← Book details Sakacin Waye Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 30

Sashe 11

Sakacin Waye Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

irin ta yau ba. A hakan ya mike ya nufi toilet din sa yana rangaji cikin mutuwar jiki. Ya sakarwa kansa shower ko ya samu sassauci. Sai da yayi wanka na sosai, yayi brush ya sake yi yadda ya kamata, hoping kada Siyam ta ji warin giyar nan daga bakin sa, ya canza kayan jikin sa zuwa Pajamas farare sol, sannan ya fesa turaren sa ‘guerlain vetiver’ ya tako zuwa dakin Siyama a hankali (with so much guilt in him), don gani yake kamar ilahirin jikin sa hoton giyar ‘desire’ din da ya sha ne. Ya yarda ta ci sunan ta ‘desire’, shan ta da yayi a yau ba ‘accidentally’ bane a’ah ‘desire’ ne na zuciya ba kuskure bane, ganganci ne. Tsabar guilty conscience din da ya lullube shi har gani yake yana bude baki da zummar magana a gaban Siyama zai yi aman giya ne. Ya yarda yadda yake tsoron bacin ran Siyam, ko yin abinda zai sa ta yi fushi ko ta yi Allah wadai da shi ko ta ce zata fasa zama da shi baya tsoron Ubangijin da yayi Imani da shi haka. Yana shiga dakin ya tadda Siyama cikin Sujjadah, sai ya ji zuciyar sa ta tsinke, gaban sa kuma ya yanke ya fadi sakamakon wani irin kwarjini na hasken Musulunci tasirin sa da izzar sa da Siyama tayi masa, ya rasa takamaimai wane aiki gare shi na kwarai a duniya da Allah ya bashi sa’ar mallakar wannan salihar yarinya ma’abociyar addini. A can baya ya san yana shirka, duk da a kasan ran sa ya san addinin musulunci shine kadai addinin gaskiya, yana shan giya, yana caca, yana yin abubuwa da yawa da ko addinin sa na Littafin Injila ya yi hani da aikata su. Abu daya ya san baya yi a rayuwar sa, kuma bai taba yi ba shine ZINA ko neman maza, hakika Allah ya kebance shi daga wannan dattin, sannan a rayuwar sa ba ya munafurci, baya nunkufurci baya giba, ba ya gaba da kowa. He’s a straight forward person a kan komai kuma a kan kowa da wata mu’amala ta hada su. Shi kan sa ya san kan sa a mutum mai fadin gaskiya komai dacin ta koda bazata yi maka dadi ko daidai da ra’a yin ka ba, wadannan sune dabi’un sa na zahiri da badini da ya dade da sani akan karan-kan sa. A yau ya yi wa Allah godiya sau ba adadi da ya bashi Siyama ya tabbata ba don ya cancanta ba, sai don Allah yana son shi da shiriya da rahma ta hanyar ta, da kuma karamci irin na al’ummar musulmi da darajja soyayya iri na wasun su (Young Abba), ya kuma gode wa Allah a karo na biyu da ya bashi addinin musulunci a yanzu, ya tsarkake shi daga shirka da kafurci. Yana rokon Allah giyar ma watarana ya barta bakidaya. Karo na farko da Hamzah ya samu kan sa yana addu’ar Allah ya sa kada ya sake maimaitawa (shan giya bisa ganganci) idan hakan mai sauki ne a gare shi, idan kuma mai yuwuwa ne Allah ya raba shi da giyar baki daya cikin kankanin lokaci, tun kafin Siyama ta kai ga ganowa. A cikin ran sa ya roki Allah ya bashi ikon kiyayewa dokokin sa a fili da boye. Duk sabida kwarjinin da Siyam ta yi masa da ya same ta cikin halin sujjadah. Bai tsaya jiran Siyam ta sallame sallahr ta ba don baya son ta gan shi cikin guilt din da yake ciki, da nadamar da ke shimfide kan kyakkyawar fuskar sa. Sai kawai ya kashe wutar dakin da ta kunna, ya lallaba ya shige cikin duvet din ta, kamar barawon da aka kama dumu-dumu ya dauko kayan sata. Yana addu’ar Allah yasa baya smell din giyar nan, duk da wanka da brush din musamman da kakkamsan turaren sa na Guerlain Vetiver da ya dauka, domin gusar da kowanne irin smell da ba kamshi ba a tare da shi. An dauki mintuna kusan ashirin a haka kafin na kammala addu’a ta da salloli na na walha, wadanda duk ina yin su ne a kan Hamzah da nema mana albarkar rayuwa gurin Ubangiji. Addu’a sosai na yi a kan mu, zaman lafiyar mu da karuwar soyayya a tsakanin mu, na rokawa ‘ya’yan da zamu haifa a gaba shiriya irin ta addinin musulunci. Na roki Allah yasa kada tushe da asalin mahaifin su da (past religion) din sa ya yi (haunting) din su, ko ya yi tasiri ga (upbringing) din su. Na kuma roki Allah ya bani ikon cika buri na na zuwa gaban Abban Abuja, kafin na samu rabon haihuwa a tare da Hamzah. Dana gama duk abinda zanyi, sai na canza kayan sallah ta zuwa kayan barci, yanzu ne zan yi barci sosai in huta gajiyar jiya yadda ya kamata, dama na tashi ne don in sallaci Dhuha, making sure ban zabi wadanda zasu dauki hankalin sa a kai na ba, sabida a yanzun hutu kawai nake bukata. Na kuma ji sanda ya shigo