← Book details Sakacin Waye Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 30

Sashe 5

Sakacin Waye Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

fadin “boye ni Baban Ahyan, Hamzah ya manta surakuwar sa ce ni!”. Tuni Hamzah har ya kai kofa a lokacin, ya fice da Siyama dauke a hannun sa, wadda kunya ta hana ni ko da motsin kirki na kwanta lum! A cikin kirjin sa. ****** MR&MRS MAWONMASE Hamzah ya kashe motar a kofar flat din sa. A jikin kofar shiga apartment din nasa, dan karamin karfe ne mai dauke da dan rubutu da ruwan gold manne da sunan sa “Hamzah Mustapha M.” da kuma nambar gida, kamar dai yadda ya ke a like jikin kofar kowanne ‘American Condo’. Ko da ya kashe motar bai yi saurin fitowa ba, juyowa yayi ya dube ni, na hada kai da guiwa na rufe fuska cikin katon mayafi na, kuma har zuwa lokacin rabzar kuka nake ban gaji ba, ina jin shi yana safke ajiyar zuciya a hankali. Irin ajiyar zuciyar da Hamzah ke yi a jejjere sai kayi tsammanin kamar a kasa muka tako muka taho tun daga gidan Young Abba. Watakila kuma nauyin da ya sha ne na dauko ni a kafadunsa tun daga falon Young Abba zuwa cikin mota? Shi ya sanya shi wannan ajiyar zuciyar? Ko kuwa gajiyar tuki ne ko na godiya ga Allah oho? Hamzah Mawonmase, shi kadai ya barma kan sa sani. Hamzah ya san a yanayin da na ke ciki yanzu bana kallon sa, amma tabbas ya san ina jin sa, duk da irin kukan fitar ran da nake yi ba zan kasa jin sa ba. Sai ya tausasa murya, ya sirantata hadi da kalmasa ta ta koma ta rarrashi, at the same time, ya kaurara ta cikin siga ta bada umarni. A hankali ya ce. “Ba zan hana ki kuka ba Habeebty, domin kin cancanci ki yi shi yau kadai, na sabo da kewar gida, amma don Allah na roke ki alfarma, iyakacin sa cikin motar nan (kukan). Ki yi ki gama yadda ran ki ya ke so, ki yi kukan barin gida ki more, amma ki ajiye shi cikin motar nan sannan mu fita”. Ba kuma tare da ya jira cewa ta ba ya ci gaba da tausasa murya wajen cigaba da fadin; “Welcome to your humble abode, My Damsel S. (ZINARIYA ta, Siyam), I wish you a joyous and happy married life. Taimaka min ki daina wannan kukan haka, domin yau ranar farin cikin mu ce, ni HAMZAH da mai dakina… SIYAMA, ki sa a ran ki yau muka zo duniya dukkannin mu, rayuwar mu ta baya ta wuce kamar ba’ayi ta ba. Da yardar Ubangiji yau zamu fara rayuwar aure mai cike da soyayya, kurakuran mu na baya an ce duk daga ranar yau sun rikide sun koma aikin lada. Ina rokon Allah ya yi mana gafara, ya raba mana wannan ladan ni da ke da su Young Abba. Ina addu’ar Allah ya bani tsahon rai da dogon numfashi, wanda zai ishe ni in rikewa Abban mu amanar da ya bani. Ina rokon Ubangiji yasa kada in bashi kunya. Yasa kada in zama butulu (mai rama khairan da sharran). Ya sa in zamo mai saka khairan da mafi kyawun khairan. Amma hakan ba zai yiwu ba sai da hadin kan ki Siyam, sai naga farin ciki ko yaya a kan kyakkyawar fuskar ki zan samu nutsuwa. Wannan kukan da kike yi sai yake birkita ni, yake yi min kama da kina nadamar aure na ne! Na gane Siyam ba kiyi farin ciki da auren mu ba yanzu, kamar yadda ni nake yi, nake kuma kan yi, su Young Abba ma suke yi. Ko da yake ma kin fada da bakin ki a gaba na cewa kin fasa gabadaya”. Hamzah yayi maganar cikin tarin damuwar da ta nuna kan ta a muryar sa, mai nuna yadda maganar dana yi din dazu ya taba zuciyar shi sosai. Soyayyar dake dankare a ran sa ta nuna kanta baro-baro cikin ‘almond shaped’ idanun sa wadanda ke kyalli kamar hawaye ya kwanta a cikin su.Zuciyar Hamzah na wani irin hankoro a cikin kirjin sa, tana bugawa da sauri kamar zata fito ta bakin sa, da zai iya da ya hadiye Siyam ya huta. Daga wannan azababben SO da yaji yana kara samun muhalli a zuciyar sa, yana sake rubanya kan sa a yau. In ya tuna Siyam ce yau a gidan sa, zasu kwana su kuma tashi tare ne gida daya, zasu wayi gari ne a kan gado