Sashe 30
Sakacin Waye Part 3 Complete Hausa Novel · about 11 min read
THE MOURNING
Iyakar gigicewa da shiga tashin hankali irin wanda Da zai shiga, a lokacin da ya rasa iyayen sa Hamzah ya shige su a dalilin mutuwar Kakar sa, Grandma Veronica.
“I’m now alone on earth, my child and my grandma are gone, is only you I have SIYAMAH”.
Su ne kalaman da Hamzah ke yawan fada tun bayan rasa Kakar sa da babyn sa.
Hakika na tausaya masa halin dimuwar da ya shiga na rashin Kakar sa wadda ta rage masa tal a duniya, fadin halin da Hamzah yake ciki a washegari bata baki ne, and I feel for him too, tunda kuwa zukatan mu sarke suke da na juna. Ya ce min babbar damuwar sa da Kaka ta mutu ba tare da ta musulunta ba.
An rike gawar Kaka a asibitin zuwa Hamzah ya gama shirin tahowa gida Najeriya domin a binne ta a Jos. Duk da yace baya so ‘yan kabilar su su binne ta, nace masa kuma bazai yiwu a yadda yake tunani ba, wato musulmai su binne ta a makabartar musulmai. Dole akan haka ya hakura ya fara shirin tahowa Najeriya tare da gawar ta.
Ya kuma ki yarda ya tafi da ni burial din Kaka, a cewar sa ‘yan kabilar su mutane ne masu rikicin addini da kabilanci na gaske. Masu tsananin kiyayya ga addinin musulunci da musulmai ‘yan arewa. Ba zasu karbe ni ba, har dai in suka ji sanadin bugawar zuciyar Kaka, cewa bakin cikin musuluntar sa ne kuma a dalili na.
Ana I gobe zai tashi Najeriya da gawar Kaka Aunty Nasara da Young Abba suka zo masa gaisuwa/ta’aziyya. Gani na a kwance ko tashi da kyar nake yi sabida nima ba wai na gama samun lafiyar jiki na bane, jego nake yi da jinya sosai, ga mutuwar kakan ta bugeni ga mara ta ta tsananta min da ciwo irin na bayan haihuwa. Aunty ta roki Hamzah izinin tafiya da ni gidan ta zuwa dawowar sa. Sai yace ta bari sai na raka shi airport a washegari ya tashi sai in taho gidan ta.
“Ai da kyar zata iya raka ka airport din, kalleta tayi sutu-sutu a kwance fa”.
Hamzah ya dukar da kai kasa, kafin ya dago yace “kiyi hakuri Aunty, bazan iya kwana a gidan babu Siyama ba. Ita kadai nake da yanzu. Bani da kowa bani da magaji”.
Aunty Nasara ta ce “kana da Allah. Kuma kana da mu Hamzah, mu iyayen ka ne, sannan Allah zai musanya maka da wasu yaran masu albarka”.
Dole suka koma gida suka bar mu tare. A daren na yi kuskuren gayawa Aunty maganar genotype dina dana Hamzah. Ba don komai ba sai don na ga ya kamata ta sani. Cewa Hamzah Mawonmase AS ne, nima kuma Siyama AS ce. Wanda ke nufin duka ‘ya’yan da zamu haifa wasu zasu zama ‘sicklers’ wasu ‘normal’ wasu kuma will become ‘carriers’.
Aunty Nasara ta shiga tashin hankali, ta shiga salati tana fadin “laifin Baban Ahyan ne, kamar ba dan zamani ba, ai yanzu an daina irin wannan kuskuren, sabida shi ya fi kowa gaggawa a duniya, bai ko yi tunanin a yi awon jini kafin auren ku ba, kamar a kan sa kike zaune. Shi dai kawai ya yi miki aure da wanda kika zaba. Ko ta bakin mahaifin ki ya ki saurarawa ya ji sai ka ce shi ya haifa masa ke”.
Ta nisa, kafin ta ce “Allah ya kawo mafita ta alkhairi, Ameen, amma dole zan gaya masa don ya dauki darasi a gaba”.
Hamzah bai san mun yi wannan maganar da Aunty ba. Yana dakin sa a lokacin yana hada kayan tafiya Najeriya a washegari Young Abba ya kira shi a waya.
Ban san me suka tattauna ba, na ga Hamzah ya shigo min at a smart pace (afujajan) yana min wani irin kallo kwayar idanun sa na juyawa kamar ba nasa ba.
Bakidaya ya birkice min. Wani ‘hidden side’ din shi da ban taba sani bane ya bayyana a gare ni yau, na rashin tawakkali da karbar kaddara da maida allura garma. Na fahimci wannan dabi’a ce ta masu shan barasa. Yana neman rasa hankalin sa, sakamakon wayar da Young Abba ya yi masa.
Yace min kai tsaye ba tare da sakayawa ba “Siyam, giya nake son sha, in ba haka ba zan zautu.
