Sashe 22
Sakacin Waye Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yau Litinin, aka ce babbar rana da ko bature yana tsoron ki, na shiga kitchen ina tunanin me zan girka masa kafin ya dawo daga ofis? Bayan na yanke shawarar sanyaya zuciya ta in maida komai ba komai ba. Kusan duka abincin kabilar Birom na iya shi yanzu, wasu na koya a yanar gizo, wasu a wurin shi kan sa Hamzan, domin sau da dama Apron yake sakawa a lokutan mu na dadi a yawancin weekends din da yake gida mu shiga kitchen tare yayi ta koya min ire-iren girke-girken su. Ya iya wasu a wajen Kakar sa tun yana karami, amma kafin yayi aure baya yi sabida rashin lokaci da rashin zaman gida, sai dai ya je restaurant ya zauna ya ci ko ya taho da shi gida idan ya baro office. A haka ya rayu a can baya. Na yanke shawarar yi masa faten Acca, tunda lallashin sa nake son yi. Kafin ya dawo, na yi faten Acca wanda na wadata shi da ganyen alayyahu da yakuwa sosai, na zuba koda da hanta a ciki wadanda na yanka kanana-kanana. Sannan na yi masa lamurjen Zobo da Abarba da zuma, na sanya kananun kankara a ciki. Hamzah bai shigo gidan ba sai wajen karfe shidda na yamma, haka kawai yau bai biya ‘Bar’ ba yace bari ya bari zuwa dare yanzu yunwa yake ji sosai, wani abu mai kyau cikin tarbiyyar Siyamah ko tana fushi ba ta horon yunwa ga mijin ta, kullum sai ta dafa masa abinci ta aje a dining, bata damuwa da ya ci ko bai ci ba gobe ma sai ta sake yi ta aje. Ya jinjinawa matan Hausawa a kan girki ga mazajen su wadda a ganin sa al’ada ce mai matukar kyau. A nashi al’adar maza sun fi mata yin girki. Lokacin da ya shigo gidan, ina daki na ina wanka a toilet dina, kasancewar da nasa mukullin yake amfani sai ya bude gidan ya shigo, a matukar gajiye ya dawo, rataye da falmaran din Suit din sa a wuyan sa, hannun sa rike da jakar kwamfutar bisa cinya, anan falo ya zauna yana tunanin abubuwan da suka faru daren jiya, zai iya tuna wasu bazai iya tuna wasu ba, kamar dai ya zagi Siyamah cikin maye, Ya Allah! Hamzah ya kama kansa da hannuwa bibbiyu yana jiran ganin ta inda Siyam za ta bullo, don ya kasa shiga dakin ta sabida nadama. Duk kamshin abincin ta ya cika falon ya cika hancin sa, ya kai duban sa ga dining table nan ya ga na shirya abinci da komai da zai bukata, amma bana wajen. Kuma bai ji motsi na daga daki ba. A wannan dan tsakanin da suke ciki, bakidaya ya rasa abinda ke damun Siyama, gabadaya ta canza masa rana daya, ta aro wasu munanan halaye farat daya ta canza kyawawan halayen ta da su, ya rasa walwalar ta da annurin ta, ya rasa farin cikin ta, ya rasa soyayyar ta kullum sai dacin rai da bakin rai, amma an ce masu shigar juna biyu na samun irin wannan mood swings din. Ko Siyam na bashi hakkin sa na aure ko ta daina bayarwa sabida ya bata mata rai bisa rashin sani ko bisa sanin sa she will forever remain a DARLING a gare shi kuma sanyin zuciyar sa (his Sweetheart). Shi ya san Siyam na da shigar ciki, wanda watakila ita bata sani ba, ya kyale ta da maganar fara zuwa antenatal ne don ta sha ce masa baza ta yarda ta haihu yanzu ba sai ta kammala karatu. Sai kace ita ke baiwa kanta haihuwar a sanda taga dama ko a sanda take so. A kullum yana mata uzurin da yake yi mata bisa dole na cewa pregnancy mood swings shine dalilin canzawar ta da (harsh behaviours) a kan sa, shi yasa ya fita sabgarta ya kyaleta ya daina lallashin nata ma don ya lura in ya matsa da son jin laifin sa ma kara tunzurata yake yi. Ba don ba zai iya seducing din ta ya kwata a sanda yake so ba, sai don baya son duk abinda zai taba lafiyar wannan Babyn dake jikin Siyama wanda tun bai zo duniya ba ya saka masa suna ADAM (Junior). In mace ce kuma Little NASARA. Domin wadannan mutanen guda biyu ko ko ya ce ma’auratan/surukan nasa, sun masa karamci, halacci da gatan da bashi da abinda zai saka musu, tunda suka bashi auren Aisha-Siyam, ba don ya cancanta ba, sai don darajja soyayya da sanin muhimmancin ta ga rayuwar dan adam, da kuma son su da addinin Musuluncin su ya samu kari, sannan kuma shi da Siyam su samu kwanciyar hankali su cika burikan zukatan su, su girbi wahalar soyayyar dake zuciyar su. Dining din ya hau ya zauna ya zuba gwaten accan a plate ya soma ci sosai, kunnen sa har wani irin motsi yake yi, a cikin ran sa ya ce akwai ‘karama’ wato ‘miracle’ a cikin hannun girkin matar sa Siyama, ko me ta tsaya ta sarrafa sai