← Book details Sakacin Waye Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 30

Sashe 28

Sakacin Waye Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ba ita ce mai hargagin nan ba, yanzun Magana take a nitse, yanayin yadda take maganar kamar wadda ake yi wa wahayi. “Me kike so da jika na?” Nayi shiru ban ce mata komai ba. Ban fita ba ban kuma dawo dakin ba. Kaka ta tako a hankali ta cimma ni, muka fuskanci juna gaba da gaba kamar masu shirin dambacewa ga mamaki na sai ta sassauta murya ta ce cikin muryar lallashi. “Ki fadi a nawa zaki fansar min da auren ki da shi. Ina da manyan gonakin dankali, duk zan sayar in mallaka miki kudin, ina da gidan kai na tankarere a Jos, shima zan baki, ke har shanu da akuyoyin da nake kiwo a gidan gona ta zasu zama mallakin ki a rubuce da shaidu, in dai har kin yarda kin amince zaki rabu da jika na (Mawonmase) ki bar masa gidan sa ki koma gaban iyayen ki.”. A wannan lokacin ne na dago ido a hankali na dube ta, idanuna fal hawaye na ce, “Kaka, ni din kuma sai aka yi rashin sa’a ba ‘yar mutsiyata bace, soyayyar gaskiya ce tasa na aure shi, har na rabu da nawa iyayen saboda shi. Ina son sa Kaka, son da harshe ba zai iya bayyanawa ba. Har ga rabo Allah ya bamu, ina zan je kuma da aure na da tsohon ciki? Ba zan iya fansar da aure na da shi da komai ba, da kin san tarihin soyayyata dashi da baki ce haka ba, ina fatan in mutu ne da igiyar auren sa a kai na. Ki bar ni in rayu da jikan ki cikin salama da kwanciyar hankali, ki bar mu mu ji da kaddarorin da ke jiran mu a gaba na ’ya’yan da zamu haifa babu koshin lafiya, kada ki zama mai tayar mana da hankali don already cikin tashin hankali muke, har abada na miki alkawarin ba zan taba cutar da jikan ki ba, tsakani na da shi soyayya ce ‘yar gaskiya da gaskiya da amanar juna”. A hankali Hamzah da ya sawo kai zai shigo dakin, jin shiru-shiru Siyama bata dawo ba, hakan ya sa ya biyo bayan ta, sai ya ja da baya a hankali, ya koma dakin sa. Bayan ya gama jin amsar Siyam ga Kaka. Bai taba jin kalaman da suka yi masa dadi daga Siyam suka faranta masa suka wanke zuciyar sa irin wadannan ba. Ya kara mata matsayi mai girma a zuciyar sa, domin ya ji dadin amsar data baiwa kaka. Kaka tace “amma kin san ba addinin ku daya da shi ba, don me zaki aure shi? Me yasa baki nemi dan naki addinin kin aura ba? Ko rasa miji kika yi cikin addinin naku? Salon ki sa watarana ya fita daga addinin sa mai albarka na iyaye da kakanni, ya shiga naki ko, sabida kin ga yana da rauni a halayya da dabi’a, kuma kin same shi yadda kike so ya riga ya mutu a son ki?” Na yi murmushi, cikin harshen hausan dana san bata ji na ce “Kaka ai sai dai kada a kuma, sai dai wani Hamzan ba wannan ba”. Na fice na bar mata dakin tana kururuwar cewa “Jesus zai yi hisabi tsakani na da ke, muguwa -azzaluma!”. Maganar ta ta karshe tayi min ciwo, amma haka na shanye na koma daki, na same shi ya yi tagumi a gefen gadon sa, ina shiga yana mikewa ya riko ni. Sai kawai ya hau ni da mahaukacin kiss. Na soma kokarin zamewa ina fadin “Mawonmase sallah zanyi fa” yace “taimake ni Siyam, ki ara min bakin ki in tsotsa, jikin ki da lokacin ki ki bani su ko na minti biyar ne, in nuna miki godiya ta bisa amsar da kika baiwa Kaka, kada zuciyata ta fashe da soyayyar da ke gudana a cikin ta”. Sai na kyale shi domin ya samu nutsuwa ko yaya ne, don na lura yana cikin damuwa ba ‘yar kadan ba a kan rigimar Kaka. Sai da ya sabbaba min wanka sannan. Yana zaune bakin gadon sa ina kan stool ina shafa mai na na din-din-din wato lotion din Dr. Teal’s. Hamzah yace “Siyam, amsar da kika baiwa Kaka, da ta ce ki fansar mata da aure na. I must confess, I’m highly impressed, na gode”. Kamar in ce masa nima na gode da soyayyar dana samu yanzunnan, zan iya cewa tafi ta kowacce rana cika min zuciya, tana cikin jerin ranakun mu da ba zan manta ba, wasu abubuwan da yawa baka san ka yi su ba, wasu kalaman daka fada min baka san ka fade su ba amma yau na ji su. Na tabbatar da matsayi na a zuciyar Hamzah na. Mawonmase, wannan ce addu’a ta. “Allah sa mu raka rayuwar bakidaya tare!”