzu bata san cewa cikin ta ya fara girman da ya isa awo ba tayi tunanin zuwa fara antenatal. Ban yi aune ba naji Hamzah ya zare tawul din jiki na ya sauke shi kasa, ya kurawa cikina ido kafin ya tsugunna ya rungume shi ya sumbaci kasan cibi na wato inda dan ke kwance, daga haka ya soma sarrafa ni ta hanyar da ya san zai samu contentment din da ya dade bai samu ba, (in the way and manner) da ya san bana iya kaucewa tayin sa. Duk wani weakness dina a wannan fannin, ni na san Hamzah ya gama sanin sa ba tun yau ba. Kamar yadda nima na dade da gama sanin nasa. Na soma tunanin kwace kaina ta ko ta halin kaka, duk da na san ba lallai in yi nasara ba a yanzu, don a irin wannan lokacin ba abinda zaka ce ko zaka yi Hamzah ya saurare ka, ko ya fahimce ka idan ba ya samu nutsuwar da yake son samu ba, da na tuna bai fa yi sallah ba, in aka bibiya tun safe. Wani bakin ciki ya taso ya tokare min a wuya, amma sai na tuna nasihar Anty na Nasara, cewa maza irin Hamzah masu tsananin bukata ta nan kawai ake cin galabar su, maimakon tureshi dana yi niyya da farko, sai na kara armasa masa komai na kara tunzura shi, ni da kaina na fidda kunya na zage ina seducing dinsa, na hana shi aiwatar da komai yau, ni ce ma nake jagorantar sa ta hanyar bashi ragamar abubuwan da ke gigita shi. Sai da na tabbatar Hamzah ya kai makura ya kai kololuwa wajen bukatuwa, yayi min maraba da dukkan zuciya da ruhin sa, ya gama sakankancewa yanzu zai samu biyan bukatar da yake ta hankoron samu, sai na janye kai na, ba don ban yi kewar sa ba nima, sai don na riga na rantse babu ni babu Hamzah, tunda ya daina sallah! Kuma ya komawa giya, sannan baya wankan janaba. In fact kawai sai ince ya koma kafircin sa, a fatar baki kawai yake amsa sunan musulmi yanzu tunda kowa ya san banbancin musulmi da kafiri sallah ce da tsarkin jiki da na zuciya. Ina mikewa toilet na nufa na maida kaya na a jiki na. Ba tare da na sake waiwayar sa don ganin halin da yake ciki ba. Ina jin sa da dakusassar murya yana fadin “Siyam yaya haka?” Muryar Hamzah ko fita bata yi saboda galabaita. Ya yi matukar gigicewa da wannan dandani haukacin na Siyama. Ba don na kasance cikin masu kyakkyawan ji ba, na tabbata da bazan ji shi ba ma. Wata dabara ta zo min, maimakon in ce masa sabida baka yi sallah ba, ni kuma bazan iya auratayya da mijin da ba ya sallah ba, sai na danne na cije nace. “Ka yi hakuri HAMZAH! Tunawa nayi ban yi sallahr Isha ba, alwallah zan yi”. Hamzah sai yayi dif! Ya shiga lissafi cikin kwakwalwar sa. Abu biyu ne ya sa shi yin dif din, sunan sa da Siyam ta ambata garangatsau kai tsaye babu wannan sakayawar ta soyayya yadda ta saba, wanda ya tabbatar masa akwai magana mara dadi a kasan ran ta. Da kuma tunawa da ya yi shi tun safe ma ai bai yi sallahr ba. Kai ba zai iya tunawa bama yaushe rabon sa da yin sallah (subhanallah). Na fara alwallah a toilet ina hawaye, Hamzah bai ce yayi riddah ba amma daina sallah ga wanda ya amshi musulunci da gaskiya yaya sunan sa? Bana so in yarda da tunani na cewa Hamzah ya yaudare ni da fake shiga musulunci don ya aure ni, tunda bai yi kama da masu fuska biyu ba. A dabi’ar sa sam babu yaudara. Ni Siyama yaya zan yi da rai na idan tunani na daidai ne? Bazan iya zama da wanda ya kasa tsaida sallah ba komin son da nake yi masa, alhalin yana ikirarin shi musulmi ne. A wannan lokacin sai na