← Book details Sakacin Waye Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 30

Sashe 26

Sakacin Waye Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

cewar Hamzah da yace ‘we are meant for each other’. Muna karya kumallo da safe bayan dukkan mu mun yi wanka mun sha ado cikin sababbin sutturah, ga kamshin turaren da kowannen mu ke amfani da shi ya kama dining din. Fuskokin mu cike da annuri kamar bamu ne masu takun sakar jiya ba. Zuwa can na aje cokali mai yatsu (fork) da ke hannu na bayan na cika bakina da ‘chips’ din da na cokalo a jiki, nace cikin rangwadar da kai. “Shaheed, yaushe zamu je gida ne? Jiya na yi mafarkin na kaiwa Abba jariri ya kore mu ni da Babyn nawa, I was scared, it was a bad dream wanda ya tunasar dani cewa har yanzu Abba na yana fushi dani”. Hamzah ya kurbi coffee din sa ya aje kofin a gaban sa ya dan tsura min ido, bai san me yasa ko kadan ba ya son Siyam ta yi maganar zuwan su gida Najeriya yanzu, don ji yake kamar idan ta samu shiryawa da Abban ta zai raba su ne ya aurawa Omar, ya dan girgiza kai da sauri kafin yace “please and please Siyam, ki yi hakuri, zan kai ki gida, zamu je Abuja da Mambillah Plateau, ‘but not in this condition’ da kike ciki. Nima kuma ba yanzu zan dau hutu ba, sai watan haihuwar ki ya kama don in samu lokaci mu haihu tare. Mu da zuwa Najeriya Siyam sai kin haihu. I’m so sorry ban cika wannan alkawarin da wuri ba. Ba zan iya barin ki ki hau jirgi ba yanzu ba, I swear sai kin sauka lafiya na rugume da na a hannu na. In ya so kin ga sai mu kaiwa Abba babynmu, maiyuwa albarkacin sa yafi saurin yafe mana, in ya koro mu kuma, sai mu zauna a gate din gidan sa koda zamu shekara kullum ya fito ya bule mu da kurar motar sa, da haka da haka har sai ya huce ko don tausayin yaron mu da ke kofar gate din gidan sa. Zuwa lokacin kuma ni da ke mun daina fada” na yi dariya na ce “ni ai ka sani bani da matsala da kai sai akan sallah Habeeby, in zaka dore daga canjin da na gani daga jiya zuwa yau, wallahi baka da matsala da ni kowacce iri. Komai bayan wannan zan masa uzuri da son da nake maka. Amma banda rashin sallah. Taimaka min ka kai ni gurin Abba in neme shi da ya yafe mini, ko na samu cikar farin ciki da sukuni a zuciya ta, in yaso ko tsire mu zai yi yasa mashi ya tsire mu”. Hamzah yayi min wata kasaitattar hararar SO, ya ce “idan duniyar ta ishe ki, dadin auren soyayya ya ishe ki, ni yanzu na saka damba a son su da jin dadin su, ki daina yi min fatan tsirewa”. “Nace duk naji, amma kuma ba haka muka yi alkawari da kai ba Habeeby, kayi alkawarin kai ni gida da shirya ni da Abba na ASAP da yin auren mu. Yau gashi har muna neman shekara baka ko so in tada zancen”. Yace har gobe alkawarin nan dana dauka yana nan Siyam. Tare da ni zamu je ga Abba. Kin wuce in miki alkawarin da na san bazan cika ba. Amma yanzu akwai abinda nake jira daga gare ki kafin mu kai da tafiyar (baby). Bana so in ce miki kuma I’m afraid of Abbah’s decision, in ya ji cewa ‘I was not born in Islam”. Wallahi tsoro nake ji, tsoron haduwata da Abba nake yi, haka Ummati sai nake hango rigimar ta irin ta Kakata ce, yanzu haka tana so ta bakunce mu, tuntuni nake so in gaya miki. Amma ina tsoron kada ta zo ta tada maki hankali, kin san ba da yardar ta nima nayi aure da ke ba, I just ignored her, amma dai na sanar da ita. Siyam my Grandma is my everything, help me respect her. Kada ki sako issue na addini a zaman da zata yi, addinin mu na gare mu, itama nata na gare ta. But always remember she is part of me! Bazan iya rabuwa da ita akan kowa ba”. Duk da na hango matsala gagaruma na shirin samu na da tashin hankalin da zuwan nata zai iya zame mana, tunda da kan sa ya gaya min bata kaunar aure na da shi da irin yadda ta daga hankalin ta akan auren mu, har da su hawan jini ta gamu da shi da kwanciya a asibiti, a cewar ta gara ya kashe ta da hannun sa a kan ya auri musulma kuma bahaushiya/bafullatana. Amma me? Sai na tuna ita din Kakar Hamzah ce wadda ta haifi wanda ya kawo min shi duniya, don haka ita makwafin Uwa ce ga ‘Dream Husband’ dina. An ce Majnoon yana girmama hatta Karen da ya fito daga ahalin gidan su Lailah…. Balle KAKAR SA…. Wadda ita ta tsaya ta rainar mun shi a bayan rashin iyayen sa, ta kuma gina rayuwar sa positively har a yanzu na samu nake mora iya mora. “Grandma is most welcome. Kuma tunda bamu da dakin baki, ina ganin mu bar mata nawa dakin, in ya