. Amma a fili murmushi kawai na yi. Ya tada sallah, nima na tayar, don tare muka yi alwallah yau, yana kuskure a alwalar ina gyara masa, a haka muka yi. Bayan mun kammala alwala na ce shi zai mana Limanci. Ya yi gardama “amma dai kin san ban iya limanci ba ko?” Nace “koya zaka yi, daga yau sunann ka Imamuddeeni, komai da koyo akan iya”. Dole ya yarda ya tada sallah na bi shi a baya. Muna cikin sallah, can muka ji tamkar an bude kofar dakin kasancewar muna cikin sujjadah sai bamu waiwaya ba, sai can an jima kadan cikin sujjada ta naji saukar abu a gadon baya na kamar tabarya kamar kujera sai da na kai kasa a kan ciki na. Stool din mudubi Grandma ta dauka ta kantara min a gadon baya na. Na baje na yi flat a kasa sabida azabar dukan wanda ya sa na saki ‘yar kara, babu bata lokaci kuma jini ya balle min na soma sakin nishi cikin azaba. Ba shiri Hamzah ya sallame sallahr sa ya juya ya yi ido biyu da Kakar sa dake tsaye tana huci kamar macijiya, Hamzah ya ce. “Kaka!” Cikin karaji. Yayo kaina ya dago ni jikin sa bakidaya, yana fadin “na shiga uku, ta kashe min Siyamah!?” Duk da azabar da nake ji a mara ta da gadon baya na da jini da ya soma naso a kasa sakamakon katakon da Grandma ta rafka min ban kasa hango rigimar da Kaka da shi kan sa Hamzah zasu iya shiga idan ya kai ni asibiti ba, don haka na daure ina cije baki don naga ya rude sosai ya gigice ya rasa takamaimai abinda ya kamata ya aikata. A wannan hali kuma idan ya kai ni asibiti a kasar nan ‘yan sanda ne zasu shiga maganar su bi diddigin komai wanda hakan zai iya daure Kaka. Nace “a’ah, ban mutu ba Shaheed. Kyale ni ka ji da ita, look, zata fadi kasa… she’s in severe anger, komai na iya faruwa da ita, kuma ka ga tana da hawan jini kada ta fadi ya zama paralysis”. Ai kuwa kamar na fada da bakin mala’iku sai gani muka yi rikija! Grandma ta fadi kasa tana shure-shure tana sambatu. Hamzah ya rasa inda zai sa kan sa, ya rasa wa zai ceta tsakanin nida ita, a karshe ya sake ni don na ce ya ji da ita zan iya kula da kai na, ya ciccibeta duk nauyin ta yayi motar sa da ita. Kafin ya kai Kaka mota ya dawo don nima ya dauke ni kan yaro kyakkyawa ya danno, babu wani ciwo mai yawa na haife yaro bakwaini cikin mintunan da basu gaza goma ba. (So Grandma induced labour). Dan da na haifa ko kuka bai yi ba har yanzu da Hamzah ya dawo dakin, ni kuma na yada jiki a gefe ina maida numfashi sai ga Hamzah ya shigo da nufin nima ya dauke ni ya sa a mota ya yi asibiti da mu. Gani na da Da, da mahaifa da mabiya duka a gefe ya kusa haukata shi. Ihu ya saka yace “haihuwa kika yi Siyam? Na shiga uku ni Hamzah, Kaka zata kai ni prison a kasar nan, yanzu yaya zan yi da ku?” Daga kwancen da nake na ce masa “cibin zaka yanke” Hamzah jiki na rawa ya ce “Siyam ta yaya? Babyn ma fa ba ya motsi fa” janyo wayar sa da ke yashe kusa da hannu na nayi na mika masa nace “kira min Aunty kawai, jaririn nan ina jin ya koma”. Maimakon ya kira Antin sai ya ga ba zai iya barin dan sa haka a kasa cikin cibiya ba. Hannun sa da jikin sa duka suna rawa ya sa zani na ya rufe jaririn, sannan ya dauke shi da cibin da komai idanun sa na fidda ruwan hawaye yana tambaya ta. “Ban gane hausar ki ta jaririn ya koma ba? Ina ya koma?”. At the same time, hannun sa daya na danna waya yana kiran Anti. Ni da na haihu haihuwar fuju’a na fi shi karfin zuciya, ni na bashi shawarar ya kira ambulance a tafi da Kaka maimakon ya yi tukin mota a halin da yake kuma ya kira min likita ta. Dana ga ya kasa kiran wayar ma ni na karba na kira asibitin mu, na yiwa likitar da ke duba ni bayani cewa tazo gida na haihu ba zato, dan kuma bai yi kuka ba har yanzu, kuma muna da tsohuwa mara lafiya ta taho da hospital van. Ko mintuna ashirin ba’a rufa ba motar asibitin ‘Mayo Clinic’ ta iso gidan mu, likitoci biyu da ma’aikatan jinya biyu suka shiga baiwa Kaka taimakon gaggawa ni kuma tawa likitar ta shige bincike a kaina da abinda ya janyo wannnan haihuwa haka ta gaggawa bayan lafiya kalau awon data yi min kwanaki biyu da suka wuce ya nuna, har ta gyara min kwanciyar jaririn, ta kuma tabbatar mana da`EDD, ga dan ta fahimci ya koma, ga jinin da ya balle min ya ki tsayawa. Duk irin kwakwar su na son jin gaskiyar abinda ya faru na ki yarda in saka sunan Kaka. Daga bisani cewa na yi zamewa na yi na fadi a toilet shine dalili. Hamzah yana gefe rungume da gawar dan sa ya kalle ni cikin tausayi jin amsar dana bayar, sai ya kama kuka riris, kamar ba namiji ba. Ga yaron sa baki kamar sa, mai kama da shi sak, kyakkyawa, ga suma a kansa yala-yala sannan hatta
Chapter 28 · 0% Book details