Sashe 3
Sakacin Waye Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hamzahn VOA!!! Hamzah Al-Mustapha. Ko ko in ce Hamzah Mawonmase!!! Sabon musulmin nan da ya dabaibaye zuciya ta ni Siyama ta ko’ina, ya hana ta salama da kwanciyar hankali tun daga shekarun kuruciya, balaga har zuwa girma na. Nauyin hakkokin rayuwar sa da jin dadin rayuwar sa bakidaya da walwalar sa, duka sun rataya a wuya na yanzu. Wannan din kadai in aka duba ba karamin responsibility bane ga diya mace. Domin shine tushen farko kuma tubalin kafa rayuwar iyalin ta. Dole ta samu sauyi a zuciyar ta a wannan ranar. Sai na shiga tambayar kai na da gaske ne ni din amarya ce yanzu? Ni, AISHATUL - SIYAMA MAMMAM GEMBU? Na zama matar aure? Matar kuma ba ta kowa ba ta Mr. Radio dina, ko kuma in ce “The Birom Man’s Bride”. Mijin kuma ba kowa bane face Mijin nan na Mafarki na, mijin burika na; dan mutanen Birom haihuwar addinin ‘christianity’. Wanda a sanda na gamu da shi ban taba hango yiyuwar aure tsakani na da shi ba ta kowacce hanya. Ya tabbata a fili, ni Siyama ina cikin rukunin mutane masu sa’ar samun tabbatuwar mafarkan su zuwa ‘reality’. Amma gashi na kasa yin farin ciki da hakan ko kankani, ko mai yasa??? Ni na san babbar damuwata ita ce kin amsar aure na da Abba ya yi. Ummati bata san an yi ba, duk da na san Young Abba yayi komai kan gaban kan sa ne sabida kaunar da yake yi mun, da burin sa na kasancewa ta cikin farin ciki na har abada da wanda na zaba nake kuma so. Ya gwammace su ya bata musu, don ni ya faranta min saboda maraici na, da kuma kaunar sa ga son ya ga ya ceci burika na da mafarkai na da kullum yake jin labari. Amma kuma sai me? Sai gashi duk da wannan assurance din dana ke da shi, ban ji farin ciki ya mamaye ni irin wanda amare ke ji a ranar auren su ba. Musamman in suka yi katarin auren wanda suke mutuwar so ne iri na. Maimakon hakan, tarin damuwa da kunci na babu gaira babu dalili ne suka taru suka danne zuciya ta, suka lullube tsagwaron farin cikin da ke saman ta wanda shi ya fi dacewa da ni, suka mai da shi damuwa tsantsa, zuciya ta da gangar jiki na suka yi wani irin sanyi lakwas. Kai ka ce ba DREAM HUSBAND dina Young Abba yasa kwanjin sa na kanin Uba ya aura min ba. A irin wannan ranar wato (ranar daurin aure), duk karfin soyayyar da mace ke yi wa mijin, sau tari zaka samu ta ragu, wasu ma matsananciyar tsana take komawa, musamman in ta tuna raba ta zai yi da gidan su da iyayen ta baki daya. To kusan hakan ce ta faru da ni nima, a wannan rana mai dimbin tarihi a cikin rayuwa ta data Hamzah, ranar da Young Abba ya damkamin sadaki na na aure, wato warawaran zinare guda uku da Hamzah ya bayar, ya bani su a hannu na ne matsayin sadaki na. Ya kuma tabbatar min (bayan dukkan kalubalen da suka faru) ‘against all odds, at long last’, yau na mallaki abinda zuciya ta da ruhi na ke so (na zama matar Hamzah karkashin igiyar aure na Musulunci). Hamzah Mawonmase dai, namiji daya cikin dubu a zuciya ta, ni Aishatul-Siyama. Wanda nayi ittifakin an halicce ni ne tare da kaunar sa tun ban san shi ba. Na girma, na kuma rayu da soyayyar fantasies din sa tare da ni, na dade ina tafiya a kan siradi na buri da begen haduwa da shi, da begen tabbatuwar mafarkai na a kan sa. Amma gashi yau dana same shi ban ji farin ciki ba. Ban yi murnar da ya kamata in yi ba. A zahiri ban tsane shi ba, kamar yadda wasu amaren ke tsanar mazajen su ranar daurin auren su, domin na tabbata nawa issue din is extraordinary dana kowa (da soyayyar sa ni a ka halicce ni, da ita na girma, cikin ta na rayu, cikin ta na budi ido). Amma duk da haka fama nake da matsananciyar fargaba, damuwa da rashin kwanciyar hankali idan na tuna reaction din Abba na nufin rashin amincewa da auren, in aka yi la’akari da irin karbar da yayi wa maganar aure na a lokacin da Young Abba ya sanar da shi. A can wani dan kankanin sako, ko in ce wani dan lungu na zuciyar kuma, bidirin farin ciki ne ke gudana irin na cikar buri, ga kuma alhini da taraddadin Abba. Wato akwai wani guilty conscience din yin aure ba da yawun Abba Na ba a tattare da ni, ba da cikakkiyar yarda da sanya albarkar sa da kuma cikakken iznin sa ba. Na tabbata abinda ya hana farin cikin nawa cika kenan. Don haka in ka ganni a wannan lokacin sai ka rasa gane a halin da na ke ciki. Na yi tagumi kawai na rasa abunda ke min dadi. Irin rafkeken tagumin da na rafka a gefen gado na na gidan Young Abba, kai