Sashe 8
Sakacin Waye Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
sirrin da aure kadai ke wanzar da shi. Bamu samu kan mu ba sai gab da kiran assalatun fari, Hamzah bai huta ba, nima kuma bai bar ni huta ba a daren yau bakidayan sa, sai da ya tabbatar duk wani hijabi dake tsakanin mu ya cire shi a yau, na gama amsa sunan cikakkiyar matar sa wadda ko yau ya fadi ya mutu sai na yi masa iddah. Ni kuma na samu cikar dukkan mafarkai na da burika na a kan sa, har fiye da yadda nake kintacen tabbatuwar su a lokutan mafarkai na. He is so genius, and so romantic beyond my expectations, ta fannin kula da matar sa a auratayya. Shi da kan sa ya taimaka min da duk irin taimakon da ya dace a yi wa amarya a daren farko, alhalin shi Hamzah ba likita bane, amma taimakon da yayi min ko wani babban likitan mata sai haka. Sannan muka yi sallahr asubah tare, amma kam a zaune na yi tawa sallahr sakamakon kafafu na duka ciwo suke min, a haka na daure nayi domin na ji dadin taimakon da ya yi min da ruwan zafi a toilet. Da muka idar da sallah muka koma cikin duvet dukkannin mu a gajiye, wani barcin asubah ya dauke mu tare, kankame cikin jikin juna kamar tare aka haicce mu, soyayyar dake zukatan mu ta kara habaka ta ninka ta farko, don a yanzu ne muka san ainahin muna son juna. Hamzah ya riga ni tashi a wayewar gari, sai bai tashe ni ba, tausayi na yake ji sosai, kan rashin daga kafar sa a ranar mu ta farko, da irin wahalar da ya san ya bani don shi kan sa bai san haka al’amarin yake ba sai yau. Shiyasa ya kasa sarrafa kan sa. Sai ya koma babban falo, ya kwanta bisa doguwar kujerar falon, yayi filo da dogayen hannayen sa masu yawan gargasa. A hankali ya lumshe idanun sa yana tuno abubuwan da suka faru daren jiya, wadanda bazasu taba shafewa daga cikin darare mafi muhimmanci a rayuwar shi ba. It was like ya je aljannah ta bakwai ya dandana ni’imar cikin ta, ya dawo duniya. Wani abun da ya bashi mamaki sai ya ji ba abinda yake son sha a wannan lokacin sai BARASA, kamar yadda yake a al’adar sa ta baya, yana shan ta ne a lokutan farin ciki dana bacin rai, abinda ya dade bai sha ta ba, ya manta yaushe rabon sa da ita, mai yuwuwa tun fara neman sa da Siyama da Young Abba ya gargade shi a kan haramcin shan ta cikin addinin da ya karba da hannu bibbiyu. A yanzun kuma he’s overwhelmed with happiness and excitement, yana neman abinda zai rage masa excitement din sa. Kada son Siyam da farin cikin data haddasa masa daren jiya su taru su kassara shi. An ce wani excitement in yayi yawa zai iya yin lahani ga zuciya da kwakwalwa. He needs something that will cool it, reduce it and if possible, giyar da ya jima bai sha ba. Dama shi din ya kan sha barasa ne a lokuta guda biyu; lokacin bacin rai ko na tsananin farin ciki, ko kuma lokutan da kadaici ko damuwar rashin iyali suka taru suka yi masa yawa, yake neman abinda zai dauke masa damuwar su. Amma Young Abba ya gaya masa as a devoted Moslem yanzu dole ya bar barasa, a matsayin sa na musulmi na hakika, wanda yayi alkawarin bin duk wasu ka’idoji na addinin musulunci, in har ya san yana shan ta. Kuma ya san haka tunma kafin ya san Siyama. A lokacin da Young Abba ya fada masa giya haramun ce (in Islam) yayi masa alkawarin bari da zuciya daya. Knowing that, barin shine kadai abinda zai bashi Siyama. Kuma tun ranar da ya hana shi din ya bari. Rabon sa da shan barasa, tun ranar da ya ga Siyam gani na farko. Amma wani abun mamaki yanzu ji yake a ran sa in bai sha ba ‘excitement’ zai kashe shi ko ya fasa masa zuciya, farin cikin da yake ciki is beyond control din sa, idan son samu ne yana son yayi moderating din sa da barasar. In ba haka ba jinin sa zai iya hawa da excitement din. Ya dade da ajiyewa ran sa alkawarin tarawa da matar duk da ya aura a rana ta farko na auren su babu jinkirtawa saboda yadda ya kame kansa daga dattin zina. Ya yi wa ranar tanadi mai yawan gaske. Bai ma san al’amarin haka yake ba sai yau da ya kusanci matar sa da yake matukar so wadda Allah ya bashi cikin kaddarar sa wato Siyama.... yayi making love mai tsafta kuma dan asali da ita wanda ya zauna ya kasa barin ran sa, komai ya faru yadda ya dade da tsarawa da son kasancewar sa, har fiye da yadda ya tsara, burin sa a kan matar duk da ya aura don so da kauna ya cika, it’s unbearable happiness da wani shaidanin bangare na zuciyar sa ke gaya masa dole ya sha barasa don rage shi, kada