← Book details Sakacin Waye Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 30

Sashe 29

Sakacin Waye Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

farcen sa na kafa dana hannu duk irin nasa ne kamar ya yi khaki. Yaro chocolate colour irin wanda nake burin haifa tare da Hamzah dare da rana. Ni dai in haifi yara masu mixed colour da zan gan su kamar ruwa biyu shine buri na a baya, yau gashi Allah ya bani, amma ko fuskata bai gani ba. Nima na shiga kukan ba kakkautawa. A lokacin Aunty Nasara ta iso, ita kadai ta iya karbar gawar yaron nan daga hannun sa ta kaiwa Young Abba da suke tare wanda ke ta sintiri a falo bayan an yanke cibin jaririn. Shi ya wuce dashi zuwa inda za’a yi masa suttura, musulmi su binne shi Aunty Nasara da Doctor Rita, suka taimakamin na tashi daga kasa zuwa toilet suka gyara ni suka yi min wanka, likitar tace zata wuce dani asibiti don su duba lafiyata sosai. Tuni dama sun wuce da Kaka. An karbi Kaka a emergency, abinki da kasar da aka san muhimmancin lafiyar dan adam, tuni suka shiga bata taimakon gaggawa, ba’a fito da ita ba sai bayan awa daya, ta farfado amma ta ki yin ko motsi, ta ki yin magana. Da ta rufe ido hoton Mawonmase take hangowa suna sallah shi da matar sa, abinda ke neman farka mata zuciya da gusar da hankalin ta, bayan ta farfado aka kaita dakin hutu, sannan ne Hamzah ya samu ganin ta. A lokacin na samu karfin jiki na. Amma duk da haka likita ta rike ni nima a asibitin, tace sai nan da kwanaki uku zata sallame ni idan na samu lafiyar jiki na sosai, ta kuma tabbatar da koshin lafiya ta. Tuni Young Abba ya sa an binne yaron. Amma wani ikon Allah ko Anti ban gayawa Kaka ce sanadin haihuwar bakwaini babu rai dana yi ba, don na san maganar sai ta zama babba, ga Kakar itama tana can rai a hannun Allah. Likita yace ta gamu da cardiac problem (matsalar zuciya) bayan hawan jinin ta. Muna tsaye gaban gadon ta ni da Hamzah a washegarin ranar, tana hawaye amma ta kasa cewa komai don bata son ko bude ido ta ganni a gaban ta, na saka a raina ba Kaka ce ta kashe min Da ba, Allah ya yi na amfanin can ne, ta doke ni sabida bakin cikin ganin jikan ta yana sallah ba da niyyar inducing mini labour ba, sai don ta huce haushin ta na musuluntar mata da jika da na yi. In ta tuno Mawonmasen ta ne yake jan sallah matar sa na bayan sa, which means shima ya musuluta har ya iya limanci, ba kamar yadda ta ke zaton matar ce kadai musulma ba, zuciyar ta yi take kamar zata buga. Ta tuno mafarkin da ta sha yi a kan sa, cewa ya canza addinin sa na iyaye da kakanni (christianity) zuwa na Annabi Muhammad PBUH ashe dai gaskiya ta gani a cikin barcin ta? Ta bude ido da kyar tana duban sa don ni ko son gani na bata yi, muryar ta bata fita sosai tace. “Mawonmase me yasa ka kawo ni asibiti? Me yasa baka bar ni zuciyata ta buga da bakin cikin ka na mutu na huta ba? Idan na rayu menene amfanin sauran rayuwata tunda ka bar mu? Mace ta janye ka......”. Ta saka kuka wiwi tana cewa “I regret coming.... Had I known abinda zan gani kenan a kasar nan da ban zo ba!”. Hamzah yace cikin sarewa, don shi bai saba da irin wannan masifar ba, daga zuwan ta zuwa yanzu kuwa ya tabbata da za’a auna jinin sa shima za’a ga cewa ya hau har fiye da nata. Don dai ya kasance namiji ne kawai Yace. “Kaka, kina so in fadi nima ko? Duk mu taru mu mace kamar yadda kika yi sanadin mutuwar Da na na farko a duniya? Ina jin Siyam ta gaya miki juna biyu gare ta, amma baki yi la’akari da hakan ba kika nemi kashe ta, wanda sakamakon hakan ni kikayi ma asarar yaron da na kallafawa rai. Dan da shi kadai nake da shi a matsayin jinina a duniya bayan ke. Ni karamin yaro ne da zaki zaba min addini Kaka? Ko kuwa kabari daya za’a saka mu in mun mutu? Cewa nake soyayyar da ke tsakani na da ke iyakacin ta gidan duniya? A lahira duk ba zamu amfanawa juna da komai ba, wannan ina ce ko a ‘bible’ kin san shi cewa lahira gaskiya ce? So ki bar ni in yi addinin dana zaba, cikin nutsuwa please Kaka, kema ina miki addu’a Allah yasa kina da rabo, bazan taba son ni ina aljannah ke kina wuta ba, don babu addinin da ya kai musulunci dadi da kwanciyar hankali, ki zauna lafiya damu, bazan