dakin ya dade a tsaye kafin ya kasha wuta ya kwanta. Riga da wando ne sakakku kuma masu kauri na saka, daga jiya zuwa yau na fahimci babban abinda ke kidima shi jiki na to gashin kai na ne, da kuma dukiyar nan dake kirji na. Don haka har hijab na kawo na saka a kai kamar mara gaskiya. Wai dai duk don kada Hamzah ya sake tayawa. Barci nake ji sosai domin lokacin kusan karfe sha biyu na rana. Ina fatan kafin azahar in tashi don yin sallah da nema mana abinda zamu ci. Duvet din na daga na kwanta daga can gefen sa, cikin dabara da wayo na saka filo biyu na jera su a tsakanin mu, sabida bana so a maimaita ‘yar daren jiya, hutu kawai nake bukata yanzun, da samun sararin shirya kalaman da zan yi masa amfani da su a kan abubuwan da suka addabi tunani na a kan sa. Na dauka Hamzah yayi barci, jin yana sauke numfashi a hankali, sai ji nayi ya mirgino inda nake, ya janye filallikan dana jera a tsakanin mu ya janyo ni cikin nutsuwa ya rungume ni tsaf, ya kuma lullube mu ruf, da lallausar duvet din. Daga sama har kasa. Cikin muryar barci, maye-maye barci-barci yace. “idan kika ce min kina son hutu, I will adhere strictly to that, ba sai kin gina mana pillows a tsakanin mu ba, don’t ever do that to me. I’m sorry for going out early, kina barci shi yasa ban tashe ki ba, ina so ki samu barcin da zaki huta sosai”. Na lumshe idanu na cikin jin dadi, shi dai bai gajiya da bada hakuri a inda ya san ya yi laifi, Hamzah Mawonmase ne, ina jin wata irin ni’ima na saukarwa ruhi na idan na tuna cewa he’s indeed my long-term dream husband, the dream guy I’m always dreaming of.... The apologizer Hamzah Mowonmase… (mutum mai yawan bada hakuri). So abu ne da ba zai fassaru ba jin sa cikin jiki na bakidaya yau, in reality (cikin ido biyu) ba’a cikin mafarki ko fantasies ba, yana bani hakurin wani dan laifin da yake ganin ya yi min, wanda ni a wuri na bai taka kara ya karya ba. Maimakon in ce komai kan abinda ya fada, sai na amayo da abinda ke damu na, ganin cewa wannan shine lokaci mafi dacewa da ya kamata in yi masa tambayar. “Yau ni da wanne suna zan kira ka ne? Kowanne na fada sai in ga bai kai ba kuma bai yi daidai ba. Mr. Hamzah mijin Aisha- Siyama Boddo? Koko The Berom Man mijin Mambillah girl, my Mr. Radio my Habeeby Hamzahn VOA, idan na yi maka tambaya zaka bani amsa tsakanin ka da Allah?” Hamzah bai san sanda ya kara kankameni ba yana dariya. Yace “Yi tambayar ki Habeebty, ko ta mecece kuma ko wacce iri ce, ban iya karya ba, kuma ko na iya ke kam bazan yi miki ba. Na yi alkawarin baki amsa”. Murya na rawa cikin jin nauyi, amma na yarda gara in amayar da damuwa ta in huta, kada zullumin cikinta da taraddadin amsar ta su taru su kashe ni, in ya so duk irin amsar dana samu in yi hakuri da ita; bi ma’ana, mai dadi ce zan samu ko mara dadi? Na cusa kaina a cikin kirjin sa cikin jin kunyar abinda zan tambaya. Hamzah bai katsi hanzari na ba sai kwantaccen gashin kaina da yake ta faman kitsewa yana warwarewa, nace “shin ka taba tarawa da wata macen kafun ni? Ina nufin, kana yin zina a can baya kafin mu yi aure? Kana shan giya? Irin wadda turawan kasar nan da sauran wadanda ba musulmi ba ke sha suna shirme da tambele a kan hanya?” Wuta ta daukewa Mr. Hamzah, na ‘yan dakikai, domin bai taba kawowa ran sa tambayoyin da zan yi masa kenan ba. Da bai yi saurin daukar alkawarin amsawa da gaskiya ba. Da gaske ya san giya haramun ce a musulunci domin ko ba’a gaya masa ba ya gane tana shagaltar da bawa daga sallah da sauran ibadodin da suka hau kan sa, ko tasa yayi shirme a cikin sallahr sa, kuma tana gusar da Imani in yayi la’akari da halin data saka shi a ciki dazu, gabadaya imanin da ya yi da Allah daukewa ya yi ya koma tunanin addinin wahala zai zame masa, yanzu kam ya yarda addinin musulunci is broad kuma yana da fadi da zurfi sannan sai a hankali zai san shi. Bai ce min komai ba, amma shirun da yayi shi ya tabbatar min bashi da amsar bani, kasancewar baya karya kuma ya yi alkawarin fadin gaskiya shi yasa ya zabi yayi shiru kawai. Sai kawai na ji kuka ya zo min. wani irin kuka mai cin rai. Idan Hamzah ya sha tarawa da wasu matan kafun ni, ni da naci wahalar soyayya shekara goma da doriya ashe fanko na samu? Na soma kokawa da shi ina hadidiye shi. Gani nake in nayi kukan nan na gama faduwa a gaban Hamzah. Cikin rawar murya da daga sauti na ce. “Ka bani amsa ko hankali na ya kwanta Hamzah, ko karya ce kayi min Hamzah zan fi son ta akan ka
Chapter 11 · 0% Book details