← Book details Sakacin Waye Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 30

Sashe 13

Sakacin Waye Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

mu da lahirar mu ba tone-tone ba. Har na ji shi cikin kokarin hade bakin sa da nawa, yana cewa “past is past SEEYAMA HAMZAH, let the bygone, bury the hatchet…please Siyam I need you now”. Muka koma farantawa juna rai kamar ba wata magana mara dadi da ta hada mu yanzun. Sai da na ga Hamzah ya nutsu, ya samu gamsuwar data dace da shi, bayan yayi wanka kamar yadda na gaya masa duk bayan intercourse sai an yi wankan janaba, irin wanda yayi na shiga musulunci ne sai banbancin niyya, ya dawo cikakken Hamzan sa wato bayan ya shirya cikin shirt da wando samfurin Bloomingdale’s, ya fito a dan gayen sa sosai wato Hamzan nan na Siyama a VOA, ya zauna daura da ni yana danna wayar sa, sai na karya murya ina mai shafa physique chest din sa ta hanyar zura hannu na cikin rigar sa na ce, “na manta in gaya maka a akwai sallah da ake yi ta neman albarka cikin aure a daren farko, unfortunately mu bamu yi ba, amma an ce better late than never, ka tashi mu yi yanzu”. Na gaya masa duk yadda ake yin sallar daren farko da muhimmancin ta ga ma’aurata. Na ce yayi alwallah mu yi, da babu gara babu dadi. Hamzah ba musu yayi alwalar ya dawo, yana daura alwalahr yana fadawa ran sa to ko don basu yi sallahr bane washegarin daren farkon su yasa ya karya kumallo da giya? Da sauri ya kawar da wannan tunanin tunda dai Allah ya cece shi daga kotun inquisitive Siyamah. Yayi alwalar da sauri musamman da yake har lokacin cikin guiltness yake, duk ya gama shan jinin jikin sa, yana tunanin ko dai Siyam ta ji smell din giyar ne a tare da shi, ko kuma wani nata ya gan shi a Bar din da ya je dazu ya kira ta ya gaya mata, shine dalilin da ya sa ta tsuye shi ta yi masa wadancan titsiyen tambayoyin? Amma ai bata san giya ba, don haka bazata san smell din ta ko alamomin shan ta ba, kuma ba tada wani anan banda family din ta Adam da Nasara. Su kuma me zai kai su Bar? Ko kawa guda daya bai taba ganin Siyama tare da ita ba. Kai ko da ta ji smell din daga bakin sa bazata tantance ba, a irin kyakkyawan brush din da ya dauka da turare mai sanyi. Da wannan ya samu karfin gwiwa ya yarda mu yi sallahr nafilar da na ce mu yi (bayan already mun riga mun gama tabbatar da auren namu sabida rashin hakuri irin namu tun gabanin nema masa albarkar). Kafin mu tada sallar nake gaya masa akwai wasu nafilfilun da ake yi kullum wadanda Annabi SAW ya kwadaitar kuma duk sunan su ya fito a Al’qurani, (Shaf’I, wutri, Dhuha) nace ya dinga yin shafa’i da wuturi kullum bayan sallahr isha’i, suna da falala sosai ga rayuwar Musulmi. Haka salatul Dhuha, idan hantsi ya dubi ludayi”. “Su din kuma ya ake yin su?” Hamzah ya tambaya da doki, babu girman kai ko kankani a dabi’ar sa. Na yi masa bayani dalla-dalla ta yadda zai samu saukin fahimta. Hamzah akwai brain, tuni ya fahimce ni. Ya kuma rike komai. Mikewa yayi muka gabatar sallahr ma’aurata na karanta masa addu’ar da zai kama kaina ya karanta. Sai da na maimaita masa kamar sau biyar sannan ya iya fada daidai, muka yi sallahr ya kuma kama kai na ya karanto addu’ar. Dukkan mu barci muke ji, don haka muna shafa addu’ar muka kwanta, bayan ya hada mana tea mun sha, yana makale dani kamar kaska. Kamar mai tsoron kada wani ya sace masa Siyam, a haka muka yi barcin. Hankali na bai kwanta da Hamzah ba, don na dauka zai nemi kari washegarin ranar, in roke shi alfarmar ya daga min kafa ko na kwana uku ne, ina bukatar hutu daurewa kawai na yi jiya, in samu in yi healing. Bawan Allah shi da kan sa ya nemi in huta din. Na yi ajiyar zuciyar samun sa’idah lokacin da yace min “Habeebty, relax, today ‘no round’ na ga daga dan shafar ki kin fara makyarkyata”. Na harare shi cikin jin kunya. Ni kadai na san wuyar da na sha jiya da shekaranjiya a hannun Hamzah dole in yi makyarkyata dana ga yana shafata kamar mussa, duk da son da nake masa yana danne komai. Sai Hamzah ya nuna min cewa ya fi ni sanin ciwon jiki na, ya fi ni bukatar hutun nawa, domin har zuwa kwanaki uku bayan nan bai yi attempting sake neman komai daga gare ni ba bayan sumba wadda dama baya gajiya mata. Ban yi zaton hakan ba kuma, domin daga ‘first night’ din mu zuwa yau na gama gano weakness din Hamzah, shima kuma ya san abinda na fi so daga gare shi, amma hakan bai sa ya fifita bukatar kan shi a kan samun lafiya