Sashe 25
Sakacin Waye Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
yi miki ba” na gyada kai na ce, “Hamzah ka san Dawanau ta garin Kano? To ita ce a kaina bakidaya Hamzah!” Hawaye suka biyo bayan furuci na. Sai Hamzah ya sassauta tone din sa, cikin sanyin murya ya ce “follow me, please Siyam”, tare da janyo hannu na ta karfi muka fito daga ‘toilet’ din. A gefen gadon mu ya zaunar damu, kafin ya janyo ni ina hawayen ina komai ina tirjewa ina ture shi, da karfi ya rungume ni a kirjin sa tsam-tsam, ya ce “Siyam, na san ruwa ba ya tsami banza, haka kawai Siyam bazata taba cewa ta gaji da ‘dream husband’ din ta ko ta daina son sa ba, sai bisa babban dalili”. Cikin tsokana Hamzah ya kara da cewa, “ni ne fa Hamzah-Mawonmase Dream Husband din siyama, ni ne wanda aka sha ‘poison’ a kan sa alhalin ko sani na ba’a yi ba, tun gabanin a san ni mummuna ne ko akasin haka, mai sallah ne ko mara sallah, aka bata da Abba da matsoraci (Ya Omar) duk saboda ni, a tunanin ki akwai abinda zai sa wannan son ya jijjiga ko ya kwaranye cikin ‘yan watannin da har yau basu kai ga cika shekara ba babu wani dalili? Ai sai dai ki fadi hakan (out of frustration) din wani bacin ran dana saka ki ba tare da na sani ba. Ki yarda da ni, Hamzah&Siyam are meant for each other. Ours is made from the heaven!!!”. Maimakon in ji kalaman sa sun min dadi, kamar yadda suke tafiya da ni da Imani na a baya, musamman idan na tsinci kaina a kan ingarman kirjin sa irin haka, yana rungume da ni, yana shafa kwantaccen gashin kaina da baya gajiya da shafar shi, yana rada min kalaman a cikin kunnuwa na kamar dai yadda muke a halin yanzu, sai na ji kalaman nasa sun rikide sun sake koma min GORI mai zafi fiye dana jiya, kamar Hamzah yau GORIn nasa na cikin ruwan sanyi ne yake mun ba irin na jiya na keke-da-keke ba, a yadda kwakwalwata ta fassara min. Wannan ya kara dugunzuma fushi na, na shiga bugun sa ko ta ina ina kokarin kwacewa daga cikin rikon sa amma ya ki cika ni, ina kuka wurjanjan ina fadin “dole kayi min gori, kana da dukkan damar yi min shi, nima na yarda ni wawuya ce, wadda ta zabi soyayya a kan ubanta, kaico na!”. Hamzah kyale ni yayi, na yi har na gaji ba tare da ya sake ni ba, ba kuma tare da ya nuna yana jin zafin dukan dana ke masa ba, ba tare da ya raba ni da kirjin sa ba, sai da na bari don gajiyar kaina, kasancewar karfin mu ba daya bane. Harshen sa na ji yana sauka a saman kunci na, yana dauke hawayen fuskata, yana side kuncin bakidayan sa affectionately. Kafin ya soma magana cikin tsananin damuwa. “Kin sani Siyam, ajiye damuwa a zuci baya maganin ta, baya kawo maslaha a cikin zamantakewar aure, ‘we must be open and straight forward to each other’ in muna son kwanciyar hankali a rayuwar auren mu. Don Allah Siyam in laifi nayi miki kiyi hakuri ki gaya min, I’m tired of your silent punishment!”. Ya dora hannu na a kan kirjin sa, daidai saitin da zuciyar sa take harbawa, ya ce “ki ji yadda ta ke bugawa da wannan gashin kumar naki. Da azabtuwar fitar hawayen ki. Ni ban damu ba, ba kuma zan damu ba don mun shekara bamu hada shimfida ba, domin ba abinda ya assasa auren mu kenan ba. Soyayya ce ta hakika ta fisabilillah Allah ya sanya a tsakanin mu, wadda itace jagorar komai, na damu ne sabida na san bazan yafewa kaina ba idan na bata miki bisa sani na, na damu ne don na san na yi miki laifin da kika kasa tara ta gaba da gaba ki fada min. Ki ka zabi ki hukuntani ta hanyar cirewa zuciyar ki soyayyata wadda ba ke kika sanyata ba, Allah ne. I think ko menene ki gayamin yanzunnan zai fi, Tsakani na da ke babu ‘yar haka kin ji SIYAAM! Wallahi na horu, na kuma yi alkawarin dainawa ko menene”. Ya kara kankame ni. Jikin sa yana shaking. Ban san sanda na riko shi cikin hannaye na ba, sabida tsakanin Siyama da Hamzah sai Allah da ya halicce mu. Cikin kuka nace “Ni fa baka taba yi min laifi ba Hamzah, koda da kuskure in dai tsakani na da kai ne, kullum cikin kyautata min kake. Idan ma ka yi min, wanda na sani da wanda ban sani ba, na yafe maka shi duniya da lahira. A wasu lokutan mai kaunar ka da gaskiya yana tausaya maka azabar Allah, ya fi so ku tashi tare cikin inuwar al’arshin Ubangiji ranar hisabi. Idan makomar sa aljannah ce, ya fi so ya shige ta tare da wanda ya ke so dinnan, zai fi jin dadin zama a cikin ta har fiye da mazan aljannah ko su miliyan za’a bashi a madadin sa. Ta ina macen da ke son mijin ta tsakani da Allah zata kasance cikin dadin