A matukar firgice na dago na dube shi. Ba tare da ya nuna damuwa da firgicin nawa ba ya cigaba da maganar sa “Yau na tabbata ni maraya ne tun kafin in binne Uwata-Kaka ta, kuma Grandma ita kadai ce jini na a duniya, ita kadai ce za ta kaunace ni da dukkan nakasu na, iyayen ki naki ne ke kadai.
Karya suke da suka ce zasu zame min iyaye, karya suke da suka ce zasu tsaya min a matsayin iyaye!”.
Girgiza kai na shiga yi da sauri hadi da zaro idanuwa ina kallon sa cikin tsoro, firgici da kaduwa, kallon da na gani cikin idanun sa ya tabbatar min yana nufin kalaman sa, na cewa in bai sha giya ba a halin yanzu zai zautu, na dauka mun dade da baiwa maganar giya baya, na dauka Hamzah ya bar komai da ya danganci sabon Allah da wasa da addini daga ranar da yayi min alkawarin canzawa, ya ce ya tuba ya bi Allah, kuma ya canza din tun daga lokacin, ni kuma na kuma karbi tuban sa da dukkan zuciya ta?
I will no more accept his “zan bari, amma a hankali, na gaji da jin kalmar “zan bari amma “(gradually)”, na gaji da wannnan statement din na rashin hankali.
Ba wannan ya fi tayar min da hankali ba kamar maganar da ya yi yanzu a kan iyaye na (Young Abba). A cewar sa ya tabbata maraya gaba da baya yanzu, in bai sha giya ta tafi da damuwar sa ba, kwakwalwar sa will crack, zuciyar sa zata buga, ya fadi yanzun nan shima ya bi bayan Kakar sa.
“Duk me ya jawo?”
Ban san lokacin da na tambaye shi ba, cikin rawar murya da tashin hankali, curiousity na neman fasa mun kai.
“She did everything good to me a duniya, everything to build my future for good, amma sakamakon ta shine na saka mata da betrayal, na canza addini na, data rai ne ni da shi, na guji kabila ta, na yi aure duka babu yardar ta, sabida son dana samu kaina ina miki farat daya, da son cika mafarkan ki su zamo gaskiya, da son cika nawa burin na auren macen dana ke so kadai, ba wadanda suke so na ba har suke willing su bar nasu addinin zuwa nawa.
Ni nawa na bari sabida naki, sabida ke nake so duk cikin matan duniya, wanda bakin cikin hakan dana aikata ya aika da ita barzahu, bayan duk duniya ita kadai ta san ciwo na”.
Saura kadan in yi fitsari a wando na sabida yadda kalaman Hamzah ke birkita ni. Ni na san dama akwai wata irin shakuwa mai tsanani tsakanin sa da Kaka, na san rashin ta will touch him in every way amma ban zaci wadannan kalaman na gushewar Imani da gushewar hankali daga bakin sa a daidai wannan lokacin ba.
Ina sane da cewa, duk da ya rasa iyayen sa tun yana karami Kaka ta sa Hamzah bai san kalmar maraici tana existing a duniya ba, saboda ta maye masa gurbin iyaye dana kakanni gabadaya, a cewar sa yau gatan sa ya fadi! Tunda ya rasa Grandma din sa, ba tare da ta yafe masa laifukan da take tuhumar sa da aikata mata ba, ya fara ganin hakkin ta a kan sa.
Gashi ni din dana yi masa sanadin rasa ta; Baba na, wato (Young Abba) ya ce masa lallai mu tsaida haihuwa, don kada mu yi ta haifar ‘ya’ya sikila ko carriers, harda bashi misali da abokin sa mai arziki ne sosai, amma yanzu sabida hidimar sikilolin yaran sa hudu bashi da komai yanzu, shi Young Abba ba zai yarda Siyam ta haifi sikila again ba, kada ta kawo musu ‘sickle cell’ a family din Ummati, don amana ce ita ta mahaifin ta a hannun sa.
In ya so zai taimaka mana muyi adopting yaro ko yarinya daga orphanage ko cikin dangi na na wajen uwa daga kauyen Gashaka.
Hamzah ya share zufa daga goshin sa, ya dube ni da budaddun idanuwa ya ce “Me Baban ki (Young Abba) yake nufi da wannan maganar? Da har zai kira ni officially ya gaya min hakan? Ba tare da ya yi la’akari da halin rashi uwa/kaka ta da na yi ba, zai kara min da wannan bakar maganar ta son kai da rashin kauna? Banda in disguise yana nufin yace yana son raba auren mu kawai?
Me yasa ma kika gayawa Abban sirrin ‘genotype’ din mu, wanda daga ni sai ke sai Ubangiji sai likitan mu muka san wannan maganar?”
Maganganu dai rututu irin na wanda ke cikin bacin rai, har ta kai shi ga yake neman rasa imanin sa da hankalin sa, ya kuma manta dukkan tarin kaunar Young Abba a gare shi. Yau daya don ya bata masa rai ya juyar da dukkan alkhairin sa, ya kalli maganar sa a baibai, ta wata fuska daban, da wata manufa daban, don haka na kasa kare manufar Young Abba da nawa laifin da yake tuhuma ta na fadawa Nasara, ita kuma farfesa ta fesawa mijin ta.
