← Book details Sakacin Waye Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 30

Sashe 19

Sakacin Waye Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

a tunani na a lokacin, ni Siyama daban nake da sauaran mata ‘yan uwa na, Yanzu na yarda babu wadda tafi wata ni da sauran ‘yammatan da ke macewa a kan soyayyar Hamzah Mustapha, idan a da ina tunanin hakan to na yarda da gaske na yaudari kai na, banbanci na dasu daya ne; ni na zabi addinin musulunci sama da Mawonmase din, amma kuma ai na bar Abba na a kan sa. Ni da shi mun zama bakin juna yanzu. Soyayya ta rikide ta zama wani abu da ya riga ya wuce cikin past kundin mu (littafin mu na baya) a lokacin da muke watanni tara kacal da aure. Ni na kasa fadar dalilin fita hanyar sa da na yi rana daya, wai jira na ke ya gaya min da kansa da bakin sa ya fita daga addinin musulunci, shi kuma ya kasa complaining ko titsiye ni a kan sai na fada masa laifin sa, kamar ya sha jinin jikin sa a kan laifukan nasa. Tun lokacin da yayi rarrashin duniya ban ce masa komai ba, ya gaji ya rabu da ni shima, ya koma baya magana kamar da, yayi cooling sosai sabida giya da yake faman sha kullum ya baro office don daukewa kan sa damuwar Siyamah. Sai ya zo ya yi min kwance-kwance a kan doguwar kujerar falo ko sofa din dakin barci na, ya kifa hular sa a kan fuskar sa, daga nan har garin Allah ya waye bana kara sanin me yake ciki. Ya daina magana kwatakwata, sallah kuma baya yi ko zan hadiyi zuciya bai sani ba. Daga ni har shi bama barcin kirki, gara ni ina tashi in yi nafilfili tsakar dare in roki Allah ya yi masa gafara, kada ya tashe shi a sahun “wailun likulli hummazatun lummazah”, shi kuwa Hamzah saidai juyi a kan kujera. Sai gidan namu ya koma tamkar gidan kurame babu mai cewa da dan uwan sa uffan. Tamkar ba amarya da angon nan na Miami Resort, masu neman cinye juna don soyayya ba. A daren yau na kasa jurewa jin sa ya shigo gidan wajen karfe daya na dare. Ko da na leka da ya fito daga motar sa da dafa bango ya idasa shigowa, wannan ya tabbatar min Hamzah a buge yake (fully intoxicated). Kuka ne mai karfi ya taho min nayi maza na saki labulen na fita falon na cimmasa. Ya zube cikin doguwar kujera yana maida numfashi yana wani irin lumlumshe ido, na tsaya a kan sa kamar an jefo ni falon. Takaicin ganin ya daga ido ya kalle ni da rinannun ‘almond shaped eyes’ din sa, ya kuma dauke kai kamar bai ganni ba, ya fusata ni matuka. Nace “kaico na da zaben son zuciya ta! Kaico na da zaben kafiri a matsayin abokin rayuwa ta, wanda ya zabi ya gusar da hankalin sa fiye da bautar Ubangiji, kaico na da tunanin zan iya maida mushriki musulmi, kaico na da auren mai fuska biyu! Kaico na akan biyewa abinda zuciyata ke so da neman samun sa kota halin-kaka. Kaico na da rashin baiwa Allah zabi da yiwa kai na addu’ar zabin Allah. Yadda ka yaudareni Hamzah, ka aure ni da sunan musulunci a fatar bakin ka Allah ya saka min tun a gidan duniya”. Sai ji kake kwaf! Hamzah ya sa kafar sa daga zaune ya kwaso ni ya warbar, saida na fada cikin kujera da baya na, yace, “ni kike cewa kaico da ni Siyama? Ana neman kafura mara tsoron Allah da sanin hakkin aure kuma mayaudariya aka same ki an gama Siyama. Ya yi murmushi cikin lumshe ido. “Wawiya kawai, sai tutiyar addini da fadin Allah a baki, alhalin bata san komai na daga martabar da Allah ya yiwa iyaye ba, ko ni da na tashi (in Christianity) da ace na tashi na tadda Babana a raye, ba zan sha poison don in rabu da shi in rayu da wata mace da sunan soyayya ba. “Kaico” ai yana wuyan ki Aisha-Siyamah, kullum tunanin ki shine kin fi kowa tsoron Allah, kin fi kowa sanin addini da kyautata shi. A hakan kuma na ga kin zabi ‘marital-sex’ din wanda kike kira kafuri kuma wanda kike so duk da kafurcin nasa, sama da Baban ki da ya haife ki, ya raine ki ya yi dawainiyar rayuwar ki da ta ilmin ki. Umhhh? Ya lumshe ido cikin maye sannan yace “Amma kullum ki yi ta nunawa mutum shi kafuri ne, bai san Allah ba sai ke, na riga na yarda Allah guda daya ne, idan wuta da aljannah mukullin kofofin su a hannun ki yake, in kin tashi hisabi ki jefa ni a wadda kika ga dama. Ni ban ce kin yaudare ni ba, ni da kika yaudara da Kalmar SO, kika koyawa wahalalliyar soyayya mai wuyar bari, sannan rana daya ban ankara ba kika yasar da ni a bakin kwalbati, ko in mutu ko in yi rai (after this deprivation) ba damuwar ki bane. Ban san soyayya ba sai a kan ki Siyam, ke kika koya mi soyayya mai wahala da wuyar bari, rana daya kin fahimtar dani cewa, you married me to have my body and my sweet sex only, tunda kin gama samun su da duk abinda kike so daga jiki na da zuciya ta, har da cikin haihuwa kin samu, shikenan ni Hamzah banida sauran amfani a gare ki ko? Kin gama da ni!”