guda, alhalin tana matsayin matar sa ta halal kuma mallakin sa daga yanzu har zuwa wa’adin rayuwar da Allah ya debar masa, sai ya ji zuciyar ta kara karfin bugun da take yi da wani irin excitement. Babu wani farin ciki a rayuwar duniya da ya wuce masa wannan yanzu. Ban daina kuka ba, shi kuma bai bar roko na a kan in daina din ba yanzu-yanzu kafin mu bar cikin motar nan. Cikin dabara ya san yadda ya yi ya hada tafin hannun sa da nawa. Ya yi crossing yatsun hannun mu cikin na juna. Sannan yayi pressing hannun nawa da kyau cikin nasa. Sai na ji wata irin nutsuwa ta saukar min amma hakan bai sa na daina kukan ba. Da dai ya ga har zuwa lokacin bani da niyyar dainawa kuma duk lallashin sa ya fara karewa, muryar sa kanta rawa take yi, sai yayi shiru, ya kwantar da kansa a kan sitiyari, fararen idanun sa sun kada sun yi jazir da damuwa, ba tare da ya raba yatsun mu ba, suna sarke cikin junan su. Mun fi karfi mintuna sha biyar a haka, kafin Hamzah ya gaji, yace. “For Allah’s sake Siyam, ina kikeso in saka raina? Da wace damuwa kika fi so in ji? Da damuwar da na ke dauke da ita a rai na ta Kaka ta kike so in ji, wadda ke kwance asibiti rai a hannun Allah, cikin ciwon hawan jinin da a cewar ta ni na sanya mata shi, ko kuwa da farin cikin da nake ciki as well, mai neman fasa zuciya ta wanda kike son rikida min shi zuwa bacin rai? This is not the kind of welcome I deserve (ban cancanci wannan tarbar ba), a dai rana irin wannan mai dumbin tarihi da matukar muhimmanci a gare ni, rana ta farko da auren mu. Ko kin san tsayin lokacin da na dauka ina jiran zuwan wannan ranar, da irin muhimmin tanadin dana yi mata?” Sai na samu kaina da ciro fuska ta a hankali daga cikin cinyoyi na, na kuma rage sautin kuka na, amma duk da haka ban yarda na bude lullubin kai na ba. Maganganun sa da tone din da yayi amfani da shi wajen furta su, shi ya sanyaya zuciya ta, at the same time, (a lokaci guda) suka taru suka jefa min tausayin sa, maraicin sa ya fito tsantsa muraran a cikin sautin sa, da na tuna kuma bashi da kowa sai Kakar tasa… Ganin yayi galaba na dago kai na, sai ya samu kwarin guiwar cewa, “can I unveil it? I mean wannan katon mayafin? And see your beautiful, alluring and charming face wadda a kullum nake mararin ganin ta?” Hamzah ya tambaya da murya mafi taushin amo da ya mallaka daga can kasan makogaron sa, sounding romantic, loving, caring and concerned to his wife. Sake dukunkune fuskar tawa nayi cikin katon mayafin kunya ta lullebe ni, sai kawai ya fito daga motar ya zagayo bangaren dana ke ya bude min kofar, yana sake fadin, “Welcome to your humble abode! My Damsel S. ZINARIYA TA! My own darling, Siyam, my wife-my life, Azumi-Boddon Young Abba da Anti Nasara kuma kanwar Ya Omar, uwargidan Hamzah Mawonmase, mother of my incoming children, the one I truly cherished and love most! Marhaban to your humble abode”. A hankali na zuro kafafu na kasa, kai na ya yi girma da wannan kirari na Hamzah, watakila don kirarin ya fito ne daga bakin dana fi so akan na kowa ba don wai yafi kowa iya kirari ba. Na kasa tankwabe wannan girmamawa, kambamawa, martabawa, darajjawa, da kulawar tasa, kafin a hankali in fito da gangar jiki na duka daga cikin motor. Ina jin shi yana fadin “na fi so ki taka ki shiga gidan ki da kafafun ki cikin aminci, mu roki Allah dukkan alkhairin da ke cikin sa, mu kuma nemi tsari daga sharrin shaidanu da abin kin da ke cikin sa”. Hamzah in yana abubuwan sa ni yanzu har ya daina bani mamaki, kamar wanda aka haifa ya kuma tashi ya girma cikin Musulunci. Komai sai ya saka Allah ko da yake suma sun san akwai Allah. Sun dai yi masa kishiyoyi ne. Hannun sa ya saka cikin nawa, muka soma takawa a hankali zuwa kofar shiga apartment din anda ke cikin rukunin gidajen ‘Ceilo Apartments’ na tsakiyar birnin Washington D.C..
Chapter 5 · 0% Book details