so ni sai in tattara abubuwan bukatata in koma naka dakin har zuwa komawar ta, ko kuwa ya ka gani?” Hamzah ya sumbaci goshi na ya ce “to say I thank you, is not enough to express the gratitude”. Sati biyu bayan haka na fara zuwa awo, bayan cikin ya riga ya girma, in the process, aka bukaci awon jini na dana Hamzah, don suna son gano genotype. A zaqule-zaqule irin na bature suka tabbatar mana yaro ko yarinyar da zan haifa zai iya zama sikila, aka tabbatar mana genotype dina dana Hamzah mai bada sickle cell children ne. Har likitar wadda ‘yar kasar Brazil ce take fadan don me muka yi aure ba tare da mun yi awon jini ba? Ko kuwa muna sane muka yi wannan gangancin? Har bayan mun bada baya ko gama fita daga ofishin bamu yi ba muka ji tana tattaunawa da likitoci ‘yan uwan ta cikin fushi tana fadin kadan daga matsalar ‘yan kasar Najeriya, in suka tashi yin aure basa tsayawa su tabbatar da rukunin jinin su sai soyayya…. Soyayyya…. Su haifi ‘ya’ya su a wahale ‘ya’yan a wahale, har karshen rayuwar su. Idan ma an samu ‘ya’yan sun yi tsawon rai kenan. Tashin hankalin da muke ciki ni da Hamzah, shi ya hana maganganun ta na karshe su bata mana rai. Ciki na irin cikin nan ne mai canza fasalin halitta, duk na bude hanci ya kara girma. Ga wasu kurarraji da suka cika min fuska na babu gaira babu dalili don kuwa ni ba shafe shafe nake yi ba. Hamzah tuki yake a hanyar mu ta komawa gida, but he cannot control his tears. Ni kuwa shiru na yi ina sauraron bugun da zuciya ta ke yi. To amma ya zamu yi da hukuncin Ubangiji? Na tuna nawa uban, ashe haka yake ji in aka ce bani da lafiya? Yasa hankaci ya tsane hawayen danun sa ya ce “a duk yadda Allah ya bani su ina son su, kuma a haka zan raine su. I wil make sure na soma tara kudi tun yanzu, na daina almubazzaranci, idan Allah ya raya min su ko su nawa ne zan biya ayi musu ‘Bone Marrow Transplant, I cannot endure to see any of my children suffering”. Yana ta magana ni kuma ina tuno nawa Abban accordingly, maganganun sa sai suke ta zame min (a food for thought), na tsananin soyayyar da Allah ya sanya tsakanin Uba da Da, amma ni na sa kafa nayi fatali da soyayyar nawa Uban sabida son cika burin rai na da abinda zuciyata ke so. Hawaye na na kara ninkuwa, begen Abba da nadamar abubuwan da na yi masa na sake kama ni, wadanda a tunanin Hamzah ina fitar da su ne don an ce ‘ya’yan mu zasu iya kasancewa masu sickle cell anemia yace kuma ba zai tsaida haihuwa ba wai sabida zai haifi Sickler ko Carrier, duk abinda zai fito daga jiki na ko ba mutum bane yana so, bashi da family bashi da wanda zai kira jinin sa bayan Kakar sa da abinda ke ciki na yanzu. Cikin wannan damuwar muke duk mun rasa walwala a ranakun da suka biyo baya. Komai namu ya tsaya cak sabida damuwa. Har sai lokacin da Kaka Veronica ta iso United States. Ni da shi muka je dauko ta a filin jirgi Hamzah na rike da hannu na. Daga can nesa na hango wata gyatuma gajeruwa cikin fararen kayan malaman addinin kirista, tana tafe rungume da Bible da sarka mai katon ‘cross’ a wuyanta wadda ta sauko har zuwa cikin ta. Ta saka farin gilashi mai kara karfin gani tana tafe a daddafe. A zuciyata na shiga maimaita, “Amantu billahi rabba, wa bil Islama Deena, wa bi Muhammadur-Rasulullahi SAW Nabiyyan wa Rasoola!”. Sau tari, na kan maimaita imani na da addini na a zuciya ta, a duk lokacin da na ci karo da ‘yan sauran addinai a kasar nan, domin gasu nan birjit har da ‘yan addinin Buddu, wato ‘Budduism’, ‘yan Sikh wato ‘yan ‘Sikhism’ da ‘yan Hinduism wato ‘yan addinin Hindu (masu bautar Saniya) ba irin wadanda bana gani a kasar ta Amurka. Hamzah bai saki hannu na ba har ta karaso inda muke, idon ta a kaina bata ko kiftawa. Kasa gaskata kyawun halittar matar jikan nata tayi, gata fara tas jawur da ita kamar sai ka wanke hannu kafin ka taba, anya kuwa ‘yar Najeriya ce da gaske kamar yadda ya ce? A fili Kaka ta ce “Jesus christ! So this epitome of beauty is what snatch away my Grandson”. Kafin ta karaso ya saki hannu na ya karasa ya rungume ta amma bai karba mata Bible din hannun ta ba, sai akwatin kayan ta data ke ja da ya karba, ya iso inda nake tsaye ya bani akwatin sannan yace in gaishe ta. Ni kuma hararar data ke ta zabga min ne ya dinke min baki ya kuma kashe min guiwa na kasa magana balle in yi mata sannu da zuwa, har muka zo shiga mota na kasa ce mata komai, sai da ta shiga gefen
Chapter 26 · 0% Book details