ka ji kamar kunnen ka zai fita don aroma da dadin dandadano. Ba karamar yunwa ya kwaso daga VOA ba, don yau ko ruwan tea bai tsaya ya sha ba ya fice tana barci akan sallayar data yi sallahr asubahi. Don haka ya yi wa abincinnan kyakkyawan ci. Sai da ya koshi ya kora da zobon Siyam mai tsananin gardi da sanyi. Ta dade bata yi masa irin wannan girkin na nutsuwa da gamsarwa ba. Daga ji ya san yau ta tsaya ta baiwa girkin attention din ta da lokacin ta yadda ta ke yi masa a baya, ba kamar a ‘yan kwanakin nan data canza musu tsarin rayuwa ba. Hatta dandanon abincin ta ya canza. Ta canza masa fuska ta kuma canza masa launin abinci. Ji ya yi ba abinda yake so yau irin su shirya, ko ba zasu yi komai na auratayya ba ta daina yi masa wannan kwanciyar ta kai da kafa da filallika a tsakiya, wadanda sai yau ya ga ba karamin izgili da raini bane ga miji kamar sa, kuma yayi mamakin kan sa da ya kyaleta tana masa hakan kwana da kwanaki bai taba ce mata komai ba. Shi ya san idan akwai abinda yafi mijin-tace to shi Hamzah ne. A kan Siyam ba shi da katabus. Yana da sanyin hali a kanta, shiyasa Siyama ta same shi yadda take so take murza zaren ta son ran ta, ba shi da saurin fushi ko kankani a kan kowa ma ba a kan Siyam kadai ba, amma in ya yi fushin, kafin a samu ya sauka za’a ci wuya, don an ce dama mai hakuri bai iya fushi ba. Kuma zai furzar da abinda ke zuciyar sa don ya huce ko zai maka dadi ko bazai yi maka ba, kamar yadda ya tabbatar ya yi wa Siyama a daren jiya cikin maye. Ba zai taba yin mummunan fushi da Siyamah ba, kome zata yi masa zai dube shi ne da fuskar kauna da soyayya, idan ya tuna sacrifices din ta a kan sa. Har gobe ya san ba zai samu mai son sa da kaunar sa a duniya kamar Siyama ba. ‘Her own love is different, is unique and is made in the heaven’. Har guba ta sha akan dai ta auri wani nata ba shi ‘dream husband’ dinta ba. Ta saba wa iyayen ta musamman mahaifin da ya haife ta duk a kan sa. In ya tuna wadannan alfarmomin da sadaukarwar data yi a kan sa, sai ya dauko uzurin da yafi kowanne girma a duniya yayi mata. Ya roki Ubangiji ya yafe mata hakkin sa data ke dauka na aure ba tare da ita kanta ta san yana nema mata gafarar ba. Yana shirin mikewa don zuwa dakin Siyam din, domin ya lallashi ‘yan kayan sa yau, yana kissima kalar lallashin da zai yi mata wanda zai sa ta sauko, kwakwalwar sa ke son tuno masa zagi da gorin da ya yi mata daren jiya cikin hali na intoxication, hankalin sa ya kara tashi, ya shiga damuwa ainun, ya soma tunanin irin kalamai da launin soyayyar aikacen da zai yi amfani da su wajen bata hakuri, ko ya samu ta yi hakuri ta daina yi masa kwanciyar nan ta kai da kafa, wannan abu na ci masa rai, yana bakanta masa, shi ko bata bashi damarmakin data bashi a baya ba, ya samu kalaman bakin ta masu nuna laifin da ya yi mata, wanda bai san ko na menene ba har yau, sai kawai wayar Kaka Veronica ta shigo masa a daidai lokacin da yake kokarin tafiya dakin Siyama. Saida ya ji gaban sa ya tsinke ya fadi, domin yau sati biyu kenan suna artabu shi da ita a waya, ta ce gidan sa zata dawo da zama, bazata yarda (Muslim girl) ta raba ta da shi ba, ita bata taba sanin akwai kauna ko soyayya tsakanin Musulmi da dan kabilar Berom ba, kuma ta ga alama Moslem girl din ta dauko hanyar hakan (hanyar raba sun), tun da yaushe rabon da ya je gida Jos? Yaushe ya taba daukan tsahon wannan lokacin ba tare da yaje inda take ba kafin ya yi aure? Yayi aure da diyar musulmi, alhalin ta ce masa bata yarda ba, bazata taba yarda ba ko bayan ran ta, yayi kunnen uwar shegu da ita da gargadin ta ya yi kan gaban kan sa, har kwanciya tayi a asibiti hawan jinin ta ya tashi sakamakon hakan amma bai je ba, sai uban kudi da ya rika turawa likitan da ke duba ta yana kuma communicating da shi ta waya a kan lafiyar tata. Da ya tabbatar ta warke an sallame ta ta koma gida, sai ya fasa zuwan da yayi niyya don a lokacin yana kan ganiyar cin amarcin sa. Again aka zo aka yi ‘Nzem Berom Festival’ na wannan shekarar, Kaka ta kira shi ta gaya masa ta kuma jaddada masa muhimmancin halartar ‘Nzem Berom’ a gare shi amma still bai je ba. Kai shi fa yanzu ba ya son duk abinda zai janyo masa cudanya da kiristocin nan, don wani wari-wari karni-karni suke masa, kallon su yake wasu dabbobi haka, marasa alkibla kuma masu najasa da rashin tsaftar jiki da ta zuciya. Hatta Kakar