in ka ganni a sannan sai nayi maka kama da mai tsohuwar takaba. A haka Aunty Nasara ta shigo daki na ta same ni bayan sun gama fafatawar su da Young Abba a kan maganar biki, tana ta mita kamar ta ari baki, (daman dai na dade da sanin Nasara ba dai mita ba), balle a ce ta samu dalilin yin ta. Fadi take tun daga bakin kofa “ni na taba ganin mutun dan gaggawa irin Baban ki?” Ta karasa shigowa dakin ta na cigaba da cewa. “Sai ki tashi haka daga tagumin nan, wanda ba abinda zai sa ba abinda zai hana. Domin kuwa Baban ki Adamu Sarkin gaggawar Gembu baki daya, shugaban rigimammun birnin Washington D.C, ya ce yau zaki tare ba daga kafa, kafar ki kafar Hamzah, kuma kada in kai ki da komai, a cewar sa already Hamzah na hanya ma, ya taho daukar ki, yanzu zai zo ku tafi”. Nasara ta dan nisa cikin damuwa, kafin ta zauna a gefe na ta kama hannaye na ta rike su cikin nata. Da sanyin murya ta cigaba da magana. “Gashi kuma Siyama ban shirya miki komai ba, domin komai ya zo mana bagatatan ba shiri, sannan a kurace (a kurarren lokaci). Na so ya bari in shirya ki ko na sati daya ne. Amma Baban naki wani irin sha-yanzu ne magani-yanzu, bana son halin nan nasa na gaggawa amma ya zan yi? Tunda shi ke iko da mu dukkanmu, ba mu ke iko da shi ba?! Siyama a yau zamu kai ki gidan miji, ta kowanne fanni bani da haufi kan tarbiyyar da muka yi maki, ko in ce, Ummati da Wasila suka yi miki muka dora daga inda suka tsaya. Amma na hore ki da hakuri, shikadai zan miki guzurin sa, idan na ce hakuri ina nufin hakuri da halin miji, shi hakurin nan da kike ji ana fada ana kara jaddadawa a cikin aure dole ne. Ki bar ganin kina son sa yana son ki kamar ku hadiye juna, kiyi tunanin shikenan baku da sauran matsala a gaban ku sai soyayya, wallahi zaman aure ya wuce tunanin ki. Dole watarana a sha Zuma..., watarana a sha Madaci. Tunda zaman abu ne na din-din-din (abu ne da bashi da karshe, kuma ibada ne. Tunda ibada ne kuwa fata a ke a dawwama cikin sa har abada. Cikin kowacce ibada kuwa sai an saka juriya, yakanah da hakuri Siyama. Ina cewa kiyi hakuri ne sabida watarana zaki ga abinda bakya so a auren Hamzah, ba kuma fata nake yi ba, a’ah reality ne na rayuwa yau da dadi gobe babu, ko ba dade ko bajima sai an samu sabani, ba don yana tubabbe ba a’ah, ko wadanda aka haifa cikin musulunci suna kuskurewa matan su, matan ma na kuskure musu, bar ganin yawan son da kike masa ko yake miki, ki dauka baza ku taba batawa juna rai ba; no body is perfect, shi kalubale a rayuwar aure wani abu ne inevitable (wanda ba makawar sa). Abin bukata shine ayi wa juna uzuri da karfin soyayyar dake a tsakani. Ki kula da girki, tunda kin ga yana son abincin gargajiyar su sosai. Musamman na tashi al’adar (Gwaten Acca, kunun Acca, tuwon Acca). To ki zage ki koya ko a yanar gizo ne. Ki dauki kan ki ‘yar kabilar Birom yanzu, addinin ku ne kawai ba daya ba. Ki kuma cigaba da nuna masa komai na addini bi da bi, kada ki gaza, kada ki kosa, tunda ke din Alhamdulillahi Malama ce mai zaman kanta, kada ki yi kasa a gwiwa kada ki yi fushi idan ya yi wani abin haushin, kada ki sare idan bai dauka da wuri ba, kada ki yi kasa a gwiwa wajen fada masa ALLAH na kallon sa, sai a hankali zai iya mastering komai. Yanzu Hamzah shi da jaririn da aka haifa ake raino ta fuskar addini basu da maraba, don haka sai kin mike tsaye kin jajirce wajen ganin kin yi amfani da ilmin addinin da Allah Ya baki wajen koyar da shi. Ki fara koya masa karatun Al’qur’ani tun daga Nasi har Baqarah. Ba wata makaranta da zai shiga da zata fi taki muhimmanci da kusanci gare shi a yanzu, tunda kullum kuna tare a gida daya kuma a gado daya. Wannan nauyin yana kan ki ba wanda zai jure shi sai ke. A zaune kuke, a tsaye kuke ko a kwance yi ta koya masa karatun Alqur’ani koda aya dai-dai ne a rana. Ta fannin tsaftar jiki bana jin ki Siyama. Na sallama miki. Allah ya baku zaman lafiya da zuri’a mai albarka ku zo ku cika mana gidannan da jikoki mu yi ta bari-bari”. Sai naji zuciyata bakidaya ta karye, dama kuma a mace take murus, idan na tuna cewa ranar rabuwa ta da Aunty Nasara ne ya zo sai ta idasa kakkaryewa da wani irin kekkecewa, shin da gaske ne? Ko kuwa dai mafarki nake yi tunda ni din dama ma’abociyar mafarke-mafarke kala-kala ce? Da gaske yau zan bar gidan Young Abba zuwa gidan Hamzah Mawonmase, amma gashi bana farin ciki as expected? Da gaske na bar Aunty Nasara da Baba na makwafin Uba wato Young