ta ba. Wannan ya kara tabbatar min zan ji dadin zama da Hamzah saboda saukin kan sa, da rashin son kan sa, da yawan tausayin sa, ga far’a ga tsokana,s bayan saukin kan nasa kuma yana da muhimmanta bukatar abokin tarayyar sa sama da nasa bukatar. ******* BAYAN SATI DAYA Ana kiran sallahr magriba, ni na fara zamewa daga jikin Hamzah na shiga toilet nayi wanka, brush da alwallah. Na lura wani irin barci mai nauyi Hamzah ke yi wanda ya wuce normal sleep, a rashin sani na (intoxication) ne. A kwanakin da ya baiwa Siyama hutu, giya ce ke debe masa kewa, kullum yana fita ya sha kadan ya dawo ba tare da na gane ba. Bana so in yarda da zargin da zuciya ta ke halarto da shi na cewa, fitar da yake dan yi dinnan ya dawo min ido a lumshe, yana fadin barci yake ji, giya yake zuwa ya sha, tunda ya tabbatar mun sau tari ya kan sha din, ita ce kuma tayi cooling din sa ya kyale ni nake ta hutawa ta. An ce zato zunubi ne, koda ya kasance gakiya, don haka na yi gaggawar jan istighfari ga zargin da ya darsu min a rai na, duk da na san cewa hakan mai iya yiwuwa ne amma na yarda da mijina har zuciya ta ba zai gaya min abinda ba haka yake a zuciyar sa ba. Tunda ya ce ya tuba ya bi Allah ba zai sake din ba. “Ka tashi haka Mr. Radio, na rasa irin wannan barcin naka na rana da yamma, wanda baka tashi yin sa sai lokacin sallah zai fita. A yi maganar duniya ka yi bakam kana faman lumlumshe ido”, na sunkuya ina fadi a cikin kunnen sa. Duk da cikin barci yake bai fasa jawo ni ba, sai ya ce “bani da suna ne wai sai Radio? Ko ni na kirkiri radio sai haka Siyama!”. Dariya ya bani sosai. Ban san me yasa bana iya ambatar sunan Hamzah kai tsaye ba, sunan na min nauyi a baki na, ko don kasancewar sa suna mafi soyuwa a gare ni, na kuma rasa sunan da ya dace in kira shi da shi, kowanne na fara sai in bari daga bisani don sai in ga bai dace da shi ba. A can baya kafin mu yi aure na kan ce “Berom Man”, idan na bushi iska in ce “Mr. Radio”, ko Mr. Hamzah, amma yanzu fa? Wane sunan ya dace in kira shi lokacin da ya karasa goge duk wata hadda da ke kaina da nau’ikan soyayya iri-iri mai sanyaya zuciya da ratsa ruhi, masu wuyar mantawa ga diya mace, kuma masu wuyar samu a mazan wannan zamanin, ya yi formatting zuciya da kwakwalwa ta duka, bai bar komai a cikin su ba, sai zallar darussan da ya ke bani kullum masu kara min so da kaunar sa? Na tuna ranar dana fara ce masa “Habeeby” a falon Young Abba ne, yadda ya rikice cikin soyayyar sunan. Ni kuma wani abin mamaki a yanzu ba soyayyar ce tafi damu na ba, ina son gyara Hamzah ne da saka ido a kan dukkan ibadodin sa. Abinda zan fi so shine Hamzah na ya koma Shaihin Malami, Ustazu, ya zubar da duk ta’adun nasara da suka yi masa katutu, ya manta tarbiyyar Kaka Veronica, ta yadda duk ranar da muka je gaban Abbana da Ummati zan bugi kirji a gaban su in nuna musu zabe na ba zaben tumun dare bane, ko sa fi yafe mini da sauri, ya kuma zamanto ba zan ji dar din gaya musu cewa a baya ba musulmi bane ko na fada ya zama da kyar za’a yarda da ni. Duk da haka daga yanzu zan cigaba da ce masa “Habeeby” don babu sunan da ya dace da shi sai wannan. Tunda ko ta ina aka je aka dawo Hamzah zai amsa sunan masoyi a gare ni. Ko in ce masa “Shaheed” tunda ya yi shahadah kuma ina so albarkar shahadar ta bi shi. Ko da naso Dream Husband dina, ban taba tunanin zai zo min a ba musulmi ba, da ya zo din kuma, a matsayin Ahlil Kitab, sai Allah ya sallada shiriyar sa ta hannuwa na, ya kuma kaddari aure a tsakanin mu da gaggawa, kenan dole in zage damtse don mayar da shi yadda nake so ya koma, don haka in har soyayyar da nake yiwa Hamzah ta gaskiya ce dole in tabbatar ya kama addini ka’in da na’in yanzu. I know it will not be easy for him and for me, Aunty Nasara ta ce babu wata makarantar addini da Hamzah zai shiga wadda ta wuce tawa, kamar yadda yace da Young Abba “It should be gradual,” nima kuma ya gaya min dazu (I’m gradually trying to follow the Islamic teachings), na yarda da shi a kan hakan, sai a hankali din, kuma zan jure kamar yadda malami ke jurewa sabon dalibi dan aji daya in tabbatar da shi a kan bautar Ubangiji. “Don Allah ka tashi karfe bakwai na magriba fa, lokacin sallah zai fita Shaheed”. Ina! Hamzah ya juya ya koma barcin sa, cikin magagi yake fadin “Siyam.... I love you. I love the new name!”. Nace “ka rike love din ka bana so, tunda ba zai taya ka kwanciyar kabari ba, nima
Chapter 13 · 0% Book details