tambayi kaina; auren Hamzah da na yi a matsayin tubabbe ‘Sakaci’ na ne ko na Young Abba ko kuwa abinda Anti Nasara ta taba hasashe ne ya ke tabbata? A farkon haduwa ta da shi in ban manta ba Anti nasara ta yi rantsuwa kan Hamzah ba zai taba musulunta sabida ni ba. Ta ce an yi dubu kafin ni, sai dai su matan su yi riddah, amma ba dai shi ya koma nasu addinin ba. Kuma hakan bai sa ya aure su ba. Ni da ya aura din kenan kaddarar sa ce da Allah ya rubuta masa da bashi da ikon kaucemawa. Kamar yadda yake a tawa kaddarar nima Ina alwalar ina hawaye, ina sharewa da tafuka na, na kasa tsayar da ruwan ido na, lokacin da Aunty Nasara ke cewa in yi hakuri a matsayin jigon zaman aure, cikin zama na da Hamzah dole watarana zan ga abinda bana so tunda tubabbe ne, jin ta kawai nake yi. A gani na a lokacin son da nake yi wa Hamzah ya isa ya tare komai, ma’ana ba abinda zai yi da zai bata min rai ko ya sa na tsane shi tunda dai ya musulunta, amma wallahi yanzu ko ganin sa bana son yi, in na tuna baya iya sallah. Na yarda nafi son addinin musulunci sama da Hamzahn VOA, kuma son da nake masa ne yasa bana so Allah ya azabtar da shi ranar gobe kiyama, ya tashi a sahun rafkanannu masu wasa da sallah wadanda Ubangiji ya saukar da surah guda a kan su, tunda ya tsallake sahun mushrikai ya yi shahada. Sai ji na yi ya shigo toilet din, ya maida kofar ‘silently’ ya rufe, jin shesshekar kuka na ya yi daga daki inda na baro shi a kwance, kukan dana kasa rikewa ya soma fitowa fili duk da kokarin rike shi dana ke yi cikin makogaro na har Hamzah ya jiyo. Fitilar bandakin dana kashe Hamzah ya kunna, towel dina na dazu ne daure a kugun sa, da mamaki yace “kukan me kike yi haka? Siyam har ta kai mu ga haka? Kina kullace da ni irin haka a kan laifin da ban san na yi ba, amma ki kasa fitowa fili ki gaya min in gyara? Is this the kind of love we believe in? Sai ki bar abin a ran ki yana cutar da ke? Shin Siyam ko kin daina so na ne yanzu? Ko kuwa kin gaji da zama da ni ne kika kasa gaya min?” Idanuna jike da hawaye sun kada sun yi jazur na dago kaina na dube shi da su cikin ido, wani abu da ba kasafai nake yi ba, wato kallon Hamzah cikin idanun sa. “Mai yuwuwa ne duka abubuwan da ka zano din haka ne! (Na daina son ka, na kuma gaji da zama da kai), ba kuma don ka yi min laifin komai ba, wannan tsakanin bawa da Ubangijin sa ne”. Sakin baki yayi cikin kaduwa da mamaki yana kallo na da tsoro, jin yau inata cewa HAMZAH gaba-gadi, sannan murya ta babu wannan taushin da girmamawar da lankwasa harshen dana saba yi masa magana da shi a kowanne lokaci. Yau da kakkausar murya nake ta fada “Hamzah-Hamzah..” har da zaro jikakkun idanu na waje. Duk da Anty tace wai lallashin sa ya kamata in yi na ji bazan iya lallashin ba, domin ya kawo ni makura. Shi karamin yaro ne da za’a lallashe shi yayi sallah wadda itace zata tserar da shi a lahirar sa? Alhalin yana ikirarin shi cikakken musulmi ne a yanzun? Ya tako zuwa cikin toilet din ya kama kafaduna duka biyun ya girgiza ni da karfi, ya ce “what has gotten into you Siyam a kwanakin nan, kina cikin hankalin ki kuwa? Ko kin yi gamo ne? Ni Hamzah yau kike cewa kin daina so kin gaji da zama da ni? Na kasa gane inda kike dosa, kina ta sa ni a duhu, kawaici na ya fara karewa da sababbin halayen da kika kirkira, kike azabtar da ni da su, alhalin ban san laifin dana