rai, alhalin tana hango mijin ta an yi makamashin wutar jahannama da shi?” “Yaa subhanallah!” inj i Hamzah, “Siyama me yayi zafi? Ki fidda ni duhun da kalaman ki ke dada sanya ni”. Na ce “kukan kurciya ne nake maka, kuma na san kana da hankali da tsinkaye (foresight) wanda ya sha bamban dana mutane da yawa, in har hankalin ka har yau bai hango SAKACIN da kake yi da addini ba, to babu amfanin in yi asarar yawun baki na wajen tunasar da kai. Saidai wani hanzari ba gudu ba Hamzah, na rantse da Allah da ya halicce ni ya halicci soyayyar dake zuciyata a kan ka, na fi son addinin musulunci da tsayar da dokokin Ubangiji a kan son da nake maka, don na san soyayyar bazata amfane ni a lahira ta ba, musamman in ya kasance bana tare da kai a gidan aljannah. Na batawa Abba a kan ka, kamar yadda ka goranta min, amma zan yi dukkan kokari na in ga ban kaucewa addini na da Ubangiji na saboda kai ba”. Da fadin haka na janye jiki na daga nasa, na mike na koma toilet din, alwallah na dauro na zo na sanya kayan sallata na shimfida darduma na tada sallah, na bar shi a cikin wani hali na kaka-nika yi da mutuwar jiki. “Sakaci da addini!”. Hamzah ya tuno kalaman Siyama, meye sakaci da addini? Ya shiga neman ma’anar kalmar ‘sakaci’ a cikin kan sa…. from different languages da ya iya. Kafin kakkaifar kwakwalwar sa ta halarto masa da ma’anar Kalmar SAKACI nan take. Sakaci a turance dai yana nufin ‘negligence’. Kenan Siyama tana nufn tana fushi da shi ne sabida yana Sakaci da addinin musuluncin sa na yanzu, ya tambayi kan sa yaushe rabon sa da sallah cikakka sau biyar a rana? Wace rana ce bai sha giya ba tunda ya aure ta? Sai daidaiku. Ya san kuma bazata kasa ganewa ba. Yana gani ita har azumin tadawwu’i take yi duk Litinin da Alhamis bai taba sha’awar gwadawa ba saboda ya san ba zai iya ba. Sai ya soma lissafin tuno daga ranar da yayi missing salloli, tun yana kara’in su duka at a time in ya dawo aiki har kara’in ma ya gaji ya watsar. Ya ga cewa renakun da yayi missing salloli suna da yawa bazasu lissafu ba, ya mike a kasalance ya shiga toilet dina ya hau alwalah, yana cewa da kan sa “Astaghfirullah”. Saida kafafun mu duka suka dauka, ni nafilfili nake shi kuma Hamzah wai ramuwar salloli yake yi cike da nadama, abin zar takaici, na gama na kwanta na bar shi akan darduma yana ta fama. Can kuma tausayi ya kama ni kamar ma yana yi yana barci ne. Ban san yaushe ya kwanta ba domin tuni barci yayi awon gaba dani, bayan na gama sake-saken yadda za’a yi Hamzah ya rike sallah a rai na. Abin mamaki yau shi ya tashe ni da asubah muka yi jam’I, raina ya dan yi haske, ina addu’ar Allah yasa ya dore. Dadi na da Hamzah akwai tsinkaye da saurin fahimtar abu, da kuma rashin girman kan yin repenting. Mun koma mun dan kwanta zuwa gari ya dan yi haske, mu samu mu yi wanka mu fita, ni ya sauke ni a school domin ina da presentation na wani assignment karfe goma na safe shi kuma ya wuce office din su. Sai ji nayi ya mirgino ni na dawo saman sa. “Siyam!”, Hamzah ya fada da taushin murya, “idan nace na tuba na bi Allah zaki yafe min? Wallahi ban san me yasa ba mantawa nake ban yi sallah ba, kin san abinda baka tashi cikin sa ba rana daya ka yi ‘adopting’ din sa. Sai a hankali……”. “Sai a hankali….. kullum zancen ka kenan Hamzah, “sai a hankali, gradually”, umh. Shin yaushe wannan a hankalin naka zata zo maka? Shin itama mutuwa sai a hankali take zuwa? Wannan fa tsakanin ka da Ubangijin ka ne ba da ni Siyama ba, duty na ne kawai in tunasar da kai a matsayi na na matar ka kuma masoyiya ta hakika, amma gaskiyar magana itace idan ka cigaba da SAKACI da addini watarana shi kan sa son da nake yi maka Hamzah na rantse neman sa zan yi in rasa…”. Yayi maza ya toshe min baki da tafukan sa. “Kada Allah ya nuna min wannan ranar!”, Ya cigaba da cewa, “kafin sannan har tabon sujjadah zai fito a goshi na, in Allah ya yarda”. Sai ya maida akalar hirar zuwa irin wadda yafi so a yi, a kowanne lokaci a kowanne yanayi Hamzah romantic ne, ni kuma don in kara jan sa a jiki, kamar yadda Anti Nasara ta shawartar, zuciya ta kuma ta haqurqurtar, sai wannnan karon ban bashi mishkila ba. Na barshi ya mori asubahin kamar ba gobe, kamar mu rike hudowar rana kada garin ya waye ya tafi nemo mana abinci, muka nishadantu, muka farantu, muka kuma gamsu da cewa, soyayyar da muke yi wa junan mu, wata ajiya ce daga Allah! Samun sabani ba ya taba ta, zukatan namu a sarke suke cikin na juna. Na yarda da