taba gajiya da zaman ki ba, na yi alkawarin kulawa da lafiyar ki. Don Allah Kaka in har kina so na, to kada ki kara magana akan addini, kada ki kara kai hannu jikin matata, kin jawo mana asarar da bazamu mayar ba, amma Siyam ta rufa miki asiri yau da ta fadi kece sanadin accident dinnan you will surely go to jail, ki nemi gafarar ta, kuma kada ki kara daga hankalin ki a kan addini na. Kowa ya yi wanda ya zaba, babu mai ingiza wani zuwa nasa addinin tsakanin ni da ke, ina so ki san cewa Siyam bata saka ni shiga Islam ba, ni nasa kai na, don na dade ina sha’awa, kin sani kuma tun lokacin muna yara ni da aboki na Hamzah Mustapha, kuma canjin addini na ba zai shafe ki ko ya rage ki da komai ba”. A wannan gabar, Kaka Veronica ta gama sarewa da al’amarin jikan nata, ta yarda Mawonmase data sani a baya ba shine yanzu ba, wannan ya gama yin nisa, daga kalaman sa zaka yarda ba abinda zata yi da zai dawo da shi addinin Christianity, ta soma wata irin jijjiga kamar mai farfadiya tana fadin “zai shafe ni mana, daga ni har zuri’a ta duka, tunda kuwa ‘ya’yan ka ma shi zaku sa su yi?! Ba zasu bi Jesus ba.” Kaka ta fada tana share hawaye da bayan hannun ta jikin ta yana rawa da wata irin kyarma. “Shikenan na rasa ka, duk wahalar da na sha a kan ka yau ka zabi kyakkyawar mace da addinin ta akai na da addinin da ya haife ka. I will not disown you, Mawonmase, sabida bani da kowa sai kai, amma a yau ba sai gobe ba kayi min booking in koma Jos. Ni Veronica bazan taba kwana a gidan da ba’a bautawa Jesus ba. Bana son lafiyar da zaka nema min din, bana so mutuwa nake so! Gara mutuwa ta da rayuwa ta ina ganin ka cikin bata da tabewa.” Hamzah ya dafa hannayen ta dake ta makyarkyata, yace “ni kuma lafiyar ki matters a lot to me Grandma, baki ga ta mutuwa yanzu ba sai kin goya ‘ya’ya na musulmai a gadon bayan ki”. Kaka tace “over my dead body! Zan goya mata ‘ya’ya, kai ni ko kusa da kai na daina zuwa. Idan baka mayar dani gida a gobe ba sai na yi fiffike na tashi zuwa kasata a kan iska.” Hamzah yayi dariya ya ce “sati biyun nan da kika yi alkawarin yi sai kin yi su a U.S, lafiya sai kin same ta in sha Allah, ko da tsiya ko da arziki sai kin rayu, sai kin goya mana ‘ya’ya Grandma”. Ta dube ni da idanu a warwaje tace “na bar ki da Yesu, ya saka min cutar da kika yi min”. Na yi mata murmushi na kama hannun ta nace “Kaka kema zaki shigo cikin addinin gaskiya da iznin Allah nan bada jimawa ba” ta yi maza ta fizge hannun ta tace “idan ke mayya ce, to kurwa ta kur. Ruhi na ba irin na Mawonmase bane sabida ni na rike Jesus, na rike addini na fiye da komai, shi kuwa tuntuni dama gafalalle ne ba ya kula da addinin sa na Yesu”. Hamzah na dariyar tsokana ya kama hannun ta yace “har na hango sunan da zamu saka miki “Nana Khadija”. Kaka ta fashe da kuka da kururuwa tana cewa da karfi. “Da na sani da ban zo gidan ka ba, Mawonmase ka riga ka halaka!”. Haka muka kwana a kanta suna tafka rigima ita da jikan ta. Ko nawa gadon jinyar ban koma ba, kwanciya nayi a daya gadon dakin na juya musu baya ina jin su ina hawayen rashin da na gudan jini na. Wannan haihuwa da komawar dan, sun kara sa min nadama a kan Abba, sun sa na kara sanin darajar sa, sun dugunzumar da zuciya ta bakidaya ga son komawa gare shi. Duk fadan nan nata da tashin hankali da munanan kalaman data ke jefa masa, shi Hamzah kokari ya ke shi ya maida shi wasa irin na jika da kaka. Kamar da wasa, cikin dare ina toilet ina fitsari a falon asibitin, bayan an saka mata karin ruwa sakamakon ta ki yarda ta ci komai, ta kuma daina magana ma bakidaya. A lokacin Hamzan yana wajen likitan ta suna tattaunawa a kan lafiyar ta, ya gama da likitan cikin tashin hankali ya dawo dakin domin likita ya tabbatar masa zuciyar Kaka ta tabu (ciwon zuciya) ya kama ta, wannan ya girgiza Hamzah ya shigo dakin da zummar lallashin ta da kwantar mata da hankali. Sai ya ga kumfa tana fita daga bakinta idanunta a warwaje harshen ta ya fito waje. Lokacin na bude kofar toilet nima na fito. Kallo daya muka yi mata ni da shi muka fahimci babu ita, ma’ana zuciyar ta ta buga; ta rasu. Saboda bakin cikin Hamzah ya musulunta.
Chapter 29 · 0% Book details