. Tunda ya fara maganar nan nake dafe da hannuwa a baki da kunci ina sauraron sa, hoping duk wadannan muggan maganganun dana ke ji yau suna fita daga bakin Hamzah Mawonmase cikin ire-iren mafarkai na nake jin su. Fata nake in farka in ga ba haka bane, fata nake in farka in gan mu cikin mayafin rufar mun nan na duvet mai tsananin laushi, muna makalkale da juna muna sumbatar juna kamar zamu cinye juna don so, ina addu’ar wannan ya kasance mafarki na guda daya rak a rayuwa da bazai taba zama REALITY ba. Amma har zuwa wani dogon lokaci mai tsaho da Hamzah ya gaji da gasa min maganganun da suka dade da nuna a bakin sa, bai taba samun damar amayar da su ba sai yau da ya samu damar data dace da shi, da ya gama ya tashi a daddafe ya shige dakin sa ya banko kofa, ban farka daga mafarkin nawa mai kama da ido biyu ba. “Lahaula walaquwwata illah billah.. Allahumma ajirni fi musibati….” kawai nake iya ambato, wasu hawaye masu zafi da dumi suna shimfido min suna sauka a kan kirji na, irin wadanda zafin su daga zuciya yake fitowa. Karfe uku na dare agogon Washington na kira Aunty Nasara a waya, tana dauka na ji dukkan kukan duniya ya kwace min. Kukan da ko sautin sa na musamman ne, wanda tun bayan awanni biyu da suka wuce nake so in yi shi na kasa, sai ajiyar zuciya da nake ta faman yi. Kewar gidan mu da al’ummar cikin sa ta dawo min sabuwa. Kewar Abba na Mamman Gembu, da tsayin lokacin dana dauka ba tare da shi ba da nadamar abinda nayi masa su suka sani yi wa Aunty Nasara wani irin kuka da kururuwa mai tsirga kwakwalwa da firgitata. Ni na tabbata alhakin Abba ne da rashin albarkar sa cikin aure na kadai suka sa Hamzah yau ya yi min abinda ban taba zato ba, an ce idan aka yi (depriving men from sexual life), suna aikata komai cikin bacin rai, amma ban zaci ko kusa Hamzah ko me zan yi masa zai taba iya yi min gorin nan ba. Aunty Nasara dana katsewa barci cikin tashin hankali ta ce. “Siyaman VOA, ya aka yi?” Na dauki lokaci ban amsa ba sai kukan nadama da kaico da kai. Cikin wannan halin na ce da Aunty “tabbas Aunty kin yi gaskiya, abinda babba ya hango yaro ko hau rimi ba zai hango ba. Hamzah ba zai taba musulunta sabida ni ba, sai don ya samu mallakar aure na da amincewa ta ga kaddarar auren sa, daga nan kuma ya cigaba da kafircin sa, tunda duk abinda yake so a Siyama ya gama samun sa. Na dakata na ja numfashi na da ke sarkewa kamar na mai ciwon asthma, na fyace hanci na sosai sannan na cigaba. “A wancan lokacin ban saurare ki ba, karewa ma na ji ki ne kawai, matsayin mai son hana ruwa gudu, sabida SO da son zuciya sun rufe min ido. Amma hakika zan dawo gaban iyaye na a safiyar gobe, ba zan zauna da shi a haka ba. Zan je kuma in fidda cikin sa tun ban haife shi ya tambaye ni dalilin kin zaba masa uba nagari ba, sai tubabbe mai shan giya. Na gode Allah da ban bari ya kai kan sa ga Abba na ba, na kara ma kaina bakin fenti a wurin sa ba, in ya ji tun asali wanene Hamzah. Aunty na dade ban gaya miki Hamzah bai bar giya ba, don kullum tunani na shine a hankali kuma immediately bayan auren mu zai bari, kamar yadda ya alkawarta muku, tun yana zuwa ‘Bar’ yana shawowa a can a boye ya dawo ya buya a dakin sa ni da gaanin sa hhar sai ta sake shi, har yanzu ya daina kunyar idanu na ya fara zuwa gida da abin sa, ko jiya na ga kwalaben giya (wine) a karkashin kujerar motar sa, wasu an sha, wasu ba’a bude bama”. Sai yanzu na fahimci nauyin barcin sa na lokaci-lokaci mai hana shi sallahr asubahi da sauran sallolin farillah ashe ba komai bane intoxication ne”. Ta kai ta kawo yau Hamzah ya sha da kyau, ta kai masa karo irin yadda ya kamata, ya yi min gori Aunty, gori irin wanda ban taba zato ba, ya fadi duk abinda ke zuciyar sa a kaina wanda ban taba sanin yana kallo na da su ba”. Don haka ki zo yanzu ki dauke ni ba sai gari ya waye ba, in ba haka ba na rantse a daren nan zan kama hanyar Mambillah, ko a kan iska ne zan yi fiffike in koma gaban Abba na, na hakura da auren, na hakura da soyayyar!”. “Innalilahi wa’inna ilaihi rajioun” in ji Anty, damuwa da tashin hankali karara a cikin muryar ta tace, “Siyama
Chapter 19 · 0% Book details