← Book details Sakacin Waye Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 30

Sashe 21

Sakacin Waye Part 3 Complete Hausa Novel · about 4 min read

tunda shi bai ma san a kan me nake fushin da shi ba, ya san dai fushi na ke da shi, (and he admit it). Sai ya kama kan sa daga shiga sha’ani na, don baya son raini ko kadan, ban taba buda baki na gaya masa akan me nake fushi da shi ba, don kada ya ce na sakawa rayuwar sa da ibadar sa ido. Ko dazun da a ce ban shiga sabgarsa ba bazai shiga tawa ba, ya bani dama ne in yi ta fushi na har zuwa ranar da jaki zai yi kaho, shi kuma ya yi amfani da damar ya yi ta shan giyar sa wadda shirin da muke yi yasa yake boyewa, tunda na fita sabgar sa sai ya koma shan abarsa da lasisi, tunda yayi iya lallashin da zai iya ya gaji ban ce ga laifin da yayi min ba. Sai ya kama kan sa daga shiga sha’ani, na don kada ya sayowa kan sa raini. Ya kuma yi wa kansa alkawarin bazai taba forcing Siyama ta kwanta da shi ba, ba Siyama kadai ba, ya fi karfin ya kwanta da matar sa (out of force) a irin son da yake mata, da kuma farin jinin samun duk irin macen da yake so cikin farare da bakaken fata da Allah ya yi masa. Na sha jin yana fadin baya son mutum mai saka ido ga rayuwar wani, sa-ido sana’ar banza ne mai muni, gashi yanzu so nake kawai mu tafi gida Najeriya in gurfana gaban Abba na, in karbi hukunci komai tsaurin sa daga gare shi, in har hakan zai sa ya yafe mini, don haka dole in kwantar da kai ga Hamzah, in lallaba shi don passport dina yana hannun sa, Young Abba ya damka masa tun ranar daurin auren mu. Watakila inna kwantar da kai na daina tsanar sa a akan rashin rike addini in samu ya katse komai nasa mu tafi gida Najeriya in gyaro ta da Abba na ko na samu rahmar Allah da kwanciyar hankali, watakila in Abba ya yafe min zan samu saukin matsalolina da Hamzah tunda na tabbata cikin kowanne hali ina son Hamzah. Hamzah da komai nasa kaddarata ne daga Allah. In samu ya yarda muje gida nan kurkusa din shine babban kalubale na yanzu, tunda alhamdulillah nan da sati hudu zan kammala karatun digiri na. Hankali na bakidaya ya koma ga Abba da Ummati, da kuma tsaunin Mambillah tushe na. Kai har ma da Anti Wasila da kannena Maryam-Jamilah da Shurah-Nadiyah, da kanin nawa da aka haifa bana nan (Hayatudden). Ban sani ba ko idan aka yi bari ana kwashewa dai-dai??? Yanzun dai gani cikin hayyaci na ina neman Abba da soyayyar sa ruwa a jallo, bayan saukowa daga kololuwar dadin duniyar soyayyahr da Hamzah ya luluka da ni, na gane muhimmancin rashin soyayyar Abba cikin rayuwa ta, mace ba soyayyar namiji kawai take bukata ba, don cikar farin cikin ta, ita soyayyar namiji sau tari ta dan lokaci ce, da zarar an biya bukatar gangar jiki komai canzawa yake yi, soyayyar iyaye kuwa itace eternal abar da bata taba canzawa bata taba yankewa koda rai ya baci. A yau gani bayan tabbatuwar dukkan mafarkan da kuma burika na, Hamzan dana kusa salwantar da rayuwata domin in tsira da shi ya tabbatar min ni wawuya ce a kan sa, kuma marar sanin darajar iyaye, wadda ta zabi jin dadin ta daga jikin Da namiji akan farin cikin wanda ya kawo ta duniya…… Ina so na gyara wannan dingimemen kuskuren nawa idan mai gyaruwa ne tsakanina da mahaifi na, wanda giyar soyayyar mijin mafarki ta rufe min ido ta sa ban taba ankara da shi ba sai yau da Hamzah ya ankarar da ni. Koda Abba ba zai bani damar shiryawa da shi kamar da ba, in dai zan samu albarkar sa cikin aure na watakila ta taimaka min…wajen ganin Hamzah ya tsaya ya amsa sunan cikakken musulmi, mai tsaida sallah, mai azumi mai bada zakkah kuma mai kuma kiyaye dokokin Ubangiji. Amma shin an taba bari a kwashe daidai???
Chapter 21 · 0% Book details