Karo na biyu dana ga Hamzah ya zauna a gefe yana kuka riris. Bayan kukan komawar dan sa. Sai jiki na ya dau rawa. Na kama kafafun sa cikin tashin hankali na ce,
“kayi hakuri Hamzah, ni fa ban fada masa ba da Aunty kawai na yi maganar nan, ka san dai ba abinda zan iya boye mata da ya shafe ni balle magana mai muhimmanci irin wannan, mai yiwuwa ita ta fada masa, shi dama Young Abba dan boko-akida ne fa, kai ne baka sani ba, kullum tunanin sa na yahudawa ne, ni ko zan yi ta haifar ‘ya’yan suna mutuwa washegari, na yarda duk shekara in dau sabon ciki in haifa maka ‘ya’ya su zame mana na amfanin can, babu wani adopting da zamu yi, namu zamu yi ta haifa mu rike.
Yana daga cikin shika-shikan Imani yarda da kaddara Hamzah, mai dadi ce ko mara dadi, barasa bata maganin maraici ko damuwa ko bacin rai, kuma bazata sa Kaka da Baby su dawo duniya ba, haka bazata canza kalar jinin dake cikin jikin mu ba, idan ka sha ta gurbata imanin ka kawai zaka kara yi yanzu. Musamman a wannana lokacin da shaidan ke son taka muhimmiyar rawa a zuciyar ka. Yana ta kada maka ganga kana hawa a kan manufar Young Abba.
Ka tuna kaunar Young Abba gare ka bana tunanin kiyayya tasa ya fadi haka yana dai guje mana wahala ne a nasa akidan da nasa tunanin. Ba kuma raba mu yake nufin yi ba.
Ka tuna alkawarin da ka yi min Habeeby-Shaheedy, da kuma wanda ka yi wa Young Abba na cewa bazaka kara sha ba kafin ya yarda ya baka aure na”.
Murya ta ta karye, nima kukan ya kece mini da karfin sa, na ce “na gama yi maka uzuri a kan shan giya da wasa da sallah daga yau wallahi”.
Hamzah ya gyada kai. Sai cewa yayi “zaki fadi haka mana tunda ke kina da iyayen da suka san ciwon ki, har suke guje miki haihuwa da ni yau, wadanda basa so ki haifa musu jika sikila, sabida ke suke so ba ni ba, kuma zasu iya raba mu su aura miki wani mijin ki samu ‘ya’ya masu lafiya musamman dan uwan ki OMAR wanda na lura har gobe hankalin ki bai bar kan sa ba, balle yanzu da ya kasance ni jini na na haihuwar marassa lafiya ne.
Kuma ai na dade da sanin cewa don shi (Omar) kike son komawa Nigeria, to har abada ke da kasar Najeriya, daga kasar Amurka zamu lula mu shiga uwa duniya mu rayu tare, daga ni sai ke a inda babu kowa!
Ya zama bani da iyaye kema baki da su, in ya so mu yi ta haifar ‘ya’ya sikila kada mu tara komai din. Kada mu kai muku su cikin family. Tunda hakan kuke gudu. An gaya muku ni duniya da tara arzikin cikin ta yana gaba na ne ko ya fiye min ‘ya’ya na?
Ba zan ce na daina sallah ba, but ba zan taba barin giya ba. Ki karbi wannan assurance din ki saba da shi sai ki zauna lafiya. Life is not fair to me at all! Ki gaya min in ban sha giya ba me zan yi yanzu? A lokacin da kuka nuna bakwa bukatar hada jini da ni cikin family din ku, ki gaya min me zan yi in ji sanyi a zuciya da kwakwalwa ta???
Kakata babu, dan da na kallafawa rai ya zo min ko a sikilan ma, babu!.
Kuma dole ki zauna da ni din har abada a inda bamu da kowa, tunda kin janyo ni cikin kaddarar ki, kin girma kina rokon Allah ya hada kaddarar mu, Allah ya amshi dukkan rokon ki ya dabaibaye zuciya ta a kan ki, sai don kaddarar mu ta zo da lalura zaku yi min halin ku na hausawa na kabilanci da ‘yan ubanci, koda ‘ya’ya masu kanjamau zamu yi ta haifa ba masu SCD ba Siyama yanzu muka fara aure, kuma yanzu zamu fara haihuwar su. Wannan sako na ne ga Young Abba, da nake rokon ki isar da shi gare shi”.
Ya mike ya janye kafar sa dana rike daga hannaye na, ya dau mukullin motar sa da sassarfa ya fita, ya bar ni da budadde kuma sakakken baki. Ina cikin tantama da tababar anya HAMZAH na ne wannan???????????????????????????
MU KARASA A LITTAFI NA 4.
TARE SUKE. TAKU HAR ABADA;
SUMAYYAHA ABDULKADIR.
1st February, 2023.
07030137870
(whtsapp only)