Sashe 6
Sakacin Waye Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
GIDAN HAMZAH MAWONMASE M atukar kyau da tsaruwa to gidan Hamzah Mawonmase ne. Mukulli yasa ya bude falon, da bisimillah na saka kafafu na cikin gidan, a zuciya ta kuma addu’ar duk da ta zo baki na nake karantawa, shi yake yi min jagora ban san ina nake saka kafafu na ba kasancewar nabi na rufe fuska cikin katon mayafi na. Ban san ya aka yi aka iso dakin ba naji dai ya kawo ni bakin gado ya zaunar dani kan wata lallausar water mattress. Sannan ya durkusa a gaba na ya yi unveiling lullubin dake kai na. A lokacin ne muka hada ido, ni da Hamzah, kafin na maida idanu na kasa a hankali cikin jin matsananciyar kunya, ban iya na yi masa kallo na biyu ba, sakamakon abinda na hango cikin idanun sa masu kama da zagayayyen dan itacen almond mai girma da nauyi ne da ya shallake karfin idanu na, almond shaped eyes din sa wadanda ke walainiya kamar cikin maiko-maiko, hawaye-hawaye dauke suke da manya-manyan sakonni. Kamar ya fahimci gudun haduwar kwayan idanun mu nake yi sai yace “Siyam, dube ni cikin ido mana. Ki gaya min how you felt this day, ko kuwa kin daina so na ne kike wannan koke-koken da suka wuce kima wadanda sun soma sike ni. Ko kuwa soyayyar ta rikide zuwa tsana ta wucin gadi daga lokacin da aka daura mana aure?” Ban yi mamakin yadda yayi saurin karantar halin da zuciya ta ke ciki a kan sa yanzu ba, in aka yi la’akari da cewa shi din kwararren dan jarida ne na jiya ba na yau ba. A hankali na cira kai na dube shi da jikakkun idanu na, na fahimci baya son nuna cewa kuka na weakens him, amma da gaske kukan nawa ya raunata shi to an extent, ya rage masa dokin da yake ciki, idanun sa sun nuna hakan, wato sun nuna karayar sa a zahiri; kukan nawa yana neman sagar masa da gwuiwa ya rage masa kuzari da doki. Gane hakan da na yi sai na shiga share hawaye na da dukkan tafukana da sauri da sauri ina nufin na daina kukan. Tafukan hannayen sa masu taushi ya saka a cikin nawa, ya hade su cikin nasa, ya dunkule su wuri guda ya matse su sosai, yayi crossing fingers din sa cikin nawa cikin samun relief na samun shawo kaina na daina kuka. Kafin ya mike ya kuma mikar da ni tsaye, sannan sannu a hankali cikin nutsuwa irin tasa ya shiga sauke lullubin kai na har ya sauke shi kasa baki daya, mayafin ya fadi saman kafafu na a kan ‘marbles’, bakin kwantaccen gashin da bai taba gani ba, bai kuma san inada shi ba na fulben Mambilla shi ya fara bayyana gare shi, kyallin sa ya haske idanun sa, santsin sa ya wadaci idon sa, wanda ko da wasa bai taba sanin haka yake wajen tsayi, sulbi da baki ba. Da wata irin azama Hamzah ya cusa fuskar sa cikin gashin nawa, ya saka hannayen sa ya tallafo wuya na ya shige cikin jiki na da azama da rawar jikin da ya wuce kima, tamkar yaron da ya sha kuka har ya shide, kafin a karshe ya samu jikin mahaifiyar sa da ya dade yana nema, ilahirin jikin sa kyarma yake yi, sannan da hanzari yake sanya ni cikin jikin sa tamkar yana tsoron wani abu zai zo ya kwace masa Siyam din, ya kanainaye ni bakidaya ya shige cikin jiki na ta ko’ina, yana mai cigaba da cusa fuskar sa da sassalkan sajen sa mai taushi ta kasan wuya na, gashin kaina ya rufe fuskar sa bakidaya har baka hango fuskar Mr. Hamzah, taushi da santsin sajen gefen fuskar shi ya sauka a masangalin wuya na, wanda ke ta tashin kamshin man gyaran gashi na musamman da mazan zamani ke amfani da shi wato (Arganavita), wanda hakan yayi sanadin tada tsigogin jiki na baki dayan su. Duk inda hannun sa ya sauka a fatar jiki na sai naji tabin nan har cikin bargo na. Ji nake tamkar Hamzah na ja na da lantarki, kafin a yi haka na ji saukar tausasan labban Hamzah a dogon wuya na, ya soma wani irin soft kiss, a yangace (in a gentle manner) cikin madaukakiyar iyawa, inda duk ya sumbata sai na ji dirin saukar sumbar a jiki na tun daga kwakwalwata har zuwa yatsar kafata, daga baya ya koma yi a urunce, wani irin hadamammen kiss, mai nuna tsahon wahalar jiran da ya dade yana yi wa zuwan wannan ranar. Daga sannan ya koma yin kiss mai wahala, wata irin wahalalliyar “sumba” Hamzah Mawonmase yake sauke min a wuya na wadda zaka fahimci ‘motive’ din ta na tasowa ne tun daga karkashin zuciyar sa a kan kowacce kusurwa ta fuska ta zuwa kasan masangalin dogon wuya na, wata launin sumba ce mai bada sauti Hamzah Mawonmase yake min, mai tsayi kuma mai zurfi, (hungrily, deeper and hot) mai tsayawa a zuciyar mace, musamman idan ta fito daga bakin mijin da