ya zama matsala ga zuciyar sa. Wata zuciyar na kwabar sa, wata na angizawa da cewa in ya sha yau, gobe ba zai kara ba ai. Ai ya gwada bari a baya kadan ya ga cewa (with time) zai iya barin, amma a hankali. Shima Young Abban, ai ya gaya masa gaskiya cewa gradually zai iya bari ba rana daya ba. In haka ne bai saba alkawari ba. Let it be a farewell tsakanin sa da barasa. A final farewell tsakanin sa da kowanne ayyukan kafurci, tunda ya mallaki Siyaman gata kwance cikin gidan sa matsayin matar sa to zai yi komai don ya tsira da ita, amma a hankali. Sai kawai ya suri mukullin mota ya fice. Karar tashin motar sa dana ji shi ya sani farkawa daga nannauyan barcin dana samu, koda yake na jima da farkawar mikewa daga gadon ne ya gagare ni, sabida nauyin da jiki na yayi min, na leka ta taga, sai na hango danjar motar sa ya fice daga gidan da mugun gudun gaske. Ko ina zashi haka kamar mai shirin tashi sama? Allah masani. Fata na dai koma ina ne ya dawo lafiya kuma kada ya dade. Yanzu ne ma na san na fara son miji na wato Hamzah Mustapha (Mawonmase), so ba na wasa ba irin wanda physical relationship (gamayyar jiki) na aure ke assasawa, tunda yanzu ne na san darajar sa da kimar sa da irin baiwarwakin da Allah ya yi masa, na baya duk shimfida ne, kasancewar a can bayan duka a kan gaibu nake tafiya, yanzu ne nake tafiya dodar a kan turbar soyayyar reality wato ta rayuwar aure na zahiri ba cikin gaibu ba. Yanzu ne nake gayawa kai na ban yi kuskure wajen dagewa da nayi na tseratar da mafarkai na ba. Hamzah ya cancanci duk wahalar dana sha a kan sa, domin gashi a dare daya shi ya fanshe min ita, ta sama da shekaru da goma. Na rantse babu inda bai shaida soyayyar da Hamzah ya nuna min jiya a gangar jiki na ba. Ko a gaban Allah kuma gabban jiki na zasu bada shaidar hakan. Cewa sun haida da iri soyayyar Hamzah mai tsayawa a zuciyar diya mace. Bayan na ji fitar sa daga Condo din mu, na kunna fitila dakin ya gauraye da haske, kasancewar ya saki fararen curtains (labulayen) dakin duka, ya kunna min room heater, ya kuma kashe duka kwayayen lantarkin dakin kafin ya fita. Making sure bai yi motsin da zai tada ni ba. Dana juya gefe na farar Singlet din sa na gani a gefe, ya manta bai maida ita jikin sa ba. Daukar singlet din nayi na zauna a bakin gado na ina murmushin tuno wasu abubuwan da suka faru jiya, a hankali na rufa ta a kana fuska ta ina shakar kamshin Hamzah. Wato na turaren Guerlain Vetiver wanda nake kira (turaren Hamzah), ya kama rigar sosai, turare ne hamshaki mai sanyin kamshi na mazan da suka amsa sunan su (men’s perfume), wanda a tsayin rayuwa ta ban taba jin turare mai dadin kamshin sa da sakawa mace nutsuwa da mijin ta hadi da tada tsumin soyayyar ta gare shi kamar sa ba. Ko kuwa don kawai ina son mai shi ne da komai nasa? Na yi kokari iyakar iyawa ta na dauke tsoron da ya same ni a lokacin, for the first time in our lives na bashi farin cikin da na san ya cancanta in bashi daren jiya, tunda shima ya gama min komai, tunda ya taimaka wajen maida mafarkai na zuwa reality. A lokacin da suka zo min a baude, har nake tunanin bazasu taba zama reality ba. Sai ya tsaya cikin dan lokaci ya cike wannan wawakeken gap din dake tsakanin mu, wato na addini ta hanyar musulunta ba don ya shiryawa hakan ba sai don a cewar sa ya dade yana sha’awar hakan, sai soyayya ta ta zame masa jagora, ya ceci soyayyar mu, ya kuma ceci mafarkai na a kan sa. Amma haka siddan sai wani bakon tunani ya zo min, kamar ina bukatar kara sanin waye Hamzah, bayan wannan dan sanin dana yi masa. Kamar sanin dana yi masa yayi kadan a matsayi na na matar sa yanzu, domin a dan takaitaccen lokaci ne komai ya faru (haduwar da auren) duka - duka bayyanar sa gare ni zuwa faruwar komai yaushe ne? Allah ne kawai ya yi ikon sa a kan mu (ya tabbatar da aure a tsakanin mu). Sai na saka fuska cikin tafuka na na rufe idanu na, da rigar singlet Hamzah a kan fuska ta. Zuciyar nan mai tsananin son Hamzah da kaunar sa…. na kalubalantar sabon tunani na a kan sa, ta hanyar jefo min tambaya; Shin Siyama akwai wani sani ne na daban da ya rage baki yi masa ba? Kin san asalin sa da addinin sa na iyaye da kakanni kuma a hakan kika ce kin ji kin gani. Zuciya mafi hankali da tunani mai kyau ta ce a’ah, akwai sanin da ya kamata na yi masa bayan wannan din, na halayya da dabi’a, wanda na yi masa daga bayyanar sa gare ni zuwa yanzu bai wadatar a