take tsananin so ne, ta kasa manta tasirinta da sauki. A kasan wuya na kadai Hamzah ke sha’anin sa, tamkar ba zai daina ba. Ya shiga nan da fuskar sa da bakin sa, ya fita can ya koma can. Ya rasa inda zai tsoma emotions din sa domin sun fi karfin control din sa. Dogon wuyan Siyam da ya dade yana bashi sha’awar ya sumbata ya ji irin taushi da sulbin sa kullum daga nesa-nesa in ya dube ta ta juya, shi ya samu yau, don haka yake neman cinyewa ta ko’ina, ya rasa inda zai sa kansa, ko inda zai sa Siyaman, yana yi yana tsarkake mahaliccin ta a fili da zuciyar sa, domin hakika ya kyautata halittar ta kwarai da gaske fiye da yadda ya ke gani daga nesa. Daga wuyan nawa ya rika moving upward zuwa sama a hankali har ya dangana da baki na. A nan ne naga abin mamaki daga dan mutanen Birom. Koko in ce daga “Berom Man” din da babu kamar sa a duniya ta da ta mafarkai na. Wato wani launin soft mouth to mouth kiss, da Hamzah ke yi a cikin baki na, tamkar zai raba ni da halshe na bakidaya daga irin tsotson kaunar da yake yi masa passionately. Gabadaya ya gigice ya fita a hayyacin sa cikin dan lokaci kalilan, irin gigicewar da ban san maza na yi a kan matan su ba. Mazarin da jikin sa ke yi, da irin kakkarfan rikon da yayi mun kadai, sun tabbatar min yau mai kwata na a hannun Mr. Hamzah sai Allah da ya halicce shi ya kuma halatta masa Siyama…… Amma na kasa taya shi da komai. Ba don bana enjoying madaukakin romancing da yake yi mun ba (wanda na sha ganin kwatankwacin irin ta cikin mafarkai na) sai don wannan ne karo na farko da irin haka ta faru da ni a zahiri, tsakanina da Da namiji, so as a first timer tsoron da ke cikin al’amarin yafi jin dadin da e cikin sa yawa. Ni na san na so Hamzah Mawonmase mafificin SO, na so komai nasa, na yi burin kasancewar mu miji da mata a darare da dama da yawan su ba zai lissafu ba, kuma na sha yin mafarkai barkatai kwatankwacin irin wadannan masu kama da ido biyu, amma na yau special ne, wato (na musamman ne) yayi matukar bambanta dana cikin mafarkai na, kasancewar na yau a zahiri yake gudana, wato zallar reality ne mai sarrafa kan sa da kan sa….yake kuma tafiya (hand in hand) da karfin soyayyar da ke zuciyar Hamzah… Na ji ni tamkar ina shawagi a kan gajimare, Hamzah ya dauke ni ya kai ni wata duniya ta daban ba wannan tamun wadda muke ciki ba, duniya ta extreme ecstasy. Wani irin scene ne ya shiga gudana wanda har abada ba zai gushe daga zuciya ta ba. Ya sumbace ni a fuska, a wuya, a ido, ya kuma bada muhimmanci sosai ga sumbatar baki na yadda ran sa yake so, hatta karan hanci na bai tsira ba yau daga warm and romantic passionate kiss din Hamzah. Kafin a yi haka naji tausasan hannayen sa suna ratsawa cikin rigar jiki na, har yayi nasarar zuge dogon zip din riga ta baki daya ta baya, kafin nayi wani hobbasa ko yunkuri na taimakon kai, ta hanyar riko wuyan rigar da yake son kaiwa kasa, ko bashi hakurin kada ya sauke min ita sakamakon wuta a kunne take, ina jin kunya ina jin nauyin sa… Ina kuma so in gaya masa ban shirya wannan abin kunyar ba tukunna (zama naked a gaban sa), sai kawai naji saukar doguwar riga ta baki dayanta a kasa….Sabida dama nauyin duwarwatsun jikin ta ya rinjaye ta. A wannan lokacin Hamzah ya gama gigicewa gabadaya, nima kuma ya gigitani fiye da kintace, ban san haka lamarin yake ba ko kadan, ashe dai da mafarki nake yi! Mafarki kuma baka taba hada shi da zahiri, kalaman da yake furtawa sun fi karfin biro na ya rubuta su, sun yi nauyi a cikin kunnuwa da kwakwalwa ta, na tabbata a lokacin ko suna na “Aisha-Siyama” ban sani ba, ko in ce na manta, sabida dadin duniyar soyayyar da Hamzah ya dauke ni ya luluka da ni, bana iya ambaton komai sai sunan sa “HAMZAH…..!” Kamar ni na rada masa sunan. Haka babu komai a rai na da zuciya ta har abada sai “HAMZAH….!”. Bana ganin kowa a gaba na sai shi kadai “HAMZAH”. Son da nake masa ko in ce muke yi wa juna wata kaddara ce rubutacciya daga Allah. Shi kuma kamar ya san hakan, kamar ya san bidirin dake gudana a cikin rai na, na kan yi mamakin yadda Mr. Hamzah ke ‘reading mind’ dina a lokutta da yawa, sai na ji yace, “you know what? Even without calling me at this moment, with the sweetest name I like most (HAMZAH) kin same ni kin gama in dai ni Hamzah ne. Let me confess the truth Siyam, na amince domin ke Ubangiji ya halicce ni, don ke aka qadarta min na zo VOA, don ke nake sha’awar addinin musulunci tun kafin in san ki, don haka you are my ‘soulmate’, na mallaka miki zuciya